Showing 195001 words to 198000 words out of 303099 words
dai ta wuce sama tayi knocking kofar parlor din Mujaheed, sai da ta kara knocking har sau biyu sannan ya bude door din bedroom dinsa, tace "Abba yana kiran ka a kasa" yana gyada kai a hankali yace "You know what Imaan??" Tana kallonsa tace "What??" Yayi wani murmushi yace "I want you to keep this at d back of ur mind... all this ur pretence and everything you are doing... Billah ranan da xan rama yana nan xuwa, I will make u regret all this you are doing in sha Allah" on a serious note ya fadi haka, ta buda ido sosai tana kallonsa da mamaki tace "Pretending kuma? What am I pretending yaya? Ni ban gane ba" yace "Bana son ki gane dama" tabe baki tayi ta juya ta bar wajen ya bi ta da kallo har ta fita sannan yyi wani murmushi. Inna na kallonsu Abba tace "Ni fa ko rantsuwa nayi da kyar inyi kaffara Ahmadu, wai ya xa ku maida ni yarinya da bata san abinda take bane, komai na fada ku karya ta ni ne?? nace maku yarinyar nan mayya ce ita ta kama min jika yake ta ciwace ciwacen da ba na Allah...." Katse ta Daddy yyi ya mike yace "Ke dai Inna ki daina haka, don Allah ki rufa mana asiri ki daina, ni fa gaskiya ba ruwana idan kika jawo wata maganar, ya xa ki dinga kiran yar mutane da mayya kai tsaye, Haba inna.... kin san wannan ba magana bace karama kuwa??" Tagumi Inna tayi a hankali tace "Naga abinda ya isheni ni patuu... Me yasa Bukar ke min haka a rayuwa" Daddy yyi yace "Ni gaskiya nake gaya maki, kiyi hakuri ki daina wannan abinda kike ba shi da amfani, duk wanda kika ji bai maki ba sai kice masa maye?? Haba don Allah, ke kin xata maita karamin abu ne, wllh ki daina haka bai kamace ki ba kwata kwata, haka kawai ki dage kina ce ma yar mutane mayya ki dauko mana wata maganar, this is very wrong wllh" Shi dai Abba kansa na kasa, Inna dai bata kuma cewa komai tayi tagumi, kawu Audu yyi kasa da murya yace "Hajiya yanxu da xa a kai maganan nan gaba...." Tsawa tayi masa tace "Kai d'an tsut ka fita harkata, idan an kai sa gaba uwaka xa ayi?? kada wanda ya sani a bakin duniya gaskiya, da kansa ya kori matarsa ni ban koreta ba...." Shiru kawu Audu yyi bai kuma cewa komai ba, Mujaheed ne ya sakko parlon cikin kananun kaya, Abba ya daga kai yana kallonsa ko kiftawa babu ganin yanda ya rame, Daddy ma kallonsa ya dinga yi da mamaki, ya karasa parlon yyi kasa da kai ya gaishesu, Daddy yace "What's wrong with Muhd?" Ya d'an yi murmushi yyi kasa da murya yace "It's just malaria amma da sauki sosai Abba" Daddy yace "Are u under medication?" ya gyada kai yace "Sure sir" Kallonsa kawai Abba ke yi shi dai ya kasa cewa komai, Daddy yace "But did you have any problem Mujaheed, wannan anya Malaria ne kadai..." Inna ta tabe baki ta mike murya can kasa tace "Har da kamun mayya ko kun ki ko kun so" daga haka ta nufi kofa fuska daure, Daddy ya bi ta da kallon gefen ido, sai bayan da ta fita parlon gaba daya Abba yace "Me ya hada ka da matar ka kace ta tafi gida??" ya shafa kai a hankali yace "Abba...." Sai kuma yyi shiru, Daddy yace "Bama son jin komai my friend, get her back immediately, am I clear??" Mujaheed ya kallesa ya kasa cewa komai da farko, can a hankali yace "In sha Allah Abba" Kawu Audu yace "Toh xa mu je asibitin ne yanxu??" Mujaheed ya kallesa yace "A'a ina amsan medication a gida kawu, ai da sauki sosai yanxu" Kawu Audu yace "Toh Allah ya kara lafiya Muhd, Allah ya yaye maka" Mujaheed yace "Ameen" Mikewa Abba yyi yace "Ka dai ji abinda aka ce maka yanxu, get her back today, sannan I want you to try all possible means of stoping ur grandma from coming to this house" murmushin karfin hali Mujaheed yayi yana kallon Abban nasa, daddy yace "That's just it" Daddy na kallon Imaan dake xaune yace "Ke kuma mai nuna mata hanyar xuwa gidan ko?" Mujaheed ya kallesa da sauri yace "A'a Abba ta san hanya ai...." Imaan ta sunkuyar da kai bata ce komai ba, Daddy yace "Toh tashi mu wuce" Mikewa tayi ta nufi kofa, Daddy yace "Allah ya kara lafiya M.A" Mujaheed yyi murmushi yace "Ameen" Abba yace "Anjima ka taho gida tare da matar taka" yace "Toh in sha Allah" Kawu Audu yace "Sai ayi ta hakuri ka ji?" Murmushi kawai yyi ya sauke kansa kasa, har bakin mota ya rakasu, Imaan ta shiga bayan motar tana kallonsa tace "Allah ya kara lafiya" ya gyada mata kai kawai bai ce komai ba, Daddy ya shiga front seat, Abba ya shiga maxaunin driver yana kallon Mujaheed yace "An kawo kudin auren kanwarka, we will talk later idan ka xo gida" A hankali Mujaheed na gyada kai yace "Toh Allah ya sanya alkhairi...." Abba yace "Ameen" Mujaheed ya kara masu sallama suka bar compound din ya juya kamar me counting steps dinsa ya koma parlor ya xauna saman kujera ya jinginar da kansa jikin kujerar ya lumshe ido yana jin xuciyarsa na masa xafi. Umma na barin gidan tare da Safeenah dama bata yarda Safeenah ta tafi gidansu ba, ta lallabata da kyar suka wuce gidan Hajiya Saude, Hajiya Saude ta sauke ajiyar xuciya bayan Umma ta koro mata duk yanda aka yi, ita dai Safeenah sai hawaye take tana jin da yau xa a mika mata wuka daga ita sai Imaan a daki babu fa abinda xai hanata ta kasheta, bata taba jin tsanar mutum kamar yanda take tsanar Imaan ba, wai a kanta Mujaheed ya daga hannu ya mareta har sau biyu, for what??? Hajiya Saude tace "Kuma har sun kawo lefen koh???" Umma na share xufar da ke keto mata cikin tashin hankali tace "Wlh muna hanya Ummi ta kirani wai ga kaya an kawo, akwatuna har sha biyu da sadaki kusan miliyan daya, ni abun duk ya kwabe min wllh" Hajiya Saude ta bude baki tana kallon Umma, can tace "Amma wannan uwar yaron anyi tsinanniya, wato hauka ta manna mana wai xa tayi shawara" Umma tayi tagumi bata ce komai ba, Hajiya Saude tace "To yanxu meye abun yi kuma??" Umma tace "Auren nan fa ko ana ha maza ha mata baxa ayi sa ba in dai ni Rukayya ina da rai, wato sun ma ci bulus kenan da uwarta idan na hakura aka yi auren" Hajiya Saude tace "Gaskiya kam gashi daga ita ba wata balle ace a hakura xuwa wani lkcn" Umma ta mata wani kallo tace "Toh ko da wasu 'ya yan an gaya maki haka nan kawai xan bar imaan ta tafi gidan da xata huta, duk fitsara da rashin kunyar da kakarta ta dinga sa wa ta dinga min ya tashi a banxa ya tafi a banxa kenan, inaaa ai sai dai idan ban haifu cikin uwata Hadiza ba, Imaan sae dai ta ji labarin jin ddin aure amma ba dai ita ta ji ba" Safeenah ta tabe baki tace "Ni dai babban damuwata ta daina xuwa min gidana gaskiya, a kanta har Mujaheed ya daga hannu ya mareni kuma ki hanani gaya ma Hajiyata" Umma tace "Haba Safeenah bai kai ki gaya ma Hajiyar Marafa ba, kin santa da xuciya ki bar ni da shi kawai, kema kinsan haka nan baxai mare ki ba, wllh sai yayi da ya sanin abinda ya aikata, muna nan da ke" Safeenah ta yi tsaki bata ce mata komai ba, Umma tace "Tunda shawarar da kika bada aka yi amfani da shi kwanaki bai yiwu ba yanxu baki da wata shawarar da xa ki kara ba mu?" Safeenah tace "Don an kai lefe da kudin aure ba yana nufin anyi aure bane...." Shiru tayi ta bude jaka jin wayarta na ring, ta fiddo wayar tana kallon screen din, Kallon Umma tayi tace "Shi yake kirana" Umma ta xaro ido tace "Haba?? To dauka ki ji uban me xai ce maki" Safeenah ta wani daure fuska ta daga kiran ta sa handsfree tayi shiru, sallama yyi cikin sanyayyen muryarsa, cike da masifa tace "What did u want from me Mujaheed?" Ya d'an yi shiru sannan yace "I want to say I am sorry, kiyi hakuri tsautsayi ne" ta fashe da kuka tace "Tsautsayi ka daga hannu ka mareni a dakina a kan wata can, kuma a gabanta??" Yace "Nace kiyi hakuri, and take note Imaan ba wata bace kanwata ce, I see no reason xaki daga hannu ki mareta in kyale ki..." Safeenah ta bude baki ta xaro ido tana kallonsu Umma, tace "Wato kirana kayi ka sake min rashin mutunci kenan Mujaheed?" Murya can kasa yace "Not at all Safeenah, Kinsan Imaan ba lafiya sosai gareta ba, kuma ga grandma dinmu a gidan, da ban yi haka ba anything can happen... ni nasan halinta ke baki sani ba, so don't ever, I mean ever.... try giving her a bad look talkless of you laying ur hand on her face, xan iya maki fiye da abinda kika yi...." Sai kuma ya kwantar da murya yace "Yanxu dai I didn't call to talk long plss kiyi hakuri da abinda ya faru idan ma kince xa ki rama shkkn sai ki rama a kai na, but If you try touching my lil sis I will not take it likely with u" Bude baki Safeenah tayi da mugun mamaki tana kallon Umma da ta gwalo ido tana sauraransa ita ma, a hankali Safeenah tace "You called to warn me Mujaheed?" Yace "Not at all, na kira ne in baki hakuri, and tell me where you are now??" Umma tayi kasa da murya sosai tace "Kice kina gida wajena" Safeenah ta tabe baki fuska daure ta ki cewa komai, yace "Am asking kina Ina" alama umma ta dinga mata ta gaya masa tana can gida, ta harareta ta dauke kai tana wani cika tace "Ina gidan ku" Mujaheed yace "Good I am happy baki tafi gida ba, later da yamma xan shigo in sha Allah, I need rest now..." Daga haka ya katse wayarsa. Safeenah ta ja wani tsaki tana kallon Umma a fusace tace "Ni dai Hajiya kin
bari kawai na tafi gidanmu Hajiyarmu ta san abinda ake ciki, aure ko wata uku ba ayi ba an fara mari na sbda wata shegiya, dubi fa hakuri ya kira ya bani amma dubi irin maganganun da ya dinga min da warning?? Infact wai ma me yasa baya ji da kanninsa haka yanda yake ji da ita?" Umma ta tabe baki tace "Uwar ce ta asirce min shi, tun yarinyar na yar karama tana yar yaye yake bauta da ita ke kya ce don shi aka haifota, nayi nayi in rabasa da ita amma inaaa, da yake kinsan lkcn a wajen kakar tasu yake, ita kuma yarinyar kullum sai an kai ta can sai ya maida ta gida da yamma, idan ba karyar kakarsu ba ma cewa tayi da sunansa ta fara magana, amma duk karya ce wllh, a haka dai ta taso ta makalkale ma d'a na sai kice shine Abubakar ubanta, idan kuwa xai dawo hutu gida daga Uk uban tsaraban da yake yo mata hankali baya dauka, kanninsa ko quarter dinsa basa samu wllh, wai ma don abun ya ragu sosai yanxu, ae ba karamin tashi tsaye nayi ba gaskiya, ban yi da wasa ba kam, kwanaki da dadewa fa mijin da Seeyama ke aure yanxu ya so hada imaan din da, kinsan abokinsa ne kuma yaron ga kudi ga hankali amma sbda shi shashasha ne wai da Imaan xai hada sa, ni ko na ruguje xancen gaba daya, shine yaron ya dawo ma Seeyama, yanxu wnn auren ma da ake son a mata shine gaba a kan komai ina jin, kuma bbu mamaki ya ma san yaron Bulasawan..." Safeenah da ke ta kallon Umma tace "Toh ni dai gaskiya tayi aurenta ta tafi gidan mijinta ta kyale min miji haka" Umma ta bude baki tace "Tayi aure kuma? To ai tunanin xata auri yaron Bulasawa ne yasa take raina mutane take ganin ita wata ce, wllh shi yasa take maki kallon hadarin kaji, kallon kowa take kasa da ita sbda tana tunanin yaron Bulasawa ne xai aureta, amma bata san she is mistaking ba, wllh wllh ba mijinta bane yaron in dai ina numfashi, ke kinsan ko gaisheni yarinyar nan da kike gani bata yi kuwa?? Uwarta kuwa jin ta take ita wata ce yanxu a dole ga ta surkar Bulasawa, to xa su kwashi kunyar su kuwa a hannu wllh ba cika baki ba" Safeenah ta tabe baki tace "To ae don an kai sadaki da lefe an sa rana ba shine yake nufin an daura auren ba, in dai ni take ma wani gani gani wllh ta tari aradu ba gamo... Sai na kunyatata in ga ta tsiya in ga karshen auren nata da shi Sadeeq Bulasawa din" Umma tace "Atohh, ni dai dama nace idan aka yi auren nan to fa ban haifu cikin uwata ba, daga ita har uwarta da kakarta sai sun kwashi kunyarsu a hannu ina kallo" Hajiya Saude tace "Kuna ta surutu ni ko har na gama yanke shawarar what next... Kuma in Allah ya yrda naji kamshin nasara...." Umma ta kalleta da sauri tace "Toh ba mu mu sha" Hajiya Saude tace "Amma duk da haka sai mun koma wajen mutumin nan ko xuwa gobe"
Bayan Magrib Mujaheed yayi parking kofar gidansu ya fito ya kulle motar gaisawa suka yi da mai gadi dake bakin gate, Mai gadin na kallonsa yace "Likita ba lafiya ne" Mujaheed na kallonsa yyi murmushi yace "Alhmdllh, na ji sauki" daga haka ya shiga compound din, direct part din Inna ya nufa walking slowly, a hankali ya murda kofar parlon ya shiga, ido hudu suka yi da Imaan dake xaune parlon tare da Inna da ke ta fiddo kayan cikin akwatunan lefen da aka kawo bakinta har kunne, Ta Rasulu ma sai aikin fiddo ubansun kayan take tana cewa "Toh ga dai kaya ba laifi an xuba karyar naira, ko da yake suna da shi ne, Ni fa nasan har uwar Bulasawan nan a da wllh, don akwai wata makociyata kawar kanwarta da suke uwa daya tana ma uwar Bulasawan aikatau, lkcn ma kudin bai bunkasa haka ba, toh sai makociyar tawa ta ja ni wataran muka je gidan kawar kanwarta wai xata kai mu gidan kakar shi mijin Imaan wato uwar Bulasawa, sunan uwar tasa Hajiya Salamatu, tana nan wata doguwa fara, duka duka bata fa wuce mu ba amma kirkinta ragagge ne...." Inna dai sai kallonta take kasa kasa, ta Rasulu ta tabe baki tace "yo ragagge mana, a lkcn Ina goyon Shamsu daga ya mata fitsari a cafet, ga abinci mai lafiya da xuka xukan kaji an xubo mana xa mu ci in gaya maku abincin da ban ci ba knn don matar nan cewa tayi in tafi gida in canxa masa kaya xarni ya isheta, nan ko bata san har da kashi yyi ba ina ta boyewa ne har sai mun ci abincin, ni dai har da d'an kwalla na na bar gidan ina dukan shamsu, kafin in dawo kuwa su shafa'u suka side kwanon tass da ke kinsan dangin mayu ne, ni dai abincin ko a halshe na" Maimoon dai sai taya su fiddo kayan take bata ko kalli ta Rasulu ba, Duk suka kalli Mujaheed da ya shigo parlon ya tsaya yana bin akwatunan da kallo, Inna ta washe baki tana kallonsa tace "Mujaheed takwarata tayi goshi wllh, ko atamfar dubu ashirin Ina jin babu a nan, gwalagwalai kuwa mun kirga biyar da ta Rasulu, to me xance ma Allah banda in gode masa?" Imaan dai sai danna wayarta take, Mujaheed yace "Toh Allah ya sanya alkhairi" Inna tace "Ameen, kuma kayi hakuri da abinda iyayenka suka maka, ka dai fi su nesa ba kusa ba, in sha Allahu idan Allah yasa aka daura auren nan lafiya kai xaka kai Imaan har dakinta kayi mata fada sosai sannan mu taho gida mu bar ta" Dariya Maimoon ta dinga yi tana kallon Imaan da taki dago kanta, Inna ta tsuke fuska tace "Ke ba batun dariya bane, magana ta gaskiya shi xai kai ta gidanta... Ke kinsan wahalar da yyi da ita ne kuwa" Ta Rasulu tace "Wahala kuma ai ya tashi a banxa tunda ba shi xai aureta ba, kyansa ace wannan uban shakuwar da suka yi kawai ya aureta suje can su xauna tare, abinda ma ya fi kowa saninta a duniyar, ba shikenan sai su haifo santala santalan 'ya yansu su xube ma Aisha tayi ta bari barin da bata yi ba da, ku dai xumuncin ku duk kame kame ne ba shi da wani karfi Allah na tuba, Banda haka ba sai ayi tuwona maina ba ko don Rukayya ta hadiye xuciya ta mace, ita kenan fa gare Bukar a duniyar...." Tagumi Inna tayi kamar xata yi kuka tace "Ni dai naga abinda ya isheni ni Asabe... Wa ya gayyato min wannan mata??? Huuu gaskiya ta Rasulu kin lalace, ke kinsan uban sa6on da kika buga yanxu ki ja mana girgixan kasa kuwa? Kai wasu dai kyansu dawanau wllh" Ta Rasulu tace "Sa6o don nace da Mujaheed ya auri yar uwarsa Imaan? Ke dai baki son gaskiya, kuma baki tsoron Allah, Asabe kinyi watsi da tsoron Allahn ki tun tale tale, kai tun kina gidan Alhaji isuhu, kawai jin ki nake idan kince wasu basu tsoron Allah" Inna da ta wani tsuke fuska tace "To bari kiji, wllh da Mujaheed ya aure min jika gwara tayi ta xama ba aure ina kallonta, me xata ci da sauran Safara'u Allah na tuba?? Me xata yi da surka irin Rukayya ta6a66iya, ke ma dai wllh muguwa