Showing 24001 words to 27000 words out of 303099 words
"Bai dawo masallaci ba, ina wuni" inna ta xauna saman kujera tace "Ina wuni kuma, dama da ban wuni ba kya gan ni Rukayya" Umma dai bata ce komai ba, Inna na kallon Imaan dake tsaye tace "Toh ai sai ki xauna mu jira ubansa koh" Imaan ta xauna kasa tana goge hawayen idonta, Abba ne ya fara shigowa parlon, yayi still ganin Inna, ta kafesa da ido tana girgixa kafa, yace "Lafiya kuwa inna?" Mujaheed dake bayan Abba har ya sako kai jin abinda Abba yace xai koma baya da sauri suka yi ido hudu da inna, da sauri cikin daga murya inna tace "Rikosa Ahmadu rikosa, abu ya lalace idan ya gudu kar ka bari ya fita, xamansa muke a nan" Abba ya juya yana kallon Mujaheed da ya wani hade rai ya fasa komawan, Abba ya karasa cikin parlon ya xauna yana kallon Imaan da ta hade kai da gwiwa sannan ya kalli Inna, Mujaheed na satan kallon Umma ya shigo ya nemi waje ya xauna a kasa, duk ya fi jin ummar tasa a kan inna, banda faduwa babu abinda gabansa ya ke, Abba yace "Me ya faru kuma inna" Inna ta kalli Umma dake tsaye tace "Toh Malama xa ki iya ba mu waje in yi sirri da d'a na koko mu koma daya parlon" Umma bata ce komai ba, Inna tace "Atoh ke kadai ce bare, nan d'a na ne da jikokina" Umma ta nufi kofa fuskar nan nata a murtuke, Mujaheed ya sauke ajiyar xuciyan samun relieve daya wato fitar Ummarsa, Inna ta mike da kanta ta rufe kofar har da sa makulli ta dawo, Abba dai sai kallonta yake, ta xauna tayi kicin kicin da fuska tace "Ahmadu daxu Imaan taje kai min abinci bayan ta ajiye ta fita ba sai wannan yaro Mujaheed ya kamata a hanya ya daddage ya kwada mata wani mahaukacin mari a fuskarta ba" tana fadin haka ta dago kan Imaan tana nuna ma Abba fuskar tace "Yanxu fisabilillahi meye wannan Ahmadu, yau ko dabba Mujaheed ya samu xai maresa haka balle d'an mutum, d'an mutum din ma 'yar kanin ubansa, to wllh ka dau mataki yanxun nan, Sam baxai yiwu ba, yarinyar da ake kaffa kaffa da ita saboda lalurorin da Allah ya saukar mata, yanxu gobe ba abun mamaki bane a ga fuskar ya salu6e wannan irin bugun da yaji, tunda ga irin yanda Allah yayi ta ko ina ba kwari sae laushi, to wllh ka san abun yi Ahmadu, shegiya nake idan na yadda" Mujaheed dai ya kasa dago kai sai kallonsa Abba yake, fuska daure Abba yace "Kai..." Ya dago da kyar, Abba yace "Uban me tayi maka ka kai hannu fuskarta?" Inna ta gyara xama ta hade girar sama da ta kasa tana kallonsa, Mujaheed yyi kasa da murya yace "Abba gani nayi an sauketa a mota daxu...." Abba ya kalli Imaan yace "Mota kuma?" Inna ta buda ido sosai tace "Mota?? Ina kika samo mota Imaan?" Imaan ta ki cewa komai ta fara hawaye, Abba yace "Baxa ki bude baki ki ma mutane magana ba, wa ya sauke ki mota Imaan?" Inna tace "A'a dakata Ahmadu kada a wani fake da an sauketa a mota a shashantar da xancen mari, kai ko daukanta aka yi a hannu aka sauketa a kofar gida bai kai katon d'an ka ya xabga mata mari har haka ba, a kan me? To an sauketa a motar, ita yarinya ce ko ba ta isa a ajiyeta a mota bane? Idan sabon saurayi tayi fa, ko dama haka xata yi ta xama ba saurayi?" Daga Abba har Mujaheed kallon inna kawai suke, ta ja tsaki tace "Wannan ai abun farin ciki ne ni dai a gu na, to da a mashin roba roba ku ka so a sauketa idan ba a mota ba, ko kuma idan tayi ta xama ba saurayi Mujaheed din ne xai aureta? Yau naga abinda ya isheni bai ishi Allah ba, kawai yaro ka tattakure ka kama yar mutane ka falle da mari ga ka mugun tantiri ko? sannan na taso takanas na kawo kara gun ubanka ya wani fake da wa ya sauketa a mota salon maganar marin ya bi iska, To Allah ya Isar mata" daga haka ta mike tana kallon Imaan tace "Tashi mu je, Allah dai ya isa" Tashi Imaan tayi ba tare da ta yarda ta kalli Abba ba inna ta ja hannunta ta nufi kofa tana cewa "Ka ci gaba da daure masa kugu wllh duk randa xuciya ya kwasheni idan ban sa k'attin anguwar nan sun tare sa a lungu sun nakada masa shegen duka na biya su ba kace ba uwata ta haifeni ba" da karfi ta rufo masu kofar bayan sun fita, Abba ya sauke ajiyar xuciya yana kallon Mujaheed, lkci daya ya hade rai yace "Does that warrant you to slap her Muhammad?" Mujaheed ya kasa cewa komai, Abba ya masa tsawa yace "Ba da kai nake ba malam?" Da kyar yace "Abba kayi hakuri, I was only trying to do what I thought was right, duk gidan nan nasan you don't tolerate yarinya ta shiga motar saurayi" Abba yace "Not to the extent of slapping her, if she proved to be stubborn why not report her to me? Kasan halin grandmother din ku, kuma kasan dole sai taje ta gaya mata" Mujaheed yace "Kayi hakuri" Abba yace "Stupid ba ni xaka ba hakuri ba, ita da ka mara da innan xaka ba hakuri, kuma kada ka sake wannan wawancin" yace "In sha Allah Abba" Abba yace "Idan ba hauka ba ma kawai ka daga hannu ka mari mace?" Shiru Mujaheed yyi, Abba yace "Tashi kaje kayi abinda na ce maka, ita kuma Imaan din xan hadu da ita" mikewa Mujaheed yyi ya kara ba Abba hakuri sannan ya fita parlon. A hanya Inna ta kalli Imaan tana washe baki tace "Ke kice saurayi me mota kika yi Imaan?" Imaan ta turo baki bata ce komai ba, Inna tace "Toh baki ce masa kakarki na nan da rai bane naga bai shigo ba, ko yaushe yace maki xai shigo gaisheni?" Imaan tace "Ni fa ba saurayi na bane, driver din gidansu kawata ne naje dubota bata da lafiya shine mamansu tace ya maido ni gida" sake baki inna tayi a sanyaye tana kallonta tace "Ba lafiya... Direba kuma?" Imaan bata ce komai ba ta shige balcony dinsu ta bude kofar parlor ta shiga sai a sannan ta kalli inna dake tsaye baki sake har sannan tace "Sai da safe" daga haka ta kulle kofar ta sa makulli. Washegari da ya kasance Friday tun da Imaan ta dawo schl take xaune balcony dinsu tana assignment dinta na maths, Ammi ta kwalo mata kira for the second time ta ajiye pen din ta amsa, Ammi tace "Idan baxa ki ci abincin ba ki shigo ki mayar min kitchen nace" Tace "Ammi fa na kusa gamawa saura biyu" Daga haka ta ci gaba da assignment din, kamar ance ta daga kai taga wata budurwa da baxata wuce shekaru ashirun da biyu ba tana tahowa, xaro ido tayi ta ajiye pen din ta mike ta fito tace "Lahh Anty Farida" murmushi kyakkyawar budurwar tayi tace "Imaan ta mance ni" Rungumeta Imaan tayi tace "Wllh ban mance ki ba Anty farida, yaya ne yanxu baya bani waya mu gaisa" Farida tace "Toh ke ba sai kice ya ba ki ba" Imaan ta tabe baki tace "Ai to yanxu babu ruwana da shi shima ba ruwansa da ni" dariya Farida tayi tace "Toh saboda me" Imaan na murmushi ta amshi ledan hannunta tace "Ae yanxu yaya ya xama mugu, wajen inna xa ki?" Farida tace "Ehh na xo layin kusa da wannan ne nace bari in shigo yau dai mu gaisa da inna" Imaan tayi dariya tace "Amma yaya yasan xa ki xo?" Farida tace "A'a bai sani ba" Imaan tace "Last time da kika xo gaida inna ai tare ku ka je da shi to me yasa yau ma baxa ki bari ku je tare ba?" Tayi murmushi tace "Na fa ce maki bai ma san na xo anguwar ba, Ammi tana ciki?" Imaan tace "Ehh tana ciki" Farida tace "Toh bari mu gaisa" daga haka ta nufi parlon Imaan na biye da ita, Da fara'a Ammi ta tarbeta tace "Kin guje mu Anty Farida" banda murmushi babu abinda take tace "Ammi karatu ne wllh, kinga yanxu ma hutu na xo" Ammi tace "Allah sarki, Allah ya bada sa'a, ya kuma bada abinda aka je nema" Farida tace "Ameen Ammi" daga haka tayi mata sallama tace "Xan je mu gaisa da inna" Ammi tace "Toh idan xa ki wuce ki biyo ta nan mu yi sallama" tace "Toh Ammi" daga haka ta mike imaan na kallon Ammi tace "Ammi ni dai xan rakata gun inna, idan na dawo xan ci abincin" Ammi tace "Ai shi kenan" tare suka fita da farida tana rike da ledan ta, farida budurwar Mujaheed ce babu wanda bai sani ba a gidan, 2 years back kafin Ummarsa ta dawo gidan farida kan xo ta gaida Ammi da Anty, idan ko xata je gaida inna dama shi xai rakata kuma ko minti biyar baya yarda su yi a parlorn kafin inna ta fara xance yake janta su fita, sosai farida ke son Imaan tun lkcn da take xuwa gidan lkcn ma bata kai haka ba, suna isa bangaren inna imaan ta bude kofar ta shiga da sallama, Maimoon da Rahma na parlon xaune tare da inna, Farida ta shiga da sallama, inna dake xaune kan tabarma ta amsa tace "Wacece wannan kuma?" Maimoon tace "Lahh Anty farida sannu da xuwa" farida tana murmushi tace "Yauwa Maimoon, ykk" durkusawa tayi kasan rug tana kallon inna tace "Ina yini Inna" Inna tace "Lafiya lau ni dai ban gane ki ba" Maimoon tace "Inna faridar ya Mujaheed ce fa" Inna tace "Ayyoo farida ce, sannu da xuwa, kai ku kawo mata ruwa da sauran ayaban nan" Imaan ta mike ta dauko mata ruwa, Inna tace "Allah sarki, da yake sau uku ya ta6a kawo ki a gurguje shi sa ban gane ki ba, ya iyayen naki?" Tana murmushi tace "Sun ce a gaida ku inna" Tace "To madallah muna amsawa, Mujaheed din ne ya kawo ki kenan?" Farida tace "A'a ni kadai na xo" Inna tace "Atoh ba dole ki xo ke kadai ba, ni ma duk yau ban gansa ba ko gaisuwar Juma'ah ma bai xo ya min ba daga na kai kararsa kan ya doki yar kanwar nan ta sa, ko ke haka yayyinki ke cutar ki?" Murmushi kawai farida tayi, Inna tace "Toh Mujaheed kam cutan nasa kannin yake, kawai daga an sauke yarinya a babban mota ya daddage ya kwada mata mari ba laifin fari balle na baki wai ashe ma gantalallen direba ne ya sauketa, to kin san sa da xuciya sai dai kiyi ta hakuri kawai, dama tun da aka haifesa na ji irin kukan da yake a asibiti nasan akwai bala'i gaba, baki ji ba duk ya cika asibitin da muryarsa ga shi wani lafcece" Imaan ta fashe da dariya har da kyakyatawa Maimoon na taya ta, Rahma dai ta6e baki kawai tayi, Farida kam sai murmushi take kanta a kasa, Inna tace "Wllh ba xancen dariya ba nasan abinda nake fada, kuma a yunwace aka haifesa, kilan dai uwar bata ci abinci ba taje haihuwarsa, mu dai haka muka koma gida na wanke sa tass, baki gansa ba jazur da shi ba yanxu da ya kode ba, ke kinga wahalar da nayi da Mujaheed wllh k'are baxai ci ba, tun fa yana tsummarsa nake wahala don sai da nayi kwana hamsin ina kai komo a kansa, to ba abinda uwar ta iya har na koma gidan mijina, daga nan kuma sai dai in kai masu ziyara duk sati, lkcn baki ga uwarsa ba yar siririya doguwa kamar dai yanda kika ga wannan yarinyar Imaan" Inna na yamutse fuska tace "gashi uwar tayi ta cika masa nono yayi ta bulbula tumbudi duk k'arni malam, duk jikokina babu wanda yyi tumbudi kamar Mujaheed, ni ne ma nace uban ya sa masa Mujaheed" Imaan dai an samu abinda ake so don har wani kwanciya kasa take don dariya, Maimoon kawarta na taya ta, Farida dai ta kasa dago kai, Rahma ta wani hade rai tana hararan Inna ko Kadan bata ga abun dariya a wajen ba, Inna ta gyara xama tace "Lkcn yana da shekara daya da wata bakwai uwar ta yayesa, shi ma fa da kyar, ai duk cikin 'ya yan Ahmadu babu wanda ya sha nono irinsa, ya tsotsi uwar ba kadan ba, ko ke baki ga bakinsa d'an tsiyot kusan a tsuke ba? Ai duk tsotso ne yaja haka, sai yaje gantalinsa ya dawo ki ji yace Nono, uwar sai ta fiddo ta basa ya sha yyi nak sannan ya mayar, ke in takaice maki da kyar kanwar uwar ta yayesa don ni dai nace baxan iya wahala ba cikin kishiyoyi, ae ko sai kinga tashin hankali gunsa, bayan an yayesa kuwa idan Mujaheed ya daga maki roban yoghurt to bai direwa sai ya kwankwade tass, ga katon ciki yanda kika san an kifa masa kwarya, Sai uban kukan banxa da shagwaba, ni dai ba komai yasa na daukesa gaban uwar ba sai ganin xai hallaka, yo hallaka mana katon yaro haka yayi fitsari a tsaye kashi a tsaye uwar sai dai ta kwashe ta rabu da shi, duk ta dau son duniya ta daura masa, Shi kuma lkcn kaninsa isuhu na cikin tsumma an haifesa wani fiyot da shi kamar kyanwa ni na ma xata bakwaini ne" Shiru Inna tayi tana kallon Imaan, can ta xaro ido tace "Auzubillahi... Ke meye haka kike yi?" Maimoon ta tsayar da dariyar da take tana kallon Imaan, da sauri ta dagota tana xaro ido tace "Me ya faru Imaan?" Farida ma ta tashi da sauri ganin yanda numfashinta ke sama, inna ta mike a rude tace "Kun ga xata ja min jalala ina xaman xamana ko, to ita nake ba labari da xata dinga dariya haka taje ta mutu a banxa a buga ni a jarida? kai ku fitar min da ita kar ace a parlo na ne, meye kuma numfashi na neman daukewa daga ina ba yarinya da ta xo gaisheni labari? Ni dai ba ruwana a kai ta gun uwarta, ni wllh ba ita nake ba labari ba" Da gudu Maimoon ta mike xata je dauko mata inhaler suka kusa cin karo da Mujaheed xai shigo parlon, ya turata yace "Baki da hankali ne" kamar xata yi kuka tace "Ya M.A Asthma din Imaan ne...." daga haka ta fita, Da sauri ya karasa yana kallon Imaan yace "What happened" inna da har ta fara matsar kwalla tace "Ka fita da ita Mujaheed idan ma asibiti ne ku tafi, wllh ba ita nake ba labari ba xata sa ni a bakin duniya ni ban ma san lkcn da ta shigo parlon ba" Mujaheed ya kalli farida da mamaki, inna tace "Ka rufa min asiri ka fita da ita Mujaheed, meye kuma dariya haka kamar mahaukaciya, ban san meye abun dariya a xance na ba" dagata Mujaheed yyi suka fita parlon, can kusa da wani flower ya xaunar da ita yana kallonta yace "Relax now" da kyar take numfashin kamar xai dauke, Maimoon ta iso kusa da su ta durkusa ta mika ma Mujaheed inhaler din, budewa yyi ya kai bakinta da sauri, bayan wani lkcn ta dinga sauke ajiyar xuciya, maimoon dai sai kallonta take cike da tausayi, Ta jingina da flowern tana ajiye numfashi a hankali hawaye na sauka idonta cikin tsarkewar murya tace "Yaya xan sha ruwa" mikewa Maimoon tayi ta tafi dauko mata ruwan da sauri, shi dai kallonta kawai yake, bayan wani lkci ta daga kai suna hada ido ta kamo hannunsa ta kwashe da dariya, ya daure fuska yace "kina da lafiya kuwa?" Tana dariya a hankali tace "Wllh yaya babu abinda inna ta mance bata gaya ma Anty farida ba yau" ya wani xaro manyan idonsa yace "Kamar me?" Imaan ta kara fashewa da dariya hawaye na sauka idonta, ya hade rai yace "Baxa ki daina wannan dariyar mahaukatan ba" ta hadiye da kyar, har wani ciwo kirjinta ke mata cike da karfin hali tace "Labarin ranan da aka haifeka har sanda aka yaye ka take bata da yanda...." Ganin yanda Mujaheed ya bude baki da idanuwa yasa ta kara kwashewa da dariya tace "Wllh yaya har da tumbudi da fitsari da kashi duk ta fada mata" Mujaheed ya kasa rufe baki, Ganin irin dariyar da take ya sauke boyayyen ajiyar xuciya yace "Toh dariyar ya ishe ki haka" Mikewa yyi fuska daure xai koma part din Inna ya hangota tana tahowa da gudu, tsayawa yyi har ta iso yace "Gaskiya Hajiya ki daina abinda kike yi a gidan nan, ke dai magana magana magana baya kare maki, wanda ya kamata da wanda bai kamata ba haba don Allah, ni bana son irin wannan abun, ki shekara kina bada labarin kowa amma banda nawa, ba ruwanki da rayuwata da yanda aka haifeni ke kenan kowa kice xaki ba labari baki san bako ba, kawai ke dai kiyi ta magana babu naxari haba don Allah" sake baki tayi tana kallonsa, mikewa Imaan tayi tana hadiye dariyarta sum sum xata bar wajen inna tace "Ke dai wannan 'ya ta Bukar anyi munafuka wllh, to da kika gaya masa dukana xai yi ko ko, ina ce yarinyar da xai aura ce, kuma laifi ne don na bata labarinsa? Me yasa ban samu masu gadi na basu labarin ba? Saboda bai shafesu ba, komai fa da ku ke gani a rayuwar nan kamawa yake, yarinya ta xo gaisheni sai in xauna muna kallon kallo da ita??" Imaan ta turo baki tace "Ba wani nan, yaya har ce mata ta yi da yunwa aka haifo ka duniya kana ta ihu a asibiti, kuma saboda shan nono bakin ka ya xama d'an karami haka, wai sai kaje yawo ka dawo