Showing 231001 words to 234000 words out of 303099 words

Chapter 78 - Imaan Book 1 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

1658

"Saboda ina son kasancewa tare da ita...." Umma ta fashe da kuka kamar yar yarinya tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, kana son kasancewa da ita fa kace Mujaheed? Ita Safeenar fa???" Abba dai ya kasa cewa komai sai kallonsa yake, Inna tace "Ehh lallai lalacewa ya tabbata a duniya, Innalillahi wa inna ilaihi raji'un..." Mujaheed yyi kasa da murya yace "Ku yi hakuri Abba ni baxan iya sakin Imaan ba..." Daga haka ya mike ya fice daga parlon, kawu Bala ya sauke ajiyar xuciya yana gyada kai yace "Allah sarki..." Inna ta mike ta fashe da kuka tace "Ahmadu duk kai ka ja mana wannan bala'in muna xaman xaman mu, kawai ka tashi sbda tsautsayi ya afka ma bawan Allah Sadeeq ka daura ma mahaukaci aure da jikata, wllh Mujaheed ya fara haukacewa banda haka ko kunya babu yace baxai saketa ba yana son kasancewa da ita, to tayi masa uban me idan sun kasance tare, ai ni naga abinda ya isheni bai ishi Allah ba, amma ba komai da kansa xai gaji ya saketa don wllh Imaan baxata tare gidansa ba, to ta tare tayi masa uban me?? Wllh ta kwaso kayanta gaba daya ta dawo bangarena ni ban yadda da auren ba, dama dai Sadeeq bai dawo bane sai in hakura ta tare gidan Mujaheed din, amma bawan Allah ya dawo kuma yace baxai iya sakinta ba...." Tana fadin haka ta daga imaan dake kuka kamar ranta xai fita suka bar parlon, Ammi ta share hawayen idonta ta mike ta fita parlon Aunty da duk jikinta yyi sanyi ta mike ta bi bayanta, Mama Hadiza ta sauke ajiyar xuciya tace "Toh Allah yasa barin auren shine mafi alkhairi" a hankali Daddy ya amsa da "Ameen" shi dai Abba ya kasa cewa komai, Umma da ta sakko kasa tana kuka sosai tace "Toh Alhaji ya xa ku yi da yaron da naji ance ya dawo???? An fa ce ba yin kansa bane, don Allah ku duba lamarin nan kada ku xama kananun mutane" Kawu Bala yace "Sae yayi hakuri, Imaan ta masa nisa, ita din matar aure ce yanxu" Umma ta mike tana kuka sosai ta fita waje da sauri ko xata ga Mujaheed amma babu shi babu alamarsa. Mama Hadiza ce ta kira Sadeeq ta sanar masa ya xo bayan ta amshi lambarsa gun Yusuf, suna xaune parlon Abba har lkcn sai ga shi, Kallonsa kawai Daddy yake don ba karamin ramewa yyi ba, duk ya fice hayyacin sa, a sanyaye ya xauna parlon ya gaishe su gaba daya, duk suka amsa suna kallonsa, cikin raunanin murya ya fara basu hakuri yace "I don't know what came over me Abba, wllh ba halina bane, don Allah ku yi hakuri ku yafe min, I am ready to marry Imaan now, Kar kuce xa ku raba ni da ita don Allah, wllh baxan iya rabuwa da ita ba...." Hawaye cike idonsa ya kare maganar, Kawu Bala yace "Sadeeq komai ya faru a rayuwa rubutattce ne daga Allah, Allah kuma ya kaddara Fatima ba matar ka bace, don yanxu haka maganar da nake maka Fatima matar aure ce...." Sadeeq ya daga kai a hankali yana kallonsa xuciyarsa na bugawa, double ya dinga ganin parlon daga nan kuma bai kara jin komai ba bai kara ganin komai ba a parlon.... Tun da Inna taji abinda ya faru da Sadeeq tayi kukanta mai isarta ta buga ma ta Rasulu waya taji ko xata xo ranan, ta Rasulu tace "Ai ki bari Asabe maganar babba ce, in sha Allahu gobe da sassafe xan shigo nima yanxu na dawo garin wllh" Inna na matsar kwalla tace "Toh sai kin xo, don ba lafiya ta Rasulu" daga haka ta kashe wayar ta ajiye tace "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un, Allah ka rufa ma Rukayya asiri ya kasance bata da hannu a abubuwan dake faruwa, idan ko ba haka ba sai dai wata ba ita ba a gidan nan...." Imaan dai na kwance kujera tayi lamo, tunda taji abinda ya faru da Sadeeq kuma wai suna asibiti take kuka, da ta tuna furucin Mujaheed sai taji gabanta yyi mugun faduwa jikinta yyi sanyi, Inna tace "Na fa ce ki kwantar da hankalin ki sai dai Mujaheed yyi ta yawo da auren ki a kansa amma har abada ke da tarewa shegen gidansa, to ki tare kiyi masa me a gidan, ko kuma yyi maki me Allah na tuba? Da kansa xai gaji ya kawo maki takardar ki ya bamu hakuri" ita dai Imaan bata ce komai ba tana jin xuciyarta ja mata xafi. Abba ne tsaye ward din da Sadeeq yake tare da Daddy sai Alhaji Bulasawa da wani frnd dinsa, Alhaji Bulasawa na tsaye kan Sadeeq sai kallonsa yake duk da bacci yake, kana ganin Alhaji kasan kasan damuwa ne sosai tare da shi, Can ya juya ya kalli Abba a karo na farko tun shigowarsu yace "Alhaji can you pls do something about this pls, I don't want anything to go wrong with my son, and yana da matsalar xuciya dama from the beginning, though it's not critical but the condition he is now can make it, don Allah ina bukatan taimakon ku ba wai don na isa ba, ku duba wannan lamarin" Da damuwa sosai yyi maganar, Abba dai kallonsa kawai yake ya kasa cewa komai, Daddy ya ja kujera ya xauna ya jinginar da kansa hade da lumshe ido, Abba ya sauke idonsa yace "In sha Allah xa a duba ka kwantar da hankalin ka Alhaji...." Alhaji Bulasawa yace "Toh na godiya" Mummy ce ta shigo ward din tare da Mum din Mariya, ganin Sadeeq ta fara kuka ta ki karasawa ciki, mum din Mariya ta karasa a sanyaye tana kallon Sadeeq din.... A haraban hospital din Abba ya kira layin Mujaheed to see if he can reach him, luckily kuwa ya shiga, Mujaheed na dagawa Abba yace "Muhd Ina son ganin ka a gida yanxu" Mujaheed ya d'an yi shiru sannan yace "Ina Zaria yanxu Abba, da Magrib xan shigo" Abba yace "Am expecting then" daga haka ya katse wayar ya xauna saman kujera yana kiran Allah a xuciyarsa, Mujaheed ya d'an yi murmushi ya ci gaba da abinda yake a office dinsa. Da daddare Imaan na parlor xaune ta sa pepper soup din da Aunty tayi mata a gaba amma ko spoon daya bata kai baki ba, Inna na bathroom dinta tana aikin wankewa tunda daxu da safe bata samu ta wanke ba, Bude kofar parlon aka yi Imaan ta daga kai da sauri Mujaheed ya shigo, tashi tayi kamar warce aka tsikara xata gudu yyi maxa ya rikota, ta fashe da kuka jikinta na rawa tace "Yaya don Allah ka bari bana so..." Ya juyo da ita yana kallonta, ganin yanda hawaye ke xuba idonta ya xaunar da ita ya xauna gefenta a hankali yace "Listen to me now Imaan..." Taki yarda ta kallesa har sannan jikinta rawa yake, murya can kasa yace "Kema kina son in sake ki koh?" Ta kallesa ta fashe da matsanancin kuka tana gyada masa kai, shiru yyi na kusan second goma, a hankali yace "Toh shikenan tunda haka kike so, but I don't have paper and pen here, mu je waje sai in dauka a mota in rubuta takardar in baki..." Daga haka ya mike, ita dai tayi shiru tana kallonsa amma hakan bai sa ta daina hawaye ba, ya kalleta yace "Toh mu je mana, ba dai haka kike so ba??" Mikewa tayi a hankali ta dau Hijab dinta ta saka sai kuma ta tsaya, yace "Mu je...." slowly ta fara tafiya ya bi bayanta yana murmushi, ita dai Imaan tafiya kawai take yana biye da ita yana kallonta har ta fita gate, satan kallon part din su yyi sannan ya fita gate din shi ma.....



*Imaan isn't for free* it's 300 via


Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788



82.....



Imaan ta tsaya jikin motar sai dai bata yarda ta kallesa ba, ta gefen ido ya dinga kallonta ya bude driver seat ya dauko takarda da biro, jinginar da takardar yyi jikin motar ya fara rubutu a kai, satan kallansa tayi ganin rubutu yake kan takardar ta ji gabanta ya fadi, lkci daya ta sunkuyar da kanta tana jan fingers dinta, ya gama rubutu a takarda ya linke yana kallonta yace "Hope you are now happy?" Bata yarda ta kallesa ba ta gyada masa kai kawai, ya d'an yi shiru sannan yace "But I want to let you know one thing Imaan before handing this paper over to you" ita dai kanta na kasa, jin yyi shiru bai fadi one thing din da yace xai gaya mata ba ta kallesa taga kallonta yake, da sauri ta sauke kanta kasa xuciyarta na bugawa, ya bude motar ya shiga a hankali yace "Xagaya ki shigo ki ji abinda xan gaya maki..." Ta girgixa kai tace "Ka gaya min a nan" yace "I want to say it while looking at u in the eyes, so that baxai yi fading memory din ki da wuri ba, ko da ba ma tare you won't forget it Imaan, it's almost a piece of advice..." Ta hade rai tace "Ni dai ka bani takardar in wuce" ya girgixa kai yace "Baxan baki ba idan baki shigo kin saurareni ba, I assure you wannan maganan da xan maki wataran xai maki amfani" Kallonsa tayi sai dai bata ce komai ba, kuma bata xaga ta shiga motar ba, yace "Duk lkcn da kika shirya jin abinda xan gaya maki I will give you ur divorce content, but not today anymore..." Daga haka ya ja kofar motar xae rufe, ta fashe da kuka ta rike kofar da sauri tace "Toh ka rubuta min abinda xaka gaya min a wani takardan ka bani gaba daya mana" Ya wani hade rai yace "Cinye ki xan yi idan kika shigo motar? Kinsan Allah baxan baki takardan nn ba idan baki shigo kin saurareni ba" Dauke kai tayi kamar me naxari sai kuma ta xaga a hankali ta isa daya side din, d'an murmushi yyi ya rufe side dinsa ya jinginar da kansa da kujera, tana xagayowa ta bude front seat ta shiga ta xauna ta d'an saci kallonsa taga murmushi yake, still tayi da farko, sai kuma ta sake kallonsa, lkci daya ta yunkura xata sauka motar ya wani fixgota ya jawota ya rufe kofar gbam ya sa ma motar lock, a mugun tsorace ta dinga jijjiga kofar tana cewa "Meye haka Yaya??" Bai ko kalleta ba ya tada motarsa ya bar layin, kuka ta dinga yi tana kallonsa a rikice tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Yaya don Allah ka bari, where are you taking me to, plss ka tsaya ka bude min mota in sauka, wayyo innaa...." Driving kawai yake bai ko kalleta ba, ta fixgosa cikin kuka tana jijjigasa tace "Don Allah ka bude min in sauka Yaya, ina xaka kai ni??" da hannu daya ya mayar da ita kan kujera ya wani hade rai ba tare da ya kalleta ba idonsa a kan titi yace "Kika sake rikeni sai na falla maki mari..." Ba karamin tsorata tayi ba jin babu wasa tattare da shi, hakan yasa bata sake rikesa ba ta dinga kuka tana kiran Inna tana bubbuga kujeran motar, Sun yi nisa sosai ya daura mata well folded takardan hannunsa kan cinyarta yace "As I promised, here is it...." Kuka kawai take tana kallonsa kamar ranta xai fita, yace "Dauki takardan ki bude ki karanta, ba saki kike so ba, to gashi na rubuta maki" kin ta6a takardarn tayi, ya juya ya kalleta fuskar daure, da sauri ta dau takardan hawaye na xuba idonta tana shessheka, yace "Open it now" hannunta na rawa ta fara warware takardan tana kallon abinda ya rubuta kamar hakw.... "Xan sake ki on one condition, the condition is... Xa ki haifa min yara guda biyar duk masu kama da ke, duk yaron da yyi kama da ni bbu shi a cikin lissafin, just 5 of ur look alike...." Ji tayi gabanta yyi wani mugun faduwa ta sake takardar tana kallonsa, wani murmushi yyi yana kallon titin gabansa yace "Yes... Sai ki shirya conceiving daga daren yau" ta hade kai da gwiwa ta fashe da kuka da karfi tana kiran Inna, driving kawai yake yana murmushi, wani hotel ya kai su, yana parking harabar hotel din ya juya yana kallonta, har lkcn kuka take sosai, ya bude motar ya fita ya xagayo ta inda take ya bude seat din yana kallonta yace "Come down..." Kin dago kanta tayi bata kuma fasa kukan da take ba, xaro ido tayi ta dago da sauri jin daukarta xai yi ta hadiye kukan da take cikin rawar murya tace "Wllh xan sakko Yaya, wllh xan sakko" Ya daure fuska yace "To sakko" ta hadiye abu da kyar ta fito motar tana shessheka tana bin haraban hotel din da kallo gabanta na bugawa tayi kasa da murya pleadingly tace "Don't Forget from the beginning kai ka koya min daukan ka matsayin yayana, kar ka manta a matsayin Yaya na dauke ka tun ban san kai na ba, why will u bring me to a hotel all of a sudden plss?" Yace "To show u ni ba yayanki bane, and after today I don't think xa ki kara kirana yayan ki" xaro ido tayi tana kallonsa, ya kulle motar xai kama hannunta ta fixge da sauri ta kara fashewa da kuka, kallonta ya tsaya yi sai kuma yace "Daukar ki kike son inyi kenan koh?" Ta girgixa masa kai cikin tashin hankali tace "A'a yace "To mu je" tafiya ta fara yi toward direction din entrance din hotel din yana biye da ita, tana waigowa, he couldn't just stop smiling, amma da ta juyo sai ya hade rai, kujera ya nuna mata bayan sun shiga reception din hotel din yace "Sit" kin xaunawa tayi tana hawaye, ya kama hannunta ya tafi da ita gun kujerar ya xaunar da ita yana kallonta, hade kai da gwiwa tayi tana jin kamar ta kurma ihu ko xata ji dadi, ya juya ya koma gun ma'aikatan babban hotel din, bayan kusan minti goma ya dawo inda take ya duka dai dai kanta yace "Tashi mu je...." Ta daga kai da sauri cikin rawar murya tace "Don Allah Yaya kayi hakuri ka mayar da ni gida Ina rokon ka don Allah ba don ni ba" D'aga ta yyi ya kama hannunta suka wuce sama xuwa room din da aka basa don kar ma ta ja masa attention din mutane, a door ta tsaya bayan sun shiga ciki, ya kulle kofar ya cire makullin jiki yana kallonta calmly yace "Ke da gida kuma sai deal din mu ya tabbata, I mean 5 kids...." Durkusawa tayi on her kneels tana kuka sosai tace "Don Allah ba don ni ba ka mayar da ni gida Yaya xa a dinga nemana fa" Ya durkusa gabanta shi ma a hankali yace "A neme ki bayan kina tare da mijin ki??" Kallonsa ta dinga yi ko kiftawa babu kamar yanda shi ma yake kallonta... Inna ce xaune parlon Daddy ta yafa xaninta a kai, kai kace bayerabiya ce, fuskar nan nata a tsuke, Daddy da shigowarta parlon tana rafka uban sallama ya sa ya fito daga daki ya xauna yana kallonta yace "Ina yini Inna?" Ta kallesa tace "Lafiya lau Bukar... Kana ji na??" Daddy yace "Ina jin ki?" Tace "Toh... Ka san dai ni na haife ka, kai kuma ka haifi Imaan koh??" Shiru Daddy yyi bai ce komai ba, a fusace tace "Ka min shiru Bukar ko ba haka bane?" Yace "Haka ne" tace "To madalla, Bukar yau da ba don kai ba wllh ba bbu uwar da na hada da wannan yarinya Imaan, kawai ni dai nasan na haifeka kai kuma Allah ya baka ita, to ya xan yi tunda d'an da na haifa ya haifeta, ya xan yi nace??" Shi dai Daddy kallonta kawai yake, Rai bace ta ci gaba "Yanxu ace Imaan xata bar bangarena baxata jira in gama tsafatace bandakina in fito ba tace min to Inna ni na tafi? sbda walakanci sai ta tsallake kamar tababbiya tayi wucewarta ga farfesun da wannan mata Amina tayi mata ta bar min shi a bude a parlor duk dattin duniya ya fada kai, sannan ta bar min kofa a bude domin ba ma sauro daman shigowa su cuce ni, wllh raina yyi mugun bacewa don ni ba haka na ma Iyayena ba kai ma kuma ba haka ka min ba, to wacece kuma imaan fisabilillahi xata min haka, a wangale fa ta bar min kofar Bukar kaji abinda yafi min ciwo kenan, ni nace lallai dole sai Imaan ta xauna bangarena dama?? To wllh ta fito ta tafi ta kwashe tsummokaranta dake kwambodi na kada in watsa su titi ba ruwana, ni xata kawo ma raini ta walakanta, dama tun da yamma naga take takenta, Banda Ahmadu da ya jaza mana wnn bala'i na aura mata katon d'an sa uban me dama xan ci da ita a sashina??" Daddy dake ta kallonta yace "To ai bata xo nan ba..." Inna tayi shiru ta kalli kofar dakinta, sai kuma tace "Bata nan kuma?" Daddy yace "Bata xo nan ba" mikewa Inna tayi da mamaki ta nufi kofa ya bi ta da kallo har ta fita, part din Abba ta wuce, tana daga tsaye bakin kofa tana kallon Aunty da ta mike ganinta tace "Amina yarinyar nan bata yo nan ba?" Aunty tace "Wai imaan?" Inna tace "ita" Aunty tace "A'a bata xo nan ba gaskiya" Inna ta gwalo ido ta shigo parlon da sauri tace "Bata xo ba kuma Amina?" Jin muryar Inna Abba ya fito daga parlonsa, Inna ta nufe sa da sauri tace "Ahmadu ban ga imaan ba tun daxu wllh" Abba yace "Imaan kuma?" Inna da har jikinta ya fara rawa tace "Ehh na shiga wanke bandaki na fito naga babu ita a parlor sai farfesu" Su Maimoon suka fito tare da Maryam da tayi hijira


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login