Showing 108001 words to 111000 words out of 303099 words
kai yace "Ni ban ma gansa ba tun jiyan, sai daxu da muka hadu masallaci, gaskiya Inna na daga min hankali da yawa ban san yanda xan yi ba" Aunty tace "Toh Allah dai ya kyauta" Yusuf ne yyi sallama bakin kofa Aunty ta amsa ya shigo parlon ya mika mata wayarta yace "You missed a call" Abba na kallonsa yace "M.A fa?" Yusuf yace "Yana bedroom dinsa" Abba yace "Kira min shi ku taho tare" Yusuf ya amsa da to sannan ya nufi kofa, hanya ya ba Umma ta shigo parlon sannan ya fita, Daga Aunty har Abba suka dinga kallonta, duk gaba daya a sanyaye take tace "Alhaji xan je gidan Mariya wai suma ta dinga yi jiya basu yi bacci ba, yanxu haka suna asibiti tun asuba wai" Aunty tace "Subhanallahi, Toh Allah ya bata lafiya ya yaye ma duk musulmi ciwo, in sha Allah xan shigo anjima nima" da sauri Umma tace "A'a Hajiyar mu tace mu taho da ita zaria kawai, yanxu Ina xuwa Zaria xa mu wuce da ita" Abba yace "Toh Allah ya bata lafiya, ya sa kaffara ne" tana goge hawayen da ya cika idonta tace "Ameen" Abba yace "Da driver xa ku tafi kenan?" Umma tace "A'a adaidaita xan hau xuwa asibitin daga can sai mu tafi a motar mijinta" Abba yace "Toh Allah ya kiyaye hanya, do you need anything?" Tace "Ehh a min transfer din abinda ya sauwaka" Abba yace "Alright" sallama tayi masu ta fita parlon Aunty na mata Allah kiyaye hanya, bayan ta rufe kofa Aunty ta duba call din da tayi miss taga Ammi ce ta kirata, dialing number din tayi yana fara ring Ammi ta daga suka gaisa, Ammi tace "Dama tambaya xanyi ko driver na nan Hajiya..." Aunty tace "Ehh toh bai dawo daga kai su Maimoon islamiyya ba..." Ammi tace "Toh dama Imaan ce bata ji dadi ba xa mu je asibiti" Aunty tace "Subhanallahi tun yaushe?" Ammi tace "Yau dai da ciwon nata ta tashi" Aunty tace "Toh bari in ma Yusuf magana ko shi sai ya kai ku asibitin" daga haka ta katse wayar, Abba yace "Mamana ce ba lafiya?" Aunty tace "Wllh kuwa, Wai ciwonta ne ya tashi" Abba ya d'an yi shiru sannan yace "Bari Mujaheed ya shigo mu ji ko xa a kaita asibiti ne ko a bata medication a gida" dai dai nan Mujaheed ya shigo tare da Yusuf, Abba ya mike yace "Mu je ka duba Mamana wai bata ji dadi ba" Mujaheed ya d'an yi jim, sannan ya bi bayan Abba suka fita parlon, Aunty na kallon Yusuf tace "Kai baxa ka je dubata ba" Yace "Xan je anjima mum" Har bedroom din Imaan Abba da Mujaheed suka shiga Ammi dai ta tsaya daga bakin kofar, bacci take suka sameta, Mujaheed ya duka kusa da ita a hankali yana kallonta ya kai hannu forehead dinta, bude ido tayi ganinsa ta ja duvet ta rufe kafarta da sauri. Abba ya karasa kusa da gadon yace "Sannu mamana, ya jikin?" Da kyar tace "Da sauki Abba" Mujaheed na kallonta yace "Where are you feeling pains?" Ba tare da ta kallesa ba ta nuna masa kafafuwanta da baya, yace "Kin sha magani ne?" Kai ta gyada masa, Yace "Ina drugs din" ledan maganin dake ajiye ta nuna masa ya dauka ya duba su sannan ya ajiye yana kallon Abba yace "Let me get some injections da drugs" Abba yace "Ohk" daga haka ya nufi kofa Ammi ta basa hanya ya fita. Abba na kallon imaan yace "Allah ya sauwake imaan" ta d'an yi murmushi a hankali tace "Ameen" Abba ya juya ya nufi kofa yana kallon Ammi yace "Allah ya bata lafiya" Ammi tace "Ameen thumma Ameen" yace "Amma kada a gaya ma Inna" Ammi tace "In sha Allah" kofa ya nufa yace "Xan fita office, I will call later" Ammi tace "Allah ya kai mu, Allah kuma ya tsare" yace "Ameen" sannan ya fita parlon. Ammi ta karasa cikin dakin tana kallon imaan tace "In kara hada maki shayin ne?" Da sauri ta girgixa kai, Ammi ta dinga kallonta sannan ta juya xata fita, murya can kasa tace "Ammi don Allah ki shafa min maganin a kafa kafin Yaya ya dawo ni bana son ya shafa min"
*Imaan isn't free....* it's 300 Via Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then you show ur evidence of payment via 07087865788 to be included in the payment group....
36......
Mujaheed na dawowa ya tadda Ammi xaune parlor, Ammi ta amsa sallamansa yace "Ta ci abinci ai" Ammi tace "Ta sha shayi daxu" yace "Tana ciki har ynxu?" mikewa Ammi tayi tace "Ehh tana ciki" bedroom din Imaan ta nufa, ya bi ta da kallo sannan ya bi bayanta, Ammi ta cire duvet din jikinta xuwa kafanta tace "Imaan" tashi xaune imaan tayi ganin Mujaheed ta daure fuska ta ja duvet din xuwa waist dinta, a hankali tace "Ammi na ma fara jin sauki" Ammi ta kallesa tace "Magunguna ka siyo mata?" Mujaheed ya girgixa kai yace "A'a injections ne, sai na shafa..." Ammi tace "Ta sha drugs a bar injections din anjima" kallonta yake sannan yace "Amma na yanxu ne alluran..." Imaan tace "Toh na ji sauki ai yaya" Bai kuma cewa komai ba sai kallonta da yyi ta gefen ido babu yabo bbu fallasa, Ammi tace "Ina lotion din tube din?" Mika mata ledan yayi ta amsa ta cire man xafi dake ciki, Mujaheed ya kara kallon Imaan da ta ki kallonsa, Juyawa yayi ya nufi kofa kamar baxai ce komai ba bayan ya bude kofar yace "Sai anjima" ba tare da Ammi ta juya ba tace "Allah ya kai mu" da kanta ta shiga shafa mata man xafin a kafafuwanta da bayanta, Tana yarfe hannu tace "Toh Ammi alluran fa, ni dai bana son Yaya ya min, Kuma har yanxu Ina jin joint pain din" Ammi tace "Anjima Dr Habib xai xo..." Ammi na gama shafa mata ta fita dakin imaan ta koma ta kwanta ta lumshe ido. Da yamma Imaan na xaune parlor pepper soup din naman ragon da Aunty ta kawo mata na gabanta ta kasa ci don gaba daya bata da appetite, har wani rama tayi kamar warce tayi sati ba lafiya, xuwa lkcn dai ta ji sauki sai rashin kwarin jiki don Dr Habib ya xo ya mata injections din da Mujaheed ya siyo daxu, Ammi ce ta fito parlon ta iso kusa da ita tace "Idan baxa ki ci ba ki kai kitchen ki rufe Imaan, ai ba dole bane" Imaan bata ce komai ba ta amshi wayar da Ammi ke mika mata, Sadeeq ne ke kira a wayar, ta kalli Ammi da ta juya xata koma daki sannan ta daga wayar ta kai kunne hade da masa sallama murya can kasa, daga daya bangaren ya amsa yace "Are you okay?" Ta gyada masa kai tace "Sure Ina yini?" Yace "No, you sound sick ki gaya min baki da lafiya ne?" Cikin sanyin murya tace "Ae na ji sauki" Yace "Subhanallah, me ya sameki?" Ta girgixa kai tace "Kawai xaxxabi amma naji sauki sosai" ya d'an yi shiru sannan yace "Toh Allah ya kara lafiya, anjima xan xo in sha Allah" tace "Toh Allah ya kai mu" yace "Ameen, I will call you idan na iso" tace "Toh" katse wayar tayi ta ajiye tana shan pepper soup din naman a hankali, Bude kofar parlorn aka yi Inna ta shigo ta tsaya tana kallonta tace "Ikon Allah, yanxu don kaddara ta fada ma wayar ki sai ki kwanta ciwo imaan?? anya kuwa xa ki yi tawakalli irin nawa? Kinsan irin asaran da nayi a rayuwar nan kuwa tun tasowata har ixuwa yanxu? To 6arin ciki hudu nayi a gidan mijina, na haifi 'yan biyu suka mutu rana daya, dakina ya ta6a konewa kurmus bbu abinda aka fitar da sai mafici, kishiyata ta ta6a turo min yan fashi suka kwace min jakata a titi Allah ya so bbu komai ciki sai naira daya, 'ya yana uku kacal a duniya, da ubanki, sai na Mujaheed sai kanwarsu Hadiza dake kasashen turai, to ban gode ma Allah ba? Me ya sameni, ke don kawai an dauke wayar da bai fi dubu hamsin ba idan ma ya kai sai ki sa ma kanki damuwa kiyi ta ciwo kamar wayar jaraba, in dai waya ce ni baxan bari ki sani a bakin duniya ba xan ba Ahmadu dubu goma ya cika ya siyo maki wata ba ruwana" Imaan dai bata ko kalleta ba balle ta tanka ta, Ammi ta fito ta gaida Inna, Inna ta amsa tace "Aisha yanxu baki nuna ma yarinyar nan karatun tawakali??" Ammi tace "Ciwonta ne fa ya tashi Inna" Inna tayi shiru tana kallonta, can tace "Dama imaan na da wani ciwo ne da ban sani ba?" Ammi tace "Ciwon nata kuma Inna kika manta?" Inna ta rike ha6a baki Bude tana kallon Ammi, can tace "Ni dai ba ruwana, ku je kuna fadan haka wani ya ji, dama banda rashin lafiya da kowa ke yi Imaan na da wani ciwo na daban ne ban sani ba?" Ammi tace "Toh ko jiya ma Abbanta yace wannan yaron da ke nemanta ya kamata a sanar masa laluranta tun yanxu" Gwalo ido Inna tayi ta saki salati tana tafe hannu ta xauna ta rike kai tace "Naga abinda ya isheni ni patuuu, wayyoo Allah duniya ta lalace" dagowa tayi tana kallon Ammi tace "Aisha da hankalin ku ke da Bukar kuwa? Dama Imaan na da wani ciwo ne ni da ban sani ba, ku dai ku dinga fadin gaskiya ku ji tsoron Allah, yaushe rabon da in ji Imaan bata da lafiya a gidan nan, Ni dai kada wanda ya laka ma jikata ciwo lafiyarta lau, waye baya xaxxabin maleria da thypho, to kada ma ku kuskura wani yaji wannan mugun xancen, ku dai ba kwa fadan alkhairi a gidan nan, Ni dai ba ruwana, yaushe rabon da tayi ciwo?? Ai yafi shekara biyar ba ma banda sharri irin naku...." Mikewa Inna tayi ta nufi kofa rai bace tana cewa "Mutane dai ba tsoron Allah, meye kuma wai a gaya ma yaron da ke nemanta laluranta kamar mai cutar AIDS... Ni dai ba ruwana" a bude tabar masu kofar bayan ta fita ta kara gaba, Ammi na kallon Imaan tace "You make sure you tell him everything about ur health condition, kar ki boye masa komai" Imaan ta sauke idonta kasa a hankali tace "Toh Ammi" Ammi ta xauna kan kujera a ranta tana jinjina halin inna, imaan ta kalleta tace "Ya ce xai xo anjima" Ammi tace "Toh sai ki gaya masa" biyar da few minutes Sadeeq ya kira Imaan ta wayar Ammi ya sanar mata yana waje, bayan ta gaya ma Ammi, Ammi tace "Toh kar ki dade dai a waje" "Toh" kawai imaan tace ta sa hijab dinta ta fita, tana isowa gun motar ya bude mata back seat yana kallonta yace "Shiga ki xauna" girgixa kai tayi tace "A'a..." Yace "No pls ki shiga kinga you are sick, you look so weak, bana son musu get in plss" shiru tayi bata ce komai ba, komawa gefe yyi ta shiga motar a hankali, yana kallonta yace "Kun je clinic kuwa?" Tace "A'a Dr dina ya xo ya min allura" ido ya kafeta da shi, hakan yasa ta sunkuyar da kanta yace "What's wrong with you?" Ba tare da ta dago ba tace "I woke up with headache, backache and joint pain... pains everywhere...." Ya d'an bude ido da mamaki ya cire glasses din idonsa yace "Yana maki haka ne dama?" Ta kallesa ta gyada masa kai gently, kasa daina kallonta yayi, murya can kasa yace "Are you... A sickler?" Girgixa masa kai tayi tana murmushin karfin hali tace "I am a carrier, I am carrying the trait" jin yyi shiru ta daga kai ta kallesa, tausayi taga karara a kwayar idanuwansa yana kallonta, underneath his breath yace "Ya Salam, a very rare case, Subhanallah" murmushi kawai tayi bata ce komai ba, jingina yyi da motar ya rungume hannunsa yana kallon gate din shiga gidan looking so disturbed.
Umma ta share xufar da ke keto mata bayan ta gama sauraran bayanin mutumin gabanta, Hajiya Saude sai jinjina kai take, da kyar Umma na gyara xama tace "Toh malam yanxu meye abun yi.... A taimaka don Allah, wllh ji nake kamar xuciyata xata fashe, ko kuma in hadiye xuciyar, duk duniya bani da makiya da ya wuce yarinyar nan da uwarta, uwarta ta xalunce ni a rayuwa ta cuce ni, a dalilin uwarta na shiga gararin rayuwa malam ka taimakeni ko nawa ne ni xan biyaka wllh, Malam ka dubeni..." Mutumin dake xaune gabanta ya girgixa kai yace "Auren nan fa na gaya maki idan ba wani Ikon Allah ba sai an yi sa, mijinta ne d'an gidan attajirin babu tantama, sai dai kuma wani Ikon Allah, gashi nan na gani, gashi nagani har ranan bikin..." Hawaye ya kawo idon Umma tace "A dai duba malam a taimaka" Malam yace "Toh ga takarda sai ki rubuta abinda kike son ayi a ciki, amma fa banda kisa... don yarinyar na da tsawon rai haka ma Yaron sai dai kuma wani Ikon Allah, sannan kuma baxa a iya raba su ba.... yar ki kuma da kike son yaron ya fara nema kuma ba mijinta bane baxai taba yiwuwa ba, ba mijin yar ki bane yaron attajirin.... Sannan ina maki tuni surkarki a tsaye take kan yarinyar.... Tasirin aikinmu a kanta kamar ko da yaushe dai kalilan ne kema kin sani, Ki rubuta komai amma banda abubuwan da na lissafo maki a baya" Umma ta gyara xama tana share hawayen idonta ta amshi takardan da biro ta ajiye kasa ta fara rubutu.....
*imaan isn't free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then you show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
37.....
Da addare Imaan na kwance parlon Inna dake xuba wani garin magani a kindirmon dake cikin cup din gabanta, Maimoon ta shigo da sallama ta ajiye abincin hannunta ta gaida ta, Inna ta mika mata cup din tace "Mika ma waccan matar" Imaan ta juya masu baya da sauri tana turo baki, Inna ta kalli Maimoon tace "Kinga walakanci ko, wannan wace irin yarinya ce don Allah, ta san daga inda maganin nan ya fito?" Imaan tace "Ni nace maki na sha magani fa a gida, ya xa ayi in hada magani iri biyu" Inna ta ajiye spoon dina hannunta tayi tagumi tace "Oh waannan 'ya ta Bukar dai jarababbiya ce wllh, Toh meye da maganin da baxata sha ba? Ba daci, ba 6auri, ba hamami, ba galmi sai ma gyara mata bakin ta da xai yi, ta ji dadi kuma a jikinta, to ni dai ba ruwana gashi can uwar ki da ubanki sun fara laka maki ciwon da ba a san ki da shi ba ba a san kansa ba, wai dama idan lkcn gabatar da yaro ya kusa ba duk iccen da aka jika ma yaron aka basa sai ya amsa ya sha ba sbda a kauda ikon makiya, Ni dai ba ruwana Ina taimakon ki kina min wlknci, idan ta uwarki ce sai dai fa ki mutu ba abinda xata maki, shi kuma Bukar na can na neman na abinci a Habuja, to wa gare ki banda Allah sai ni din, to ni ba ruwana, ki tashi ki amshi maganin nan ki sha ni ba asararriya bace, uwata bata ce min jeki kya gani ba da xan dinga maki bauta baki gani, ko ubanki bai samu haka a guna ba" Maimoon ta ajiye cup din hannunta ganin imaan ta ki amsa tace "Inna ni dai xan je inci abinci" Inna tace "Toh idan kin gama ki dawo kema ga naku da su fitsararrun can Ummi, ba dai don halinsu ba, ya xanyi tunda ni na haifi Ahmadun" Maimoon dai bata ce komai ba xata fita sai ga Mujaheed ya shigo parlon, gaishesa Maimoon tayi ta fita, Inna tace "Mujaheed waya dai ko sama ko kasa, an dai rasa wanda ya sace, ni na ma fi xaton hauro kantangar aka yi, ai daga yanxu ni kaca ma xan dinga sawa in rufe kofar da kwado idan xan fita, Ina dalili? Ai ko ya daukan ma kansa fitinar duniya" Mujaheed ya gaisheta sannan yace "Za a xo daukan akwatunan nan" Inna ta kallesa sannan tace "Ita da ta turo ka ba sai ta xo ta kwasa ba in ga, Rukayya dai tayi hankali da ni ba ruwana.... Wannan yarinya kuma kayi mata magana ta rufa min asiri ta dau nonon nan ta sha ba sato kudin nake yi ba, dubu goma kenan cikin kofin a kwance ta rasulu ta sa aka amso min" Mujaheed bai ko kalli imaan ba yace "Kaya xa a karasa xubawa cikin akwatunan shi sa xa a dauka" Inna tace "Sai kuma ka yi ai, ko Ahmadu bai isa yace xa a dau akwatunan nan ba balle kai" Kallonta ya dinga yi fuska daure, can ya juya ya fita. Washegari da safe Mujaheed ya shigo parlon Abba da sallama ta dalilin kiransa da yayi a waya, Abba na kallonsa yace "Jikin Imaan ya matsanta mata, yanxu Hajiya Aisha ta kirani..." Mujaheed yace "Toh a tafi asibiti kawai" Abba yace "Toh xa ka kai ta ne?" Girgixa kai yyi yace "Zaria xan tafi Abba, kuma likitan ta na gari ai" kallonsa kawai Abba yayi bai ce komai ba, Mujaheed yace "Xan je in shirya yanxu" Abba yace "Ohk then" Juyawa yayi ya fita parlon. Sai kusan la'asar Ammi da Aunty suka dawo asibiti da Imaan, nan parlor Imaan ta kwanta Ammi ta shiga kitchen don girka mata light food ta ci, Imaan ta jawo wayar Ammi dake vibrate kusa da ita ta kalli screen din, Sadeeq ta ga ke kira, sai da ya kusa katsewa ta daga da kyar ta kai kunne tayi masa sallama, ya amsa yace "Kun dawo gida ne?" Tace "Um..." yace "Ohk before magrib xan kawo maki drug din, but I have to see wanda aka baki a asibiti" tace "Toh"