Showing 57001 words to 60000 words out of 303099 words

Chapter 20 - Imaan Book 1 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

1682

ba yyi reverse, Inna tace "Ni bikin Imaan da na Maimoon ma gaskiya sae na xabi wa enda xa su raka su daki, iyaka kawai in xauna bayan mota ni da su don ina fatan ya xamo rana daya, Mujaheed ya ja mu in kai su dakunan su ya maida ni gida idan Allah ya yarda, ba katuwar da xata bi mu" Mujaheed dai driving yake har ya bar layin ya hau saman titi, lkci lkci ta madubi yana kallon imaan da ta ki yarda ta kalli gaban motar, inna tace "Mujaheed kaga kawayen uwar ka kamar mayu kuwa, wllh da kyar na kora su, duk sun ban wahala, ita ina ta samo su haka wasu lafta laftan mata ba kyan gani kamar aladu? kaii Rukayya dai shahararriyar mahaukaciya ce wllh" taka brake Mujaheed yyi bayan ya tabbatar bbu motar dake bayansa ya gangara gefen titi, inna ta saki salati tace "Lafiya Mujaheed, me ya sami motar" ya bude motar ya fita ya bude side dinta yana kallonta yace "Ita uwar tawa ce mahaukaciya?" inna ta bude baki tana kallonsa, sai kuma ta kalli Imaan tace "Ga reshen bishiya can, sauka ki karyo ki kawo masa...." Imaan ta hade kai da kafarta tana dariya kasa kasa, a fusace inna ta kunduma masa xagi tace "Na ce mata mahaukaciyar sharri na mata, da hankalinta ina ita ina gunduma gunduman matan da ta ajiye matsayin kawaye, wasun su idan suka xaune kanta shegiya nake idan bata suma ba bayan sun latse ta" yace "Ku saukar min a mota ku samu wanda xai kai ku gida Hajiya" kamar jira Inna take ta sauka da sauri tana kallon Imaan tace "In dai kin san motar ba ta Bukar bace ki sakko ki bar masa tsiyar sa" Imaan ta hade rai tace "Inna bai ce har da mu ba fa" Irin kallon da Mujaheed yyi mata yasa ta sauka da sauri don ya dade bai mata irin kallon ba, Inna ta kalli Maimoon tace "Ke kuma idan ba ta Amina bace motar ki sakko kema" Maimoon ta bude front seat ta sakko, inna ta fara matsar kwalla tace "Ku sama min Adaidaita sahu" ko kallonta Mujaheed bai yi ba ya rufe back seat dinsa ya shige motarsa ya kara gaba, inna ta bi motar da kallo tace "Allah dai ya isa, kuma sai Ahmadu ya min iyaka da Mujaheed yau, ni xai toxarta ya walakanta a bakin titi a kan Rukayya" Imaan ta tsayar da adaidaita ta fada masa inda xai kai su, Mai adaidaita yace "Ba can xan yi ba" bai gama rufe baki ba inna ta shige adaidaitan ta xauna, Imaan da Maimoon suka saki baki suna kallonta, Mai napep din ya juya yana kallonta yace "Baaba nace ba can nayi ba" a fusace tace "Dalla can mu je d'an nan, ko baka ganin dare yyi ne xaka ce min ba can kayi ba, jika na ne fa ya watsar da mu a titi yanxun nan yyi wucewarsa daga nayi ma katuwar uwarsa gyara, banda haka yaushe xaka gan ni bakin titi tsaye da gata na, motocin 'ya yana sun fi biyar wllh, ko da yake in mun je gidan ma xaka gane abinda nake nufi, ko kai so kake inyi ta tsayuwa kamar yar iska bakin titi?" Shiru yyi bai ce komai ba, Inna ta kalli su Imaan sannan ta kallesa tace "Yaro idan baxa su shiga ba ja ni ka kai ni gida, su kuma Allah ya kawo masu mafita, mu je ni dai" murmushi mai napep din yyi, Imaan ta turo baki ta shiga Maimoon ma ta shiga, inna tace "Atoh da kun tsaya jiran d'an sahun da xai je ku kwana a wajen" suna isa gida dama inna ta sauka napep din ta nufi gate tana gyara yafin mayafinta, Maimoon ta kalli Imaan dake dariya ta ja tsaki ta bude jakarta ta fiddo dubu daya ta basa ya bata canji ta wuce ciki, can suka ga inna har ta shige parlon su Maimoon, Imaan ta nufi part din su Maimoon ta bi bayan Inna, babu kowa parlon Abba hakan yasa inna ta dawo main parlor tana kallon mutanen da ta wuce da farko tace "Ahmadu baya nan ne" Daga kitchen Aunty ta leko tace "Bai shigo ba inna, kun dawo lafiya?" inna bata tanka ta ba ta fice parlon, bata tsaya ko ina ba sai part din su Imaan, ba kowa parlon sai kamshi dake ta tashi, cikin daga murya inna tace "Salama alaikum" Imaan ta bude kofar bedroom dinta tana lekowa, Inna tace "Ina Bukar din?" Daddy ya fito daga daki yace "Har kun dawo inna" karasawa cikin parlon tayi ko takalmanta bata cire ba ta xauna saman kujera tana share guntun hawayen idonta, Ammi dama na jin irin sallamar da inna tayi tasan ba lafiya don haka bata fito ba, duk xaton ta k'aran imaan ta kawo, Imaan da har ta cire kayanta ta sa Hijab kawai ta fito da sauri, Daddy na kallon inna a hankali yace "In ji dai lafiya inna" a fusace tace "Ina fa lafiya Bukar, shegen d'an ku ya watsar da ni tsakiyar titi gefen jaji yayi wucewarsa, daga nayi ma Rukayya gyara" Shiru Daddy yyi yana kallonta da mamaki, ta fashe da kuka tace "Gaskiya Bukar idan ba a bi min hakkina ba yau duk a station xa mu kwana gwara in kai karar can a bi min hakkina, da girmana da matsayina da martabata Mujaheed xai juye ni tsakar titi yyi wucewarsa?? Ae wannan babban magana ce wllh" Daddy ya sauke ajiyar xuciya yace "Subhanallah me ke damun Mujaheed haka" Inna ta tsaida kukan da take tace "Toh ai ba ni xaka ma tambayar ba, waya xaka dauka yanxu ka kirasa, kada ma ka nuna masa ina nan, kawai ce masa xaka yi ya xo xaka aikesa yanxun nan, daga nan sai kaji me ke damunsa ko wiwi ya fara sha bamu sani ba" Daddy ya kara sauke ajiyar xuciya, inna tace "Sae wani sauke sauken ajiyar xuciya kake Bukar, ko tsoron sa kake ne inyi ta kai na?" Yar dariya kawai daddy yayi ya dau wayarsa, inna ta tsuke fuska tace "Wllh yanda ya min tijara a kan uwarsa kai ma haka xaka masa tijara akan taka uwar, kuma idan baka ce masa aikensa xaka yi ba wllh baxai xo ba nan kuma xa mu kwasa mu tafi police station " Daddy dai bai ce komai ba yayi dialing number Mujaheed ba a dau lkci yana ringing ba ya daga, Daddy yace "Muhammad kana kusa ne?" Daga daya bangaren Mujaheed yace "Eh Abba" daddy yace "Toh ka xo parlor na yanxu" Mujaheed ya d'an yi shiru, kafin yace "Toh Abba" Daddy yace "Don't keep me waiting fa naji kayi shiru ko baka kusa ne?" Yace "Ina nan" Daddy yace "To ina xaune ina jiranka yanxu" Mujaheed yace "Toh" daga haka daddy ya katse wayar, inna tace "Kai xaka kwana a ciki wllh idan yaron nan bai xo ba Bukar" Daddy dai bai ce komai ba, Mujaheed ba don yanda yake jin kunyar daddy ba da fa ba xai je ba don yasan sarai inna na can, kuma da Abbansa ne ma ya kirasa ba lallai yaje ba, jallabiyarsa kawai ya xura ya fita dakinsa, banda girgixa kafa babu abinda inna take, da sallama ya shiga parlon, ba tare da ya kalli Daddy ko ita ba ya tafi ya xauna kasan lallausan carpet din parlon yace "Barka da dare Abba" Daddy yace "What happened between you and ur grandma yanxu?" Mujaheed ya daga kai yana kallonta yaga yanda ta wani tsuke fuska tana kallon sa, ya maida kansa kasa, inna na nuna Imaan dake kwance kan kujera tana kallonsu tace "Idan sharri na masa ga 'yar ka kwance kusa da kai ka tambayeta ka ji ko ba tsakiyar titi ya juye mu ba" Daddy ya juya ya kalli Imaan, a fusace Inna tace "Ke tashi xaune ki basa labarin abinda ya faru, ba tsakiyar titi Mujaheed ya sauke mu ba, naga kamar tantama Bukar yake" Imaan ta mike xaune tace "A'a ba fa tsakiyar titi bane inna, gefen hanya ne....." Rai bace Inna tace "Amma wannan anyi shegiyar 'ya... Dama akwai bambanci tsakanin gefen titi da tsakar titi, ke dai munafuka ce wllh" Imaan ta harareta ta gefen ido tana turo baki ta koma ta kwanta, Inna tace "Wllh Bukar gefen hanya yayi watsi damu, kuma kafin ya sauke ni don Allah mai yace min Imaan" da sauri Imaan ta daga hannu tace "A'a ba ruwana nima ban sani ba" Bude baki inna tayi tana kallonta, daddy yace "Yanxu dai ki tashi ki tafi ki bar ni da shi inna" inna tace "In tashi in tafi ka basa hakuri shima ya tafi xaka ce min" Tana fadin haka ta mike tace "Tun farko ma ban san me ya kawo ni gun Bukar ba, duk inda Ubansa ya tafi ai ya ci ace ya dawo yanxu" daga haka ta fice parlon fuska daure. Daddy ya hade rai yana kallon Mujaheed yace "Saboda baka da kirki xaka ajiye su bakin hanya Muhammad?" Mujaheed yyi kasa da kai bai ce komai ba, Daddy yace "Yanxu ka kyauta kenan, idan Hajiyar ka ce ko min abinda tayi maka xaka mata haka?" Yace "Kayi hakuri Abba" Daddy yace "Haba Muhammad, I am highly disappointed at you, this is very rude and stupid of you, she is our mother fa, no matter how she behaves baxa mu canxa ta ba" Mujaheed bai iya cewa komai ba, daddy yace "Ka tashi ka bi ta ka bata hakuri yanxu" yace "Toh, ayi hakuri Abba" Daddy ya kalli imaan yace "Ke kuma I've warned you times without number ki daina fada mata magana anyhow amma baki ji ko, xan fara sa6a maki soon wllh idan baxa ki canxa naughty attitude din nan ba, will you dare talk to ur mother that way?" mikewa xaune tayi kamar xata yi kuka, Mujaheed ya tashi yace "Xan je in sameta yanxu Abba" daga haka ya fita parlon. Washegari da safe da kyar imaan ta tashi tayi wanka tayi breakfast da Ammi ta ajiye mata a dinning, Ammi tace "Idan kin gama ki dau magungunanki ki sha kada in tuna maki, kuma da Ac kika kwana ko?" Ta xaro ido tace "Ammi wllh A'a" Ammi tace "Toh ga mura nan na shirin kama ki" Ta langwabar da kai tace "Jiya fa da daddare a napep muka dawo, kin ji sanyi kamar xanyi freeze a hanya" Ammi ta fiddo kindirmo a fridge yayi sanyi sosai ta ajiye mata a dinning din tace "Gashi ki kai ma inna inji daddyn ki, you make sure kin goge min dinning table idan yayi stain" Ta marairaice tace "Ammi my legs are aching me fa" Ammi ta harareta ta wuce dakin ta, Imaan na gama breakfast ta tashi ta dau kindirmon ta tafi kai ma inna, Tana shiga parlon bayan ta ajiye tana kallon inna dake ta kukkula dubulan da cin cin a leda sai ga Umma ta shigo parlon da sallama, Inna ta kalleta ta ci gaba da abinda take ta amsa sallaman ba yabo ba fallasa, Umma ta dafa kujera tace "Ina kwana inna" inna tace "Lafiya lau" Umma tace "Ya gajiyan taro" inna tace "Bana tare da gajiya duk ya bi lafiyar gado" Umma tace "Toh Alhmdllh Allah ya saka da alkhairi yaji k'an mahaifa" inna tace "Ameen" karasawa tayi kusa da inna ta ajiye ledan hannunta tace "Ga wannan dai ba yawa" inna na kallon ledan tace "Meye wannan din? Ke imaan xo ki bude" imaan dake xaune ta mike ta karasa kusa da Inna, Umma ta bi ta da kallon gefen ido, durkusawa tayi ta bude ledan ta ciro atamfa da pack din sabulu guda biyu da turare mai tsada" Inna ta bude atamfar tana kallo da kyau, tace "Holland ce wannan din?" Umma tace "Ehh" inna ta tabe baki tace "Toh, da dai basirar ki ce hakan da sai ince Allah yyi albarka, amma wannan ko kaffara baxan yi ba Ahmadu ya sa ki, Allah ya masa albarka ya kare min shi duk inda xai shiga, Allah ya ci gaba da hada kansu da d'an uwansa Bukar ya raya mai 'ya yansa yayi masu albarka, ita kuma wannan da ya aurar Allah xaunar da ita da mijinta lfya, ke kuma nagode da isar da sako" Umma ta dinga kallonta ko kiftawa babu, Imaan sai danne dariyarta take, Inna ta ci gaba da kulla dubulan dinta a leda, Umma tace "Sai anjima" inna tace "Mu jima da yawa" daga haka ta nufi kofa, inna na kallon Imaan tace "To ke sai kiyi ta kanki, don wllh jiya Mujaheed ce min yyi xai kakkarya ki ya xane ki, wai ya ganki da wani mai mota a tsaye a kofar gidan seeyama, imaan ina kuma kika samo mai mota kike ta boye min ban sani ba ni Asabe??" Umma ta d'an dakata bakin kofa jin abinda inna ke cewa, Imaan ta turo baki tace "Shi sa ma xan tashi in tafi yanxu kar ya xo nan, to har kun shirya ne inna?" Inna tace "Haba dai sai kace wata yarinya, to me yyi min da baxa mu shirya ba, wai na ce ma Rukayya mahaukaciya, ke ki ji fa? to me ta min xan xageta banda abunsa ma dai, kawai daga ina mata gyara? Ni fa na yarje ma Ahmadu ya aureta wllh, baki ganta ba a lkcn yar siririya yanda kika ganki, kamar iska xai hure 'yar banxa ta fadi, gashi iyayenta basu da komai basu kuma ba wani ajiya ba, wani d'an akurkin gida fa gare ubanta a lkcn, to ni ban masu bakin ciki ba don xuciya ta fess mai kyau ne na yarda Ahmadu ya auro mana ita a haka, ke kinga wahalar da nayi da ita kuwa? Wllh kare baxai ci ba, gashi ba abinda ta iya a lkcn, har girki ni ke sa ta kan hanya ina koya mata, kishiyoyina su yi ta jin haushi yanda nake ji da ita bana son ko k'uda ya ta6ata har dai ta samu cikin wannan yaro Mujaheed, sai kin ga wahalar da nayi mata sbda laulayin da ta dinga yi ba kakkautawa, to ni duk ba wannan ba don nasan sakayya ta dai na gun Allah, to don kuma yanxu Rukayya ta xama abinda ta xama sai me xai dameni ni patuu? ga dai Amina na bina sau da kafa ga Aisha, ni dai abinda na sani shine Mujaheed ai xai yi auren, to nan xata d'an dana ko da dadi ko babu, abinda duk abinda ka shuka shi xa ka girba, tsaf xan karance ma yarinyar xaman da xata yi da ita, muna nan da ku sai an dinga xuwa daukata shari'a a mota...." Imaan har wani kwanciya tayi kan kujera tana dariya amma ba mai sauti ba, Umma da ta makale jikin kofa ta fita ta sa takalmanta, inna ta tabe baki tace "Wllh Mujaheed da gwiwowinsa bibbiyu ya durkusa ya dinga ban hakuri tun ban kai ga gaya ma ubansa ba, to tunda naga yyi nadama kawai sai na yafe masa don ba halinsa bane gaskiya bai taba juye ni a tsakiyar titi ba tunda mu ke" Imaan ta fashe da dariya tace "Jiya dai ya juye ki ai"


*The book Imaan is not free, you read for free ur cup of coffee*🤷🏻‍♀️

It's 300 via Fcmb 3276052019
Hauwa Bello Jiddah

Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp digit 07087865788 to be included in the payment group.


19. Imaan









Umma na komawa bangarensu kallo daya tayi ma Mujaheed dake xaune dinning yana shan coffee tace "Ka sameni daki yanxu" sosai gabansa ya fadi ya bi ta da kallo har ta haura sama, bai iya ya karasa shanye coffee din ba ya mike ya bi bayan ta, tsaye ya ganta tana safa da marwa a dakin, Yace "Gani Umma" ta juya tana kallonsa fuska daure tace "Mujaheed ina son sanin meye matsalar ka don kaga shegiyar yarinyar nan da mai mota jiya har kake ikirarin hukuntata" ya xaro ido yace "Ban gane ba Umma" Ta masa wani mugun kallo tace "Bana son ka gane dama ai, warce kaje ka ba sakon take fadi yanxu naji, dama baka raba kanka da makiyan nan nawa ba har ynxu Mujaheed? Mujaheed ka gaya min meye hadin ka da yarinyar nan Imaan?" Yace "Haba Umma, ke yanxu maganar inna kike dauka, kila ma don ta ganki yasa ta kirkiri haka, ni a ina na ganta har muka yi wannan xancen da ita?" Shiru Umma tayi tana kallonsa, a ranta kuwa tunani take kila hakan ne ma, ganin Umma tayi surrender, Mujaheed yace "Kawai ta fada haka ne don ki sa a rai, ni yaushe nake da wannan lokacin ma a gidan nan yanxu" Umma ta sauke ajiyar xuciya tace "Sae ma kaga rashin mutuncin da ta min kayan da na kai mata, ni na ma ji dadin da ta gane cewar in don ta nine baxan bata ko tsinke na ba, basirar Abban ku ne kamar yanda ta fada" Mujaheed yyi murmushi bai ce komai ba, Umma tace "Gobe xan baka sako ka kai ma Hajiya Mansura ta marafa, bata samu xuwa bikin ba amma ta bada gudunmawarta dubu dari, cin cin da su alkaki xaka kai mata daga nan nasan xa ku hadu da Safeenah, tana nan ba ta koma makaranta ba, ni so nake nan da 'yan watanni a fara xancen naka bikin" shi dai Mujaheed bai ce komai ba banda kallonta da yake, ta xauna gefen gado tace "Kar fa kace min ka manta gobe kayi ficewarka, xuwa sha biyu in sha Allah xaka kai masu, tunda gobe lahadi" ya shafa kai yace "Allah ya kai mu" daga haka ya nufi kofa ya fita. Imaan ta kara leka samirar dake cike da cin cin da dubulan da alkaki da inna ta basu su kai ma ta rasulu aminiyarta, ta tabe baki tace "Wllh duk kin kwashe ma tsohuwar, mu fa har ynxu ba mu ci ba" inna ta tsuke


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login