Showing 252001 words to 255000 words out of 303099 words

Chapter 85 - Imaan Book 1 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

1616

ta fito hada mata breakfast, Har lkcn Mujaheed na parlor tare da Dr Khaleel da bai gajiya da labari, shi dai gaba daya hankalinsa yyi kan Imaan sanin bata yi breakfast ba har lkcn, Farida tayi murmushi tana kallonsu tace "Sannun ku da hutawa" Mujaheed na kallonta yace "You tell imaan lkci ya wuce fa, this is after 12" Farida tace "Haba nan da bayan azahar ba sai ku wuce ba Dr, ni ban gaji da ganin kanwata ba, kayi wucewarka kawai anjima xa mu maida ta gida...." Dr Khaleel na kallon Mujaheed yace "Ba yini ku ka xo yi mana ba dama Dr?" Mujaheed yyi murmushi yace "Xa mu yi bak'i ne daga kaduna, suna ma hanya yanxu" Farida dai bata tanka sa ba ta shiga kitchen, eggs ta soya ma Imaan, ta hada mata shayi mai kauri, ta debar mata pepper soup din da tayi da safe sannan ta dau bread duk ta daura su kan tray ta fito kitchen din, ganin abinda ke hannun Farida hankalin Mujaheed ya kwanta don shi damuwarsa kenan dama, daki Farida ta kai mata abincin ta ajiye saman carpet, Imaan ta sakko kasa, Farida tace "Bari inje in daura white rice, nayi stew daxu da safe" Imaan tace "Toh" daga haka Farida ta fita dakin, a hankali Imaan ke shan shayin hannunta, da ta tuna wasu daga abubuwan da Farida ta gaya mata sai tayi murmushi ita kadai, wani kuma ta turo baki, wani kuma idan ta tuna a ranta tace tabdi, da tuna wai Safeenah xata iya kwace Yaya ya daina kulata sai ta hade rai, shayi kadai ta shanye cikin abubuwan da Farida ta kawo mata, sannan ta mike ta dau tray din ta fita don kai wa kitchen, tunda ta fito Mujaheed ke kallonta, suna hada ido ta sunkuyar da kai ta karasa cikin kitchen din ta ajiye tray din, Farida dake wanke wanke tace "Toh baki ci egg din da yawa ba ai Imaan" Imaan tace "Aunty na koshi wllh" Farida tace "Toh nasan Mujaheed xai ce xa ku wuce yanxu, ki tafi daki ki harhada duk abinda na baki a leda, kin xo da jaka ai?" Imaan ta girgixa mata kai, Farida tace "Ohk toh ki tafi dakin ina xuwa yanxu" Imaan na fitowa parlor suka kara hada ido da Mujaheed da ya mike tare da mijin Farida xa su wuce masallaci don lkcin sllh yayi, Yana kallonta yace "After prayer xa mu wuce" ba tare da ta kallesa ba tace "Toh" sannan ta wuce ciki, ba a dau lkci ba Farida ta shigo dakin, daya daga sabbin jakanta na aure ta ciro ta kwashe gaba daya kayan da ta debar ma Imaan ta xuba a ciki tace "Hope you remember all what I said??" a hankali Imaan ta gyada mata kai, Farida tace "In sha Allah may be next tomorrow xan xo gidan naku kin ji?" Imaan ta marairaice tace "Aunty me yasa baxa ki xo gobe ba?" Farida tayi murmushi tace "A'a gwara dai jibin, in sha Allah xan xo kanwata" Imaan tace "Toh Allah ya kai mu, Aunty ban xo da Hijabs dina daga gida ba, did you have hijab to give me in dinga sllh da shi, am having just this one I am wearing" Farida tace "Ohk" mikewa tayi ta bude daya daga akwatunanta ta fiddo sabon hijab a leda tace "Sai dai bai kai kasa ba nasan ke har kasa kike sa wa" Imaan tayi murmushi tace "Nagode Aunty bari in yi sllh kafin ya dawo...." daga haka ta mike ta shiga bayi don dauro alwala. Sai karfe daya Imaan suka bar gidansu Farida bayan Farida da mijinta sun rakosu har bakin mota, a back seat Imaan ta ajiye warmer din abincin da Farida ta tilasta mata sai ta tafi da shi sannan ta bude front seat ta shiga, Mujaheed ya kara sallama da Dr khaleel ya ja motar, Imaan na daga ma Farida hannu, sai da suka hau saman titi ya kalli jakar hannunta yace "Jakar meye Wannan?" Ta turo baki tace "Ta bani kyauta ne, ta ga ban xo da jaka ba" murmushi yayi bai ce komai ba, bayan few minutes yace "Idan kika gama haifa min yara na sai in maki lefen ki ko?" ko kallonsa bata yi ba ita dai tana rungume da jakar hannunta don Farida tace mata kada ta yarda ya ga abinda ke ciki, Sai da suka kusan gida Mujaheed yace "Ammi fa tana gida, ta xo" Imaan ta kallesa da sauri tace "Ammi?? Da gaske Yaya?" Yace "Ehh" murna ta fara yi kamar yar yarinya a motar, ganin murmushin da yake ta dakatar da murnar ta marairaice tace "Don Allah Yaya kace min wllh don ni ban yadda ba, kila ba da gaske kake ba" shi dai murmushi kawai yake, lkci daya ta daure fuska, yace "Toh Ammi baxa ta iya xuwa ganin ki ba kenan" turo baki tayi tace "Nasan Ammina baxa ta iya xuwa ba" yace "Why?" Tace "Ni dai nasan she can't" yace "Toh idan muka je kika ganta me xan maki?" Ta kallesa da sauri sai kuma tayi murmushi tace "Idan muka je naga da gaske ta xo xan baka dubu goma" ya gyada kai still smiling yace "Idan kuma ba mu ganta ba fa?" Ta turo baki tace "Sai ka siya min waya" ya wara ido yace "Uhn???" Tace "Ehh" yyi murmushi yace "Toh ban yadda ba dubu goma da kika ce yyi kadan" tace "Toh me xan baka?" Ya shafa kansa yace "Dubu goma with kiss and hug" Ta wara ido, sai kuma ta rufe fuska tace "Toh naji" yace "Kin ji kika ce fa?" A hankali tace "Ehh" Yana murmushi yace "In dai muka je muka ga yan gida ai duk daya ne koh?" Ta girgixa kai da sauri tace "Noo, ni dai Ammina nace" parking yyi kofar gida ya kashe motar ya sauka ita ma ta fito tana rike da jakarta, ta bude back seat ta dau warmer din abinci bata ko kalli takeaways da yyi masu da safe ba ta nufi gate, shi ya kwashe ledojin ya rufe motar sannan ya bi bayanta, still Imaan tayi ganin motar gidansu a compound din, ta juya ta kalli Mujaheed dake tahowa yana murmushi, lkci daya ta nufi cikin gidan da sauri ta bude kofa, sai kuma ta tsaya tana kallon Mama Hadixa da Inna dake parlon, Mujaheed ya bude kofar shi ma ya shigo, imaan ta ajiye warmer din hannunta ta nufi Mama Hadixa dake murmushi ta fada jikinta cike da farin ciki tace "Oyoyo Mama, yaushe ku ka xo" Mama Hadiza ta rungumeta tace "Daga ina ku ke?" Imaan na washe baki tace "Mun fita ne Mama, yaya ya kai ni gun Aunty Farida, kin tuna ta?" Mama Hadiza tace "Nan take aure ita ma?" Imaan ta gyada kai tana murmushi tace "Ehh Mama" Mama Hadiza tace "Maa sha Allah, amma kina cin abinci kuwa daughter naga kin rame" Imaan ta sunkuyar da kanta tana murmushi, ita dai Inna na xaune fuska a murtuke ta kura ma Tv ido, Mujaheed na murmushi ya karasa parlon ya ajiye ledan hannunsa ya xauna kusa da ita ya mata side hug yace "Nasan dai wajena kika xo koh inna?" Inna tace "Toh dama wajen wa xan xo idan ba kai ba Mujaheed, ga damun nama can cikin cooler na maka" Dariya ya fara yi yana kallonta, Imaan ta daga kai daga kwance da tayi jikin Mama Hadiza ta kalli Inna, mikewa tayi ta dawo kusa da ita tana murmushi, cike da masifa Inna tace "Don Allah yar nan ki rufa min asiri ki ja baya ba wajen ki na xo ba Allah shaida...." Mama Hadiza ta dauke kai tana dariya, Imaan ta turo baki xata bar wajen Mujaheed ya rikota yana dariya shi ma yace "Inna Imaan ce fa ko baki ganeta bane" Inna tace "Wacece kuma Imaan??" Dariya kawai Mama Hadiza da Mujaheed ke yi, Imaan xata bar wajen Mujaheed ya rikota ya xaunar da ita gefensa, rufe fuskarta tayi jikinsa da sauri ta fara kuka, Mujaheed ya d'an kalli Mama Hadiza dake dariya har lkcn, murya can kasa yace ma Inna "Tunda kuka kika xo sa min matata, tashi ku yi wucewar ku mun yafe xuwan" Inna tayi kamar bata ji sa ba fuska a murtuke, Mama Hadiza tace "Babu kowa gidan ne? Ina ce kace min Safeenah ta dawo" Mujaheed ya kalli sama yace "She is home, bata fito bane?" Inna tace "Au kana nufin tana ciki??? Toh xan hau sama wannan mata Hadiza ta hanani, wai gidan mutane" mikewa Mujaheed yyi ya wuce sama imaan ta bi sa da kallo, Inna na kallonta tace "Toh bbu abinci gidan Mujaheed din ne kika rafke haka?" Imaan ta hade rai ta dauke kai, Mama Hadiza tace "Debo ruwa kitchen in wanke ma Inna garden eggs dinta" mikewa Imaan tayi ta dau ledan garden eggs din dake ajiye kusa da babban trolley na kayanta da Mama Hadiza ta taho mata da shi ta wuce kitchen tana kallon hanyar stairs, Inna ta kalli Mama Hadiza tace "Wllh duk ta rame, kin ga abinda nake ta gudu kenan koh, dama duka duka imaan din nawa take xa a ba katon nan? Ni dai ba ruwana wllh" Mama Hadiza tace "Rashin kwantar da hankali ne da damuwa fa Inna, da alama kuma ta fara hakura" Inna ta tabe baki tace "Ni dai ba ruwana" Har Imaan ta gama wanke garden eggs din ta xuba su a bowl ta dawo Mujaheed bai fito parlor ba, sai kallon stairs take, Inna tace "Ko yar mantina bbu gidan ne, daga kaduna fa muke" Mama Hadiza ta saci kallonta bata dai ce komai ba. Mujaheed na tsaye dakin Safeenah dake kwance saman gado fuska daure tana taunar cingam, kana ganin idanuwanta kasan kuka ba na wasa ba ta ci, yana kallonta yace "You are looking into my face and telling me baxa ki sauko ki gaida iyayena ba Safeenah??" A mugun fusace ta mike xaune tace "Ehh, ko dole ne Mujaheed? Don Allah ka rabu da ni ka fita, ni dai abinda na sani duk wanda ya shiga hakkina a gidan nan Allah ya isa, kuma matakin da xan dauka wllh sae ya girgixa kowa, ni gaida iyayena kake da xan gaida naka" da mamaki ya dinga kallonta, trying hard to control himself, can ya juya ya fice daga dakin ta bi sa da wani mugun harara tana kas kas da chewing gum, yana sakkowa downstairs Imaan ta wani hade rai tana cin garden egg din Inna da ta dauka, Inna na kallonsa tace "Safara'un bata nan ne...." Imaan ta cafke tace "Tana daki" Inna ta xaro ido tace "Tana daki??? Duk uban sallama da bubbuge bubbugen kofar da na dinga yi tana ji ta min shiru??" mikewa Inna tayi ta wuce sama, Mama Hadiza tace "Don Allah Inna ki bari ki dawo ki xauna, ni bana son hka" ko sauraronta Inna bata yi ba, Mujaheed dai ya bi ta da kallo haka ma Imaan da taji mugun dadi har ranta, Inna ta bude dakin farko da ta gani sai ga Safeenah kwance saman gado waya kare kunnenta tana jin bude kofa ta katse wayar da sauri, Inna ta saki baki tana kallonta, can tace "Amma ke dai barbadaddiya ce Safara'u, ashe kina cikin gidan nn kiji shigowar dangin mijin ki kiyi mukus a daki kamar Mayya, Ni fa na haifi Uban Mujaheed din, Hadiza kuma kanwar Ubansa ce, ashe ke salubabbiya ce Safara'u?" Safeenah tun da ta kalleta sau daya ta dauke kai tana cin chewing gum, Mama Hadiza ce ta hauro sama, Inna tace "Wllh ga ta nan Hadiza ina mata magana ko gaisheni ma bata yi ba tana min cin cingam din karuwai, anya wannan matar aure ce kuwa? Toh dadin abun dai ko kashi mai rai bata ta6a haifa ma Mujaheed ta ajiye ba balle Ahmadu ya samu barbadaddun jikoki kamar ta, kuma in sha Allahu Imaan ce xata cika gidan nan da 'ya ya muna nan da ku...." Mikewa Safeenah tayi ta daina cin gum din bakinta tana kallon Inna, duk xamansu da Mujaheed bata ta6a kawo haihuwa a rai ba sai ynxu da Inna ke mata gori, Safeenah tayi wani murmushi tace "Warce uwarta juya ce xata cika gida da 'ya ya?" Mama Hadiza tace "ke karamar mara kunya kama kanki kada in baki mamakin da bakiyi tunani ba, mara tarbiya kawai shashasha, tunda kika mana haka to har uwar da ta haife ki ma xaki iya walakantawa haka" Safeenah tayi wani murmushin rainin hankali ta mike ta shige bathroom tana cewa "Ae na xama kandagaren bakin tulu, babu yanda aka iya da ni, Mujaheed dai ko an ki ko an so nice ta farko gidansa ba a isa a canxa wannan ba" key ta sa ma bandakin, inna ta juya ta fita tana kwala ma Mujaheed kira.... Mujaheed na ganin Mama Hadiza ta wuce sama dama ya mike ya koma kusa da Imaan da ta hade rai, dauke kai tayi ya juyo da ita yana murmushi yace "Our deal...." Mikewa take son yi ya ki bari ta tashi nan ya rungumeta giving her a romantic kiss, ga mamakinsa bata yi yunkurin stopping dinsa ba, sai dai yana jin yanda xuciyarta ke bugawa, muryar Inna da ya ji ya sa shi saketa da sauri ya matsa daga kusa da ita, masifa kawai Inna take kamar xata ari baki, Sakkowar Mama Hadiza ya sa Mujaheed ya mike, Mama Hadiza na kallonsa rai bace tace "Har mu yar iskar yarinyar nan xata walakanta haka Mujaheed??" Mujaheed ya kasa cewa komai, Inna ta xauna a hankali tace "Ni har xagina ma tayi ban kulata ba" Mujaheed yace "Ku yi hakuri don Allah Mama..." Mama Hadiza tace "In sha Allahu a dalilina bbu abinda xai sami aurenta na dai san xata gani a kwaryarta, the main point here is imaan baxata xauna gida daya da ita ba, sam baxai yiwu ba, tun wuri ka fara shirin raba masu gida" Inna tace "Atoh, jikata baxata xauna da mayya irin Safara'u ba wllh, yarinya shegiya kawai mara tarbiya ni take tauna ma cingam tana balan balan da shi?? To wannan lafceciyar uwar tata tayi ma haka ba ni ba" Shi dai Mujaheed bai ce komai ba amma sosai ransa yyi mugun baci, Mama Hadiza ta xauna har lkcn ranta a bace tana girgixa kai tace "Uwar ka dai ta cuce ka wllh, domin wannan ba yarinyar aure bace, kwata kwata bata da kirki" Inna tace "Atoh, gwara da kika gane ma idonki, da ni ce na koma gida nake fada karyatanin da kuka saba xa ku yi, barin mutumin nan Bukar, a sannu xa ayi walkiya halin kowa ya fito nan ba da dadewa ba kuwa, ni dai abinda na sani shine duk wanda ya kuskura ya ma jikata wani mugun abu to wllh wllh watan mutuwarsa a duniyar nan ya tsaya cakkk don baxan yadda ba sai na hallaka sa" ita dai Mama Hadiza bata ce komai ba. Mikewa tayi daga karshe tana kallon Imaan tace "Mu tafi sama am not staying long here...." Imaan ta mike a hankali ta bi bayanta, Mujaheed ya bi ta da kallo, sai da suka isa stairs ta juya ta kallesa langwabar mata da kai yyi, ta make kafada ta bi bayan Mama Hadiza, dakin da take suka shiga, Mama Hadiza na bin dakin da kallo tace "Nan ne dakin ki?" Imaan tace "Tun da muka xo a nan nake" Mama Hadiza ta xauna gefen gado tana kallonta tace "Babu matsala koh?" Shiru Imaan tayi, Mama Hadiza tace "Kar ki ji komai ki gaya min meye matsalar ki kinga soon xa mu wuce" Imaan ta durkusa kusa da ita a hankali tace "Mama kawai dai sai matarsa ta yi ta tsokanata haka daxu da safe ta shigo min daki tana xagina" Mama Hadiza ta bude ido sosai tace "What?? Ta shigo tana xagin ki a kan me?" Imaan tace "Wai na auri mijinta, kuma take cewa bai kwana dakina ba sai nata" Mama Hadiza ta kankance ido tana kallonta rai bace tace "Shi Mujaheed din me ya hanasa kwanciya dakin ki?" Murmushi imaan tayi kamar baxata ce komai ba sai kuma tace "Ni ce nace bana so" Mama Hadiza tace "Ashe ke wawuya ce ban sani ba, kuma Ina maki kallon me ilimi ashe ba haka ba imaan?" Imaan ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba, maganganu sosai Mama Hadiza tayi mata yawanci duk babu banbanci da wanda Farida tayi mata sai abinda baka rasa ba, ita dai kanta na kasa, Mama Hadiza tace "Idan ma xaki cire wannan kunyan ki cire ni dai na gaya maki, idan ko ba haka ba kin dinga kwasan takaici da gori kenan gun jakar kishiyar nan taki in har kika yarda ta gano abinda ku ke ciki" Imaan ta goge hawayen dake sulalowa idonta a hankali tace "Toh Mama" cikin kwantar da murya Mama Hadiza ta ci gaba da bata shawara sannan ta daura da nasiha, Imaan na kallonta a sanyaye tace "Mama yaushe Ammi xata xo ita?" Mama Hadiza tace "Ke ma kin san baxata xo ba, amma nan da wata daya ai xai kai ki gida na sani" Imaan tace "Toh" Mama Hadiza ta bude jakarta ta ajiye mata abubuwan da ta kawo mata ta yi mata bayani sannan ta mike tace "You keep them safe sai ki fito parlor" daga haka ta fita dakin, Imaan ta mike ta xubasu a jakan da Aunty Farida ta bata sannan ta fita dakin ta harari kofar dakin Safeenah ta sauka kasa, Inna na xaune kan carpet ta bararraje tana cin shinkafa da miyar da Farida tayi, Mama Hadiza ta xauna tace "Ina Mujaheed din?" Inna tace "Ya je siyo maki abinci, ni dai ga wani nan na samu" Inna na kallon Imaan tace "In har kika yarda kika ba mayyar kishiyar ki daman raina ki baki dinga cin ubanta ba to gaskiya an cuce ni da aka sa maki sunana, irin gallazawar da nayi ma uwarsu Bala da


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login