Showing 18001 words to 21000 words out of 303099 words
wahala da kowa" Inna tace "Kee na Mujaheed k'are baxai ci ba, ni nasan me nake cewa, ina fa tsaye bakin kofar dakin haihuwa daga safe har dare sannan aka haifesa, sai kin ga wahalar da ya ba uwar d'an banxan, ai ko aka haifosa lafcece ya kusa biyun wani jaririn, duk ya cika asibiti da kuka nyaaa ke kina gani kinsan sadauki aka haifo, gashi jajir da shi fari hulll, gashin kansa kuwa ga bak'i ga cika yanda kika san d'an balarabe, ke ki bari kawai, nan dai muka koma gida na wanke sa tass, baki ga uwarsa ba lkcn yar siririya kamar xata karye ba yanxu da ta ci kudin d'a na iya ci ba ta koma kamar buhun masara, kullum zanyi wanka da sassafe daga gidana in tafi gidan Ahmadu yi ma fitsararren yaron nan wanka, don babu abinda uwar ta iya wai tsoron jaririn ma take don bala'i, a haka har yayi wata uku ya koma yanda kika san bredi wato ya xama wani lukeke, ga kyau tsantsa, ba sai uwar tayi ta cika masa nono yayi ta tumbudi ba duk k'arni??" Imaan ta fashe da dariya har da kyakyatawa tace "Shi yayan?" Inna tace "Wllh shi, to ni ko ina xan iya kazanta da k'arni, oh oh nan na taka mata burki, ga uwar kazama dn har sannan tana tashen kuruciya ni fa ko abincin gidan bana iya ci da, ana haka har Mujaheed ya kai shekara biyu, ba sai naga ana neman hallaka yaron ba, ba shi da aiki sai kukan banxa, fitsari a tsaye kashi a tsaye, ga uban shan yogurt, to da yake ba yanda na raini ubansa ba kenan bakina a leko na daukesa, kin ji mafarin komawansa waje na kenan, kuma Mujaheed bai bar gu na ba sai da uban ya biya masa kudin karatun likita a kasashen turai bayan ya gama sakandari, to ace banyi wahala da d'an banxan yaron ba kuwa, tsakaninsa da iyayensa fa sai dai bayan kwana biyu yaje ya gaishesu ya dawo, ko k'uda bana yarda ya ta6a min shi balle shegun kishiyoyina da duk suka mace yanxu, Allah dai ya ji kansu amma shari'ar mu da su sai a lahira...." Imaan tace "Ni lokacin ma ba a haifeni ba koh?" Da mamaki Inna tace "Oh oh kaji wata magana kamar na ta6a66u, wa ke ta ke, ke da aka haifa jiya jiya, a hannuna fa kika fado, ai wannan labarin da nake baki a lkcn mu duk mun dauka uwar ki juya ce...." Imaan ta mike xaune ta hade rai tana kallon inna, inna ta gyara xama tace "An auro uwar Mujaheed da shekara uku fa Ubanki Bukar ya auri bafillatanar uwar ki tana tallan nono a lkcn, a gidan sa fa tayi wnn karatun da take takama da shi" Imaan ta daure fuska tana kallonta, inna tace "Bayan an auri Uwar ki Aisha da yan watanni na tursasa Ahmadu ya sake aure shine fa ya auro Uwarsu isuhu, don a lkcn Rukayya na tashen rashin kunya duk an hure mata kunne, ga kazanta duk ta bi ta ru6ar min da gidan d'a na, To ita kuma uwar isuhu lkcn kawar Mamarki ce, kin ji musabbabin rashin shirin Rukayya da mamanki har yau, Rukayya ta dinga jin haushin Aisha tunda kawarta ta aure mata miji, Uwar su isuhu na shigowa da wata goma sai gashi ta haifo wannan d'an albarkan isuhu shi ma dai a gabana aka haifesa ina tsaye, ke ko uwar ki shiru kamar malam ya ci shirwa, ke in takaice maki har bayan shekaru aru aru sai dai uwar ki ta ci ta sha tayi kashi duk tayi bake bake a gida babu haihuwa babu dalilinsa, babu yanda banyi da Bukar ya karo mata ba amma yaron nan ya bijire min to duk ta shanye min shi ta rarraba min sunansa inda bai kamata ba, ke kinga bafillatani? To wllh kiji tsoronsa mugwaye ne na kin karawa, ni dai na dage rokon Allah ba dare ba rana don Allah ya warware abinda tayi ma d'a na, to wllh karshe sai da Ahmadu yayi 'ya ya shidda sannan uwar ki ta haifo ki, murna gun mahaifinki kuwa ba a cewa komai, duk lkcn fa ba mu san ba lafiyayya bace ke din, nayi ta xuba idon xuwan kanninki amma shiru, astagfirullah wa ya sani ma ko sai a lahira idan ana haihuwar tunda gashi yanxu kin doshi ashirin, kuma tun da kika fara wayo Bukar ya kulla adashin da ba kwasa da asibiti, shine ake nan har yanxu jiya e yau, ni yanxu mai kwasan ki ma nake tausayi wllh kada ya kasa rike ki, wannan idan talaka kika aura ae sai dai mu xo wataran mu dau gawarki muna koke koke, to banda haka sata xai yi ya kai ki asibiti? abinda Bukar yace min a kalla magungunan ki suna yin kusan dubu hamsin duk wata, wa xai iya wannan idan ba mai kudi ba irinsu yaran d'an tata, mu dai Allah ga mu gare ka, ka yaye ma jikata wannan iska da ya sa ta gaba yake cutan ta, ita kenan gun d'a na" Imaan na hararanta tace "Daga labarin yaya kin wani dawo bada labarina kamar an tambayeki, har na gaji da jin labarin nan a gidan nan" inna tace "Toh wa ke ta wani yaya da barin gidan xai yi gaba daya, ai yau sai ya san ya ta6a uwar masu gida" Da sallama Abba ya shigo parlon, Inna ta daure fuska, Daddy ma ya shigo parlon Mujaheed na biye da shi a baya, inna na ganin Mujaheed tace "Ni dai n shiga uku, mutumin nan ya fitar min a parlo don ba ruwana" Mujaheed ya durkusa d'an nesa da ita ya sunkuyar da kansa yace "Kiyi hakuri inna" inna tace "Oh oh Allah, ni dai wllh sai naga kamar tsoron yaron nan ku ke Ahmadu, ni cewa nayi ku taso sa ya bani hakuri? Me xanyi da hakurinsa, idan da amana Mujaheed zae dinga fifita uwarsa a kai na kuwa? Ni da na ci fitsarinsa na ci kashinsa ba irin wahalar da ban yi da shi ba, wannan wani irin fitina ne, me yasa Isuhu baya min haka?" Shi dai Mujaheed bai dago ba, inna tace "Toh ni dai a bar min parlo na" Daddy yyi murmushi bai dai ce komai ba, Abba yace "Mu dai sai dai mu ce kiyi hakuri, shi kuma nasan maganinsa" inna ta wani tsuke fuska bata ce komai, Imaan dai na kwance sai murmushi take, Abba na kallon Mujaheed yace "On a serious note Mujaheed be careful... you had better respect yourself in this house, and mind you no matter how she does her things, how she behaves, how annoying she might be, she is still my motherr, yes she is my mother I can't change her from who she is, and you have got to respect her to the fullest, you keep that grandma and grandchild play aside since she doesn't cherish that, she have got all right to complain of ur mother, let her be entitled to her opinion, today shud be the last that she will complain of ur attitude toward her Muhammad am I clear" Mujaheed bai iya ya dago kansa ba yace "in sha Allah Abba" Daddy yace "Maa sha Allah" inna da sai tabe baki take tace "Oho dai duk a banxa tunda baxa ku iya koransa a gidan ba" Mujaheed yyi kasa da murya yace "Kiyi hakuri" tace "Tashi ka bani waje, ba dai aure xaka yi ba wataran, wllh duk sai matar ta rama min abinda uwarka tayi min a duniyar nan, takanas xan tattara kayana wllh in koma gidanka da xama duk ni xan dinga koya ma yarinyar, nan Rukayya xata ji ko da dadi ko babu" Mujaheed dai bai ce komai ba, Abba yace "Leave now" mikewa yyi yana hararanta ta gefen ido ya fice daga parlon, Imaan ta fara dariya kasa kasa. Ranan juma'ah da daddare Inna na xaune parlonta Imaan kuma na kwance kan kujera gaba daya ta gaji da labarin da inna ke bata, tana son tashi ta wuce amma ciwon da kafarta ke mata yasa ta kasa tashi, tun magrib take wajen bayan ta kawo mata abinci har wajen tara da rabi yanxu, Inna tace "To kin ji abinda ya raba ni da uwar d'an gwate kenan, kuma fa lkcn kakanku bai san ina xuwa ba, kai jama'a na xuba farin jini gun masu kudi wllh" Imaan dai bata tanka ta ba, bude kofar parlon aka yi Mujaheed ya shigo da sallama, Inna tace "Dama shi kadai ne me shigo min da sallama banda su oh oh" Ta gefen ido Imaan ta kalleta, ya ajiye ledan hannunsa yace "Gashi" ta jawo ledan tana budewa tace "Lahh kaza ce kamar yasan ina marmari wllh " Imaan ta mike xaune, inna ta hade rai ta rufe ledan, mikewa Mujaheed yyi ya dauko plate ya ajiye gabanta, ta mayar gefe tace "Ni dai wllh kuna takura ni gidan nan kai da Imaan ba haka isuhu da su maimoona ke min ba, su basu da sa ido" ta hade rai ta bude ledan ta dau cinya daya ta dungura masa a plate din, dariya yyi ya dauka yace "Ni fa na siya maki kazar ba Abba ba" Inna tace "Auuu" kara bude ledan tayi ta fiddo tsoka daya ta manna masa kan plate din, Ta kalli Imaan tace "Naga kina son albasa da kabeji dauko kwanon can da kika ci abinci in kwashe maki in hada maki da tsoka daya" Imaan tace "Ni nace maki xan ci kaza?" Inna tace "Toh na sani? Gani nayi kin xabura kin tashi kamar Bukar ya siyo min" Daga haka ta kai cinya baki tana ci tace "Allah maka albarka Mujaheed duk cikin jikokina kafi jin k'aina wllh, shi sa ma kana aure zan tattara yanawa yanawa in koma gidan ka na rantse" ya xaro ido yace "Gidan wa?" Ta kallesa tana washe baki tace "Gidan ka" yace "A'a wllh ga yar gaban goshin ki nan kice kuma gidana" tace "Waye yar gaban goshi na?" Yace "Gata nan xaune" inna tace "Oh oh ni gidan ka xan xauna xai fi min kwanciyar hankali, idan matar ka xata rainani nasan xajka taka mata burki kai da baka son abinda xai ta6a ni, wannan salubabbiyar kuma ai yunwa ma kadai ya isa ya koro ni, ni fa ban jin imaan ta iya girki tunda take ko tafasasshen ruwan xafinta ban taba d'andanawa ba" dariya Mujaheed yyi, Imaan ta wani hade rai tana kallon inna, Mujaheed yace "Kinga idan tayi aure xaki d'an dana idan kin koma gidan ta da xama" Inna tace "Ni fa baxan xauna gidan imaan ba gidan ka xan xauna wllh" yace "Wllh baxa ki xaunar min gida ba sai dai nata" Inna tace "Toh me yayi xafi haka, wannan satin idan nayi gidan ka wani satin sai inyi a gidan ta duk da nasan a rame dai xan dawo daga gidan nata amma dole naka naka ne, idan na koma gidan ka sai in murmure" Mujaheed yyi dariya yace "Inaaa ba wannan xancen gidan mijinta ko gidan Yusuf xai fi maki kwanciyar hankali amma gida na kam sai dai ki hangesa daga nisa shi ma kuma a photo, Kinga duk sanda mijin nata ya gaji sai ya koro ki da ita" Inna tace "Wai tsaya Mujaheed da kake wannan xancen da kudin asibiti mijin xai ji ko da nawa dawainiyar ka fa san irin cimar da nake ci bana banxa bane, gwara dai a bar sa ya ji da jinyarta, ni kuma in xauna gidan ka ko Yusuf koh Maimoon, amma ina ni ina xaman gidan imaan ga yunwa dai kiri kiri tunda ba girki take ba sai a wani fake da ciwon numfashi kamar yanda uwarta ke cewa" fuu imaan ta mike xata fita cikin rashin sani plate din da ta ci abinci ta bari wajen ya xamar da ita sai ga ta rijib a kasa, wani ihu ta fasa da karfi tana cewa wayyo kafarta, Inna ta xaro ido ta mike da sauri ta bude kofa tace "Ni dai na shiga uku da jaraba, yi maxa fita da ita Mujaheed, fitar min da ita kar ma ace a parlo na ta fadi" Mikewa Mujaheed yayi yana mata wani kallo yace "Baxa ki tashi ba" cikin kuka tace "Wayyo yaya kafana ya rike baxan iya tashi ba" Inna ta gwalo ido tace "Ka ji ko? Mujaheed ka fitar min da ita kada a sani a bakin duniya" Ganin da gaske ta kasa tashi Mujaheed ya daga ta, ta zaro ido tana yarfe hannu tana cewa wayyo kafarta, inna duk ta rude tana ce ma Mujaheed ya fitar da ita, ko fita basu gama yi ba ta tura su gaba daya, ta kulle kofarta tasa makulli tace "Dama kada a kuskura ace a parlo na ta fadi wllh don ba ruwana" Mujaheed ya xabga ma imaan harara yace "Baxa ki tsaya da kyau ba" cikin kuka tace "Wllh ba karya nake ba yaya kafar ya rike min" kalle kallen wajen ya fara yi, can yayi tsaki ya dauketa kamar yar baby ya nufi bangarensu da ita, gam ta rikesa tana rera kuka.🌟⭐ *Imaan* ⭐🌟
_By khaleesat Haiydar_✍🏻
8.....
Yau Thursday Imaan na dawowa schl bayan tayi wanka ta ci abinci ta fito parlor ta xauna kusa da Ammi dake xaune, ta langwabar da kai tace "Ammi ina son xan je supermarket in siya pad da turarurruka" Ammi ta kalleta tace "Duk uban turarrukan da kika kwaso ranan sun kare kenan Imaan?" Yar dariya tayi tace "A'a ba su kare ba amma sun kai rabi" Ammi tace "Toh sai ki kira babanki bani da kudin da xan baki ki karo turare" Imaan ta bude ido tace "Ya min transfer din 30k ranan da xai tafi ai" Ammi tace "Tohhhh har 30k, lallai kam Allah ya taimaka" dariya Imaan tayi ta mike ta koma daki, Hijab dinta gogagge har kasa ta fiddo ta saka sannan ta dau karamar jakarta ta sa atm card ta feshe jikinta da turare ta fito parlor, ta durkusa kusa da Ammi tace "Toh Ammi ba ni kudin transport don Allah" Ammi tace "Ki duba gaban mirror a daki" tashi tayi ta shiga ta dauko sannan ta dawo parlon, tace "Yauwa Ammi ina son xan biya ta gidansu Mariya, tun Tuesday bata xo schl ba bata da lafiya" Ammi tace "Waye kuma Mariya?" Imaan tace "Lahh wannan da ke xuwa dubani wani lkcn idan bani da lafiya" Ammi tace "Kice min dai gidansu xa ki je ba supermarket ba" Imaan tace "A'a fa Ammi, kawai tunawa nayi, Ban ma san ko xan gane gidan ba fa tunda sau daya muka taba xuwa da Maimoon, idan ban gane ba kawai sai in dawo gida" Ammi tace "Gwara dai ki gane don ki dubota tunda tana yawan xuwa duba ki" Imaan tace "Toh Ammi" daga haka tayi ma Ammi sallama ta fita Ammi na tunatar da ita tayi addu'an fita gida, tana isowa part din su Yusuf taga Umma da wata kawarta xaune a waje kan fararen kujeru, Imaan ta dauke kai duk da sun hada ido har ta wuce su ta nufi gate, Hajiya Salaha tana kallon Umma tace "Wace fitsararriya ce wannan kuma" Wani murmushi Umma tayi tace "Yar wajen Aisha" Hajiya salaha tace "Ikon Allah ita ce ta girma haka?" Tabe baki Umma tayi, Hajiya Salaha tace "Ita Aishar ta sa kar ta gaishe ki gidan nan kenan?" Umma tayi yar dariya tace "Ga dahir kin gani, ai fa ko idona xai makale cikin nata shegiyar baxata gaida ni ba uwar ta hanata" Hajiya Salaha tace "Tabdi ita wannan yar ficicciyar yar?" Umma tace "Ba shine bayan na dawo gidan nan naga ita da Mujaheed da bai san ciwon kansa ba bai san ciwon mahaifiyarsa ba tamkar su yi 6ude, ya maida Aisha kanwar uwarsa bashi da tamkar ta gidan, ita kuma yar mai ciwo yau mai ciwo gobe tunda sickler ce idan kin ga abinda yake mata ko kanninsa su Ummi bai masu, in takaice maki duk dai Aisha ta bi ta shanye min shi yanda ta shanye kanin ubansa, yanda kika san xai mata sujjada" Hajiya Salaha tace "Ikon Allah" Umma tace "Ae tuni na tashi tsaye, nice can nice nan, da taimkon Allah da taimakon Magajiya na kwato d'a na da karfi da yaji, yanxu ko ga maciji basa yi a gidan bangaren ma ya daina xuwa, I can't risk that, uban waye bai san tsafi Aisha take ba, gashi dai ta hana kanin babansa karo matar da xata haifo masa 'ya yansa duniya ta rufe masa baki ta hada sa da 'ya sickler kullum ana hanyar asibiti ana kashe Dan banxan kudade, Allah kenan, kuma in dai ina numfashi a haka yarinyar nan xata kare yau lafiya gobe babu, in Allah ya yarda sai yar nan sai ta xame masu jaraba duk sai ta tsiyace su muna nan muna gani, kee duk wanda xata ra6a ma wllh sai ya tsiyace, haka nan kuma xata yi ta xama ba mashinshini.... to ubanwa xai iya da ita ta kassara tattalin arxikinsa, ni fa duk duniya billahil azim bani da makiyiya da ya wuce Aisha, wllh xan iya yin komai don in toxarta ta da yarta, ni ko kishiyata ban jinta yanda nake jin Aisha, kuma yanda tasa aka toxarta ni aka min kishiya sai na toxarta ta ita ma ko ba jima ko ba dade, ina nan dai kan bakana lokaci kawai nake jira" Hajiya Salaha tace "Ae ko kar ki yarda wllh, ki mata fiye da wanda ta maki ma" Umma tace "Yanxu gobe ma akwai inda xa ni tare da magajiya da sai ki fito mu je tare, wani take take na fara gani nake son taka ma abun burki tun wuri" Hajiya Salaha tace "Haba na me kuma?" Umma tace "Ki ji fa don walakanci yanxu sai su yi ta makala ma Mujaheed ita ya kai ta asibiti, ga uban kudaden da xai kashe wanda nasan ko