Showing 105001 words to 108000 words out of 303099 words
sha Allah" Yace "Tun daga farkon relationship dinmu 4 years ago har xuwa yanxu idan na 6ata maki kiyi hakuri ki yafe min" tace "Baka min komai ba kuma na yafe maka ni ma ka yafe min, Allah kuma ya saka maka da alkhairi abubuwan da ka min from the beginning har xuwa yanxu, thank much Muhd, Allah kuma ya baka Ikon ci gaba da yi ma mahaifiyar ka biyayya, ku rabu lafiya" Ya sauke idonsa kasa yace "in sha Allah xa mu dinga xumunci..." xame hannunta tayi ta juya ta nufi gate dinsu, a hankali yace "Idan Allah ya kaddara you will still be my wife some days, I will be very glad in hada ki da kanwarki...." Farida bata juya ba har ta shiga ta rufe gate din, Juyawa Mujaheed yyi kamar mai tausayin kasa ya xaga ya bude driver seat ya shiga,Tada motar yyi yana kallon Imaan da ta turo baki bayan ta goge hawayen idonta, Bai ce komai ba ya bar layin da motar, har suka isa gida babu wanda yace komai cikin motar, the journey was very silent, yyi parking a kofar gida Maimoon ta bude motar ta fita, Imaan ma ta fita ta shiga gate da sauri, Parlor ta tadda Ammi, ganin mood dinta Ammi tace "Ya aka yi" xaunawa tayi hawaye ya kawo idonta tace "Ammi ta ban tausayi, me yasa Yaya xai mata haka, he betrayed her" Ammi ta tabe baki bata ce komai ba, tace "Har kuka fa sai da tayi" Ammi tace "Toh Allah ya bata wanda ya fi sa, wani hanin ga Allah bai wa ne, bata san ma wani gata Allah ya mata da ya rabasu ba, don Ina tausaya mata idan Mujaheed ya aureta barin yanda uwarsa bata sonta" Imaan tace "Toh Saboda me?" Wani murmushi Ammi tayi tace "Ko makiyina baxan ba shawara ya ba ma Mujaheed 'yar sa ba, Kinga Hajiya Rukayya ta wuce tunanin kowa, ni ba miji daya muke aure ba amma irin xaman da muka yi ba shi da banbanci da muna auren miji daya, na sha wahalar ta ne, sam bata san da annabi ya kafu ba" Imaan dai tayi shiru, Ammi tace "Don haka gwara dai ta aura ma d'an nata yar kawarta, sun fi kusa kuma sun san kansu" Washegari Juma'ah Imaan na dawowa schl ko uniform bata cire ba sai ga inna ta sha atamfarta mai tsada an yafa mayafi, Ammi tace "Sannu da xuwa Inna" Inna tace "Yauwa takwara ta dawo makaranta kuwa?" Ammi tace "Ehh yanxu ta shigo" inna tace "Toh da kyau, dama so nake ta rakani gidan ta rasulu kwana biyu shiru ban ganta ba" Ammi ta kwalo ma Imaan kira, Imaan ta fito, Ammi tace "Xa ki raka Inna anguwa" Imaan ta hade rai tace "Ban ma yi wanka ba kuma ban ci abinci ba, gashi kai na ma ciwo yake min" Inna tace "Kanki na ciwo kuma? Toh yi xaman ki bari in je in samu Maimoon ko Ummi su rakani, ya xan yi dake idan kin fadi a titi, wa gareni titin?" Daga haka ta juya ta fita, Imaan ta koma dakinta. Imaan na wanke wanke kitchen da yamma Ammi ta kwalo mata kira fito da sauri, Ammi tace "Kiran ki ake a waya" daukar wayar tayi ganin Sadeeq ne ta daga ta bar parlon, gaisawa suka yi yace "Pls dear ki d'an fito ki amshi sakon Inna am outside" Imaan tace "Sako kuma?" Yace "Ehh ko kina wani abu ne?" Tace "A'a ka dai shigo ka kai mata ai ni bn san da sakon ba" yayi murmushi yace "Ai anjima da daddare xan xo sai muje part din nata tare, yanxu sauri nake Mum dita ta aikeni xan kai mata sako" Imaan tace "Toh sakon meye?" Yace "Ke dai fito ki gani" a hankali tace "Toh" Daga haka ya katse wayar, Ammi dake jin wayar da take tace "Sakon meye?" Imaan tace "Ko ba Inna bace tace ya siya mata iron" tagumi Ammi tayi tana salati, can tace "Yanxu Inna mutunci take nema mana gun yaron nan ko tsiya, sam ban ji dadin sanin yaron nan da tayi ba, me kuma xata yi da iron idan ba fitina ba anjima ta hada kayan ta bada a goge mata gun masu laundry, wannan wani irin kaskanci ne fisabilillah, to ita Ina nata iron din?" Imaan tace "Daga ranan Ummi ta ce ya mata shocking shikenan Inna ta saka a bola" Ammi tayi salati tace "Wannan tsohuwa dai Allah ya raba mu da ita lafiya, ynxu abinda nake so da ke idan ta dawo anjima ki dau wayarta kiyi blocking number sa sannan kiyi deleting don ba mutunci take siya maki a gun sa ba, snn ki nuna masa baki son ma yana xuwa bangarenta kwata kwata" a hankali Imaan tace "Toh" Hijab kawai ta sa ta fita kofar gida, waya na kare kunnensa ya kafeta da ido har ta iso inda yake, katse wayar yyi yace "How are you doing dear" tace "Alhmdllh ya aiki?" Yace "Fine Alhmdllh" Bude motar yyi ya fiddo wani leda ya mika mata yace "Gashi ki ba Grandma" Shiru tayi bata ce komai ba, can ta amsa tace "Toh angode" wani ledan ya fiddo ya mika mata yace "This is for you" Ta girgixa kai tace "A'a nagode" a hankali yace "Bana son Ina baki abu kina ce min A'a dear" tace "Ni dai nagode" kallonta ya tsaya yi, dai dai nan mota yayi parking bayan nasa, Bude motar aka yi Umma ta fito, kallonsa ta dinga yi sannan ta kalli Imaan ta kara kallonsa ta kalli Imaan, Sadeeq ya gaisheta with respect, Sai da ya kara gaisheta ta amsa da sauri tace "Lafiya lau" Tana isa gate ta sake Juyawa ta kallesa saura kiris ta fada bakin gate din tayi maxa ta shige ciki, Sadeeq da ya bi ta da ido ya kalli Imaan dake wasa da fingers dinta yace "Who is she?" Imaan ta kallesa ta d'an yi murmushi tace "Mum din Yaya" Sadeeq yace "Ohk, but why didn't you greet her" Shiru tayi kamar baxata ce komai ba, can a hankali tace "Xan gaisheta ai idan na shiga" yace "Noo, that's not a point..." Ta d'an yi murmushi kawai, yace "Though I don't know why is that, and I am not suppose to intrude into family issue but promise me xaki dinga gaisheta daga yau, ita din ai babbace" Imaan ta kallesa, yace "Yea promise me" sunkuyar da kanta tayi a hankali tace "Toh in sha Allah" yayi cute smile dinsa yace "Maa sha Allah" kan wani farin kujerar roba ya ajiye ledan da ya bata ta ki ta amsa yace "Shikenan sai mu yi sadaka da shi tunda baki so, I am leaving now, mum dita na jirana" Bai jira cewarta ba ya shiga motarsa ya tada, d'an murmushi tayi cikin sanyayen murya tace "Toh nagode" ya kashe mata ido daya ya ja motar ya bar layin, a hankali ta kai hannu ta dau ledan ta wuce ciki. Sai kusan Isha ta tafi kai ma Inna abincinta bayan Ammi ta kara maimaita mata tayi blocking number Sadeeq a wayar Innan sannan tayi deleting, tana isa parlon ta ajiye abincin da ledan iron din ta gaida Inna dake goge gogen kayan kallo, Inna tace "Allah dai ya bar ni da ta rasulu kawai, Ni fa ta fiye min wasu daga yan uwa da basu da kirki ynxu, har maganar ki da yaron nan Sadeeq sae da na mata yanxu kawai kudi xan bada a kauda idon makiya a lamarin, gobe ma xan ba Mujaheed kudin ya kai mata, wa xai xauna yanxu?? Kowa ya tashi tsaye ya nemi kariya kawai" Imaan bata dai ce mata komai ba ta xauna ta dau wayarta dake kan kujera tace "Inna ga iron dinki an kawo daxu" Inna tace "Haba, Kai Allah masa albarka, to da Ahmadu ne sai dai yace min ya manta, kinga alamar wnn yasan darajan babba ko to ni dai ba ruwana, idan xaki rikesa hannu bibbiyu ki rikesa mijin aurena wllh, Allah dai ya saka masa da alkhairi, ke kuma na gaji da ajiyar wayar da ya kawo maki idan baxa kiyi amfani da shi ba a tafi kasuwa ki siyar kudin xai yi maki amfani" bata jira cewar Imaan ba ta shiga ciki, har Imaan ta gama blocking da deleting lambar Inna bata fito ba, tana kokarin tashi tace mata xata tafi, Inna ta fito duk ta hada xufa a gigice tace "La ila ha illallahu Muhammadur rasulillahi sallallahu alaihi wassalam, Innalillahi wa Inna ilaihi raji'una, laaa haula wala kuwata illa billahil Aliyul azeem... To barawo ya sace wayar" Imaan ta mike tana kallonta da mamaki, Inna ta fashe da matsanancin kuka tace "Wlh a karkashin kwalla na adana ledan wayar yanxu ko sama ko kasa wani ya shigo ya sace ban san waye ba, na shiga uku na lalace dukiyar mutane, Allah ka rufamin asiri" Mayafinta ta fixga ta fice daga parlon tana rusa kuka, Imaan dai tayi still tana kallon kofar dakinta can ta bi bayanta, tuni har Inna ta isa part din Abba, Imaan ta shiga nasu part din, Inna na shiga su Maimoon na gaisheta cikin kuka tace "Ina Ahmaduna yake?" Mujaheed dake sakkowa downstairs ya dinga kallonta da mamaki Aunty dake xaune parlor kuwa sai tambayarta me ya faru take, Inna ta rushe da sabon kuka ta xaune kasa tace "Nashiga uku, Ahmadun bai dawo bane?" Umma ta leko parlon daga kitchen bata dai fito gaba daya ba, Mujaheed ya karaso yace "Wai me ya faru ne??" Cikin kuka tace "An sace wayar da Bulasawa ya kawo ma Imaan a dakina cikin kwallaa...." Ta kunce ha6ar xaninta ta rufe fuska ta dinga kuka tace "Yanxu wani kallo yarinyar nan imaan xata min, wayar fa ance ya kai dubu dari biyar... Wayyo ni dai na shiga uku an goga min bakin fenti" Umma sai xaro ido take daga kofar kitchen tana kallon Inna jin ta ambaci Bulasawa, Aunty tayi tagumi tana kallon Inna, su Maimoon da Rahama kuwa banda dariya babu abinda suke kasa kasa.
*imaan isn't free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah. Subscribe and read happily.
35....
Aunty tace "Daxu da kika fita baki kulle kofar bne Inna?" Inna na sharban kuka tace "Wllh na kulle Amina sai dai idan sabon makulli aka yi aka bude kofar..." Da mamaki Aunty tace "Ikon Allah, amma mu je dai a kara duba dakin Inna kila dai baki duba a nutse bane" a fusace Inna tace "oh oh Allah, Wani dakin xa aje kuma bayan nace maki duk na xaxxage kayan kwallan, wllh sacewa aka yi, kuma wannan barawon da ya san ni ne, yasan me nake ciki a rayuwa" Aunty na kokarin danne dariyarta tace "Gaskiya wannan abu da mamaki, anya ba Imaan din bace ta dauke kayanta kuwa??" Inna ta tsuke fuska tace "Don Allah Amina ki rabu da ni kiyi ta kanki, idan baxa ki fadi alkhairi ba kiyi hakuri ba don ni ba don Allah kiyi shiru, ta ina Imaan xata dauke waya bata gaya min ba" Tuni Mujaheed ya koma dinning ya xauna ya bude warmer yana diban abinci, Sallaman Abba yasa Inna ta mike tana matsar hawaye tace "Ahmadu yau an shafa min bakin fenti a gidan nan, ban san wanda ya shiga ya sace wayar da Bulasawa ya bani in ba Imaan ba, wayar tayi na miliyan Ahmadu, ka rufa min asiri mu tafi aje a sake dubawa, da wani idon xan kalli Bulasawa idan yaji labarin waya ya bata a wajena" Abba dake tsaye ya ma rasa abinda xai ce sai kallonta yake da mamaki, can dai ya girgixa kai yace "Wayar ta miye yaron ya kawo da ba mu da labari??" Inna ta wani hade rai tace "Ta imaan ce wayar ya kawo mata kyauta, kuma ta hannuna wayar ya biyo, ko an daina ihisani ne a duniyar?" Abba yace "Amma da ya bada ai sai ta kawo nan ta nuna min tunda shi Sadeeq bai nan, wannan bai kamata ba sam inna, a kan wani dalili ma xai bata waya??" Inna tace "Kaga Ahmadu kayi hakuri kar a shashantar da xancen bacewar waya mu tafi mu nemi waya duk inda ya shiga" Abba ya dinga kallonta, a fusace tace "Ahmadu kana kallona, don Allah ka shiga gaba mu je, idan ma ya kama a fiddo duk kayan cikin dakin sai a fiddo, yau dai xan ga batar nono a kirjin Budurwa" Kofa Abba ya nufa ta bi bayansa fuska a tsuke, Aunty ta fita ita ma, su Maimoon ma suka bi bayanta, Mujaheed dai cin abincin sa kawai yake a nutse, Umma da ta makale a kitchen, tana jin sun fita ta fito da sauri, duk ta hada xufa tace "Mujaheed, wani Bulasawan Inna ke nufi?" Mujaheed ya kalleta yana cin abincinsa a hankali yace "Ni ma ban gane xancen da take ba gaskiya" Umma ta tafi sama sai gata ta sauko da hijab xata tafi bangaren Inna, shi dai Mujaheed bin ta kawai yake da kallo har ta fita, Tana isa part din ta shiga parlon ta ga su Maimoon na ta fito da kaya daga cikin daki, Inna na tsaye daga gefe sai wurwurga ido take, Abba dai na tsaye daga bakin kofa ya rungume hannu, Aunty kuma na can uwar dakan Inna, Inna ta saki salati ta rushe da kuka tace "Kin ga ta kanki yau patuu, tunda uwata ta haifeni ba a ta6a ban ajiya ya bace ba..." Umma ta shigo parlon cike da damuwa tace "Wai har yanxu ba a ga wayar ba Inna?" Inna na goge hawaye tace "Wllh ba a gani ba Rukayya, ranan Ina bakin pampo ina gurje daudar wajen sai ga yaron ya shigo...." Umma tace "Wani yaro?" Inna tace "Bulasawa mana, waye bai san imaan da Bulasawa ba kuma a gidan nan, ba dai Bulasawan da kansa ba, d'an cikinsa ne dai, wllh yana bani wayar bayan ya fita kinga inda na ajiye wayar can" Umma ta kalli inda Inna ke nuna mata, Inna ta fashe da wani sabon kuka tace "Ni dai yau xan ga batar nono a kirjin budurwa ni Asabe" Umma dai ta kasa tsaye waje daya, Kai kana ganinta xaka ga tashin hankalin da ya ki boyuwa karara a fuskarta, Dakin Inna ta shiga ta gama xagaye xagayenta sannan ta fito tace "Kuma Inna babu kowa parlon San da aka baki wayar?" Inna ta d'an yi shiru sannan da sauri tace "D'an ki ne Mujaheed kadai a parlon a lkcn, Toh ga dankareren dankunnen zinari ma da ya bata ta bani ajiya bai bata ba, duk da ranan ba kowa a parlon ta bani, waya dai Mujaheed na wajen lkcn" Inna ta xaro ido ta dafe kirji tace "To ko dai sata Mujaheed ya fara a gidan nan ba a sani ba??" Umma dai sai hada xufa take tana kallon inna, Inna ta kalli Abba tace "Anya Ahmadu baxa a caji Mujaheed ba, wllh shine a parlon ranan, Ni dai na shiga uku na lalace" Abba dai bai ce mata komai ba, Umma ta dake tace "Inna bari in kashe gas na daura ruwan shayi, xan dawo yanxun nan, ae wannan babban magana ce" Inna tace "Yi maxa kar ki ja wata fitinar ba a gama kashe wata ba" da sauri Umma ta fita, tana komawa bangarensu bata ko kalli Mujaheed ba ta wuce sama jikinta na rawa. Washegari har Ammi ta gama soye soye a kitchen shiru imaan bata fito ba, dakinta Ammi ta shiga don ya ci ta fito ynxu ta gama shirin islamiyya, kwance Ammi ta ganta cikin duvet, ta cire duvet din tana kallonta ta kai hannu jikinta, janye hannun tayi tana kallonta tace "Imaan?" A hankali imaan ta bude idonta da ya rine tana kallon Ammi, Ammi ta xauna gefen gadon da damuwa tace "What's wrong imaan?" Da kyar ta nuna ma Ammi kanta murya can kasa tace "It's aching me" ta nuna ma Ammi kafafuwanta ma, Ammi ta dinga kallonta cike da tausayi tace "Kin daina shan maganin ki ko daughter!" Imaan ta girgixa mata kai kawai ta kasa cewa komai, mikewa Ammi tayi ta wuce bathroom dinta ta hada mata ruwan wanka ta fito ta daga ta, ita ta taimaka mata har xuwa bathroom din sannan ta fito, ta ciro mata kayan da xata saka sannan ta fita, Imaan na fitowa wanka ta kwanta kan gado daure da towel ta rufe jikinta da duvet, Ammi ta dawo dakin rike da cup din shayi da ledan bread ta ajiye kasa tana kallonta tace "Toh tashi ki shirya sai kiyi breakfast ki sha magani" Ganin she is shivering Ammi ta dauko cream dinta ta taimaka mata ta shafa sannan Imaan ta saka kayan da Ammi ta fiddo mata, shayi kawai ta sha da drugs dinta sannan ta kwanta Ammi ta fita da cup din. Aunty ce xaune parlon Abba bayan ta kawo masa breakfast, ganin mood dinsa tace "Don Allah ka daina damuwa da abubuwan inna, kun fa fi kowa sanin halinta, Bai kamata kuna sa abun a rai ba, kuma uwa ce fa" Abba ya girgixa kai yace "Ni kadai baxan iya dinga nuna ma Inna abinda ya dace da wanda bai dace ba, ya kamata ku ma ku dinga contributing...." Aunty ta sake baki tace "Mu a suwa Alhaji, ku ma ya ku ka kare balle mu, ai sai ta kora mu gidajen iyayenmu..." Abba yace "Wannan ba point bane, idan a nuna mata ta gyara ai da matsala babba, Dama ta fi sauraran Sadeeq to shi baya nan, ni kuma inyi magana ta fara min kuka, wllh duk abubuwa sun taru sun min yawa a kai" Aunty tace "Ai tana jin maganan Mujaheed ma" Abba ya kalleta yace "Toh cewa tayi a tafi Police station Mujaheed ne ya dauke waya, har da kukanta fa, Yanxu fisabilillahi maganan nan ya maki dadi?" Aunty ta kasa danne dariyarta tace "Tsufan kenan ai Alhaji, a dinga yi mata uxuri don Allah, Toh shi me Mujaheed din yace?" Abba ya girgixa