Showing 246001 words to 249000 words out of 303099 words

Chapter 83 - Imaan Book 1 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

1610

"Good night" shiga dakin tayi bata tanka sa ba ta nufi kan gado tayi rub da ciki, ya bi ta da kallo sannan ya rufe kofar a hankali, Safeenah ta sulalo daga saman gadon tana kuka kamar ranta xai fita, wato a dakin Imaan dai xai kwana kenan yau, tunanin hakan yasa taji kamar ta kurma ihu ko xata samu saukin xafin da take ji a xuciya. Mujaheed ya bude dakinsa yana kallon ciki, ganin Imaan ta kashe wutan dakin ya luluba switch din ya kunna, kwance ya ganta ta rufe har kanta da bargo, ya rufe kofar dakin ya rage kayan jikinsa ya shiga bathroom, wanka yyi ya fito ya saka pyjamas dinsa sannan ya kashe wutan dakin ya karasa kan gado ya cire blanket din jikinta murya can kasa yace "Did you perform ablution before lying down?" Duk da imaan na jinsa taki cewa komai idonta a rufe, ya kai hannu fuskarta ta mike a fusace tace "Meye haka na fara bacci xaka shigo min daki ka tasheni Yaya?" Ya d'an shafa kai yace "Dama shigowa nayi in ce maki sai da safe, and to make sure kin sha drugs din ki" tana kallonsa da idanuwanta da suka yo waje tace "Ina xaka?" Yace "Wajen matata da kika xo hutu wajenta mana kanwata....." Bai jira cewarta ba ya juya ya nufi kofa ta bi sa da kallo kamar idanuwanta xa su yi magana, ko kiftawa babu har ya fita dakin ya kulle kofar a hankali not making any sound, Imaan ta cire bargon jikinta ta sauko daga kan gadon da sauri....




*Imaan isn't for free* it's 300 via


Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788



87.....



Imaan har ta isa kofa sai kuma ta dakata bakin kofar, ta durkushe kasa ta hade kai da gwiwa lkci daya ta fara kuka tana jin xafi a ranta, ta fi minti goma wajen kafin ta mike a hankali ta koma saman gado ta takure waje daya ta rufe fuskarta da pillow tana shessheka, har karfe daya bata yi bacci ba, daga karshe ta mike a hankali ta shiga bathroom ta dauro alwala ta fito ta shimfida darduma ta dau Hijab ta fara sallah, bata san iya lkcn da ta dauka tana sllh ba, daga karshe ta kwanta saman darduman don har rufewa idonta yake sbda bacci, lkci daya kuma baccin ya dauketa. Da asuba Mujaheed ya bude kofar dakin a hankali ya shiga ya kulle sannan ya kunna wutan dakin, kwance ya ganta saman darduma ta rufe fuskarta da hijab, ya isa gabanta ya durkusa yana kallonta ya sa hannu ya sauke hijab din daga fuskarta, bacci ya ga take yi, yyi murmushi ya ja dogon hancinta gently, a hankali ta bude idanuwanta ta daura kansa jin kamshin da ya cika hancinta, sanye yake da jallabiya ya sakar mata good morning smile ta dauke kai da sauri ta hade rai, yace "Me yasa kika kwanta kasan tiles da sanyin nan?" Bata tanka sa ba, ya mike yace "It's time for subhi prayer" still bata ce komai ba ya juya ya nufi kofa, a hankali ta juya tana kallonsa har ya bude kofar ya fita ya kulle, Mikewa xaune tayi lkci daya hawaye ya kawo idonta. Har gari ya washe imaan na xaune saman darduma tana azkar duk da baccin dake fixgarta, amma sai da ta gama ta mike ta hau saman gado nan da nan bacci ya dauketa, ba ita ta tashi ba sai kusan karfe tara, ta fi minti goma xaune gefen gadon sannan ta ja tsaki ta mike ta shiga gyaran gadon, tana gamawa ta cire kayan baccin jikinta ta linke ta dau sabon towel da ya siya mata jiya ta daura, sannan ta dau brush da maclean ta shiga bathroom, tana daure da towel bayan tayi wanka ta fito ta dau hijab dinta ta koma bandakin ta fara Hijab din da detergent, har ta gama sannan ta dauraye bandakin ta fito, ta gama shafe shafenta, ta feshe turare ta dau daya daga sabbin abaya ta saka ta kara feshe jikinta da turare sannan ta dau bucket da hijab dinta ke ciki ta fita xata shanya a waje, tun da ta fito daki ta ke jin kamshin soye soyen da ya cika gidan, ta tabe baki har ta sauko downstairs, Mujaheed na xaune parlor cikin kananun kaya, Safeenah na kusa da shi duke a kasa tana setting breakfast da ta gama girkawa, ta wani cakare cikin riga da wando da ya fito da ainahin komai nata, ta daure gashinta da ya xubo har shoulders dinta, labari kawai take masa yana kallonta yana kallon Tv, kai kana ganinta kasan farin ciki ne fal ranta a moment din, murmushi Mujaheed yyi jin abinda tace yace "To me yasa kika fara ci?" Safeenah da tun sakkowar Imaan suka yi ido hudu, ta wani juya ido cike da shagwaba tace "Saboda mijina na ci mana, ae duk abinda kke so dole in so sa ni ma..." Mujaheed kawai gyada mata kai yake yana murmushi, ta mike ta xauna kusa da shi ta sakale hannu wuyarsa tace "To ka mance lkcn da kake cewa sai na ci?" Ya d'an bude ido yana kallonta yace "Ni??" Maimakon ta basa amsa sai kawai ta saka mashi baki a nasa, dauke kansa yake son yi da mamaki amma ta ki barin yyi hakan, irin kiss din da ta san yake so ta shiga masa, tun yana basarwa har ya fara give up sai dai bai mayar mata ba, Tun da Imaan taga haka bata sake yarda ta kalli direction din su ba, sai dai da kyar take daga kafarta har ta isa kofar parlon ta bude a hankali ta fita xuciyarta na bugawa, Jin sound din bude kofa Mujaheed yyi saurin mikewa xaune yana kallon kofar amma tuni ta rufe, Safeenah tayi lamo jikinsa yana kallonta yace "Wa ya fita?" Ta langwabar da kai tana juya ido a hankali tace "Mu nawa ne gidan yanxu?" Janyeta yyi jikinsa bai ce komai ba, tana murmushi ta xamo kasa tace "Should I make the coffee for you now?" A takaice yace "No" ko kallonsa bata yi ba ta shiga hada masa coffee din a mug, Duk da yanda Imaan ta so kar tayi kukan da ke cinta a rai amma hakan ya faskara, tana gama shanya hijab din ta xauna saman dakali ta hade kai da gwiwa ta fashe da matsanancin kuka tana jin xuciyarta na mata xafi, ita kanta bata san dalilin abinda take ji a ranta ba a lkcn, bata yi minti biyar wajen ba ta mike a hankali tana goge idonta, ba karamin sanyi ta ji ba kukan da ta yi, ta dau bucket tana tafiya a hankali har ta isa entrance din gidan, nan kuma gabanta ya shiga faduwa coz she can't imagine seeing what she just saw for the second time, baxata iya withstanding dinsa ba, slowly ta bude kofar just to keep them alert, sannan ta shiga parlon amma bata yarda ko da wasa ta kalli inda suke ba xuciyarta na bugawa har lkcn, ta wuce sama kamar me counting steps dinta, Mujaheed ya bi ta da kallon gefen ido, Safeenah dai tana aikin hada shayinta da xata sha xuciyarta fess tana satan kallonta, Bayan kusan minti bakwai Mujaheed ya mike Safeenah tace "Ina kuma xaka ga breakfast na xuba maka darling" Ba tare da ya kalleta ba ya fara tafiya yace "Mu kadai xa mu yi breakfast din??" Ta mike da sauri ta sha gabansa ta riko hannunsa tace "Haba dear, shine sai ka je kiranta da kanka, ai ko ni sai in je in kirata dama ba mu gaisa ba yau, But you know what baby?? wllh duk naji abubuwan da ka gaya min jiya da daddare kuma in sha Allah I will adhere, I will try my best mu xauna lafiya da ita, na yarda wannan kaddara ta ce, kuma babu bawan da ya isa ya wuce kaddarar sa, na ji na yarda xan dau Imaan matsayin kanwata kamar yanda kace, don haka give me the space to start doing this from today, xan je mu gaisa in kirata yanxu, daga nan ba sai mu fara fahimtar juna ba?" Tana masa lallausan murmushi tana murxa hannunsa ta kare maganar, shi dai kallonta kawai yake, bata jira cewarsa ba ta sake sa ta wuce sama tana murmushi, a hankali ta bude kofar dakin Imaan ta shiga bbu ko sallama, Imaan dake kwance ta rufe fuskarta da pillow tana shessheka a hankali, ta ki dagowa duk da taji an bude kofa dakin, Safeenah tayi wani dariya tana kallonta daga head xuwa toes, Imaan ta bude ido da sauri jin dariyarta xuciyarta na bugawa ,sai dai still bata dago kanta ba, Cike da isa Safeenah tace "Kinga consequence din auren mijin wata koh??" Imaan dai bata dago ba kuma bata ce komai ba, Dariya Safeenah ta fara yi sosai tace "Ban taba ganin amaryar da miji bai dokinta sai a kan ki, har xai tsallake ki ya tafi gun uwar gidansa ya kwana a faranta masa rai, kina gidan kuma kwanan ki, isn't this a big shame to you? To what will one expect bayan kowa yasan tusa masa ke kawai aka yi ya aure ki, kuma shi din mijina dama a ko da yaushe mai biyayya ne, yyi biyayya ya aure ki ba don yana so ba sae don bbu yanda xai yi, to abinda baki sani ba mijin wata mijin aro ne, yanda kika shigo gidan miji na a xabure haka xa ki fita a xabure ki bar min gidan mijina, don ko mahakaci yasan wllh tllh tusa masa ke aka yi, baya yin ki ko na second daya, da yana yin ki ko yaya ne baxai ki kwana dakin ki ya tafi dakin first wife dinsa a daren ki na farko gidansa ya kwana ba, don haka tun yanxu yarinya ki fara sanin matsayin ki gidan nan, I think that is all I have to say to you now, and can you kindly come downstairs for breakfast, he instructed I come and get you don baxai iya hawa sama kiran ki ba...." Imaan ta goge idonta da pillow ta mike xaune tana kallon Safeenah tana murmushi tace "Xan nuna maki ke ce kika auri mijin wata ba ni ba, kuma aron nasa ma ni ko na second daya baxan baki ba, nan ba da jimawa ba xa ki san ba tusa masa ni aka yi ba, shine ma mai tusa kansa gareni, kuma xan nuna maki ke aka tusa ma Mujaheed yyi biyayya ya aura ba ni ba, sai ma kinsan ni ce silar auren ki da Mujaheed xa ki dawo hankalin ki...." Safeenah tayi wani dariya lkci daya ta daure fuska tana huci tace "Karya kike wllh, ke dai ce kika aura mijin wata mijin aro, Mujaheed ba class din ki bane bbu abinda xai ci dake, tsautsayi ne kawai ya ja auren ku, amma wllh ba mijin ki bane shi din...." Tana magana hawaye ya cika idonta duk da daurewan da tayi kada hakan ya faru, tana girgixa kai tace "Wllh ba mijin ki bane shi din, ke kin kasance makwadaiciya me son abun duniya, kuma kyan ki ire iren su Bulasawan, don su xa su fi iyawa da sauran ciwo, tsautsayin da ya hana d'an gidan Bulasawa auren ki shi xai kara sa mijina ya sake ki shi Bulasawan ya aure ki kuje can ku karata, in sha Allahu nan ba da dadewa ba xa ki bar min gidana da mijina ki tafi, ba D'an gidan Bulasawa ba, in har xa ki iya auren shi Bulasawan ma da kansa ki tafi ki auresa, banxa kawai ragowar ciwo...." Imaan tayi murmushi tace "Son da mijinki ke ma ragowar ciwo wllh da kin samu just 10% na kalan son daga garesa da ba haka ba, mark my words.... sai kin xama abun tausayi a gidan nan in dai ni ce, banxa kawai jahila mahaukaciya..." Safeenah da ta yo waje da ido jikinta na rawa tace "Ni kike xagi???" Imaan ta sakko da kafafuwanta daga saman gadon dai dai shigowar Mujaheed dakin, ta mike tana kallonta tace "An xage ki din kiyi abinda xa ki yi, karya nake ke ba jahila bace? Ko kin ta6a leka islamiyya??" Kallonsu Mujaheed ya tsaya yi da mamaki, Safeenah na kallonsa ta fashe da matsanancin kuka tace "Kana ji ko dear, ni wai take ce ma jahila mahaukaciya daga na shigo na gaisheta nace ta sakko mu yi breakfast, meye laifina a nan Mujaheed don na shigo nace ta sakko mu karya..." Kuka take sosai tana kallonsa, Wani dogon tsaki Imaan ta ja tace "Makaryaciyar banxa kawai" daga haka ta nufi bathroom kamar xata tashi sama ta shige tayi banging kofar da karfi, Mujaheed da ya bi ta da kallo baki bude ya mayar da dubansa kan Safeenah dake kuka sosai, karasawa yyi kusa da ita a hankali ya jawota jikinsa murya can kasa yace "I am happy da baki kulata ba, kinga yarinya ce, she still don't know what she is doing, but I will teach her discipline" daga haka ya ja ta suka fita dakin tana shessheka....
Abba ne tsaye parlon Inna tare da Mama Hadiza da ta rungume hannu, a fusace Inna tace "In har baxan tafi da kayan sawa ba to wllh sai dai kowa ya fasa xuwan a hakura kawai, ya xa ayi in tafi waje me nisa har Zaria ban je da kaya ko kala uku ba, Ni fa ba kwana nace xan je in yi kamar gantalalliya mara mafadi ba, amma ai yana da kyau duk matafiyi ya dinga yawo da kaya sbda bacin rana, kaji min dai sai kace kun fi ni sanin abinda nake, wllh ban taba tafiya bbu jakar kaya ba ko da kuwa awa daya xan je inyi a waje, sabida fatara sai in tafi da xanin jikina kadai ina yawo a garin zaria kamar almajira..." Abba yace "Toh inna tafiyar da xa aje a dawo a ranan ina amfanin tafiya da kaya? Me xa kiyi da kayan, Da driver fa xa ku je ku dawo" Inna tace "Yau naga jaraba, Ina ruwanka da rayuwata ne Ahmadu, Kai xaka yi tafiya ko ni? Yanxu idan na bi hanya Ina ta kwarara masu amai a mota kayan Imaan ko na Safara'u xan je in canxa a gidan??" Mama Hadiza tace "Zaria fa xa mu je ba Lagos ba Inna" A mugun fusace inna tace "Ko maraban jos xa mu ba ruwan ki kiyi ta kanki, bbu shegen da ya isa sa ni in fita gidan nan da xanin jikina kadai kamar a kaina talauci ya kare..." Daddy ne ya shigo parlon da sallama shima yyi shirin komawa Abuja ranan, yace "Har yanxu ba ku fito ba Inna..." Inna tace "Ina fa xan fito Bukar, ai tafiyar nan ina jin babu shi don ni dai baxan bi hanya bbu kaya ba gaskiya, Kai ko da ban yi amai ba a hanya to ni nasan kafin mu isa Zaria xan jike shataf da gumi, to uwata ce min tayi je ki kya gani da xan xauna da kaya ina warin xufa Bukar???" Daddy yace "Haba inna sai kace warce xata sokoto ko gombe, nan nan Zaria fa xa ku, ku dawo anjima, idan ba xama kike son xuwa yi a gidan ba ina amfanin tafiya da kaya?? Sai dai in xauna masu kike son yi kawai, amma sau nawa kike xuwa kano kice ke ko jaka baxa ki dauka ba? Gashi har rana yyi ba ku kama hanya ba, hakan is not good" shiru Inna tayi bata ce komai ba sai yan idanuwa, Daddy ya juya ya fita parlon, Mama Hadiza ta dau warmer dake cike da dambun nama da Inna tayi ma Imaan ta fita parlon tace "Muna jiran ki a mota" Abba na kallon Inna da ta sunkuyar da kai a hankali yace "Ae sati uku xa su yi xarian sai su dawo kaduna, idan ya so sai ki..." A fusace inna tace "Rufe min baki malam, Ina ruwana da ko kwana nawa xa su yi a Zaria? Ko nace maku xuwa xan yi in xauna masu kamar shashasha tsofe tsofe da ni, me Mujaheed da Imaan xa su bani wanda Allah bai ban ba? Yaran da aka ma auren dole auren jaraba wa yasan halin da suke ciki ma yanxu, wllh In don ta kai da Bukar ne ni baxan ma je ba don baku da kirki barin wannan mutumi Bukar, da 'yar sa ce kadai a gidan wllh na ma fasa xuwan gaba daya, to amma ni yanxu gun Mujaheed kawai xanje ba gunta ba wllh, bbu ruwana don ubanta ba ma son xuwa in je gidan yake ba, ubanta ba shi da kirki" tana fadin haka ta mike ta fice daga parlon ba tare da ta dau jakar kayanta kusan kala shidda da ta hada ba a Ghana must go.



*Imaan isn't for free* it's 300 via


Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788





88....




Safeenah na kitchen tana wanke wanke ranta fari fess ko kadan bata ji haushin xagin da Imaan tayi mata ba ganin Mujaheed bai yi supporting dinta ko na second daya ba sannan ya yadda da tsarin da tayi masa, sai murmushi take ita kadai ganin abubuwan na tafiya yanda dai take so kafin Mummynta ta iso gidan, Mujaheed na xaune parlor idonsa a kan tv amma bai ma san me ake yi ba, gaba daya hankalinsa na sama, can ya kalli breakfast da ya ajiye Safeenah ta bar ma Imaan a parlon sannan ya kalli agogo, karfe goma har ya gota hakan yasa ya mike ya tafi kitchen don daukan cup da spoon ya dau tray ma, Safeenah na kallonsa da mamaki tace "Me xaka yi da su kuma dear?" Yace "Imaan haven't Breakfasted..." dauke kai tayi ta wani hade rai tana dauraye plate din hannunta tace "Toh ai idan tana jin yunwa da ta sakko tunda mun ajiye mata mun fita hakkinta,


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login