Showing 90001 words to 93000 words out of 303099 words
bai kuma ce mata komai ba. Duk yanda Ammi ta so Imaan ta jirata su fita tare kin yarda tayi don tuni ta kira Sadeeq bayan daddy ya amince ta tafi gidan gwaggo ta sanar masa, sai gashi ko 15 mins ba ayi ba ya kirata wai yana saman layin nasu yana jiranta, Ammi ta dinga kallonta da mamaki ganin ko gama rufe karamin trolley din bata yi ba amma xata ja haka ta fita, cikin tsawa Ammi tace "Wai saurin uban me kike haka Imaan??" Waigowa tayi da sauri tace "Ba komai fa Ammi" Ammi tace "Rashin natsuwa ce kenan, ke kam yaushe xaki yi hankali ne irin na sauran jama'ah, dubi fa yanda kike jan jaka a bude saboda hankali ya maki kadan" Daddy dake xaune dinning yace "Komai dai ace sai anyi fada, this isn't fair" Ko tanka sa Ammi bata yi ba, Imaan ta durkusa a hankali ta karasa rufe jakar, Ammi tace "toh xaki iya daukar jakar har bakin titi?" Imaan tace "Ai ba nauyi Ammi, kuma ja xan yi tunda titin layin na da kyau" Ammi tace "Toh Allah ya kiyaye" daga ma Daddy dake kallonta hannu tayi ta fita, ta rufe kofa kenan sai ga Mujaheed ya taho daga part din inna, kallonta ya dinga yi tayi saurin dauke kai gabanta na faduwa, kallon Sashin su yyi sannan ya kalleta yace "Ina xa ki?" Backing dinsa tayi, tayi kamar tana gyara jakar ne ta turo baki tace "Gidan gwaggwo" Jin bai ce komai ba ta leka sa daga durkushen da take, kallonta taga yake yi har sannan ta kara turo baki, jin tafiyarsa ta saci kallon gefenta taga gate ya nufa, sai da ta jira taga fitarsa gaba daya, bayan few minutes ta ja jakarta ta xuwa gate, tsaye ta gansa jikin motarsa ya rungume hannu, gabanta yayi mugun faduwa, ji tayi kamar ta rushe da kuka, tayi saurin dauke kai xata nufi saman layin yace "Xo ki sa jakar a mota" Da sauri ta kallesa sai kuma ta fashe da kuka ba hawaye tace "Yaya Ammi da Daddy fa cewa suka yi in tafi da kai na kar wanda ya kai ni wllh" Wani mugun kallo ya mata yace "Before the count of 3 do what I said now" jingina tayi da gate hankali tashe tace "Don Allah yaya ka wuce wllh bana son ka kai ni xan je da kai na" hade rai yyi sosai ya daga finger dinsa daya yyi indicating da one, sannan two, bata jira ya nuna third finger din ba ta ja jakar hawayen gaske na xubo mata ta bude back seat ta ajiye ta rufe, cikin rawar murya tace "Xan dauko hand bag dina" bai tanka ta ba ya xaga ya shiga driver seat ta koma cikin gidan ta fashe da matsanancin kuka, parking space ta tafi ta tsaya ta yi dialing number Sadeeq, yana fara ring ya katse ya kira ta, ta kai kunne cikin sanyin murya tace "Don Allah kayi hakuri Yaya xai fita aiki yanxu shine yace xai yi dropping dina, ni kuma baxan iya cewa A'a ba kar ya min fada" Sadeeq yace "Ohk no problem imaan, anjima da yamma xanje can gidan in sha Allah" a hankali tace "Kayi hakuri don Allah" yace "Noo ba komai dear, ai yaya ne, kar mu yi laifi ko" tace "Toh nagode" daga haka yyi mata sallama ya katse wayar ta nufi gate fuska daure ta fita, bude motar tayi ta shiga tana cika tana batsewa, ta gefen ido ya kalleta ya tada motar ya bar layin. Sun yi nisa sosai kamar mai counting words dinsa yace "I told u what to tell Abba... but you told him a different thing saboda kin raina ni koh?" A d'an tsawace ya kare maganan, Kin cewa komai tayi sai ma kauda kai da ta yi tana kallon waje, parking yyi ganin haka ta juya da sauri tana kallonsa kamar xata yi kuka tace "Don Allah kayi hakuri yaya, ai ya ma daina kirana, tun shekaranjiya ni bai kira ni ba ma" Fuska daure Mujaheed yace "In ga wayar ki?" Xaro ido tayi tace "Yaya ai yana gida" tana magana tana kokarin boye wayar a jikinta, fixgota yyi, ta yi wani kara ta riko hannunsa tace "Wayyoo yaya me nayi maka..." Ya dage Hijab din jikinta ta xaro ido tace "Yayaaa ka bari" bai saurareta ba har sai da ya kwace wayar, dubawa yyi yaga ta sa password, ya mika mata yace "Bude..." Make kafada tayi tana wani murmushi, ya dinga kallonta kafin ya daura wayar kafarsa ya ci gaba da driving din, har suka iso gidan gwaggwo bai sake ce mata komai ba, ita ma bata ce masa komai ba, yayi parking kofar gidan, bude motar tayi ta fita, shi ma ya fito, ta bude back seat ta dau jakarta ta rufe motar, danna lock yyi ya wuce cikin gidan ta bi sa da kallo kamar xata yi kuka, can ta bi bayansa, Gwaggwo ce xaune parlor tare da wasu yan uwanta duk maxa, Mujaheed ya xauna kasa ya gaisheta sannan su ma ya gaishe su, Gwaggwo da fara'a Gwaggwo ta amsa tana cewa "Ikon Allah, yau Mujaheed ne gidan namu, dama kana garin Mujaheed" ya d'an yi murmushi yace "ina nan Gwaggwo ya kwana da yawa" tace "Lafiya lau... Ka guje ni Mujaheed" Har sannan yana murmushi yace "Kiyi hakuri gwaggwo yanayin aiki ne, xan je anjima da yamma in dawo tun da kina da baki" Imaan ta xaro ido jin abinda yace, Gwaggwo tace "Ka tabbatar Mujaheed" yace "Xan dawo da gaske" tace "Toh madallah, sai ka dawo, Allah ya kiyaye hanya, ina nan ina jiran ka" Imaan dai na makale jikin kofa ta ki shiga gidan, Mujaheed ya fito, kallo daya yyi mata ya dauke kai ya nufi gate, ta bi sa da sauri tace "Don Allah yaya ka ban wayata" wani kallo da ya tsoratata ya mata, ta koma baya a hankali, ya nufi gate ya fita gidan.
Tun da yamma yayi hankalin Imaan ya tashi, tasan yanxu kila Sadeeq ya kira ta wayar Mujaheed kila kuma ya daga, sannan ga Ammi tana gidan, duk abun ya taru ya mata yawa, ita kadai ce kwance dakin Gwaggwo don anty Halima na tare da kawayenta, ana idar da la'asar sai ga Halima ta shigo dakin ta mika ma Imaan wayarta tace "Imaan gashi abokin ya Muhsin xai maki magana" da sauri Imaan ta mike daga kan darduman da take xaune bayan ta idar da sllh ta amshi wayar Anty Halima ta juya ta fita, xaunawa tayi gefen gado tayi masa sallama a hankali, ya amsa yace "Is ur fone down?" Xaro ido tayi da farko ta rasa abun cewa can tace "Um, ka kira a kashe koh?" Yace "Sure" ta langwabar da kai tace "Ehh a kashe yake" yace "Ohk, ina waje fa" ta wani xaro ido again, a hankali tace "Toh ina xuwa" yace "Ohk I am waiting dear" mikewa tayi ta fita, rasa wanda xata gaya ma ana kiranta a waje tayi don tsoron sanar da Ammi take, gwaggwo ta shiga nema, ta sameta a Wani empty room tare da Ammi da maman Halima, ta gaida maman Halima da ta amsa mata da fara'a tace "Ya Abban ki Imaan?" Imaan tace "Yana lafiya mama" daga haka ta nufi gun Gwaggwo ta durkusa murya can kasa tace "Gwaggwo wai Sadeeq yana waje yana jirana" Ammi dai sai kallonta take don bata san abinda take gaya ma mahaifiyar tata ba, Gwaggwo tace "Sadeeq dai da na sani abokin Muhsin?" Imaan ta sunkuyar da kanta, Gwaggwo tace "Ikon Allah, saurayin ki ne kenan" imaan ta boye fuskarta, gwaggwo tayi dariya tace "A'a gaskiya naji dadi, Sadeeq ai yaro ne mai hankali da sanin darajan mutane, tashi ki tafi ina gaishesa, ko kwana uku da suka wuce ya xo gaisheni da Muhsin, gaskiya nayi farin ciki da wannan al'amarin" Ammi dai sai kallon Imaan take, mikewa imaan tayi a hankali ba tare da ta yarda sun hada ido da Ammi ba ta fita, tana fitowa parlor ta ji sallamar Mujaheed, still tayi inda take tsaye, Gwaggwo na jin muryar sa tace "Ashe dai da gaske yake xai dawo" Mamaki ya sa Ammi ta kasa cewa komai jin muryar sa ita ma, mikewa Gwaggwo tayi ta fito parlor murmushi dauke fuskarta tana amsa sallaman tare da few mutanen dake parlon, shigowa yyi suna hada ido Imaan ta juya masa baya da sauri kamar xata yi kuka, ya nufi kujera ya xauna Gwaggwo na masa sannu da xuwa, ta kitchen imaan ta bi ta fice daga gidan. Sauke glass Sadeeq yyi ganin ta, ta sunkuyar da kai har ta isa jikin motar, ya fito ya jingina gefenta smiling cikin cool voice dinsa yace "Good evening" kasa kallonsa tayi, a hankali tace "Ina yini?" Yace "Lafiya lau Imaan, ya Ammi fa?" Ta kalli cikin gidan tace "Tana ciki" yace "Amma ba tare ku ka xo ba ai?" Ta girgixa kai tace "Na riga ta" har sannan ta ki yarda su hada ido, a hankali yace "Kinyi kyau sosai, I love the Hijabs you are wearing, you look so cute in them" boye fuskarta tayi tana murmushi, ya dinga kallonta, kamar warce ta tuna abu ta xame hannunta da sauri tace "Na manta na daura abu a kitchen kar ya kone" yace "Xa ki wuce ciki knn?" Cikin sanyin murya tace "Kayi hakuri, ai mun gaisa" ya d'an yi murmushi yace "Sure, amma ina son mu yi hira sosai, I told you I've got plenty things to let you know imaan" tace "Toh may be later koh?" Yace "After Magrib or Isha?" Ta gyda masa kai, yace "Ohk then, Allah ya kai mu lkcn, before then wait...." Yana fadin haka ya bude motarsa ya fiddo wani abu kamar box mai kyau yace "You put this on for the wedding" kin amsa tayi, gently yace "Take plss Imaan" ta kallesa a sanyaye, ya gyada mata kai murya can kasa yace "Take it" risinawa tayi ta amsa tace "Nagode" ya mata murmushin da ya bayyana dimples dinsa ta mayar masa da light murmushi sannan tace "Sai anjima" daga haka ta nufi gate ya bi ta da ido har ta shiga gidan, sosai gabanta ya fadi ganin Mujaheed ya fito parlon gwaggwo, ya dinga kallonta ta fara tafiya a hankali, kamar warce aka ture ta durkushe nan kasa ta fara yarfe hannu tana xaro ido, ya karaso inda take yace "Daga ina kike?" Hawaye har ya kawo idonta tace "Ammi ta aikeni, yaya na gurde kafar fa" bai tanka ta ba ya nufi gate fuskarsa daure, ta bi sa da kallo gabanta na faduwa ta dinga addu'ar Allah yasa Sadeeq ya bar layin, kallon box din da ta boye a Hijab ta dinga yi kafin ta bude a hankali taga babban dankunnen gwal mai kyau sai talli yake a kwance cikin fancy box din....
*The book Imaan is not free, you read for free ur cup of coffee*🤷🏻♀️
It's 300 via Fcmb 3276052019
Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp digit 07087865788 to be included in the payment group.
29....
Mikewa Imaan tayi da sauri ta nufi cikin gidan tana waigan ko Mujaheed ya dawo har ta shiga ta kulle kofa, dakin gwaggwo ta wuce ta boye box din a cikin trolley dinta, tsoronta daya yanxu Ammi, bata san me xata ce ba idan ta ga dankunnen, bayan Magrib suna cin abinci tare da Anty Halima da wata kawarta, wayar Halima ya fara ring, dauka tayi bayan taga mai kiran ta kalli Imaan tace "Wai ina wayar ki?" A hankali Imaan tace "Yaya ya kwace min" Halima ta xaro ido tace "Saboda me?" Buda hannu Imaan tayi alamar bata sani ba, Halima ta mika mata wayar tace "Toh gama magana tukun" karba Imaan tayi ta kai kunne bayan ta daga hade da yin sallama, Sadeeq ya amsa mata daga daya barin yace "Har yanxu baki yi charge din wayar ki bane Imaan?" A hankali tace "Ehh" yace "But naga akwai wuta ai yanxu, ina ma anguwar" ta langwabar da kai tace "Wayar na gida fa" yace "Ohk after Isha xan kira ki, it's almost time now" tace "Allah ya kai mu" daga haka ya katse wayar, Imaan ta ajiye gefen gado, Halima tace "Haka kawai Mujaheed din ya amshe maki waya?" Tace "Ehh wai saboda abokin Muhsin na kirana" Bude baki Halima tayi tace "Toh shi ina ruwansa" Imaan ta buda hannu tace "Nima ban sani ba" Rabi'ah kawar Halima tace "Yayanki ne kuma?" Halima tace "Cousin dinta dai" Rabi'ah ta d'an bude ido tace "Toh ko son ki yake?" Still Imaan tayi tana kallonta da wani expression, can tace "Yaya ne fa... Yayana ne shi" Rabi'ah tayi dariya sosai tace "Wai yaya ne, to haka kawai baxai dinga hana ki waya da samari yana kwace maki wayar idan babu wani abu a kasa" Imaan ta ajiye cokalin hannunta a hankali tace "Abu kamar me?" Halima tace "Tukunna dae me yace maki da yaga Sadeeq din na kiran ki?" Imaan ta jingina da gado tace "Kawai ya hanani waya da shi ne, har blocking dinsa yyi ni kuma nayi unblocking dinsa, a gida ma da Abba ya kira ni xai tambayeni meye tsakaninmu da Sadeeq kafin in je ya sameni wai ince ban san sa ba" Dariya sosai Rabi'ah take, Halima tayi murmushi tace "Tabb, lallai Mujaheed" Imaan dai sai kallonsu take don bata san me ya basu dariya ba, Rabi'ah ta ajiye spoon din hannunta tana kallon Imaan da kyau tace "Toh wllh son ki yake...." Imaan ta xaro ido ta koma baya da sauri tace "Don Allah ki daina cewa haka plss, wllh yaya na ne fa, Anty Halima yaya fa ne" Halima tayi wani murmushi tace "As far as ba ciki daya ku ka fito da shi ba ki daina deceiving kanki Imaan Mujaheed son ki yake, so mai tsanani ma kuwa, ni dama tun lkcn da yake kawo ki nan few years back ina ganin irin kallon da yake maki nasan ba a banxa ba da abu a kasa, sannan kulawar da yake maki ko kanninsa basa samun haka, abinda Mujaheed ke maki a da ya wuce shakuwa ko so na 'yan uwantaka, ke dai ce ban san lkcn da xaki yi wayo har ki fahimci inda ya dosa, wai yaya ne... A'a ba yaya ba..." lkci daya hankalin Imaan ya tashi ta fashe da kuka sosai tace "Wllh ku daina cewa haka ba kyau, ni ba wani so na da yake yi, ina ce maku yayana ne fa, to taya xai so ni, ni kanwarsa ce fa..." Dariya kawai Rabi'ah take don imaan tayi mugun bata dariya nan kuma ta yarda har sannan Imaan na tare da yarinta ba kadan ba sannan ga ta only child shi sa abun ya taru ya mata yawa, Imaan ta mike da sauri ta fice daga dakin ta koma wani daki ta xauna kan gado maganganunsu na mata yawo a kai, fashewa tayi da matsanancin kuka ta fada kan gadon tace "Ni baxan ma kwana a gidan nan ba, ta ya xa a ce wai yaya na so na, wai yaya fa?? Allah ya kiyaye wllh" Imaan bata ta6a jin abu ya tsaya mata a rai irin abinda Halima da kawarta suka gaya mata ba, wai Mujaheed sonta yake, tabbb, ji tayi ita gaba daya duniyar ma babu wanda take jin haushi kamar Mujaheed din, duk da tasan baxai ma taba yiwuwa ace yana sonta ba, amma abinda suka gaya mata yasa ita taji bata ma son sa shi a ido, bata son ganinsa kwata kwata, lamo tayi kan gado very restless, aka bude kofar dakin ta juya da sauri, Halima ta shigo tace "Gashi Sadeeq ya kira" Imaan ta mike xaune a hankali ta amshi wayar ta kai kunne tare da masa sallama, ya amsa yace "I am outside Imaan" tace "Toh bari in fada ma gwaggo" daga haka ta katse wayar ta tafi ta nemo gwaggo ta gaya mata, Gwaggwo tace "Toh ya shigo mana ai ba kowa parlon ma, ce masa yayi shigowarsa kawai" Imaan bata ce komai ba ta sa Hijab dinta ta fita, tsaye ta gansa ya jingina da motarsa, ta karasa kanta a kasa ta tsaya keeping a enough distance tsakanin su, kallonta kawai yake, ita ko bata yarda ta kallesa ba, a hankali yace "What's wrong imaan you look disturbed" da sauri ta daga kai ta kirkiri murmushi tace "A'a ba komai fa, ya gida" yace "Lafiya lau" tace "Gwaggwo tace ka shigo ciki ba kowa a parlor" Yace "No ni baxan shiga ba kunyarta nake ji yanxu" murmushi Imaan tayi tace "Toh akwai kujeru a compound ai, shi ma baxa ka shiga ba?" Ya shafa kansa smiling sweetly yace "Ohk then mu je" ita ta shiga gaba ya bi bayanta har suka shiga cikin compound din. Sai da ta fara xama kan farin plastic chair sannan ya xauna shi ma yana kallonta, dauke kai tayi ganin kallon da yake mata yace "Amma ba dai kunyata kike ji ba" murmushi tayi tace "Shi nake ji mana" Yayi dariya yace "Aa kiyi hakuri kar ki ji plss" Ita dai bata ce komai ba, bayan few seconds yace "Did you know what imaan" ta daga kai ta d'an kallesa, cikin sanyin murya yace "I am hoping to spend the rest of my life with you" Imaan ta sauke idonta kasa, yace "I was born and bred in Uk, yawancin rayuwata duk can nayi sa, daga baya na dawo Nigeria gaba daya, I've neva for once thought xan hadu da mace yar Nigeria inji ina son rayuwa na har abada da ita sai kan ki Imaan, my ex was white ita ma it's not as if I have much feelings for her, it's just to while away time... Here in Nigeria frndship kadai ne tsakanina da yan mata, Ni ban san meye so ba, I don't even believe in it until I met you few months back, pls don't break my heart imaan, it's too fragile for something