Showing 3001 words to 6000 words out of 303099 words
tsaida kukan da take bayan ta gane biyota yyi, ta fizge hannunta ta kwasa a guje, kiris ya rage ya kamata ta shige parlonsu ta banko kofar tasa key, Ammi dake xaune parlon tana kallo ta mike tace "Meye haka Imaan?" Dariya ta fashe da ta wuce daki da sauri tace "Sauri nake in xo in kwanta fa Ammi" tana shiga bedroom din ta ta sa makulli. Har Imaan ta fara bacci wajajen karfe goma Ammi ta bude kofar dakinta, bude ido tayi Ammi ta hade rai tace "Uban me kika debo ma inna a dakinta?" Ta mike xaune da sauri tace "Na debo mata abu kuma? Haka ta ce?" Ammi tace "Kinga na raba ki da xuwa sashinta ki dauko min magana ba ki ji ko? To ki fito mata da duk ma abinda kika daukan mata gata can bakin kofa" Imaan ta turo baki ta sauko daga saman gadon ta bi bayan Ammi da ta fita, ido hudu suka yi da inna da ke tsaye bakin kofa ta tsuke fuska, Imaan ta hade rai tace "Ni me na dibar maki xaki biyo ni cikin daren nan" Inna tace "Duk cikin jikokina babu mai ta6a min kaya ban basa ba sai ke, duk kece mai mugun halin nan don haka maxa ki fito min da alkaki na, don ba a rame na bar sa ba ina sane da abinda nake ba fara haukacewa nayi ba" Ammi dai ta nemi waje ta xauna, Imaan ta 6ata fuska kamar zata yi kuka tace "Wai yaushe naje da har xan dibar maki kayan ki ni da ba ci ma nake sosai ba, to ma ba xaki gansa hannuna da xan fita ba" Wani tsawa Ammi ta yi mata tace "Kin tafi kin dauko abinda kika diba ko sai na mare ki" Imaan ta harari inna ta wuce kitchen sai ga ta ta fito da ledan alkakin, Inna ta saki baki ta warce ledan tace "Naga Ikon Allah ni Asabe, da yake Aisha ce ta xauna ta min tuyar bayan ta kwa6a dole ki kwaso ki kawo maku ku ci, to ni kar in sake ganin kafafuwanki a bangarena don halin ki abun tsoro ne, wannan ai ba tarbiya aka maki ba ki shiga har karkashin gadon mutane ki jawo kwalla ki debe min kayana, yanxu banda jinin ka jininka ne kin xata idan na ja Allah ya isa baxai bi ki ba, ni wllh darajar d'a na kike ci a gidan nan gaskiya, kar in sake ganin ki a parlona ni dai dama baki tsinanamin komai sai dai ki malale kan kujera kina mik'a, duk kin ru6ar min da kujeru" tana kai wa nan ta juya ta wuce, Imaan bata yarda ta kalli Ammi ba ta wuce daki ta rufe kofa tayi kwanciyarta tana turo baki.
Maa sha Allah, I am back by Allah's grace... daily update in sha Allah, but if schl shud resume anytime soon xan dakata da posting for some weeks coz I will be having exams in sha Allah. Hope you guys will love the *book*, though I know I never disappoint my fans when it comes to writing in sha Allah....
Khaleesat Haiydar...
[6/11, 12:34 PM] +234 703 570 1601: 🌟⭐ *Imaan* ⭐🌟
_By Khaleesat Haiydar_✍🏻
2......
Washegari da safe Imaan ta fito parlor shirye cikin well ironed uniform dinta da beret dake kanta, kitchen ta shiga gun Ammi, Ammi dake juye ruwan shayi flask tace "Yau ma baki yi combing gashin ba koh" ta jingina da kofa cike da shagwaba tace "Wllh Ammi xafi, baxan iya ba" Ammi bata ce komai ba ta gama xuba ruwan a flask ta xuba mata nata a cup dinta ta hada mata shayin sannan ta mika mata, Karba Imaan tayi ta fita xuwa dinning, Ammi ta kai mata dankali da kwan da ta soya mata ta ajiye tana kallon agogo tace "Kiyi sauri kar su jira ki don Allah" Imaan ta xaro ido tace "Ammi kullum fa ni ke jiransu" Ammi tace "Toh kar kiyi saurin" daga haka ta wuce kitchen don yin wanke wanke, imaan na gamawa ta kai plate din da cup kitchen, ta dauko jakarta, Ammi tace "Ki duba gaban dressing mirror a daki na akwai duba daya ki dauka, dakin ta shiga ta dauko sannan ta fito tace " Ammi sai na dawo" Ammi tace "Ohk Allah ya tsare kiyi addu'a kafin ki fita, and you make sure baki mance ko wani book ba tunda hankali bai ishe ki ba" dariya kawai tayi ta fita gidan bayan tayi addu'a, Can parking space din su Yusuf ta tafi ta tsaya don nan take jiransu, yawanci Yusuf ke kai su wani lkcin kuma Anty ta ajiye su tunda tsohon driver dinsu ya tafi, Tana ta tsaye jikin mota ta hango plant din su Ummi, Rahma da Maimoon don duk ajinsu daya wato ss2, kamar xata yi kuka ta dinga kallon waken nasu da duk ya fito da ganye, ga nata can an lalata mata, kallon entrance din gidan tayi lkci daya ta nufi wajen da plant din suke da kafa ta haure gaba daya biyun banda na maimoon don kowa ya sa sunansa, sai da ta tabbatar roots din sun fita sannan ta koma jikin mota da sauri, Ummi ce ta fara fito sanye cikin uniform irin na jikin Imaan sannan Rahma sai Maimoon, Babu wanda ya kalleta cikin su banda Maimoon da tace "Imaan kin gama maths assignment din ki" Imaan tace "Ehh na gama" Maimoon tace "Toh idan mun shiga mota xan kwafa plss ban yi ba" Imaan tace "Ohk" Mujaheed ne ya fito rike da makullin mota fuska kamar hadari, Imaan ta xaro ido tana kallon Maimoon murya can kasa tace "Shi xai kai mu?" Maimoon tace "Ehh ya Yusuf baya nan ya tafi Zaria daxu, shine Anty tace ya Mujaheed ya ajiye mu, shine yake fushi" Imaan ta turo baki bata ce komai ba yana bude motar ta shiga back seat tare da Maimoon da Rahma, Ummi ta shiga gaba, har suka bar gidan babu wanda yace komai cikin su, Imaan ta bude jakarta ta ciro assignment din ta ba Maimoon, tafiyar minti ashirin ke kai su makarantar su, amma saboda gudun da yyi cikin few minutes suka iso, yyi parking dai dai makarantar yana kallonsu da kyau yace "Dama kuna tashi ku fara trekking din dawowa gida don baxan xo daukan kowa ba" a hankali Ummi tace "Ya M.A ai soon Abba xai dau mana wani driver fa" yace "Sauka malama" bude motar tayi ta fita, tuni Imaan da Maimoon ma suka fita suka shige cikin makarantar. Anty ce ta xo daukan su bayan sun tashi ranan, Anty na kallon Imaan dake ta yamutse fuska tace "Me ya faru Imaan" a hankali ta nuna mata kanta, Anty tace "Toh idan kin koma gida kin ci abinci sai ki sha magani ki kwanta ki huta" to kawai imaan tace, ko da suka isa gida har bacci ya dauketa Maimoon ta tasheta ta bude ido, Anty tace "Toh shiga gida imaan" kai kawai ta gyada mata ta fita ta nufi part dinsu tana dingishi. Ruwan xafi Ammi ta hada mata ta shiga tayi wanka sannan ta ci abinci, Ammi ta bata magani tace "Sai ki daure kiyi shirin tafiya islamiyya it's too early ki fara fashi this week, today is Monday" Imaan bata ce komai ba, Ammi na fita ta koma kan gado ta kwanta kamar xata yi kuka, hudu da minti biyar Ammi ta shigo dakin jin shiru bata fito ba, ganin har bacci ya dauketa ta kai hannu jikinta taji da dumi, girgixa kai tayi ta juya ta fita, Maimoon ne ta shigo parlorn sanye da uniform din islamiyya, Ta gaida Ammi sannan tace "Ammi imaan muke jira" Ammi tace "Bata jin dadi ku tafi Maimoon" a hankali Maimoon tace "Allah ya sauwake" sannan ta fita, Ammi na girkin dinner a kitchen wajen karfe biyar Imaan ta fito daki, wani internal heat kawai ta ke ji, kuma tana kunna Ac tasan sauran ta dinga lekan kitchen kamar xata yi kuka, a hankali ta nufi kofar fita ta bude kofar yanda baxa aji kara ba sannan ta fice xuwa part din inna don ta je ta kunna Ac, Inna na wanke gun tap dinta da take sa ma kwado ta daga kai tana kallon Imaan tace "Baki tafi islamiyyar bane yau" Imaan ta turo baki tace "Ehh" daga haka ta shige parlon, kunna Ac tayi ta kwanta kan kujera dake kallon Ac din ta lumshe ido, inna na gun tap din har sannan sai ga Mujaheed, ta mike tana kallon sa tace "Baka ji bayana ba Mujaheed kamar xai balle, ko kai baka ga yanda wajen pampon yayi haske ba tun daxu nake ta gurza gashi sai kyalli yake, ai kazanta bata da kyau, yanxu kaga ko tuwo aka xuba a wajen mutum xai iya xaunawa ya ci" Mujaheed dai bai tanka ta ba ya shige parlorn bin bayansa tayi, ya ajiye ledan hannunsa yace "Gashi Abba yace a kawo maki" tace "Toh Allah yayi masa albarka... Dama raina na son kayan marmarin" xai fita Inna tace "Mujaheed kaga yarinya nan abinda ya kawota kenan ta xo ta kunna Ac wata cutar ta kamata ace ai a parlorn inna ne, to ni dai ba ruwana ka kashe min kayana taje can ai su ma suna da shi, duk yanda aka yi kuma uwar hanata kunnawa tayi shine ta taho ta kunna nawa salon ace parlorn inna to Allah ya fi ki babu me sa ni a bakin duniya" Mujaheed ya kalli Imaan da tayi rub da ciki kan 3 seater din ya tabe baki xai fita Inna tace "kai ya ina maka magana xaka fita, idan uwar ka Rukayya ce xaka mata haka Mujaheed?" Fuska daure ya juyo ya xauna yana kallon ta da kyau yace "Wllh idan kina sa mahaifiyata a baki Hajiya xa mu kwashi yan kallo dake a gidan nan, komai sai kice uwata" Inna ta saki baki tace "Kai ni kake daga ma murya" yace "Toh ki daina sako mahaifiyata a xancen ki idan baki son a daga maki murya, ke kwata kwata rayuwarki baki son xaman lafiya daga kice wannan yayi maki sai ki ce wannan yayi maki...." Inna ta gyada kai tace "To ka tara kuma ka samu, xaka san ni ka fada ma bakar magana" Tana fadin haka ta kashe Ac dinta, Imaan ta mike xaune kamar xata yi kuka tace "Meye xa ki kashe min inna" Inna tace "Bukar yasa na kashe, na ku lalacewa yayi xaki taho min nan, ni dai a daina xuwa ana sa ni magana ana min rashin kunya gaskiya" imaan ta marairaice tace "Don Allah inna ki kunna xafi nake ji a cikin jikina" Inna tace "Toh baxa ki ji xafi a jikin ki ba ga magani nan an kawo maki tun daga Nijar kin ki amsa sai yawo kike min da hankali kamar ni xai amfana, duk tashi fadin da nake a kanki ba ki gani, mutum bai san inda xai dace ba, idan an baki magani sai kiyi biyayya ki amsa ki sha sai kiga Allah ya yaye maki wannan ciwace ciwacen da ba a san kansa ba" Imaan tace "Wa yace maki ba a san kansa ba, to ai da shi aka haifeni kuma ba warkewa...." Inna tace "Oh oh Allah, Mujaheed kaji irin fitinar da take ja ma kanta da bakinta ko, kai wannan 'ya ta Bukar anyi doluwa wllh, ke fata kike kar ki warke d'a na yayi ta cacan kudi, duk cikin jikokina babu mara tunani dama irin ki" Imaan ta hade rai tace "Ehh na ji, ki kyaleni da ciwo na Babu ruwanki, baxan kuma sha maganin ba don ina da na asibiti da nake sha, ni bance ki dinga amso min magani ba dama ai" inna tace "Kada Allah ya sa ki sha, to ni Allah na tuba a haka ma wa xai yi sha'awar aurem ki yau ciwo gobe lafiya duk tattalin arxikinsa ya kare a asibiti, tun kina mitsitsiyar ki nake wahala da ke kan maganan magani shi sa ma kika yi kyan gani, ke da kike kamar kwarangwal da taimakon Allah da taimkona da magungunan da nake amsar maki gun malamai shine kika marmaro, in dan ta uwar nan taki ce ai sai dai ki mutu tana kunshe daki ba fita xata yi ta nemo maki magani ba tana jiran na asibiti, Toh wllh daga yau na fita harkan ku ki ji da ciwon ki nima inyi ta kai na" Imaan ta fashe da kuka tace "Ehh naji, ki kyaleni tunda ba dole bane shan maganin ki" daga haka ta fice daga parlorn da gudu, Inna tace "Duk xa ku yi bayani bari iyayen naku su dawo" Mujaheed ya tabe baki ya mike ya fice mata a parlorn shi ma. Imaan na kwance kan kujera bayan isha Ummi ta bude kofar parlorn tana tsaye daga bakin kofa tace "Abba na kiran ki a bangaren Inna Imaan" daga haka ta fita, Ammi dake cin abinci xaune parlorn ta kalli Imaan da ta wani juya bata dai ce komai ba, bayan kusan minti biyar Ammi tace "Amma dai kin ji abinda tace Imaan" Ta juyo kamar xata yi kuka tace "Wllh Ammi kafana ciwo yake min ban san ko xan iya tashi ba" Ammi ta galla mata wani harara tace "Sai ki rarrafa ai tunda baxa ki iya tashi ba" hawaye cike idonta ta mike ta sa Hijab ta fita tana taka kafar da kyar. A hankali ta bude kofar parlorn Inna ta shiga da sallama, Abba ne xaune parlorn sai Inna da Anty, Imaan ta sunkuyar da kanta ta karasa kusa da Anty ta xauna kanta a kasa ta gaida su, Abba da Anty kadai suka amsa, inna ta wani tsuke fuska, Imaan dai bata ko kalleta ba, Inna tace "Wato shi Mujaheed din jira yake kaje ka ciccibo sa da kanka koh?" Abba ya kalli Imaan yace "Tashi ki tafi can bangaren ki kira min Yayanku" Imaan ta mike ta d'an harari inna ta gefen ido ta fice a parlorn, tana isa part din su Mujaheed ganin bbu kowa parlor sama ta haura ta tsaya corridor tana kallon door din dakinsa har ta mance rabon da ta je kusa da kofar, bude kofar Umma aka yi sai ga shi ya fito, ta matsa da sauri don kusa da kofar dama take tsaye tace "Abba yace in kira ka" ko kallon ta bai yi ba ya fara sauka stairs, ta murguda masa baki ta bi bayansa, har suka isa part din Inna bai juya ba, ya bude kofar ya shiga da sallama, kusa da Anty Mujaheed ya durkusa kansa a kasa, Abba sai kallon sa yake yana girgixa kafa, Imaan ta shigo parlorn ganin inda ya durkusa tace "Waje na ne nan" Murmushi Anty tayi, shi kam ko kallon ta bai yi ba balle ya motsa, Inna tace "Ahmadu na fa gaji da xama nan kamar warce xa a ma gafara, aji da ni in tashi in shiga ciki in kwanta" Abba ya kalli imaan yace "Samu wani wajen my friend" ta harari Mujaheed ta koma wani wajen ta xauna, Abba na kallon Mujaheed yace "Muhammad ita innar ka mayar abar wasar ka a gidan nan?" Inna ta tabe baki tana jijjiga kafa, Mujaheed bai dago ba kuma bai ce komai ba, Abba yace "Am I not talking to Mujaheed" ya dago a hankali yace "Abba kayi hakuri don Allah" Abba yace "Stupid, ni ma kake ba hakuri?" Ya kalli inna yace "Kiyi hakuri inna" dakatar da shi tace "A'a malam a gaban ubanka xaka ce min inna kenan, wllh Ahmadu daxu yana nuna ni da yatsa a can bakin kofar kamar xai make ni Hajiya yace min, ni na ma xata duka xai kai min bayan ya gama kashedin, to gaskiya da sake, sam yaranka basu da d'a'a basu da kunya Ahmadu, isuhu ne kadai dama mai gudun bacin raina duk da shi ma ko aiki xai kashe ni baya taimakona, to ynxu Mujaheed da wani ne da ya xo ya gan ni durkushe ina faman gurje gun pampo ba amsa xai yi ba ya taya ni, to wllh bai amsa ba sai xagina ma ni da yayi daga karshe, a xo har sashina a dinga ci min mutunci, to hirrr don duk ranan da aka isheni tattara kayana xan yi in bar gidan nan kuma sai anyi shekara duba ana nemana" Mujaheed ya d'an daga kai ya kalleta ta gefen ido ya maida kansa kasa, Abba dai bai iya yace komai ba, Anty tace "Kiyi hakuri inna, a yafe masu" Inna tayi kasa da murya tace "Wllh Amina daga nace kai kuwa Mujaheed haka kake ma Mamarka a gida ina ma magana xaka wuce, kuma fa cikin lallami nayi tambayar kawai ba sai ya sakar min aradu a kai ba, ita kuma wancan lankwasasshiyar mai kama da yar tsana bbu abinda ta mance bata gaya min ba daga nace Imaan ga maganin da na amso maki saboda ciwon ki da ba a san kansa ba ba a san dalilinsa ba, wllh Ahmadu sae kaga wanke ni da yarinyar tayi tasss har da ce min ba ruwana da ciwonta kuma ciwon ba me warkewa bane" Imaan ta fashe da kuka har da shessheka, Abba yyi mata tsawa cikin rawar murya tace "Abba xagina fa ta ke yi wai...." Abba ya dakatar da ita yace "Keep shut" ta hadiye abinda xata ce tana hawaye, Mujaheed yace "Kiyi hakuri Inna" Inna tace "Atoh ya xan yi idan ban hakura ba, dama wanda aka cuta ake ba hakuri, amma daga kai har ita kar in sake ganin kafufuwanku a bangarena, tunda kun raina ni, Isuhu da Maimuna sun ishe ni" Fada sosai Abba ya dinga ma Mujaheed da kansa ke kasa, inna sai matsar kwalla take ita a dole an 6ata mata rai, hakuri Mujaheed ya kara bata, Anty ta sa Imaan ma ta bata hakuri, mikewa Imaan tayi da sauri ta fice parlorn tana kuka, Inna tace "Sai ubansa na magana yayi ta sinne kai kamar na