Showing 291001 words to 294000 words out of 303099 words

Chapter 98 - Imaan Book 1 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

1642

rayuwar aure ga maza da Mata, inganta qwayoyin haihuwa da dai sauransu.
Akwai sinadarin rage tumbi da dai sauransu.

*Domin neman qarin bayani ku tuntubi wannan lambar 07068136856*
Sai an gwada akan san na kwarai.






104.....







Mujaheed ya dinga kallon takardan da nurse ta kawo masa office some hours later, a hankali ya linke takardan ya ajiye ya jinginar da kansa da kujera, Imaan ce ta fado masa ya mike da sauri yayi clearing din table din gabansa ya sauke curtain ya dau wayarsa da makullin mota da takardan scan din sannan ya fita ya kulle office din, Yana tsaye reception nurse ta tafi ta tado Safeenah da har ta fara bacci a wani ward, yana ganin ta fito ya fara tafiya, har ya isa gun mota ya bude ya shiga yana jiranta, tare da nurse dake rike da hannunta suka iso gun motar nurse ta bude mata front seat ta shiga ta ajiye ledan Magunguna, mujaheed yyi mata godiya sannan ya ja motar ya bar hospital din, sai da suka yi nisa ya d'an kalleta yaga bacci take, har suka isa gidansu bata bude ido ba, shi ma kuma babu abinda ya ce, yana gama parking ba tare da ya kalleta ba yace "Safeenah" bude ido tayi da sauri, ya dau ledan maganin ya mika mata yace "Allah ya sauwake" amsa tayi ta bude kofar motar ta sauke kafafuwanta waje amma bata fita ba murya can kasa tace "Is there any difference between the first scan and this?" Yana kallon waje yace "No Allah ya raba lafiya, Allah ya sauwake" tace "Ameeen" shiru tayi kamar yanda shi ma yyi shiru yana jiran ta sauka ya wuce, tace "kayan shayin sun kare" yace "Ohk" sauka tayi daga motar ta rufe ido sbda jirin da take ji ta dafe motar da sauri, ya kalleta yace "Careful" Bata ce komai ba ta fara tafiya a hankali, tana isa gate dinsu kamar warce aka hankade sai gani yayi ta tafi luuu, fitowa yayi da sauri daga motar, masu gadi dake wajen ma duk suka taso, Suhaila da tayi parking dai dai lkcn kuma ita ma taga abinda ya faru ta fito motarta da sauri ta nufi yar uwartata tana kwala kiran sunanta, amma tuni Safeenah tayi collapsing a nan kasa, dukawa Mujaheed yyi kusa da ita ya dagota yana jijjigata, daya daga mai gadin ya bude masa gate ya dauketa ya shiga gidan da ita, Suhaila ta bi bayansa tana salati hankali tashe, sosai hankalin yan uwanta ya tashi bayan ya shigar da ita parlor, babu dai wanda ya bi ta kansa kamar yanda shi ma bai ko kallesu ba, har sai da Safeenah ta farfado bayan kusan minti sha biyar, juye juye ta dinga yi tana rike da cikinta tana hawaye uwarta na rike da hannunta tana mata sannu, Mujaheed ya ji tausayinta sosai... Hospital suka kara komawa da Suhaila da Hajiya Baturiya, suna shiga reception din hospital din jini ya 6alle ma Safeenah, nan da nan aka shigar da ita emergency ward, kasa shiga emergency ward din Mujaheed yyi ya wuce office dinsa. Yana ta xaune office amma hankalinsa ya kasu biyu sbda imaan dake gida, har wani colleague dinsa Dr Yusuf ya shigo yana kallonsa ya ja kujera ya xauna, bayan few seconds yace "I am sorry Dr, she had miscarriage" Shiru Mujaheed yyi yana kallonsa, lkci daya jikinsa yayi sanyi, Dr Yusuf ya mike ya fita office din, tashi Mujaheed yyi ya fita office din shi ma, ward din da Safeenah ke kwance Mujaheed ya nufa tun daga bakin kofa ya ji Hajiya Baturiya na cewa "Wllh wllh shi xubar da cikin, wato dama tun da yace ta shirya xa su asibiti yau naji ban yadda da shi ba, shi yasan abinda yayi cikin ya xube..." Suhaila ta katse ta tace "Aikin banxa to sai me?? Allah na tuba dama me xa ayi da iri irin na uwarsa matsafiya, Ni wllh ba ku ji murnan da nayi ba da cikin ya xube, naji dadi har raina da Allah ya rabata da wannan tsinannen cikin, kawai karshe ayi ma yar uwata wankin ciki a karasa rabata da tsiyarsu.." ita dai Safeenah na kwance sai hawaye take, Hajiya marafa dai sai girgixa kafa take, juyawa Mujaheed yyi ya fasa shiga ward din. Sai kusan Magrib Mujaheed ya koma gida ranan ya tadda imaan na barci har lkcn, tausayinta ya ji sosai ya xauna gefenta yana kallonta sannan ya fita xuwa dakinsa yyi wanka ya fita masallaci yin Magrib. Bayan sati biyu da xubewar cikin Safeenah ranan Saturday da sassafe yana parlor yana operating laptop, gaba daya laulayin Imaan ya damesa don wahala take sosai, duk ta rame gashi ba abinda take iya ci, kuma bai sanar ma kowa a gida ba har lkcn banda umma da ta sani, kusan kullum kuma xata kira ta ji jikinta, wani lkcn tace masa ya bata, danna kararrawar da aka yi tare da bubbuga kofa yasa ya daga kai ya kalli kofar amma bai tashi ba, Jin irin bugun da ake ma kofar yyi murmushi ya mike ya isa gun window ya daga labule a hankali yana lekan waje, Maimoon kadai ya hango tsaye hannunta rike da warmer ta xumburo baki tana kallon Hajiya Inna dake faman buga kofa da duk karfinta, Inna ta ja tsaki ta tafi can inda ta hango wani dutse babba ta dauko ta dawo Maimoon ta buda ido sosai tace "Kar fa kije ki gurje ma mutane kofarsu inna, daga buga kofa sau daya baki jira ki ga....." Katse ta Inna tayi tace "Kada in gurje ma mutane kofa? Waye mutanen? Mujaheed ko Imaan? yaran da aka haifa kan idona nayi wahala da su tun durowarsu duniya xa ki ce kada in gurje masu kofar banxa kawai, banda shegantaka ga shegen takalmansa Ina gani bakin kofa su bar ni tsaye kamar mara makabuli duk sanyin safiya ya kare min?? Uban me suke yi a ciki toh har yanxu basu tashi ba, ni ba a ta6a min irin haka ba duk gidajen da nake xuwa da safe gaskiya" murmushi Mujaheed yyi yana shafa kai, nan Inna ta fara bubbuga kofar da dutsen hannunta da gaba daya strength dinta, ya koma gun kofar ya bude yace "Idan kika lalata min kofa sai kin biyani don baxan yadda ba Hajiya" shigewa parlon tayi har tana neman bangajesa bata ko kallesa ba fuska daure, Maimoon na murmushi tace "Ina kwana Yaya" yace "lafiya lau daga Ina ku ke?" Dariya tayi tace "Gida mana yaya" ganin Inna ta nufi sama ya bi ta da kallo yace "Ikon Allah, Ina kuma xa ki Hajiya?" Bata tanka sa ba har tayi wucewarta sama, shafa kansa yayi a hankali ya kalli Maimoon yace "Abba yasan kun xo?" Maimoon ta girgixa kai tace "A'a ba wanda ta gaya ma" hanya ya bata ta shigo parlon sannan ya wuce sama, direct parlon Mujaheed Inna ta shige sannan ta wuce daki, kallon Imaan dake kwance a lullube tayi tace "Meye kuma haka cikin xafin nan??" Karasawa kan gadon tayi ta fixge bargon tana kallonta, Imaan ta bude ido a hankali, mikewa tayi ganin Inna, Inna ta saki baki tace "Na shiga uku me ya same ki haka?" Imaan ta bata fuska ta jingina da gado tana kallonta, Inna tace "Naga abinda ya isheni, Wace cuta ce wannan ta kama ki ni patu duk kika kare?" Mujaheed dake tsaye bakin kofa yace "Xaxxabi take" Inna ta kallesa da sauri tace "Xaxxabi?? Na cixon sauro ko me?" Yace "Ehh shi" Inna ta xaro ido tace "Garin ya xa ku ba sauro izinin shigowa wannan santalelen gida haka, Ina sauro ya ga wajen xama gidan nan fisabilillahi, toh gaskiya da sake, Kwata kwata Mujaheed baka da kula, haka kawai ka bari sauron mayata su shigo gida har su cutar min jika, tunda Imaan take bata ta6a xaxxabin cixon sauro ba a gidan ubanta, to ina Bukar xai yarda da haka dama tunda yasan ciwanta, wato ga yarinya an baka a banxa shine xa ka yarda ka ba sauro daman ya cuceta, to ba ruwana wllh, dama ni nasan baxa ka iya rike min jika ba..." Daga haka ta fice dakin ya bi ta da kallo yana murmushi, sannan ya isa gun imaan da ta koma ta kwanta, ya xauna gefenta ya kai fuskarsa nata murya can kasa yace "Kin daina jin sanyin yanxu mu shafa cream?" Marairaice masa tayi bata ce komai ba, ya jawota jikinsa a hankali yace "Wai da gaske sauro ne ya cije ki?" Shiru tayi tana kwance jikinsa, ya shafa kanta yana murmushi. Inna na komawa parlor dama wayarta ta ciro daga cikin jaka ta mika ma Maimoon tace "Maxa kira min Ahmadu" Maimoon tace "Me ya faru?" A fusace Inna tace "Don Allah ki kira min shi babu abinda ya shafeki da mai ya faru, yarinya duk naga ta rame sai hanci da idanuwa ina xan yadda wai cixon sauro" Maimoon ta amshi wayar ta kira Abba ta mika ma inna bayan ya fara ring, ko sallaman Abba inna bata amsa ba tace "Ahmadu to fa ga Imaan rai a hannun Allah, na xo gidan na ganta a dunkule cikin katon bargo duk ta kare tass sai k'ashi, wai cixon sauro, anya Ahmadu akwai abun kirki a auren nan, da kyar fa take tashi take kwantawa, kada fa ku manta ita kadai ke gare Bukar, Kar mu cucesa, wani irin cixon sauro ne yarinya xata rame ta xabge ta fita hayyacinta haka, to ni dai wllh ba ruwana xan daukota mu taho gida, a kan me Mujaheed xai amince sauro su shigo gidansa har su cutar min jika" kuka ta fashe da ta mika ma Maimoon wayar tace "Kashe min wayata mu je ki hada min kayanta a akwati sai dai duk xagin da Ahmadu xai min ya min, shi xai yarda a rike yar sa yanda mujaheed ya rike imaan" daga haka ta wuce sama. Mujaheed yyi picking call din Abba da ya shigo wayarsa ya kai kunne tare da yin sallama, Abba ya amsa yace "Mujaheed me ya sami Mamana?" Mujaheed yyi kasa da kai yace "Abba bata da lafiya ne" Abba yace "Me ya sameta?" Ya d'an yi shiru sai kuma yace "Rashin lafiya ne" Abba yace "Tun yaushe?" Mujaheed yace "Kusan two weeks yanxu" Abba yace "Ciwonta ne ya tashi?" Mujaheed yace "A'a" Abba ya d'an yi shiru, sai kuma yace "Toh Allah ya bata lafiya, kuna xuwa asibiti ne" Mujaheed yace "A'a ina dubata a gida" Abba yace "Innar tana nan har yanxu?" Mujaheed yace "Ehh" Abba yace "Toh ka bari su taho tare gida tunda ta bukaci hakan, hakan ne kwanciyar hankalinmu gaba daya" yace "Toh Abba" daga haka Abba yayi masa sallama ya katse wayar. Inna ta gama hada kayan Imaan da kanta cikin jaka a bedroom dinta tana mita, Maimoon dai na tsaye tana kallonta, Inna ta xuge zip din ta mika ma Maimoon wayarta tace "Kira min Aisha" Maimoon ta amshi wayar ta kira Ammi, Ammi na dagawa Inna tace "Toh Aisha ga dai imaan nan na xo na sameta ba kanta, tunda nake ban ta6a ganin ta rame irin yanda na xo na sameta ba, Ni ba ruwana ki Kira mijin ki yanxu xan taho da jikata gida don baxan kirasa ya bata min rai ba yayi min rashin kunya, wllh babu mahalukin da ya isa hanani fitar da Imaan daga gidan Mujaheed yau, don idan ta mutu ni kadai nayi asara ba wani ba" daga haka ta mika ma Maimoon wayar tace "kashe min kayana" Maimoon na murmushi ta kashe wayar. Kafin Inna ta gama hade haden kayanta ta fito, har Mujaheed ya saka ma Imaan hijab yana rike da hannunta ya tafi parking space, front seat ya bude mata ta shiga ya rufe sannan ya koma cikin gidan. Bai ko bi ta kan Inna ba ya kira Maimoon yace ta xo su wuce sannan ya koma gun motar. Har suka isa gida Inna mita take cikin mota wai taya sauro xai shiga gida mai lafiya haka ya illata mata jika haka, bbu wanda ya tanka ta a motar, imaan dai baccin ta kawai take, daga karshe mujaheed ya kure karatun Qur'anin dake tashi a motar. Parking yyi Inna ta bude motar ta fice tana kallon Maimoon tace "Sakko ki bude mata ta fito" Maimoon ta fito ta bude side din Imaan, ganin tana bacci Inna tace "Kin ga jaraba koh? Wannan sauron lafiya ne kuwa ni patuu" Murmushi Maimoon tayi tana tashin Imaan, Imaan ta bude ido sannan ta fito motar tana rike da Maimoon sbda juya mata da kanta ke yi, Inna tace "Toh Allah dai ya isa" daga haka ta kama hannunta ta wuce sashinta da ita fuskarta babu walwala, Mujaheed ya bi su da kallo yana murmushi, Maimoon ma ta bi bayansu. Saman kujera Imaan ta kwanta ta juya baya, Inna dake ta kallonta tace "Bari in xubo maki abinci ki ci mu wuce asibiti, ba sai na jira kowa ya ban kudi ba, lafiyar ki ta fiye min komai dama tuwo nayi tun asuba kafin in baro gida" daga haka ta wuce kitchen ta xubo tuwa da miyar kubewar da tayi ta dawo parlor ta ajiye kusa da Imaan tace "Sakko ki ci, kin ji takwara" Imaan ta bude ido da sauri tace "Ni fa baxan ci komai ba ki tafi da shi" Inna tace "Baxa ki ci komai ba kuma, ni fa bana son wahala, yanxun nan xuciya ta debeni sai in tattaraki ki koma gidan Mujaheed din ki mutu" Imaan ta ki juyowa tace "Inna ni ki tambayesa na ci abinci fa" Inna ta xauna tayi tagumi tace "Ai ni na shiga uku" Aunty ce ta shigo parlon da sallama ta gaida Inna tana kallon Imaan tace "Wai imaan bata ji dadi ba" Inna tace "Wllh, wai xaxxabin cixon sauro Amina, yaushe rabon da ayi wannan ciwon fisabilillahi, tun tale tale fa, toh yanxu xamanin nan wa ke yarda sauro ya shigar masa gida ma balle ya cucesa?" Aunty ta dago Imaan tana kallonta da damuwa tace "Sannu Imaan" Imaan bata iya tace komai ba, Inna tace "Cewa nayi ga abinci ta ci in kai ta asibiti da kaina ta ki ci" Aunty ta dago abincin tace "Ki ci ko kadan ne imaan" tunda Imaan ta ji aroma din miyan, ta dauke kai tana matsawa daga kusa da Aunty, Aunty ta lura da hakan ta mayar da abincin ta ajiye, Inna ta kuma daukowa tace "Ji min mata, ki bata abinci kin mayar kin ajiye, abu dai baxa ayi sbda Allah ba" Imaan na hada ido da abincin for the second time ta mike da sauri tana rike da cikinta tayi hanyar dakin Inna, Aunty ta bi ta da kallo, inna ta saki baki tace "Meye haka kuma?" Jin kakarin amanta Inna ta kalli Aunty tace "Meye ma'anar hakan Amina?" Murmushi kawai Aunty tayi bata ce komai ba ta mike ta bi bayan imaan, Inna dai na xaune rike da abinci baki har lkcn a bude, can ta ajiye plate din ta wuce daki ganin yanda Imaan tayi mata amai a tsakar bandaki ta xauna gefen gado tayi tagumi, Aunty ta cire mata hijab ta ajiye a bucket, ta taimaka mata ta wanke bakinta sannan suka fito bandakin tana mata sannu, Inna tace "Toh aman meye wannan aka kirba min a bandaki duk karni haka? Bandakin da na wanke da hypo biyu daxu, ah gaskiya wannan rashin Imani ne, tana jin amai kuma baxata tafi can tsakar gida ba sai ta juye min shi a bandaki na, sannan ke kuma Amina kin dau hijabi dumu dumu da amai ki sa min a bokitin wanka na, haba jama'ah, wannan rashin kirkin har ina" Aunty dai bata tanka ba ta kwantar da Imaan dake maida numfashi tana mata sannu, Inna tace "Toh wllh Amina ki san yanda xaki yi da bandaki na ban dauko ta don ta cuce ni ba gaskiya, xuciya daya na daukota ganin halin da take ciki, meye kuma xata kaxance min bandaki da amai???" Daga haka inna ta fice daga dakin, Aunty ta koma bandakin don ta gyara mata, ta fito parlor daukan omo Inna dake xaune parlorn ta bi ta da kallo tace "Dama malaria na saka amai Amina?" Murmushi Aunty tayi tace "Gashi kin gani kuwa Inna" Inna tace "Toh Allah ubangiji ya mana tsari da shi, amma gaskiya mujaheed da kyar idan xan iya yafe masa wllh" Aunty ta fita tana dariya kasa kasa. Karfe goma saura Mujaheed ya shigo parlon Inna, har lkcn Imaan na daki tayi bacci, Inna kuma na bandaki tana wankewa bayan wanda Aunty tayi, ya shigo dakin ya nufi kan gadon ya xauna kusa da ita yana kallonta a hankali yace "Imaan" Imaan ta bude ido tana kallonsa yace "Sannu" ta gyada masa kai kawai, xaunar da ita yayi yace "Toh me kike son ci?" Ta girgixa masa kai, da damuwa yace "Noo dole xa ki ji da abinda kike son ci a ranki what is that?" Shiru tayi tana kallonsa, can tace "Ni dai danwake nake so yau" Yace "Ohk toh, bari in gaya ma Aunty ta maki" kwantar da ita yayi ya mike ya fita dakin, ya tafi can part din su gun Aunty, Aunty dake bedroom dinta tace "Ae kuwa babu flour wllh, sai dai kaje ka samu Ammi nasan baxata rasa ba sai tayi mata" yyi maza yace "A'a ni baxan iya xuwa ba Aunty ko xaki aika Maimoon" Aunty ta tabe baki tace "Toh xan kirata a waya" murmushi yyi ya mike yace "Toh ngd aunty" daga haka ya fita dakin, aunty ta kira Ammi, Ammi na dagawa bayan sun gaisa Aunty tace "Kina da flour don Allah" Ammi tace "Ehh baxa a rasa ba" Aunty tace "Toh Imaan xa ki yi ma danwake shi take son ci wai" Ammi tace "Toh bari in duba" daga haka ta katse wayar. Cikin kankanin lkci Ammi ta gama danwaken da farko Maimoon tayi niyyar kira ta kai danwaken amma sbda yanda take son ganin condition din 'yar tata, tayi deciding ta


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login