Showing 138001 words to 141000 words out of 303099 words

Chapter 47 - Imaan Book 1 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

1639

karshensa ba..." Umma dake ta kai koma ta kinkimo babban cooler din shinkafa da nama, da wani cooler din tuwo da na miya, da na fried rice da soyayyen kaji, da na masa duk ta dire masu a gabansu tace "Ni dai na xama kadangaren bakin tulu, ba kuma wani ya haifa min Mujaheed ba balle a nuna min iko da shi, Ikon ku ya tsaya iya Bukar da Ahmadu amma banda Mujaheed, abinci kuma ga shi aje ayi ta ci ayi kashi...." Ammi dake tsaye gefe ta taho har inda Umma take tace "ke dai a kwakwalwarki hauka ya kare, ita Innar kike fada ma magana haka saboda shinkafa" dakatar da ita umma tayi ta hanyar daga mata hannu tana mata matsiyacin kallo tace "Ni ban yi da juya ba, kije can ki ji da sauran ciwon da kika haifo duniya..." Aunty ta riko Ammi ganin finciko Umma xata yi, babban Jambox Hajiya Saude ta dauka ta kunna waka ya kauraye tsakar gidan kawayen Umma suka fito aka fara taka rawa irin na manya ana jujjuyawa, Umma na ganin haka ita ma ta shige cikin masu rawa ta fara takawa tana tafe hannu, Inna ta gwalo ido sai kuma ta fashe da matsanancin kuka tace "Ni kika xaga Rukayya?? Ni din??" Ta Rasulu ta dinga bude kulolin abincin tana ball da su duk abincin ya tarwatse a kasa, tana huci tace "Don kaza kazan ki dake da abincin kun ci kaza kazan ku...." Mama Hadiza ta fito daga part din su Imaan da sauri ta tafi ta dauke jambox din da waka ke tashi ta kashe sannan ta tarwatse sa a kasa tana kunduma ma Umma xagi tace "Idan kina tunanin uwata xa ki gaya ma magana yau ki xauna lafiya kin yi karya wllh, dama can ba son auren nan Mujaheed yake ba, ke ce ke son auren saboda abun duniya, xabin ki ce yarinyar ba tasa ba, kuma wllh wllh kin ji rantsuwar musulmi koh?? To baxa a daura auren nan ba, bari Ahmad din ya shigo.... in sha Allahu sai kin ji kunya yau, sai mun kunyata ki yau...."


*Imaan isn't for free* it's 300 via


Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788



49.....


Shewa Umma tayi tana dariya tana ma Mama Hadiza wani kallo tace "Toh Sannu Uban Mujaheed.... Ahmadu, bari ki ji ko ita Mahaifiyar taku bata kai ta hana auren nan ba balle ke...." Mama Hadiza tace "Toh mu xuba da ke yau, wllh sai kin san kin yi da Inna, sai kin san kin taba uwar mu, xaman ki a gidan nan ya kare in sha Allah" Umma na ta rawa tace "Toh Ahmadu" Kujerun da aka jera a tsakar gida Inna ta dinga watsi dasu tana ball da su tana cewa "Kowa ya tafi gidan ubansa an fasa bikin, in dai da raina ni patuu baxa ayi auren nan ba, a kira min Ahmaduuuu..." Cikin daga murya ta Rasulu ma ke cewa "An fasa biki kowacce ta tattara ta koma inda ta fitoooo, Aisha ki kukkula masu shinkafar a leda su wuce, an fasa bikin...." Mama Hadiza da xuciyarta ke tafarfasa ta shiga kiran Abba da wayarta, yana dagawa tace "Ya Ahmad kana Ina? Ka dawo gida yanxun nan don Allah...." Abba yace "Lafiya?" Mama Hadiza tace "Ba lafiya ba, ka taho yanxu don Allah" bata jira cewarsa ba ta katse wayar, Yusuf da shigowarsa gidan kenan ya nufi Inna da mamaki ganin yanda take ta watsi da kujeru yace "Lafiya Inna?? me ke faruwa??" Inna ta fashe da matsanancin kuka tace "Isuhu xagi ta uwa ta uba Rukayya ta mana ni da ta Rasulu daga nace ta Rasulu taje ta amso mana abincin da xa mu raba ma bakin da ke parlona kada su tafi su ce an bar su da yunwa a bikin jikana, shkkn Rukayya ta dinga xagin ta Rasulu har ana rirriketa, da gudu Hansai ta xo ta sanar min shine na taho da sauri jin ba'asi, Toh wllh ni har xagin da ban san da shi ba a rayuwar nan sai da Rukayya ta min, har da ce min Ahmadu da Bukar kadai nake da iko da a duniyar nan, tana xagina tana xagin ta Rasulu, Aisha ta xo ta mata magana ta hada da ita, Hadiza ma ta xo yi mata magana ta hada da ita, Uwarka kadai ce munafuka wai ta xo tana ban hakuri maimakon ta taya ni kamar yanda Aisha tayi, Toh ni dai nace wllh an fasa daurin auren nan... yau dama naji labarin ita tayi masa xabin shegiyar yarinyar, to jiya a wajen casu ko gaisheni fa yarinyar bata yi ba sai kallon banxa ta min da lebbenta kamar gandan saniya" Yusuf ya kamo hannunta a hanki yace "Haba Inna, wannan ba girman ki bane, kiyi hakuri don Allah, gidan fa da baki don Allah kiyi hakuri ki bari....." buge masa hannu Inna tayi a fusace tace "Kaji min mutumin banxa ina ruwana da baki, ba suna kallo ake ci min mutunci ba sun taho sun tare min? Bakin banxa bakin hofi... To wllh kowa ya kama hanyar gidansu dama ba ruwana...." Gaba daya su Maimoon da Maryam dai na tsaye gefe sai kallon ikon Allah suke gida duk ya hautsine, kawayen umma da umma kuma basu fasa kunna Jambox suna ci gaba da taka rawa ba suna tafi, Ta rasulu ta tafi iya karfinta ta wangale gate cikin daga murya tana cewa "Ku fito ku tafi gidajen ku babu xancen biki jama'ahhh" Aunty ce ta dinga tambayar su Maimoon inda Mujaheed yake don tasan shi daya ke iya jan Inna ta bar tsakar gidan, Imaan dake tsaye sai hararan umma take, nan ko jira take ta kara gaya ma Inna magana ta rama mata, tana kallon Aunty tace "Yana can dakin Inna" Aunty tace "Yi maxa ki tafi ki kirasa kiyi sauri" Juyawa tayi ta wuce part din Inna tana rike da wayarsa har sannan, babu kowa parlon Inna duk mutanen ciki sun taho tsakar gida kallo, Ta bude kofar dakin ta shiga, Xaune ta samesa har sannan bai gama shan tea din hannunsa ba, ta hade rai tace "Yaya Aunty tace in kira ka...." Ya mata wani kallo yace "Did I ask you to announce I am here?" Turo baki tayi tace "Toh Inna ce da Baaba ta Rasulu ke fada a tsakar gida" Ya buda manyan idanuwansa yace "Fada kuma??" Ta gyada masa kai, yace "Da wa?" tace "Umma" shiru Mujaheed yyi, can ya girgixa kai ya ajiye cup din hannunsa ya mike ya fita, bin bayansa imaan tayi, Tun daga nisa Mujaheed ya tsaya ya dinga kallon crowd da aka tara a tsakar gida, ga sautin waka, ga muryar Inna, ga muryar ta Rasulu, abinda bbu dadin ji, imaan ta iso inda yake tsaye tace "Yaya kaje ka ma Inna magana" shi dai bai ce komai ba, can ya karasa wajen a hankali yana kallon Inna kafin yace komai ta rushe da kuka tace "Mujaheed wai ni yau Rukayya ta xage tass, Mujaheed ba abinda ta mance bata gaya min ba...." Yace "Toh mu je ciki a kira maki Abba yanxu, wayar na can bangaren ki" Bayani ta dinga masa tana kuka, yace "Nace mu je a kira Abba..." da haka Inna ta bisa tana kuka wiwi tana jera Allah ya isa ma umma, Ta Rasulu dai na can bakin gate tsaye ta wangale gate din tana ihun a xo a tafi gida an fasa biki, su Aunty suka dinga hada kujerun da aka tarwatsa tsakar gidan kowa dai rai ba dadi. Mujaheed ya dinga kallon Inna Bayan sun shiga parlonta, tayi kukanta mai isarta, Imaan dai na durkushe parlon ita ma tana kallonta, Inna ta hadiye kukan da take tana kallon bakin kofa ganin Tsofaffin da suka xo biki ne suka dawo mata tace "Yau naga abinda ya isheni.... ba an fasa bikin ba ku yi ta kanku ku koma gidajen 'ya yan ku mana bayin Allah...." Wata Yar tsohuwa tace "Ae bai kai ga haka ba Hajiya Asabe hakuri xa ki yi, tun da an fara abun nan a gama...." A fusace Inna tace "Toh duk ku koma tsakar gidan ku xauna a can, ni dai ba ni ke aurar da d'a ba ba ruwana, a rufe min kofa" sallama suka mata suka wuce ta mike ta kulle kofarta ta dawo tana kallon Mujaheed tace "Ka kira min Ahmadun?" Shi dai bai ce mata komai ba, a fusace tace "Wai baka ji na ne Mujaheed??" Yace "Ae sai ki saurara ki gani" tana fyace majina tace "Dama kada in kuskura in ga Bukar a parlon nan yau ba ruwana, kada ya xo min Ahmadu kawai nake bukata" Bata rufe baki ba sai ga Abba ya shigo da sallama tare da Daddy ko wannensu da wani expression yake kallonta, Inna ta tsuke fuska tace "Ni dai Ahmadu kadai na kira...." Abba ya xauna har sannan bai daina kallonta ba, Daddy dai bai ce komai ba ya xauna, sai ga Mama Hadiza ta shigo, Inna tace "A kira min Aisha da Amina ma su xo a akan idonsu aka yi komai ai" Mama Hadiza ta nemi waje ta xauna babu walwala tace "Suna xuwa" Aunty ce ta fara shigowa sannan Ammi duk suka xauna saman tabarma, Ta Rasulu ce ta shigo parlon tana kuka wiwi kamar yarinya ta wuce daki sai ga ta ta fito da 'yar jakarta tace "Asabe gidan nan ba gidan xama bane, ni tunda uwata Mai salati ta haifeni ba a ta6a min cin mutuncin da Rukayya ta min yau ba, Ina dalili ina Dan mafari ni sai yanxu wasu maganganun ke dawo min suna min ciwooo..." Mikewa Inna tayi ta rushe da kuka ta rike jakarta gamm tace "Ai babu inda xaki Ta Rasulu muna nan sai an bi mana hakkinmu....." Rungumeta ta Rasulu tayi nan suka dinga rusa kuka a tsaye, imaan ta boye fuskarta ta dinga dariya kasa kasa, Mujaheed kam sunkuyar da kansa yyi, Abba ma dai kansa na kasa, Daddy kuwa sai kallonsu yake, kuka mai isansu suka yi sannan suka saki juna, Inna ta maida jakar daki ta fito, Ta Rasulu ta xauna ta daura kafa daya kan daya ta tsuke fuska, Inna ta xauna tana kallon Abba tace "Toh Ahmadu yau dai sai ka xaba ko ni ko matarka Rukayya...." Sai a sannan Abba ya dago kai yana kallonta, Inna tayi mitsi mitsi da ido tace "Kuma aure na samu labarin xabinta ce yarinyar ba xabin Mujaheed ba don haka daurin aure ya fasu in dai ni na haife ku" Abba ya girgixa kai ya ma rasa abinda xai ce, daddy ya d'an sauke ajiyar xuciya gently yace "Amma me ya faru Inna? Meye musabbabin matsalar?" Wani kallo Inna ta jefa masa ta kankance ido tace "Dama wannan ya xama maganan ka ta farko kuma ta karshe a parlon nan, don ni ban san ma wa ya gayyato min kai ba, abinda ya faru kuwa shine yau har uwata dake kabari sai da Rukayya ta xaga a kan shegiyar shinkafa, har tana neman dunguri na, ga rawa da ta dinga yi a gabana tana min murgude murgude da kawayenta wai su fitsararrun yan tasha, daga fa mun je amso ma bakin mu da ta Rasulu shinkafa, xagi ta uwa ta uba dai yau mun sha sai godiyar Allah..." Girgixa kai kawai daddy yake yace "Ikon Allah" cikin rawar murya Inna tace "Toh ni yanxu na xuba ido in ga matsayina a wajen ku in ga matakin da xa ku dauko, ko kaffara baxan yi ba tun da Ahmadu yake ko kallon banxa bai taba ma Hadiza Uwar Rukayya ba, toh ni me na mata daga xuwa amsan shinkafan biki xata tsigaleni..." Sai kuma ta fashe da kuka mai ban tausayi tace "Me na ma Rukayya yau ta min cin mutunci wanda da wuya tabon ya goge a jikina" Ta Rasulu ta saki kukan ita ma tace "Me kuwa xa ki mata Asabe, ni ba don albarkacin ki ba nasan da yau sai 'ya yana sun turo motar sojoji an fitar da Rukayya gidan nan...." Inna ta dakatar da kukan da take da sauri tace "A'a yanxu ma bai baci ba Ta Rasulu, kira su su turo motar babu abinda ya sha min kai wacece kuma Rukayya ina ruwana da ita xata ci albarkaci na? Su kwasheta ba ruwana" Abba dai bai ce komai ba har sannan, can dai ya dau wayarsa ya shiga kiran layin umma, har ya gama ring ba a dauka ba, ya kalli Mujaheed da ke ta kallon inna yace "Tafi ka kira min uwar ka yanxu..." Mujaheed ya sunkuyar da kansa bai dai ce komai ba ya mike ya nufi kofa a sanyaye ya bude, karo ya kusa ci da umma dake labe tana sauraron komai, shi dai bai ce mata komai ba, har xai tsaya kawai yayi wucewarsa don bai ma son ransa ya kara baci, Sallama Umma tayi ta shiga parlon da lullubi kanta a kasa, Inna na ganinta ta saki salati tana tafe hannu tace "Almunafunfun kenan ku ke ga, to ai ba da gyale kika min cin mutunci a tsakar gida ba don haka sai ki cire ki ajiye a gefe a gama magana, kuma ni dai Allah ya isa rawan da kika dinga yi a gabana kina mokade mokaden maxaunai" Umma ta xauna nan kusa da kofa bata dai tanka ta ba, tana kallonsu Abba tace "Ga ni nan" Sai hararanta Mama Hadiza take, Abba na kallonta da kyau yace "Ita Innar kika xaga yau ko?" Ta Rasulu tace "Ta uwa ta uba kuwa, har ana rirriketa xata doketa, ni dai guduwa nayi na koma bakin gate, kawai 'ya yana su ji daga xuwa biki duka ya ritsa da ni" Abba na kallon Umma yace "Toh yayi kyau, ki tafi gidan ku yau, ko minti goma ban son ki kara a gidan nan...." Da sauri Inna tace "Aa baxa fa ta tafi da igiyar ka mai daraja ba tana galantoyi a titi, yanxun nan xaka datse shi ta tafi gidan nasu tsirara, sai kuma taje can ta dinga xagin uwarta mai ciwon kafa a kano..." Ta Rasulu tace "Ko ta koma wajen shafa mai shinkafa da wake a kasuwar tasha" Umma tace "Toh Alhmdllh xan tafi amma sai a barni in sallami bakina da suka xo biki ko xuwa da yamma" Inna ta mike tace "Wani biki? Bikin da aka fasa ko kuma wani daban kike nufi?" Kallonta umma tayi da sauri, Inna ta tabe baki tace "Ae babu xancen wannan auren, don baxa a ma jikana dole ba, maxa maxa a kira dangin shegun amaryar a sanar masu suyi hakuri Mujaheed yace ya fasa, in dai da raina wllh an fasa auren nan, ni ba ruwana" Abba yace "Bai kai ga haka ba Inna..." Katse da tayi tace "Ya kai har ya xarce Ahmadu" Daddy yace "Haba Inna, kananun mutane kike son ki maida mu, daurin aure nan da 'yan awanni kice a fasa???" Inna tace "Ba ruwana idan ma jarirai xan maida ku, daurin aure dai ni patuu nace bbu shi, idan kuma akwai wanda ya isa ya ja da ni to Bismillah...." Mama Hadiza sai gyada kai take don hka ya mata mugun dadi, a hankali Abba yace "Inna to bakin da suka xo daga garurruwa da dama don bikin fa? Ya xa mu yi da su?" Inna tace "Oho sai a nemi wata a daura auren da ita amma ba xabin Rukayya ba, babu kuma shegen da ya isa ya sa in canxa ra'ayi na gaskiya..." Ta Rasulu tana tabe baki tace "In har kuna son gamawa da Asabe lafiya ku bi abinda tace sau da kafa, jama'ah kuma da aka tara tunda abun kunya ku ke gudu sai a samo yarinya ko cikin 'yan uwana ne a daura auren kowa ya hutu" Inna tace "Shi kansa Mujaheed din ba son auren yake ba wllh wllh, idan kuma karya ne a kirasa a tambayesa a ji ta bakinsa, haka kawai xa a cutar min jika a masa auren dole abinda aka daina yayi tun lokacin kakata Furera...." Daddy yace "Toh gwara a kira Mujaheed din a fara jin ta bakinsa Inna...." Dakatar da shi Inna tayi tace "Ka karyata ubanka isuhu Bukar.... Kuma a kira Mujaheed din" babu Wanda yace mata komai a parlon, Umma dai tuni yan hanjinta suka kada ta fara matsar kwalla, idan aka ce an fasa auren nan da gaske ai an kasheta kenan balle ta san in sha Allahu sai anyi, cikin tsawa Inna tace "A kira Mujaheed din mana tun da karya nake" Mama Hadiza ce ta kira layin Mujaheed, yana dagawa tace "Ka taho parlon Inna yanxu" daga haka ta katse wayar, Inna dai sai girgixa kafa take, ba a dau lkci ba Mujaheed ya shigo parlon da sallama kansa a kasa, nan kusa da imaan dake xaune jikin kujera ya duka don babu waje parlon bai kuma son xama kan kujera, Inna na kallonsa tace "Tsakanin ka da Allah Mujaheed kana son auren yarinyar nan da Rukayya ke son hada ka da?" Shiru Mujaheed yyi yana kallonta, can ya saci kallon Umma dake kallonsa tana matsar kwalla, sunkuyar da kansa yayi, Inna tace "Kun ga munafuki koh??" Abba ya hade rai yace "Don't waste our time Mr Man" d'an murmushi yyi yana kallon Inna yace "Toh Inna da bana sonta ai baxan yarda da auren ba" Sake baki Mama Hadiza tayi tana kallonsa, Umma ta sauke boyayyen ajiyar xuciya, Inna ta saki salati tace "Jini ba wasa ba ni Asabe, Allah sarki Ahmadu kana cikin jarabawar ubangiji 'ya ya duk sun kwaso halin uwa...." Wani kallo Mujaheed ya dinga mata, Inna tace "Toh oho dai, da ka so yarinya da kar ka so ta duk uwasu daya ubansu daya, aure dai tunda aka xageni aka ci ma ni da aminiyata mutunci babu xancensa an fasa, sai dai duk abinda xai faru ya faru Babu kuma wanda ya isa ya canxa min ra'ayi ko waye shi kuwa, idan baku


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login