Showing 81001 words to 84000 words out of 303099 words
sa ta xura Hijab din makarantarta ta dau jaka tana kallon Ammi dake parlor kamar xata yi kuka tace "Ammi fa kila xai yi amfani da wayarsa don Allah ki bani in kai masa plss" Ammi ta daga kai tana kallonta, da sauri Imaan ta fice daga parlon don ta san sauran, parking space ta tafi ta tsaya tana jiran su Maimoon su fito, Mujaheed ne ya fito tare da Yusuf, Imaan ta dinga kallon hannunsa da mamaki ganin wayarsa, bai ko kalli inda take ba ya nufi gun motarsa ya bude ya shiga, Yusuf dake kallonta yyi murmushi yace "Why are you looking at him that way" kamar xata yi kuka tace "Ya Yusuf jiya ya dauke min wayata shine nima naje dakinsa na dauke nasa toh yanxu ga na sa a hannunsa ban san ya aka yi ya dauke ba, ni kuma nawa har yanxu ya ki bani" Yusuf yace "Toh me yasa ya dauke wayar ta ki?" Tace "Nima ban sani ba kuma har daki na ya shiga ya dauka, ni dai wllh ya bani waya ta xan je in gaya sa da inna" Yusuf ya kalli Mujaheed da har ya tada motarsa amma idonsa na kansu, dauke kai Yusuf yyi yace "Yaushe har ku ka fara shiri da Mujaheed da har ya shiga dakin ki ya dauke waya?" Ta turo baki tace "Ni ba wani shirin da mu ke, kawai ganinsa nayi a dakina bayan Ammi da daddy sun fita" Yusuf ya sake kallon Mujaheed da yaki driving din motarsa, ya dauke kai, Imaan tace "Ya Yusuf ka yi masa magana plss kuma fa ana kirana a wayar" Yusuf yace "Wa ke kiran ki?" Boye fuskarta tayi ta fara dariya, Yusuf ya dinga kallonta, ta xame Hijab din da ta rufe fuskarta a hankali, sai a sannan ya sauke idonsa yace "Baxa ki gaya min ba" ta wara ido tace "Ya Yusuf wani ne, he is my friend" jin Yusuf bai ce komai ba tace "Ni dai kafin su fito bari in je in gaya ma inna" daga haka ta wuce ya bi ta da ido kamar yanda Mujaheed ma ya bi ta da kallo, waje ta ga inna tana ta faman goge window with seriousness, Imaan tace "Ina kwana inna" Inna ta d'an kalleta kafin ta dauke kai tace "Aa ba wani inna ina kwana, ke din ce xa ki xo gaisheni takanas da safe, ke dai fadi abinda ya kawo ki ina ji" Imaan tace "Toh ko ba yaya bane ya dauke min wayata tun jiya ya ki bani" Kamar xata yi kuka ta kare maganar, Inna ta ajiye tsumman hannunta a bokiti da mamaki tace "Waye kuma yaya?" Imaan ta rungume hannunta xata yi kuka, inna tace "Lallai ba lafiya, shi Mujaheed din akwai wani alaka ne tsakanin ku wanda ni ban sani ba da har xai dauke maki waya? ko sata ya fara yi ba a sani ba a gidan, ni dai naga abinda ya isheni, gaskiya wannan d'a na Ahmadu yana cutar mu a gidan nan, to meye kuma xai dauke maki waya kamar shi ya siya? ko yana bin ki bashi ne? Toh a gaskiya ya kamata Mujaheed yyi aure ya kama gabansa na gaji da maganarsa kuma haka Allah ya gani nayi kokari, shekara kusan talatin da biyu ana abu daya, wannan ai fitinanne ne mara son xaman lafiya, mu je gun Ahmadu in ji ko shi ke koya masa ya dinga walakanta ni a gidan nan" daga haka inna tayi gaba imaan ta bi bayanta, Inna ta tsaya kamar warce taga mugun abu ta juyo da sauri tana kallon Imaan tace "Toh da ya dauke wayar ta ina Bulasawan ke kiran ki?" Imaan tace "Toh ba wayar na wajensa ba, kila ma ana ta kirana ya daga" Inna ta saki salati tace "Ashe yau xa a ga barbadin fitina a gidan nan, mu je gun Ahmadun" Yusuf na nan tsaye inda yake, Mujaheed kuma ya wuce kenan inna ta iso kamar xata tashi sama, Yusuf na kallonta yace "Ina kwana Inna" a fusace ta juya tana kallonsa tace "Da ban kwana ba xaka gan ni, ko a titi kake gaida uwarka Amina, to hirr dinka... Dama duk gantalallen da yace jikata xai sa ma ido ya dinga yi ma bakin ciki to yyi ta kansa inyi nawa a gidan nan, ba ruwana, kada ma ka sake gaisheni bana so, ko kuma in tsine ma gaisuwar...." Kallonta kawai Yusuf yake bai ce komai ba, Inna ta wuce kamar xata tashi sama, imaan da ta ki yarda ta kallesa ta bi bayanta, Anty na goge goge parlon Abba inna ta shiga imaan na biye da ita, Anty tana kallonta tace "Ina kwana Inna?" Inna tace "Ke ba xancen ina kwana, Amina ashe kema jaraban kika haifa ban sani ba sai jiya, ashe Isuhu ma ba mutumin kirki bane na banxa ne ni ban sani ba, ashe halinsa daya da tijararren nan Mujaheed, to Ahmadu ya ga ta kansa kuwa don wannan ba yaran nunawa bane, banda haka ta ya xa su nuna bakin ciki da hassadansu a fili kan jikata, daga Allah ya axurtata da mai kudi saurayi sabon jini sai hassada ya tashi? toh wllh su cire idanuwansu kan imaan, shi Isuhu tsabar shaharan da yayi a fannin bak'in ciki ce min yyi a bar xancen sabon saurayin ma gaba daya, ke ki ji min mugunta, kice min lalacewa bai xo duniya ba?? saboda mamakin abinda yace min sai nake tambayarsa ko idan aka bar batun sabon saurayin su xa su aureta?? Budan bakin katon sai ce min yyi to na sani ko su xa su auretan? Ke ki ji wani sa6o fa, kawai ya ja gida ya rushe da ni a ciki" Inna ta fara matsar kwalla tace "Yanxu Isuhu bai ji kunyar gaya min haka ba, idan ba ta6ewar basira ba dama ina su ina Imaan daga shi har Mujaheed din, wllh ta fi karfinsu, me garesu da har xa su rike min ita salon wataran in xo daukar gawarta ina kuka suna bani hakuri, haka kawai su kai ni su baro, yanxu fisabilillahi Allah ya dubeni ya fiddo mata dai dai ita kuma sai bakin cikin yan uwa ya tashi, to Allah ya so ni dama ba abinda na hada da su, ba dangin iya balle na baba, kawai ni dai nasan na haifi Ahmadu shi kuma ya haifesu, ni sai ince Bukar ya tattara ya bar gidan ma...." Shigowar Abba yasa ta dakata, Abba na kallonta yace "Lafiya inna?" A fusace tace "Ina fa lafiya Ahmadu isuhu da Mujaheed sun fi karfina, kawai yaro ya dage ya kwace ma yarinya waya sai kace Rukayya ce ta siya wayar, to wllh kafata kafar wayar nan yau idan ba haka ba in bar kowa da Allah, kuma gaskiya a daina bata min rai gidan nan don duk ranan da xuciya ta debeni idan ban bi Bukar Abuja ba ace bani bace" Abba dai ya kasa cewa komai, Ajiyar xuciya Anty ta sauke tace "Toh ina Mujaheed din?" Inna tace "Sai ki tambayeni Mujaheed ba tare ku ka kwana gidan nan ba ke kuma" Abba ya dau wayarsa yyi dialing number Mujaheed, Mujaheed na driving ya daga wayar, Abba yace "Where did you drop imaan's phone?" A hankali Mujaheed yace "It's with me" Abba yace "Bring it back now" daga haka Abba ya katse wayar, inna ta xauna kan kujera tana kallon Imaan tace "Xauna mu ga ta inda wayar xai fito" Imaan da ta ki yarda ta kalli Abba ko Aunty ta karasa kusa da inna ta xauna, Inna tace "Ahmadu dai bai yi sa'an 'ya ya ba gaskiya, don Mujaheed da Isuhu sai su iya kashe mutum" Anty ta ci gaba da aikin da take yi, Inna sai girgixa kafa take bayan kusan minti goma sai ga Mujaheed ya shigo parlon, Inna tace "Huuuu an dai ji kunya, fito da wayar da ka dauke" Mujaheed dai bai ko kalleta ba ya mika ma Abba wayar, Abba ya mike ya ba inna, inna ta karbe ta mika ma imaan tace "Tashi mu je, daga yau dama duk inda kika ga Mujaheed ki canza hanya da gudu don ba mutumin kirki bane" Imaan ta mike ta bi bayan inna, inna ta bude kofa tana cewa "Sai kuma ka sace wayar Rukayya idan ta ajiye ba dai na imaan"
Karfe biyar saura na yamma Sadeeq yayi parking kofar gidan su Imaan ya kashe motarsa ya jinginar da kujeran motar, Muhsin dake kallonsa yace "Ya da gyara xama kuma Doctor" Sadeeq ya shafa kansa a hankali yace "Ni fa I told you ban taba xuwa gidansu yarinyar da nake nema gun iyayenta ba, I don't even know where to start from, to idan ma na shiga me xan ce masu? All that aside, ni ban ma san me yasa ake nemana ba" Muhsin yyi dariya yace "Toh dama kuwa ina xaka je gidan su yarinyar da kake nema bayan duk turawa ne Sadeeq, kaga kawai idan baxa ka iya shiga ba mu rabu da su mu koma kada mu je ka kunyata ni gaskiya" Sadeeq ya sauke glass din idonsa yana kallon Muhsin, can yyi murmushin sa mai kyau cikin cool voice dinsa yace "In koma fa kace" Bai jira cewar Muhsin ba ya mayar da glass dinsa ya bude motar ya fita, sanye yake da kananun kaya da suka yi matukar amsan jikinsa, Muhsin ya fito motar yana kallonsa yace "Ehh lallai Abokina ya xurma da yawa" Sadeeq dai bai tanka sa ba ya gama danne danne wayarsa ya kai kunne, bayan wani lkci yyi kasa da murya yace "Abba gani a waje" Abba dake xaune parlonsa tare da Daddy yace "To madallah bari they will lead you in now" Ba a dau lkci ba Yusuf ya fito kofar gidan, Kallon Sadeeq ya dinga yi har ya isa inda suke, suka gaisa Muhsin yace "Ashe dai Engnr kana gari?" Yusuf yyi murmushi yace "Sure ina nan, ya aiki" Muhsin yace "Alhmdllh" Yusuf ya shiga da su compound din har xuwa parlon Abba, Sadeeq na shiga parlon ya cire glass yyi kasa da kai har xai xauna saman kujera sai kuma ya fasa ya xauna kasan rug ganin nan Muhsin ma ya xauna, har sannan bai dago kansa ba ya gaida su Abba da Daddy, duk suka amsa suna masa sannu da xuwa, Daddy yace "Muhsin abokin ka ne dama kenan" Muhsin yace "Ehh Abba abokina ne" Daddy ya gyada kai yace "That's good" Abba ya kalli Yusuf da ya xauna yace "Where is M.A?" Bude kofar parlon aka yi sai ga Mujaheed ya shigo parlon da sallama can ciki, kansa a kasa ya xauna kusa da Yusuf sannan ya kalli Sadeeq da idanuwansa ke kan TV, gaisawa yayi da Muhsin, sai a sannan Sadeeq ya kallesa yace "Barka da yamma" Mujaheed yace "Same to you" Abba na kallon Sadeeq yace "Can I know you plss son" Sadeeq ya sauke idonsa kasa yace "Sunana Abubakar Sadeeq Ahmad, ni haifaffen garin Kaduna ne, mahaifina asalinsa d'an kano ne, na gama karatu na and I am working as a medical practitioner now" Abba yace "Maa sha Allah, a wani anguwar ku ke?" Yace "GRA muke" Abba yace "Ohk can i know ur dad?" Sadeeq ya d'an yi Shiru kafin yace "Alhaji Ahmad sunansa, d'an kasuwa ne Abbana, yana kuma xaune nan Kaduna" Abba ya gyada kai cike da gamsuwa, bayan few seconds yace "What is ur intention toward my daughter Abubakar?" Sadeeq ya kasa dago kansa, Daga Mujaheed har Yusuf kallonsa kawai suke, can ya dago kansa a hankali yace "Abba sonta nake da aure...." Mikewa Yusuf yyi yana kallon Abban nasa yace "I want to excuse my self plss..." Abba ya gyada masa kai ya juya ya fita parlon, Abba yace "Toh naji dadin jin hakan daga gare ka Abubakar amma kasan ajin da Imaan take yanxu?" Ya gyada kai a hankali yace "Na sani Abba" Abba yace "Ohk good, wani xancen kuka yi da kakarta last time da ka xo?" Murmushi yyi ya sunkuyar da kansa, Abba yace "Yes go on" Yace "Abba ce min tayi idan tayi magana da ku xata sanar min in turo magabatana" Abba yace "Ohk, kai d'an wajen Ahmad Bulasawa ne?" Sadeeq ya gyada kai kawai, Abba yace "To yayi kyau, yanxu dai I want to ask for a favor from you Sadeeq" Sadeeq ya daga kai a hankali yana kallonsa, Abba yace "But before then bari in maka wannan alkawarin, Sadeeq in dai Imaan ta amince tana son aurenka, wato ta yarda da kai, sannan iya binciken da xanyi idan ban ga wani flaws dinka mara kyau ba ni nayi maka alkawarin xan baka Imaan in sha Allah, yea it's a promise I am making" mikewa Mujaheed yyi yana kallon Abba yace "Abba I want to pick a call" bai jira cewar Abba ba ya fita, Sadeeq dake kallon Abba yace "Toh nagode Abba" Abba yace "Toh favor da nake son ka min ynxu shine.... Kakarta nake son ka samu amma ba yau ba, but cikin satin nan, sai ka ce mata mahaifin ka bai kasar yanxu kuma xai dau lkci kafin ya dawo, yana dawowa kuwa xaka sanar masa xancen auren... Am doing this to allow my daughter finish her secondary schl, wato na da shekara daya, kasan yanda tsoffin nan suke, there is nothing da xan gaya mata da xata fahimce ni, amma kai idan kace mata haka to an gama komai, kaga ko da tana gamawa ne sai ayi magana amma yanxu kam I don't think xan iya bada ta tana ss2, that aside.... my promise of giving u my daughter's hand in marriage will count only on one condition ko da ta gama secondary schl, the condition is that xaka yarda ko bayan kun yi aure ta ci gaba da karatu a dakinta" Sadeeq ya d'an yi murmushi yace "In sha Allah Abba" Abba yace "Toh Allah ya mana xabi mafi alkhairi" Sadeeq yace "Ameen Abba na gode sosai, Allah ya kara girma" Abba yace "Allah maka albarka" daga haka Abba yace masa xai iya tafiya, nan suka yi sallama da Daddy da Abban sannan suka fita parlon. Muhsin na kallonsa yace "Mu je in gaida Mum dita" Sadeeq ya xaro ido yace "No kai dai kaje zan jira ka a waje" Muhsin yyi dariya yace "Common Mum dita fa na ce maka..." Da kyar ya ja Sadeeq suka nufi part din su imaan, Bell Muhsin ya danna, Ammi na kitchen xata fito Imaan ta bude kofar dakin ta, Wani kallo Ammi tayi mata tace "Kika san waye bakin kofar xa ki tafi a haka?" Imaan ta xaro ido ta juya ta koma ta dau Hijab dinta ta sa ta fito ta nufi kofar, bude kofar tayi, lkci daya tayi still tana kallon Sadeeq, Muhsin yace "Toh ko mu bi ta kanki" da sauri ta juya ta bar wajen, kafin su shiga parlon har ta koma dakin ta ta kulle, Dariya Muhsin yyi ya xauna, Sadeeq that was uncomfortable shi ma ya xauna, Ammi ta fito kitchen ganin Muhsin tace "Ka shigo anguwar kenan" yayi dariya yace "Ammi takanas nan fa na xo wllh" tace "Keep quiet kai din" yace "Ki tambayi abokina Ammi" Ammi ta karasa shiga cikin parlon tana murmushi tace "Toh sannun ku da xuwa" Muhsin ya gaidata, tun da Sadeeq ya kalleta sau daya bai sake yarda ya kalleta ba shi ma ya gaisheta, ta amsa da fara'a tana masu sannu da xuwa, Muhsin yace "Kawai ce masa nayi ya rakani in gaida Mum dita" Ammi tace "Toh kun kyauta kuwa nagode, sai dai abokin naka kamar d'an uwan mu ne Bafillatani" Dariya kawai Muhsin yake, Sadeeq dai yyi murmushi bai dago ba, Ammi ta tambayi Muhsin yayanta sannan ta tambayi Sadeeq iyayensa, Sadeeq yace "Duk suna lafiya lau" Ammi na kallon kofar dakin Imaan tace "Imaan" Muhsin yace "Kawai daga gani na shine ta shige daki saboda bata da gaskiya bata gaida mutane ko a waya" Dariya Ammi tayi tace "Ae ban san yanda xanyi da ita ba, ko nace tayi sai tace ta manta" Sai da Ammi ta kara kiranta ta fito da kyar, wannan karan Hijab har kasa ta sa, Ammi tace "Baxa ki gaida yayanki ba kika shige daki?" Bata yarda ta daga kanta ba har ta iso cikin parlon kamar munafuka ta xauna kasa kusa da kujera tace "Ina yini Ya Muhsin?" Yana murmushi yace "Lafiya lau Imaan, ya gida?" Tace "Lafiya lau" ta saci kallon sadeeq da yaki kallon inda take tace "Ina yini" yace "Lafiya lau" Ammi tace "Ki dauko masu ruwa fridge" mikewa tayi ta wuce kitchen, Ammi tace "Jiya mun yi waya da yaya yace gobe xai dawo" Muhsin yace "In sha Allah, haka yace min" Imaan ta shigo cikin parlon ta durkusa ta ajiye tray din ruwa da lemon five alive sai glass cups biyu, Ammi tace "Na gama girki bari in xubo maku" Muhsin yace "A'a ki bar shi kawai Ammi a koshe mu ke..." Ammi tace "Idan kai baxa ka ci ba sai abokin naka ya ci, ya sunansa ma dai?" Dariya Muhsin yyi yace "Sunan Daddy garesa" Ammi tayi murmushi tace "Ikon Allah, mai gida ne ashe" Muhsin ya kasa daina dariya, Imaan na ajiye drinks din dama ta shige daki ta kulle kofa, Ammi na shiga kitchen Sadeeq yyi kasa da murya yace "Don Allah ka rufa min asiri mu wuce Muhsin" ko kallonsa Muhsin bai yi ba ya mike ya bi bayan Ammi kitchen, har ta fara xuba masu abincin a plate yace "Ammi kinsan waye muke tare da kuwa?" Ammi ta juya tana kallonsa tace "A'a, waye?" Kasa daina dariya yyi yace "Wllh surkin ki ne, saurayin Imaan" Ammi ta saki serving spoon din hannunta tana kallon Muhsin baki sake tace "Amma baka da kirki Muhsin shine ka bar ni ina ta xuba a parlor?" Dariya kawai Muhsin yake, Ammi tace "Ni dai ba ka kyauta min ba, haba naga yaro ya ki sakin jiki, ita kuma Imaan sai na