Showing 15001 words to 18000 words out of 303099 words
ji zafin da take ta jira ba, ta dau sauran malt dinta ta fita, xaunawa tayi reception ganin bata gansa ba, bayan kusan minti goma sai gashi ya sakko, yana kallonta ya nufi kofa, da kyar ta mike tace "Yaya na fara jin jiri" yace "Toh ko in bar ki a nan" da sauri ta girgixa masa kai ta isa gunsa, saura kadan ta fadi gun fita, ya kalleta sau daya yyi gaba, back seat ta shiga ta kwanta tana maida numfashi, ya shiga motar ya tada suka bar asibitin, wani pharmacy ya tsaya xai fita tace "Yaya wllh idona juya min yake" nan ma dai bai tanka ta ba, drugs dinta da sabbin da Dr Mukhtar yyi prescribing ya siya mata sae lucozade boost babba biyu, duk ya ajiye bayan motar, har suka isa gida yyi parking a parking lot din daddy bacci Imaan take, daga cikin motar ya dinga lekan apartment dinsu gabansa na faduwa, ya juya ya kalleta, sannan ya fito daga motar, ya bude back seat yace "kee" bude ido tayi da sauri, yace "Sakko" ba musu ta fito daga motar da kyar, ya dau magungunan da drinks din ya rufe motar, da sauri ya juya ganin kiris ya rage ta fadi ya kara kallon apartment dinsu, kamo hannunta yyi ta jingina jikinsa. Har suka isa bangarensu, ya bude kofar ya shiga parlon hade sallama, Imaan ta kwanta saman kujera ya ajiye drugs din hannunsa da lucozade boost ya kalleta kafin yace komai daddy ya fito parlon, yace "Har kun dawo kenan?" Mujaheed yayi kasa da kai yace "Eh mun dawo Abba" dukawa yyi ya dau ledan maganin ya fiddo gaba daya, ya bude wanda xata sha a lkcn yana kallonta yace "Tashi ki sha magani" Daddy ya tafi kitchen don dauko table water da cup, Mujaheed daure fuska kamar tana ganinsa yace "Baxa ki tashi ba?" A hankali ta bude ido ta mike xaune kamar xata yi kuka, daddy ya iso parlon ya ajiye ruwan da glass cup yace "So how much is the bill doctor" kallonsa Mujaheed yyi, sai kuma yyi murmushi yace "Bill kuma Abba" Daddy yace "Eh ba asibiti ku ka je ba, ga kuma drugs ka siyo" ya girgixa kai yace "A'a Abba, I have settled everything, Allah ya bata lafiya" daddy yace "Toh madalla, Allah ya yi albarka" Mujaheed ya debi ruwan ya mika mata tare da drugs din ta amsa, tana runtse ido ta kai baki sannan ta sha ruwan, mikewa Mujaheed yyi yace "Xan koma daddy Allah ya bata lafiya" Daddy yace "Ameen thanks Son" daga haka ya fita parlon, daddy na kallonta yace "Toh tashi ki shiga ciki ki kwanta" ba musu ta mike ta wuce bedroom dinta. Mujaheed na shiga parlonsu ya kalli mahaifiyarsa dake sakkowa downstairs, kai kana ganin shirin da tayi kasan fita xata yi, Anty dake parlor tana kokarin sa turaren wuta a burner ta kalli Mujaheed tace "Har kun dawo kenan, ya jikin nata?" Gabansa ya fadi sosai, ya hadiye abu da kyar yace "Eh na dawo" Anty tace "Daxu Abban ku ke gaya min ka kai Imaan asibiti, da naga breakfast dinka baka yi ba" kasa cewa komai Mujaheed yyi, ya d'an saci kallon Umma da ta tsaya stairs tana kallonsa baki bude, Anty tace "Ji walakanci ba da Mujaheed nake magana ba" Da kyar yace "Anty ba fa ni na kai ta ba, Abbanta ne ya kai ta" Shiru Anty tayi ganin yanayinsa, can ta saci kallon inda yake kallo, d'an tabe baki tayi ta duka ta ci gaba da abinda take, Umma ta juya ta koma sama, da kyar Mujaheed ya ja kafarsa xuwa dinning, har Anty ta gama abinda take Mujaheed na xaune bai taba komai a dinning table din ba, tace "Idan baka ci ka kai min su kitchen a ba almajirai" ya marairaice yace "Anty da baki yi magana a gaban Hajiya ba" Anty ta maka masa wani kallo tace "tunda uwata ce ita ba" Bai ce komai ba, bayan wani lkci ya mike ya fita parlon ko a mafarki bai ma son haduwarsa da Umma, to me ma xai ce mata ta yadda, part din Inna ya nufa, ya sameta xaune kan tabarma rike da cazbi tana ta xuba gyangyadi, kwanciya yyi kan kujera ya lumshe ido, inna ta yi gyangyadin ta mai isarta sannan ta bude ido, a tsorace ta koma baya ganin sa tace "Meye wannan?" Shi dai bai tanka ta ba bai kuma bude ido ba, tace "Wannan dai ba yi bane ina Lazimi kato ya fado min parlor ba sallama" Ba tare da ya bude ido ba yace "Kina gyangyadi dai" rai bace tace "Ya xaka ce ina gyangyadi ga carbi hannuna, ai asararre ne xai yi gyangyadi a wannan lokacin walha fa na gama ina lazimi ka shigo sadaf sadaf ban sani ba" Mikewa xaune yyi yace "Akwai ruwan shayi?" Tace "Eh akwai wanda uwarka ta kawo min" ya kalleta bai ce komai ba, tace "Can din hanaka ruwan shayin suka yi?" Komawa yyi ya kwanta, tace "Sai dai in sa Aisha ta dafa maka don baxan iya ba, baka ji bayana ba tun safe nake aiki, ko kai baka ga ko ina fess ba, leka dakina ma kaga yanda yake talli" shi dai bai ce mata komai ba, tace "Duk na tattara ma yarinyar nan me shigo min daki ta kwanta ta bar min tsummokaran dankwalayenta idan ta tashi tafiya, suna can baranda na ajiye mata, sai kaga hasken da dakin yyi wllh, ni dai da xata taimaka ta daina shigar min daki don Allah, ni tsoron da nake jiye mata idan tayi aure, ko ina fa ta samu barin kayanta take kamar mahaukaciya, Bukar dai ya haifo abinda ya fi karfinsa" mikewa Mujaheed ya sake yi ya shiga kitchen, ba a dau lkci ba ya fito rike da cup din ruwan xafi yace "Ina kayan shayin?" Makulli ta kunce a habar xaninta ta mika masa tace "Saboda ire iren su Imaan nake adana kayana, ba ruwana" Ya tabe baki ya amshi makullin ya shiga dakinta, closet dinta ya bude yaga gwangwanin madara manya har biyu da milo biyu sai kwalin sugar uku, da kwalin lipton girgixa kai yyi ya sauke madaran da Milo, muryarta yaji a bayansa tace "Da dai ka bari in xuba maka Mujaheed kada ka min barna" Wani kallo ya mata, ya debi cokalin Madara har uku ya xuba, ta bude baki cikin tsawa tace "Kai ubanka ne ya siyo min xaka diba haka, Bukar ne dai mai siyo min kayan shayi, shi Ahmadu sai dai ya jibge min kayan abinci kamar mayunwaciya, kudin nan fa da wahala ake samun su" shi dai bai tanka ta ba har ya gama hada shayin sa ya fita, tayi kwafa ta kwashe kayanta ta maida closet din ta kulle da makullin tana cewa "Ae dai gobe rana ce" Daga haka ta fito parlor. Har kusan azahar Mujaheed na bangaren Inna, har ya gaji da jin muryarta gashi bai taho da earpiece balle ya toshe kunnensa ba. Yana kokarin tashi ya je yyi alwala jin an kira sllh aka bude kofar parlon ya kalli kofar da sauri, Imaan ta shigo parlon rike da warmer, har ta rame ciwon kwana daya sai manyan idanuwa, Inna ta saki baki tace "Wacece wannan kuma?" Imaan bata ko kalleta ba ta ajiye warmer din hannunta, inna ta rike ha6a tace "Ni dai naga abinda ya isheni bai ishi ubangijina ba, yanxu fa sai ace jikinta ne ya tashi, fisabillah dubi yanda yarinya ta zabge ta koma fiyot kamar kyanwa Mujaheed, anya iyayenki na son ki kuwa yar nan, haka xasu xuba ido suyi ta kallonki kina wahala ga magani kasadan na wani malami a Maiduguri ance min babu ciwon da baya warkarwa, dubu hamsin aka ce xa a basa Bukar ya maida ni ban san abinda nake ba kamar shi ya haifeni, ta rasulu kawata xata cuce ni ne ake tunani? ce min fa tayi xata min hanyar samun maganin don can bayan tsauni mutumin yake, kuma babu kalan iskan da bai warkarwa da ciwace ciwacen da ba na Allah da annabi ba irin na yarinyar nan, amma iyayenta sun ba tsinannun turawa karfi sun amince masu dari bisa dari ba saurarana xa su yi ba, dubi don Allah yanda ta fige, lafiya muka rabu jiya amma ga iskan har ya tashi tunda gashi bata je makaranta ba" Mujaheed yace "ina kika ce mai maganin yake" Inna ta gyara xama tayi kasa da murya tace "Wllh a bayan tsauni ta rasulu tace yake, sannan aikinsa yanda kasan yankan wuka, sha ynxu maganin ynxu, duk xata fitsare ciwon da iskan inji ta rasulu" yyi murmushi yace "Ikon Allah, boka ne kenan?" Buda baki tayi tace "Kaji salu6a66e ko, ni dai ka rufa min asiri kar ka ja min kasa Ahmadu ya kafa min sabon babin wa'axi, kai ynxu fata kake inje wajen boka d'an nan" yace "Atoh, mutumin kirki dai baxai je bayan tsauni ya xauna ba" tace "Yo ai ni ce gantalalliya ma da nake xancen nan da kai na mance ashe d'an aiken turawan ne kai ma, Allah wadaran naka ya lalace, ba damuwa ni da ya xame ma dole xanje samo mata magani kuma kada wani shege ya min maganan banxa, Allah kuma ya tsine ma turawan nan dai" Imaan dake tsaye bakin kofa har sannan ta tabe baki tace "Kar ma ki amso ni baxan sha ba, daddy yace min in daina hada na asibiti da gargajiya" a fusace Inna tace "Kya tsufa a gida ina kallonki kina kallona don wllh babu namijin da xai auri ciwo da kudinsa ki karar masa da tattalin arxiki a asibiti, wllh baxan bari a cucesa ba duk sai na xayyane masa lalurorin ki don ni ba yar cin amana bace, ni yar gaskiya ce, ke ce ciwon kafa, kece ciwon baya, ke ce ciwon kai, ke ce ciwon mara, kece sanyin k'ashi, kece xaxxabi, kece ciwon jiki, ga shegen son jiki sannan in rufe masa da cewa duk iska ne da ba a san kansa ba, ba ruwana wllh" murmushi Mujaheed yyi ya mike ya fita don yin alwala, Imaan ta mata wani kallo bata son magana saboda daddy ta juya kawai ta fice mata daga parlonta tana murguda baki.
I am soo grateful for the birthday wishes from families, friends, fans, and love ones, Allah bar xumunci ya kara mana shekaru masu albarka.
[6/11, 12:34 PM] +234 703 570 1601: 🌟⭐ *Imaan* ⭐🌟
_By khaleesat Haiydar_✍🏻
6.....
Hatta islamiyya Imaan bata iya taje ba ranan banda bacci babu abinda take, xuwa lkcn jikin ya mata sauki sai dai rashin kwari, Daddy dake parlor a study area dinsa ya kalli Ammi dake parlon ita ma yace "It's almost six madam baxa ki tada Imaan ba?" Ta kallesa tace "Kafin magrib xan tasheta" yace "Amma jikin ba xafi koh?" Tace "Ehh ba xafi but she's weak" yace "Allah ya bata lafiya" a hankali Ammi tace "Ameen" bayan wani lkci ta kallesa tace "Am really disturbed with Imaans health ailment... She have suffered a lot but always claiming strong, and...." Sai kuma tayi shiru, a hankali ta ci gaba "I don't want to loose her" Daddy na kallonta yace "Allah plans best, ke dai ki ci gaba da yi mata addu'a a ko da yaushe wataran sai labari, Allah xai yaye mata" Ammi tace "In sha Allah" Bayan magrib Ammi na kitchen taji muryar inna a parlor, fitowa tayi ta gaida ta da ladabi tace "Sannu da xuwa inna" inna tace "Ina mijin naki?" Ammi tace "Ya fita masallaci" Inna tace "Daxu Imaan ta xo duk tayi wani fayau fayau da ita, jikin ne ya matsa mata koh?" Ammi tace "Ehh wllh, amma taji sauki ma yanxu, tana daki xata yi sllh" Inna tayi kasa da murya tace "Yanxu 'yar nan idan shi mijin nan naki boko ya gama cutarsa ya ratsa sa ta ko ina ke baxa ki maida hankali ki tashi tsaye kiyi ta kanki da 'yar ki ba? Fisabillilah meye laifin maganin gargajiya Aisha, komai sai ace sai asibiti ga na gargajiya kasadan?" Ammi tace "Gaskiya ne inna" Inna tace "Wllh malamin a bayan tsauni yake" Ammi ta d'an bude ido tana kallonta, tace "Ga aikinsa kamar yankar wuka, duk xata fitsare jaraban ta dawo kamar mutane, amma ni tsoron magana nake Bukar da Ahmadu ba kirki ne da su ba sai su karee min rashin mutunci suce boka ne alhalin ba boka bane kawai Allah ne yyi xamansa a bayan tsauni, ta rasulu ta sha xuwa can kuma ana kwana daya da rabi a hanya kafin a kai, tunda kika ji haka ai kinsan akwai kamshin nasara, tafiyar kwana daya har da rabi ai kuwa akwai nasara....." Shigowar Daddy ya sa tayi shiru, daddy ya gaida ta da ladabi ta amsa masa sama sama tana kallon Ammi tace "Kina ji 'yar nan bari in koma na bar kofa bude kada yaran gidan nan su min aika aika ga dambun nama ta can daki, dama Mujaheed sai xarya yake min tun safe, ko shi ya isa ya kwashe, yanxu dai yaushe mijin naki xai koma?" Ammi tace "Xuwa gobe in sha Allah" Ammi tace "Toh idan ya tafi ki taho sashina ki same ni mu karasa maganar a can don sirri ne" daga haka ta nufi kofa daddy na mata sai anjima ko tanka sa bata yi ba. Bangarensu Mujaheed inna ta nufa tana cewa "Ita kuma Amina bara inje inji ko lafiya ban ganta yau ba" Mujaheed ne xaune parlor sai Yusuf, Hajiya na dinning tana jera abinci Rahma na taya ta, gaba daya Mujaheed bai yarda sun hadu ranan ba sai yanxu da ta riskesa a parlor ta fito kitchen, Inna na kallon Yusuf tace "Kai ina uwar ka, lafiyarta yau bata xo gaisheni ba" Yusuf yace "Yanxu da daddaren nan xaki kamo hanyan xuwa nan inna" Hajiya ta karaso parlon tayi kasa da kai tana daga tsaye tace "An yini lafiya Inna" Inna tace "Rukayya idan Hadiza ce xa ki gaida ta a tsaye sandandan haka?" Juyawa Umma tayi ta koma ta ci gaba da abinda take ba tare da ta bata amsa ba, inna ta kara da cewa "Sannan kiyi min rai ki rufa min asiri ki daina gaisheni kwata kwata a gidan nan idan kin gan ni, don Allah bana bukata, wnn ae kanki kike munafurta, kuma Allah ya tsine ma gaisuwar" Wani kallo Mujaheed ke ma inna fuskarsa daure, inna tayi kwafa tace "Mu xuba dai, xamu ga mai kwashewa, ae kema ga naki d'an ya isa aure ba don ya tsaya shashanci ba xaki ji ko da dadi ko babu" mikewa Mujaheed yyi yace "Ke dai ba dai alkhairi ya kawo ki nan ba sai fitina da complaint, haba don Allah, gaba daya ba a ta6a maki dai dai...." Inna ta bude baki tace "Ni kake xagi Mujaheed?" A fusace yace "Mu bar sa a hakan" daga haka ya wuce ta kamar xai tashi sama, Yusuf ya bi sa da wani kallo, tuni Umma ta shige kitchen ranta fari fat duk da haushinsa da take ji, Yusuf ya mike yace "Yi hakuri muje in raka ki" Inna ta fara matsar kwalla tace "Isuhu kaga abinda Mujaheed ya min ko? Da ina kusa da shi babu mai hanasa make ni.... Ina mahaifin ku yake" Yusuf yace "Ke dai mu je, Abba bai dawo ba" Da kyar Yusuf ya lallabata suka fita parlon tace "Wllh in har Mujaheed zae ci gaba da xaman gidan nan sai dai ni in tafi" Yusuf ya danne dariyarsa suna isa part din su Imaan ta bude kofa, daddy dake xaune yana duba laptop ya mike ganinta tace "Bukar babu abinda Mujaheed ya mance bai gaya min ba yanxun nan daga nayi ma uwarsa gyara, sai ku xaba ko ni ko shi a gidan nan" daga haka ta rufe kofar. Yusuf dai tuni yyi gaba, suna isa part dinta ta rushe da kuka tace "Sai yanxu abun ke min ciwo isuhu, kai kaga wahalar da nayi da Mujaheed kare baxae ci ba wllh" Yusuf yace "Sai kiyi hakuri, Mujaheed din ki ne fa" a fusace tace "Mujaheed dinsu dai, bari dai mahaifin ku ya dawo xai gaya min ko shi ke koya masa ya min rashin arxiki" kiran Isha da ake yasa Yusuf ya bar part din inna, tare Daddy ya je gun Inna da Imaan bayan isha, Inna ta fito daga daki ta shimfida tabarma ta xauna tace "Wllh Bukar daga nace ma Rukayya ta daina gaisheni a gidan nan don na munafurci ne, shi kenan Mujaheed ya hayayyako min yana huci..." Daddy yace "Kiyi hakuri Inna, ina fita xan je in samesa yanxu" a fusace tace "Oh oh babu xancen samunsa, kawai ni ba na son ganinsa gidan ne ko kuma ni in tafi ai dama ya isa aure sai yyi ya koma gidansa baxan xauna tare da shi wataran ya mareni ba, wai ku me yasa baku san ciwon uwar ku ba, uwarsa fa na yi ma fada shine ya min rashin arxiki haka, kai ko ga ka xaune sandandan gabana kana bani hakuri, ya fi karfin ka ne mujaheed din ko kuma uwarsa ta fi naka ne, Ahmadu dai bai ba yaron tarbiyar da ya ratsa jikinsa ba wllh" Daddy ya mike yace "Xan dawo anjima inna" daga haka ya nufi kofa tace "Yauwa, ka titsiye sa sai ya gaya maka ko ni sa'arsa ce kafin ya bar gidan" shi dai bai ce mata komai ba har ya fita, Inna tayi kwafa tace "Xai san ya ta6a uwar su yau" Imaan dai na kwance kan kujera tana kallonta, Inna tace "Ni na ma fara tsoronsa tunda abinda ya zama kenan yanxu" Imaan tace "Toh ke me ya kai ki bangarensu" inna tace "Ya za ki ce min haka 'yar nan, ni da gidan d'a na kuma kice me ya kai ni?" Imaan dai bata ce komai ba, Inna tayi kwafa tace "Ke kin ga wahalar da nayi da Mujaheed?" Imaan tayi dariya tace "Ae ke dama kullum sai kice kin yi