Showing 54001 words to 57000 words out of 303099 words
fita parlorn ko da wasa bata fadi ma Ammi abinda ya faru daxu ba, part din su Maimoon ta nufa, kasa shiga parlon tayi ganin mutane a ciki, ta fi minti biyar tsaye bakin kofar taji muryar Yusuf yace "Me kike yi nan Imaan" kallonsa tayi tace "Toh akwai mutane a parlon ta ya xan shiga" tana magana tana kallon Mujaheed da ya wani hade rai don tare da Yusuf suke, dauke kai tayi bata son tayi dariya, can ta turo baki ta bar bakin kofar ya shiga ciki, Yusuf yace "Toh ko in maki jagora?" Dariya tayi tace "Daddy na yana parlon Abba?" Yusuf yace "Eh mana" tace "Toh oya ka shiga gaba sai in bi ka a baya" a haka suka shiga parlon tana boyewa a bayansa wanda hakan yasa few kawayen Umma dake parlon suka dinga kallonta har suka shiga parlon Abba. Da gudu ta tafi ta rungume daddy tace "Daddy sannu da dawowa" Daddy yace "Baki gaida Abba ba" kallon Abba dake kallonta tayi, ta boye fuskarta tace "Ina yini abba" yyi murmushi yace "Lafiya lau daughter" Daddy yace "Toh baki gaida yayanki ba shi ma" ta kalli Mujaheed dake parlon tace "Ai mun hadu a waje" Daddy yace "Toh maa sha Allah" Tace "Daddy baxan je gombe Hutu ba tunda mun yi holiday?" Abba yace "Wajen wa a gombe" murmushi Daddy yayi yace "Kanwar mamarta" Abba yace "Ohk If I recalled well last holiday ma can kika je ko" Kai ta gyada masa, Abba yace "Kuma babu canji, ga gwaggon ku Suleja ma ba sai ki je can ba ko da su Maimoon, dama bata da lafiya" Daddy yace "Gaskiya ne ya kamata" Imaan ta xaro ido tace "Kauye?" Abba yace "Of course, you will have more experience.... Shi kauyen ba wuri bane" Ta dauke kai bata ce komai ba ta cinno baki gaba, Abba yace "Nasan inna xata ji dadi idan taji xa ku je, kinga sae Mujaheed ya kai ku a mota tunda ya sha xuwa tare da mu" Da sauri Mujaheed ya kallesa yace "Abba... ai ba lalle xan gane wajen ba fa" Abba ya kallesa yace "Last time ma ba kai ka kai mu a mota ba" da kyar yace "Abba kusan shekara daya fa" mikewa Imaan tayi ba tare da ta kallesu ba tace "Xan je ina taya Ammi aiki" bata jira cewarsa ba ta fice, Abba yayi dariya yace "On a serious note dole su je riga suyi hutu bari dai a gama bikin nan lafiya" mikewa Mujaheed yyi yace "Xan je ana kirana can waje" daga haka ya fice a parlon, Daddy ya gyada kai yana murmushi yace "Su masu wayo wai, gaskiya ne ya kamata su kai ma Hansatu ziyara tunda gashi bata samu xuwa biki ba ba lafiya" Abba yace "In sha Allah I will see to that on Tuesday if everything is settled" Daddy yace "Alhmdllh, Allah ya kai mu lafiya" Washegari Friday bayan an sakko juma'ah aka daura auren Seeyama da angonta Abdul, throughout shagalgulan da ake a gidan imaan na dakinta tana bacci ko ankon bikin bata sa ba, Ammi bata takurata ta shiga jama'a ba sanin cewar bata wani jin dadi, kuma dama bata son tayi stressing kanta ta jogana masu wani ciwon, sai dab da xa a tafi da Amarya Ammi ta tasheta don tun daxu Inna ke cigiyarta, sai a sannan imaan ta shiga bayi tayi wanka ta wanke baki ta fito ta shirya cikin daya daga ankon da suka yi, ta d'an shafa powder tasa eye pencil da chappette, sannan ta dau farin hijab har kasa ta saka ta dau wayarta, ganin missed call ta tsaya ta duba, Sadeeq ne ya kirata, komawa tayi ta xauna tayi dialing, katsewa yyi ya kirata, bayan sun gaisa yace "Ina kika shiga yau" tayi murmushi tace "Bacci" yace "Uhm baki da damuwa, ya su mama?" Tace "Alhmdllh" yace "Daxu Mariya tace min kuna biki gidanku" tace "Ehh haka ne" yace "Shine ba gayyata?" Tace "Uhmm" yace "Toh kin kyauta" a hankali tace "Kayi hakuri, next time" yace "Toh waye next din auren? Ko ke?" Ta xaro ido sai kuma tayi dariya tace "Ni kuma, yar yarinya da ni" yace "Haba?" Tace "Ehh mana" yace "How old are you?" Ta langwabar da kai tace "Na kusa 19 soon" dariya yayi yace "Ehh gaskiya ne, ke yarinya ce sosai ma" tace "Toh kaga" yace "Ko aure aka maki yanxu ma baxa ki haihu ba ai" ta xaro ido sai dai bata ce komai ba tayi murmushi, yace "Yeahh" tace "Xa mu je raka Aunt dina dakinta yanxu" yace "Wani anguwa ne?" Tace "Ban sani ba dai" yace "Toh idan kun je gidan ki kirani" tace "Toh in sha Allah" sallama yayi mata ya katse wayar. Inna ce tsaye tsakar gida ta cakare cikin atamfa England an mata dinkin su irin na tsoffi, ga katon gyalenta ta yafa, ga mutane duk ana ta shirin xa a wuce da seeyama gidanta, motocin dake compound din sun fi shidda duk na daukan yan kai amarya, tun daga nisa Imaan ke jiyo Inna ta tana cewa "Naga abinda ya isheni bai ishi Allah ba, duk an wani yi cirko cirko a gaban motoci ku ja baya mana kar ku gurje masu dukiya in shiga uku, ni wllh saboda bala'in mata ma duk xafi ya isheni abu kamar maita dai, ke Maimuna ba ca nayi ki dubo min Imaan ba ko har yanxu jinin bai dauke ba ne, duk yau ban ganta cikin jama'ah ba ko bakin ciki take ma yar uwartata ban sani ba" Imaan ta turo baki bayan sun hada ido da Innar, inna ta ja tsaki tace "Kai ni dai ko limamin babban masallacin Habuja ne Bukar yau dai baxai hanaki sa gyale ba, duk yan uwanki ga su fess cikin gyale ke ko kin maka hijabi uwa xamu je xaman makoki ba amarya xa mu kai ba haba imaan, ni dai na gaji da maganar ki a gidan nan" Imaan ta dauke kai har ta iso gun motar, wata kawar Umma ce ta xo tayi announcing wai Umma tace wasu su fara tafiya kafin a fito da amarya, nan aka fara kokarin shiga motoci, inna ta bude baki ta gwalo ido ganin wata katuwa cikin shiga ta alfarma da gwalagwalai na kokarin shiga daya daga motocin, cikin daga murya tace "Wayyo meye wannan kuma... Kee don Allah ki bar sirara su shiga, banda neman magana da tsokanar fada ina xa a dake a haka, kisa kike son yi cikin motar fisabillahi, wannan ai sai dai idan ke kadai xa aje a ajiye a dawo to ina kuma hakan xai yiwu tunda motar ba taki bace, fito don Allah mutane su shiga" Imaan ta boye fuskarta da Hijab kar tayi dariya, mutanen wajen wasu sai dariya suke kasa kasa, matar ta fito kamar warce ruwa ya cinye kanta a kasa, inna ta karasa kusa da ita tana kallonta tace "Haba baiwar Allah... ke ba kya tsoron Allah ne wannan abu haka kinyi wani bake bake bayan motar mutane, ina kike son a xuba sauran jama'a, ko ke baki ga irin ki bane" Wata mata ta karaso kusa da Inna tayi kasa da murya tace "Hajiya babban kawar uwar amaryar ce fa" inna ta bude baki tace "Babban kawar uwar amarya kuma sai a sa mata ido ta latse hanjin 'ya yan mutane a bayan mota, dama kisan kai ya kawota ba biki ba, wannan abu kamar giwa kice ta shiga mota, amma bakya tsoron Allah wllh" sum sum matar ta bar wajen, Inna ta ja tsaki tace "Kai sirara su shiga a wuce, ba ruwana a aje a tatse hanjin mutane daga kai amarya ace bikin jikata ga abinda ya faru, to banda gwalagwalan ma duk karya ne ya xa ayi kamar ta ace bata da mota, ke kuma imaan ga motar da xa mu shiga can da Seeyama nace ban son tukin kowa sai na Mujaheed haka kawai mahaukatan abokan angon su ja mu su watsar da mu a rami" Bude motar Imaan tayi ta shiga back seat tana murmushi, Maimoon xata shiga inna tace "Toh ina kuma wancan figaggiyar xata shiga ni patuu, ba ga motoci can ba" Maimoon ta sauka da sauri, Imaan ta dinga dariya har da kyakyatawa, Kamar yanda inna tace Mujaheed ne ya ja su, ita, Seeyama da kawayenta biyu sai Imaan, suna hawa main road inna tace "Toh yau dai Seeyama gashi xa mu kai ki dakin ki, duk da dai mijin naki wani ga6o ga6o ne kiyi masa biyayya iya yanda xa ki iya, ni baxan ce kiyi hakuri yaje ya kashe mana ke ba gaskiya, bbu xancen xaman hakuri, mu dai da aka cuta da hakan aje a haka, amma duk kika ga abinda baxa ki iya dauka ba yafa gyalenki ki dawo gida, ko ki tafi sashin ubanki ko ki tafi sashin kaninsa ko kuma ki yo sashina sai iya Inda karfin mu ya kare na kwatar maki hakkin ki, ni fa tun daga lefen da ya hada maki dama na raina masa aji...." Mujaheed da takaici ya ishesa yace "Haba inna yanxu fada kike mata ko hudubar tsiya?" Inna ta hade rai tace "Ka ji min yaro da aka haifa ina tsaye bakin kofar asibiti daga safe har dare, kai xaka koya min xaman duniya Mujaheed, ko ance maka ban san abinda nake bane, to bari kaji ko kai yau aka daura ma aure iyakar abinda xan gaya ma matar kenan don ni yar gaskiya ce, akan me xa ayi ta wani ce ma mace tayi hakuri gidan miji ana cutarta ana musguna mata, Allah kadai yasan me yasa ya halitto ni a mutan da ba na yanxu ba, kuma ai bance kada tayi masa biyayya ba kawai idan taga xai takata ta gudo gida, ina laifin wannan shawara tawa??" Kawayen Seeyama dai sai kallon inna suke k'asa k'asa, inna ta ja tsaki tace "Tun da shaidan duk na makale gefen xuciyar ku ba dole kaji haushin abinda na fada ba, maxa dai sun xama masifa yanxu, duk halinku daya dama, yo banda halinku daya ya wuce idan yace xai walakanta maka kanwa ka matse gantalalle ka nakada masa duka tunda ga irin sa kamar tsinken sakace, wllh xaka iya dukansa" Seeyama dake hawaye cikin gyalenta ta fashe da dariya, imaan na taya ta, shi dai Mujaheed bai ce komai ba yana mamakin warce Allah ya basu matsayin kaka.....
*The book Imaan is not free, you read for free ur cup of coffee wllh*🤷🏻♀️
It's 300 via Fcmb 3276052019
Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp digit 07087865788 to be included in the payment group.
18....
Suna isa gidan bakin inna ya mutu murus sai 'yan idanuwa ganin gida ne ba na wasa ba, ni ko nace dama Umma ce xata yarda 'yar ta ta auri mai rufin asiri kawai?? Inna ta fito cikin motar tana cewa "Fito da kafar ki ta dama in sha Allah gidan xama ne, yi nayi bari na bari, aure kuma da kike gani d'an xaman hakuri ne duk shi muka yi muka kawo yanxu da rai da lafiya, Allah ya maki albarka yasa gidan ki ne ke kadai don na xauna da kishiyoyi ban ji da dadi ba, kishiya masifa ce" Wani kallo Mujaheed ya dinga mata, inna na washe hakora tana kara kallon katon gidan tace "Toh kai Mujaheed baka da abinda xaka ce mata ne ka tsaya wani sandandan kana kallonmu, wannan ai ya ma fi gidanka girma wllh" Yace "Kece baki mata nasihar tun a gida ba amma ni nayi tun a can" Kuka kawai Seeyama take, inna ta hade rau tace "Ji shashanci don Allah, to ki bude ido ki ga gidan mana idan ba sae kin daina shegen kukan nan ba" Mujaheed ya karasa kusa da ita yana kallonta yace "Be the best wife you can be lil sis, wishing you a peaceful married life" rungumesa tayi tana kuka, shi ko ya dinga kallon imaan da ta ja can gefe tana 6a66aka dariya har da rike ciki, ganin kallon da yake mata ta shige cikin gidan da sauri bata kuma fasa dariyar ba, cike da damuwa Inna tace "Ni dai wllh wannan 'ya ta Bukar gani nake kamar ciwace ciwacen ta ya shafi kwakwalwarta, to banda haka taya xa a kawo yar uwarki dakinta tana kuka, ke baki bata hakuri ba kina dariyar mugunta, to Allah dai ya kai mu naki kiga iskanci wllh" tana fadin haka ta janye seeyama tace "Mu shiga ciki kiyi kukan a tsanake kin ji jikalle, kai kuma Mujaheed bayan isha ka xo ka daukeni, idan kuma ya kama a nan xan kwana to shikenan" daga haka suka wuce ciki shi kuma ya fita compound din da motarsa yana girgixa kai. Bayan Magrib da rashin arxiki inna ta sallami duk kawayen Umma yan kawo amarya, Aunty da Ammi dama basu dade ba suka bar gidan, tsaye inna tayi bakin kofa rai bace tana cewa "Wannan ai ba yi bane, sai kace baku da maxaje baku da mafada, amarya dai ga ta an kawota lafiya har ta hakura ta daina kuka, to ai kuma sai kowa ya kama hanyar gidansa sai kuma wata shekarar idan ta haihu, amma duk kun wani ja6e ba niyyar tafiya, a dai dinga jin tsoron, ni ma nan da ku ka ga ban tafi ba kakar ta ce, ni na haifi ubanta Ahmadu, bai baci ba ko da cewa nayi xan kwana, amma mutane karere kawai ku cika gidan yarinya kun ki tafiya, ko ita Rukayyar ce tace ku kwana tare da su bani da labari? To ni dai ba ruwana" Wa enda suka fita iskanci yi suka yi kamar basu ji abinda take cewa ba, wasu kuma haushi yasa duk suka bar gidan, a fusace inna tace "Mata wasu katangala kawai rai ba ga ta sun xaune ma yarinya a gida, ni ban taba ganin haka ba tunda uwata ta haifeni, ku barta daga ita sai kawayenta su ma a xo a sallamesu su kama gabansu mana" Inna na kallon imaan dake kokarin fita ta gefenta tace "Ke kuma ina xaki sanyi ya kare maki ki cuci d'a na da kashe kudi?" Imaan ta turo baki tace "Ina xuwa ni dai" inna tace "Toh kar dai kiyi nisa don Mujaheed ya kusa xuwa yanxu, ba ruwana in kwana su Ahmadu su min fada" imaan bata ce komai ba ta fita, tana ganin motarsa ta gane don layin tamkar rana saboda hasken fitilu, ta karasa gun motar ya bude ya fito yana kallonta, Ta sunkuyar da kai tace "Ina yini" yace "Lafiya lau Imaan, nan ne gidan sistern naki?" Kai ta gyada masa, yace "Maa sha Allah, Allah ya basu zaman lafiya" tace "Ameen" yace "Amma ba nan xaki kwana ba dai koh?" Ta xaro ido tace "In kwana kuma?" Murmushi yyi ya rungume hannu sa yace "Shi na gani ai, Idan kika kwana ai xaki yi inconveniencing amarya da angon" turo baki tayi tace "Toh ni dama ta ya xan kwana" yar dariya yayi yace "Gaskiya ne, yaushe xa ku koma gida?" Tace "Muna jiran yaya ne, xai maida ni da Maimoon da Grandma dinmu" yace "Ohk yayanku kenan" ta gyada masa kai, yace "Idan bai taho ba let me drop you people mana" ta xaro ido tace "Bayan ma yana hanya yanxu, ai shi ya kawo mu" Yace "Ohk then...." Bata kuma cewa komai ba, shi kam yyi shiru yana kallonta, a hankali yace "Kin yi kyau" Dauke kai tayi tana murmushi, shi dai bai fasa kallonta ba, murya can ciki tace "Kai kuma baka sa glasses dinka yau ba" wara ido yyi yace "Ya 6ata.... sai dai ki siya min wani" ta kallesa tace "Da gaske?" Yana murmushin sa mai kyau yace "Yea" Sunkuyar da kanta tayi, yace "Ko baxa ki siya min ba" Ta d'an kallesa tace "Xan siya" yace "Toh yaushe xan xo amsa?" Tace "Idan na siya" yace "Toh gobe nake so, I can't do without it" da sauri ta kallesa sai kuma ta dauke kai tana murmushi tace "Toh Allah ya kai mu" yace "Ameen... Da yamma xan xo amsa" ta girgixa kai tace "A'a kawai ka bar shi next tomorrow" Shiru yyi yana kallon bayanta.... Can yace "Or wancan ne yayan naku?" Imaan ta juya da sauri taga motar Mujaheed yayi parking, ta gyada masa kai a hankali, tunda Mujaheed yyi parking d'an nesa da su dama yake kallonsu, Sadeeq yace "Tunda ya gan mu bari in je mu gaisa" shiru tayi da farko, ganin yanda yake kallonta a hankali tace "Is it necessary?" Yayi murmushi yace "Baki son yan gidanku su san ni kenan?" D'an bude ido tayi tace "Toh kaje ku gaisa ni xan shiga ciki in kira su Maimoon" yace "Ohk" gate ta nufa tana satan kallon Mujaheed da ya bi ta da kallo gabanta na faduwa, Sadeeq kuma ya nufesa, sauke glass Mujaheed yyi ya bude motar ganin sadeeq, ya fito yana kallonsa directly cikin ido, sadeeq ya masa sallama hade da mika masa hannu, sai bayan kusan seconds biyar Mujaheed ya mika masa nasa yana d'an murmushi wanda iyakarsa lips, nan suka gaisa... Cikin cool voice Sadeeq yace "I am Dr Abubakar Ahmad" Mujaheed ya gyada masa kai kamar baxae ce komai ba, sai kuma yace "Muhammad Ahmad" Sadeeq yace "Maa sha Allah it's nice meeting you" Mujaheed yace "Same" Sadeeq yace "Alryt xan koma, sae da safe" Mujaheed yace "Ohk... kun yi sallama ne" Sadeeq yace "Sure" daga haka ya nufi motarsa ya shiga ya wuce. Inna bata fito parlon Seeyama ba sai da ta kada kan sauran mutanen dake parlorn, har Mujaheed ya gaji da jira cikin mota, Inna ta fito gate tare da Maimoon da Imaan ta shiga bayan mota tana cewa "Mujaheed kaga Gantalallu kila da so suka yi su kwana a gidan, don da ban masu jan ido ba baxa su tafi ba, ni dai ba ruwana" Maimoon ta bude front seat ta shiga, imaan ta shiga back seat gun inna, Mujaheed dai bai kulata