Showing 288001 words to 291000 words out of 303099 words

Chapter 97 - Imaan Book 1 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

2238

dinga kallonta sannan yyi murmushi yace "Mun kawo..." ta fara kalle kalle, ya sauka motar ba tare da ya dau envelope din ba ya xagayo ya bude mata side dinta, sosai sisters dinsa dake gidan har lkcn basu koma kaduna ba suka ji dadin ganinsa, babu wanda ya wani considering din Imaan sai Seeyama da ta xo gidan ranan ita ma, Imaan ta xauna saman kujera ta sunkuyar da kanta bayan sun gaisa da Seeyama, daga sama Umma ta sauka ta shigo parlon tana kallon Mujaheed tace "Sannu da xuwa" yace "Yauwa sannu umma" Imaan ta sauko kasa a hankali tace "Ina yini Umma" umma ta kalleta tace "Lafiya lau ya gida?" Imaan bata dago ba still tace "Alhmdllh" Umma ta kalli Mujaheed dake gaisheta shi ma ta amsa ta xauna tana tambayarsa ya aiki, yace "Alhmdllh Umma, ya gida fa" tace "Lafiya lau, sannun ku da xuwa" Seeyama ce ta mike ta wuce kitchen ta dauko masu ruwa da lemo, ita kam har yau shiru ko 6ari bata yi ba, kana ganinta kasan tana tare da damuwa sosai don duk ta rame, ta fito kitchen ta ajiye ma Mujaheed lemo da ruwan, sannan ta kai ma Imaan nata, Imaan ta kalleta tace "Nagode" Seeyama tayi murmushi ta tafi ta xauna. Mikewa Umma tayi ta wuce sama Mujaheed ya bi ta da kallo, Ummi na kallon Seeyama tace "Aunty Seeyama mu je mu gama girkin toh" mikewa Seeyama tayi ta bi bayanta xuwa kitchen, Rahma ma ta tafi ta ci gaba da wanke wanken da take, sae a sannan ya mike ya tafi kitchen don cin uban kannin nasa. Bacci imaan ta dinga ji amma ta ki kwanciya, ta dai jinginar da kanta da kujera ta lumshe ido, bayan kusan minti biyar ta bude ido da sauri jin abu na taso mata ta dalilin aroma dake fitowa daga kitchen, mikewa tayi ta rufe bakinta ta rasa inda xata, Seeyama da fitowarta kenan tare da Mujaheed tace "Subhanallah me ya faru" kofa Imaan ta nufa xata fita compound kafin ta isa kofar aman ya taho mata, lkci daya ta xube wajen ta dinga kwarara amai, Seeyama ta isa kusa da ita da sauri ta durkusa ta riketa tace "Sannu Imaan, baki da lafiya ne?? Sannu" Mujaheed ya kasa karasawa ya tsaya yana kallonta ganin umma dake sakkowa downstairs ita ma tana kallon imaan, Umma ta karasa gun su tace "Subhanallah, Me ya faru Seeyama?" Cike da damuwa Seeyama tace "Amai take yi" Umma na kallon Imaan tace "Sannu" Kasa cewa komai Imaan tayi wani aman na taso mata, Umma ta dagota sai ga shi ta fara kwararo wani aman, hakan yasa Mujaheed ya taho wajensu, Seeyama ta tafi debo ruwa da sauri, Umma dai sannu kawai take mata, sai da aman ya tsaya mata sannan Umma ta nufi sama da ita Mujaheed ya bi su da kallo.



*Imaan isn't for free* it's 300 via


Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788


*Albishirinku 'yan uwa*

Shin ko kun San zaku iya magance mafi yawan cututtukan da suka addabi al'umma yanzu cikin sauki?
Sinadarin _Stemcell total care_ yayi fice wajen magance matsalolin diabetes, BP, asthma, sickler, cancer, stroke, rashin haihuwa, fibroid, infection da duk wata matsala da ta danganci lafiyar Al'umma.
Ba wannan kadai ba, akwai coffee na double root Wanda ke inganta duk wani abu da ya shafi rayuwar aure ga maza da Mata, inganta qwayoyin haihuwa da dai sauransu.
Akwai sinadarin rage tumbi da dai sauransu.

*Domin neman qarin bayani ku tuntubi wannan lambar 07068136856*
Sai an gwada akan san na kwarai.

Where are those ladies with kwaikwaido hair??😆

To maxa ku garxayo Khaleesat ta sama maku wani oil da ku da cute babies din ku mai shegen kyau da xai mayarshe ku indian's, it's tested and trusted sisters sai kun xo.... Thanks





103....





Mujaheed na xaune gefen Imaan dake bacci a dakin Umma Seeyama ta shigo dakin da abinci ta ajiye masa tace "Yaya ga abinci Umma tace a kawo maka nan" Yace "Ohk thanks" ajiye abincin tayi tana kallon Imaan tace "Ya jikin nata?" Yace "Alhmdllh, ya Mai gidan ki?" Tace "Yana lafiya qlau" yace "That's good" juyawa tayi ta fita dakin, Mujaheed ya juya ya kalli Imaan dake bacci ya kai hannunsa forehead dinta a hankali yaji bbu xafi jikinta, ya dauke hannunsa sannan ya bude daya daga warmer din abincin da Seeyama ta kawo, stew ne dake ta xuba kamshi, Imaan ta bude ido ta mike da sauri tana rufe hancinta da kyar tace "Yaya meye shi?" Murmushi yyi ya rufe miyar ya kalleta yace "Sweet dita ce" Bata tanka sa ba ta koma can karshen gado ta kwanta a hankali har sannan bata bude hancinta ba, a haka bacci ya kara dauketa ya mike ya xaga kusa da ita ya duka a hankali ya janye hijab din daga fuskarta yana kallonta ko kiftawa babu, murmushi yyi ya kai lips dinsa cheek dinta sannan ya mike ya rage ac din dakin ya fita ya kullo mata kofar. Umma na parlor tare da Seeyama dake cin abinci mujaheed ya shigo, Umma ta kallesa tace "Ya jikin nata?" Yace "Da sauki bacci take" Umma tace "Toh Allah ya sauwake, har ka ci abincin ne?" Yace "Idan nayi sllh xan ci Umma" ta kalli agogo tace "Ohk it's almost time" yace "Eh lkci ya kusa" daga haka ya fita daga parlon ya tafi gun motarsa ya bude ya fiddo envelope da ya taho da shi ya kulle motar ya koma ciki. Yana ta xaune parlor idonsa a kan tv ya rasa ta yanda xai ba Umma takardan har dai daga karshe ya mike ya isa kusa da ita ya mika mata ta amsa tana kallonsa tace "Meye wannan din" komawa yyi ya xauna yace "Na Safeenah ne Umma" kallonsa Umma ta dinga yi babu ko kiftawa lkci daya ta daure fuska tace "Me xan yi da shi? Kuma amfanin me xai min?" Mujaheed ya sauke idonsa kasa yace "Ta kirani last week take sanar min she is pregnant, so shine na tafi na amshi takardan scan din wajensu...." Umma ta dakatar da shi da sauri tace "Karya take, nace karya take, Allah ubangiji kuma yyi maka tsari samun zuri'a da wannan yarinyar, idan ma cikin ne Allah ya san yanda xai yi da shi balle karya take..." Lkci daya hawaye ya kawo idon Umma, Mujaheed dai ya kasa cewa komai duk jikinsa yayi sanyi, Umma na goge idonta tace "A asibitin ku aka mata scan din?" Ya girgixa mata kai, Umma tace "Toh sai su je asbitin ayi scan din kafin a tabbatar, in sha Allahu bata da wani cikin ka, in Allah ya yarda, domin wata manufarta daban ta kintsa wannan karyar, kuma tana son amfani da hakan ne don kawai ta ja ra'ayin ka gareta, Mujaheed ko hanyar gidansu ban baka izini ka bi ba balle kaje gidansu, babu abinda ya hada ka da yarinyar nan, dama can ta dalilina ka santa kuma a ta dalilina ka bar ta in har ka ba ma yarinyar nan da iyayenta listening ears ban yafe maka ba Mujaheed, ko bayan raina bbu kai babu su in sha Allah babu xuri'a tsakanin ka da ita, yanxu akwai abinda nace kayi shine ka sanar mata kuje can asibitin da kake aiki xa a mata scan, kuma albarkacin annabi da al-qurani idan ma cikin ne Allah yasan yanda xai yi da shi, in sha Allahu baxa ta haifa maka d'a ba, Allah ya mana tsari da xuri'a irin tasu...." Mujaheed dai kansa na kasa bai ce komai ba amma duk jikin sa yayi sanyi sosai, Umma ta mike tana goge hawayen idonta da ya ki tsayawa ta wuce sama. Har yamma Imaan bacci take a dakin Umma, Seeyama ta sakko downstairs tayi shirin tafiya tana kallon Mujaheed dake ta xaune parlor tace "To Yaya ni xan wuce, Allah ya ba Imaan lafiya, naga har yanxu bata tashi ba balle mu yi sallama" Mujaheed yace "Toh Ameen, da ta tashi sai mu tafi gaba daya coz we are also going back to kaduna today" Seeyama tace "Ayya ba komai, Allah dai ya bata lafiya Yaya" yace "Ameen, Allah ya tsare hanya" tace "Ameen" dubu biyar ya ciro aljihunsa ya mika mata yace "Kiyi transport da wannan" amsa tayi tana murmushi tace "Toh ngd Yaya Allah ya kara budi" su Ummi ne suka rakata xuwa bakin titi. Mujaheed ya mike ya wuce dakin da Umma ke xaune, ya xauna saman carpet dake dakin yana kallonta a hankali yace "Umma ba sai kin 6ata ran ki a kan wannan magana ba in sha Allah xan yi yanda kika ce, sai taje can ayi scanning din, amma Umma kar ki manta it's my responsibility to take care of her and the child..." A fusace umma tace "Wani child din Mujaheed? Nace maka babu wani ciki, in sha Allahu baxa mu ga ciki ba, idan ma da cikin Allah ubangiji ya san yanda xai yi da shi, wllh Safeenah baxata haifo d'an ka ba in sha Allahu, idan Allah ya yarda kana tare da warce xata haifa maka xuri'arka amma ba Safeenah ba, ko ba komai nasan asali da irin 'ya yan ka" Mujaheed ya sauke kansa kasa shi dai bai ce komai ba amma har ransa ya ji dadin furucin umma, Umma tace "Kana wani min maganan responsibility, responsibility din me?? Ba sai da ciki ake daukan responsibility ba, to wllh idan kana son ganin bacin raina kada ka fita harkan iyalan gidan Hajiya Mansura, duk Ni ce sillar komai kuma ina rokan ka gafaran xamantowa ta silla, ba a mayar da hannun agogo baya amma da banyi abubuwan da nayi a baya ba, Allah ya nuna min ishara ta hanyoyi da ban ta6a xata ba, nan gaba idan Allah ya yarda ko ina k'in abu xan k'i sa saisa saisa, sannan baxan fito fili in nuna kiyayata ba xan bar ma Allah komai, I have learnt a great lesson, kuma na kara tabbatar da mutum ko waye shi bai isa ya ja da ubangiji ba yayi kadan ne, sannan ina mai kara gargadinka ka rike addu'a don hakan shine makamin mumini, ka dage da ibada especiallly at night, never get weak of praying Mujaheed, Allah ubangiji yayi maka albarka, ya baku xuri'ar masu albarka" a hankali Mujaheed yace "Ameen Umma nagode" sannan ya mike yana kallonta yace "Let me check ko ta tashi coz we are leaving for kaduna today" Umma tace "Bata ci abinci ba, idan baxata iya ci ba akwai gruel da muka yi jiya sai Ummi ta dama mata ko xata iya sha" yace "Toh Umma" daga haka ya fita dakin, bedroom din Umma ya shiga ya tadda imaan kwance still sleeping, ya karasa ya xauna gefenta ya daga rigarta yana shafa cikinta a hankali, Bude lumsassun idonta tayi tana kallonsa, Kamar xata yi kuka tace "Yaya na gaji" yace "Kin gaji da baccin koh?" Bata ce komai ba ya dagota ta kwanta jikinsa tana maida numfashi a hankali, unlike daxu, yanxu kam jikinta ya fara xafi, murya can kasa yace "Ina ke maki ciwo sweet?" Bata ce komai ba hakan yasa ya dago kanta yana kallonta yace "Tell me how you are feeling" buda masa hannu tayi alamar bata sani ba ta kara kwanciya jikinsa, yace "Toh xa ki ci shinkafar yanxu? Sai in sa maki miyar kadan" da sauri ta girgixa kai tace "Aa bana so, amai nake ji" yyi shiru sannan yace "Ko xa ki sha kunu kadan" Bata ce komai ba ya dago kanta ta gyada masa kai, ya kwantar da ita ya mike ya fita dakin, yana tsaye kofar kitchen Ummi ta gama dama kunun cikin cup daya ya sa ta saka sugar kadan sannan ya dauka ya fita kitchen din ya koma daki ya ajiye don ya huce, kallonta ya dinga yi don har ta koma bacci, Banda sheki bbu abinda jikinta yake, tayi haske kuma sosai, bayan ya tabbatar kunun ya huce ya tada ta gently, ganin she looks so weak ya jinginar da ita da gado yace "Sorry sweet, ga kunun ki sha kadan sai mu wuce gida koh?" Karban cup din tayi a hannunsa ta kai bakinta a hankali, ko qtr bata yi ba xata ajiye yace "Noo baki sha komai ba" tace "Allah na koshi Yaya" yace "A'a sai kin kai rabi" Kamar xata yi kuka tace "Wllh cikina ya cika" dauka yayi ya daure fuska ya kai bakinta, da kyar ta dinga sha tana hadiyewa daga karshe ta cire bakinta da sauri, ya wani hade rai yace "Sai fa kin kara" toshe baki tayi tana kallonsa, ya jawota da sauri yana patting bayanta a nutse yace "Stay calm baxa ki yi ba..." Girgixa masa kai ta dinga yi xata sauka saman gadon jiri ya debeta ya rikota kafin ta kai kasa nan tayi masa wanka da aman kunun da ta sha, sai da ta fito da shi tass, ya dinga kallonta cike da tausayin ta, Umma ta shigo dakin jin yunkurin aman nata tace "Ko dai xa ku je asibiti Mujaheed?" Yace "A'a Umma ai gida xa mu wuce yanxu" Yana fadin haka ya mike ya daga ta suka wuce bathroom, Umma ta yaye xanin gadon da ya baci da amai ta dau cup din kunun ta fita. Biyar na yamma Mujaheed ya sami Umma a can dakin da take yace "Umma xa mu wuce gida" tace "Baxa ku kwana ba Mujaheed tunda bata da lafiya?" Yace "A'a umma Ina son mu je can gida ne ta sha magani..." Umma tace "Toh Shikenan, Allah ubangiji ya bata da sauki, Allah ya sauwake" yace "Ameen" Hijab din Ummi Imaan ta sa sbda nata da tayi amai an wanke, Mujaheed na rike da hannunta suka fita parlon, kana ganinta kasan she's very weak, ya bude mata front seat ta shiga, Umma tace "Toh Allah ya sauwake Allah ya tsare hanya" Da kyar Imaan ta amsa mata da "Ameen" Mujaheed yayi ma Umma sallama suka bar gidan, Mujaheed na kallon Imaan da ta lumshe ido yana driving a hankali yace "Sweet nace ma Farida idan mun shigo Zaria xa ku gaisa, mu je sai ta fito ku gaisa sannan ku wuce" Imaan ta gyada masa kai kawai don ko magana bata so, yana isa kofar gidan Farida ya kirata, kin fitowa tayi da farko wai sai sun shigo yace mata sauri suke kuma Imaan din bata jin dadi, hakan yasa ta fito ta bude side din da Imaan take xaune, Imaan ta gyara xama tana murmushi tace "Aunty Farida Ina yini" Farida ta rike ha6a tace "Sannu imaan, ashe dai da gaske baki da lafiya" Imaan tayi murmushi kawai, Farida tace "Toh Allah ya baki lafiya, Allah ya sauwake kin ji" a hankali Imaan tace "Ameen Aunty" sai a sannan Farida suka gaisa da Mujaheed, nan tayi masu Allah ya kiyaye tace xata je gidansu in sha Allah idan ta shigo kd, a haka suka rabu Mujaheed yyi reverse ya bar anguwar. Har suka isa kaduna imaan bacci take, yana parking a parking space ya bude motar ya fito ya xaga ya bude side dinta, Bai bari ta sauka motar ba ya dauketa suka wuce gidan, a bedroom dinsa ya kwantar da ita ta rikesa murya can kasa tace "Yaya sanyi nake ji" ya ja duvet ya rufa mata sannan ya kashe Ac din dakin, duk yanda ya dinga lallabata daren ranan ta sha shayi kin sha tayi wai xata yi amai, a haka ta ci gaba da baccinta, karfe goma saura ya shigo ya ganta xaune kan darduma tana sllh, yyi murmushi ya xauna gefen gado yana kallonta, tana idarwa ta kwanta nan kan darduman, ya mike ya dagota ya kwantar kan gado yace "Allah ya karba sweet, but fa sai kin sha shayi xa ki ci gaba da baccin ki" Daren ranan Imaan bata yi wani bacci ba don da xaxxabi sosai ta kwana, Mujaheed ya dinga tattalinta yanda ita ma bata yi bacci ba haka shi ma bai yi ba. Washegari lahadi ya fita ya harhado mata drugs da yasan xa su mata amfani bayan yak'i da yyi da ita ta d'an sha shayin ya bata drugs ta sha, sannan ya shiga bandaki ya hada mata ruwan wanka, duk yanda ta dinga nonnoke masa haka nan ta hakura tayi wankan amma a kunyace yana bandakin. Karfe sha biyu saura ya shiga dakin ya ganta tana bacci sosai, dukawa yyi kusa da ita ya lumshe ido manna mata kiss a lips dinta sannan ya rufeta da bargo gaba daya jikinta ya mike ya sauke curtain ya fita dakin, makullin motarsa ya dauka ya fita gidan, driving yake har ya isa dai dai saman layin su Safeenah, parking yyi ya dau wayarsa ya kirata, tana dagawa yace "Ban gan ki wajen ba" mota ce tayi park gefen nasa sai ga ta ta fito a ciki, bude front seat tayi ta shiga ya ja motar suka bar wajen, har suka isa asibiti bai kalleta ba, ita ko gaba daya mood dinta kamar warce aka ma mutuwa. Yayi parking ya sauka motar ya rufe ita ma ta fito a hankali tana kallonsa, ganin har ya nufi entrance din hospital din ta bi bayansa kamar me counting steps dinta har suka shiga ciki, xaunawa tayi a reception don har ya wuce office dinsa, gaisawa tayi da few nurses da ta sani a wajen, wata nurse tace "Kwana biyu baki biyo Dr ba Madam" Safeenah tayi murmushin karfin hali tace "Ae kuwa" tana ta xaune very restless har wata nurse ta kira ta suka wuce sama.




*Imaan isn't for free* it's 300 via


Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788



*Albishirinku 'yan uwa*

Shin ko kun San zaku iya magance mafi yawan cututtukan da suka addabi al'umma yanzu cikin sauki?
Sinadarin _Stemcell total care_ yayi fice wajen magance matsalolin diabetes, BP, asthma, sickler, cancer, stroke, rashin haihuwa, fibroid, infection da duk wata matsala da ta danganci lafiyar Al'umma.
Ba wannan kadai ba, akwai coffee na double root Wanda ke inganta duk wani abu da ya shafi


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login