Showing 162001 words to 165000 words out of 303099 words

Chapter 55 - Imaan Book 1 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

1671

sake kiranta, sakkowa tayi daga kan gadon tana goge idonta duk da hawayen ya ki tsaya mata, ta nufi kofa ta bude ta fito parlor, Ammi na kallonta tace "Yaushe kika shigo?" Da kyar ta bude baki tace "Ban dade ba" shiru Ammi tayi tana kallonta da mamaki, Imaan ta sunkuyar da kai gabanta na faduwa sosai, Ammi tace "Kukan me kike?" Ta girgixa kai tace "A'a ba komai" Ammi ta mata wani kallo tace "Zo nan" sosai xuciyarta ke bugawa ta karasa ta duka kasa tana kallon Ammi tace "Gani" cikin tsawa Ammi tace "What's wrong with you?" Duk yanda ta so dakewa kasawa tayi, ta fashe da kuka sosai, duk yanda Ammi ta so boye tashin hankalinta a lkcn kasawa tayi, Tayi kasa da murya tace "Nace me ya faru imaan, kukan me kike yi, talk to me daughter" Cikin rawar murya tace "Da gaske Ammi ba komai" Ammi ta wani hade rai tayi mata wani tsawa tace "Baxa ki bani amsa ba, kukan uban me kike, me aka maki?" Imaan dai ta kasa cewa komai sai hawaye, mikewa Ammi tayi hakan yasa ta tashi da sauri ta koma baya ta fashe da sabon kuka, tsayawa kallonta Ammi tayi, can ta wuce daki da sauri ta dau wayarta ta shiga kiran layin gwaggwo, ta kira ya fi sau a kirga gwaggwo bata dauka ba, kowa kuma yasan gwaggwo haka take da waya, Ammi ta shiga kiran Halima, bayan sun gaisa Ammi tace "Halima Imaan ta je gidan ki?" Halima tace "Ehh ta xo daxu amma ai ta wuce" Ammi tace "Karfe nawa ta bar gidan naki?" Halima tace "Shidda dai kamar yayi, lafiya Ammi?" Ammi tace "Lafiya lau, Ina tace maki xata daga gidan naki?" Halima tace "Bata koma gida bane Ammi?" Ammi tace "Tambayar ki nake" Halima tace "Tace kila ta wuce gida ko kuma ta tafi wajen gwaggwo" Ammi tace "Toh sai anjima" daga haka ta katse wayar, Gwaggwo ta sake kira har ya gama ring bata dauka ba, ta kuma kira nan ma haka, ajiye wayar tayi ta fito, ganin Imaan bata parlor ta wuce dakinta, jin tana bathroom Ammi ta tsaya, gaba daya hankalinta ya tashi sosai, Imaan na gama alwala ta fito, sosai ta tsorata ganin Ammi, ta sunkuyar da kai a hankali tace "Ammi ba komai fa" Ammi tace "Daga gidan Halima kin koma gidan gwaggwo ne?" Ta girgixa kai tace "A'a" Ammi tayi kasa da murya tace "Toh ki gaya min me ya faru" cikin sanyin murya tace "Ba komai fa Ammi, kawai dai kamar bana jin dadi ne" Ammi tace "Baki jin dadi kuma?" Ta gyada kai, Ammi tace "Ina ke maki ciwo?" Ta girgixa kai tace "A'a ba inda ke min ciwo, kawai dai bana jin dadi" shiru Ammi tayi tana kallonta, can tace "Toh ki yi sllh ki fito yanxu" imaan ta gyada mata kai Ammi ta juya ta fita, har Imaan ta idar da sllh ta kasa daina hawayen da bata san dalili ba, tayi kokarin daina hawayen amma hakan ya faskara, har sannan she is just shock, fashewa tayi da kuka a hankali, ta jinginar da kanta jikin gado. Ammi na idar da sllh tayi ta jiranta ta fito amma shiru, hakan yasa ta mike ita ma gaba daya ta rasa me ke mata dadi, gashi ta kara kiran gwaggwo bata dauka ba tasan wayar na can karkashin pillow, A hankali ta bude kofar dakin ta ganta xaune kan darduma ta jinginar da kai da gado tana bacci, Ammi ta karasa inda take ta duka ta kai hannu jikinta ta ji ba xafi, Bude ido imaan tayi ganinta ta ja baya, Ammi na kallonta ta xauna gefen gadon tace "Tell me what's wrong with you plss imaan" D'an murmushin karfin hali tayi tace "Ammi ba komai fa, i am better now" Ammi ta dinga kallonta kafin tace "Toh fito ki ci abinci" tashi tayi a hankali ta dauke pray mat din ta linke ta bi bayan Ammi xuwa parlor, Ammi ta xuba mata abinci a kitchen ta kirata, Mikewa Imaan tayi daga xaunen da tayi a parlor ta tafi kitchen ta amso abincinta ta dawo parlor ta xauna, Sosai Ammi ke studying dinta tana cin abincin sai dai bata ce mata komai ba, ganin xata je ta ajiye abincin da ko rabi bata ci ba Ammi tace "Dawo ki cinye abincin nan" kamar xata yi kuka tace "Ammi ya min yawa" Ammi tace "Dawo ki cinye na ce" babu yanda ta iya haka ta koma ta xauna tana tura abincin da kyar, har ta cinye taje ta ajiye plate din a kitchen ta dawo parlor tana kallon Ammi tace "Ammi ina son xan kwanta" Ammi tace "Ishan fa?" tace "Ba bacci xan yi ba kawai xan kunna kallo a ciki" Ammi bata ce mata komai ba hakan yasa ta wuce daki Ammi ta bi ta da ido har ta rufe kofa. Ammi dai na ta xaune parlor har takwas da rabi aka yi sallama bakin kofa, amsawa tayi Mujaheed ya shigo parlon, Ammi na kallonsa tace "Sannu da xuwa" Ya d'an yi murmushi ya xauna yace "Ina yini Ammi" Ammi tace "Lafiya lau, ya gida" yace "Lafiya Alhmdllh" tace "kwana biyu?" Yace "Alhmdllh" Ammi na kallonsa tace "Baka da lafiya ne" yar dariya yyi yana shafa kansa yace "Aa, am okay, me kika ga" ta girgixa kai tace "A'a ba komai, a xubo maka abinci" yace "A'a Alhmdllh" shiru yayi yana kallon movie da ake yi a tv, can ya kalli Ammi yace "Abba yace Imaan ta je" Ammi tace "Ohk, tana ciki Ina jin ta kwanta, let me wake her" ya kalli agogo sannan ya kalleta yace "Bata da lafiya ne?" Girgixa masa kai Ammi tayi tace "She's ohk" Ammi na kallon kofar dakinta ta kwalo mata kira, ta kirata yyi sau uku amma shiru, can Ammi ta mike ta tafi dakin, kwance ta ganta ta rufa da duvet, Ammi ta karasa ta cire duvet din da sauri Imaan ta rufe idonta, da mamaki Ammi ke kallonta tace "Imaan kina son in bata maki rai a gidan nan yau ko, baxa ki gaya min meye damuwarki ba, wani abun ya faru ne baxa ki gaya min ba" Imaan taki yarda su hada ido ta mike xaune tana goge guntun hawayen idonta a hankali tace "Ammi kiyi hakuri ni nace maki ba komai fa" Ammi tace "Wani abun ya hada ki da gwaggwo ne" Imaan tace "A'a ni ban ma dade a gidanta ba, Ammi it's just mood swings" Ammi tace "Toh xan kira daddyn ki yanxu kuwa in gaya masa, don baxan yadda ki sa min ciwon kai ba ina xamana, wannan ai walakanci ne, ke yarinya ce xaki xauna kina kuka ki ki fadin matsalar ki kice min mood swings, ko iskancin ki na da ne xai dawo yanxu, kuma ki tashi ki fita Abba na kiran ki...." Juyawa Ammi tayi rai bace ta fita a dakin tana mamakin hali irin na Imaan, tasan ko da rufeta xata yi da duka ta dage a kan sai ta gaya mata kukan me take to taurin kanta baxai taba bari ta fadi ba, ita kanta taurin kan Imaan na damunta ne ba kadan ba, parlor ta koma ta xauna tana kallon Mujaheed tace "I don't know what's wrong with her, tun daxu take kuka, na tambayeta meye matsalar ta taki gaya min, kuma kukan na iskanci ne da jin dadi, dama ranta a bace ta bar gidan tunda nace kar ta kwana inda xata je...." Mujaheed na kallon Ammi yace "Kuka kuma" Bude kofar dakin Imaan tayi ta fito kanta a kasa, Mujaheed ya dinga kallonta har ta karaso cikin parlon ta xauna kasa tace "Ina yini Yaya" yace "Lafiya lau, what's wrong?" Kin cewa komai tayi, Ammi sai kallonta take, can kuma dai ta tashi ta wuce daki, Imaan ta hade kai da gwiwa, ya mike ya dawo kusa da ita ya durkusa yana dubanta yace "What happened imaan, an maki wani abu ne?" Ta dago kanta ta wani turo baki tace "Ba komai" shiru yyi yana kallonta, can yace "Tashi mu je Abba na kiran ki" Mikewa tayi shima ya tashi ya nufi kofa ta bi bayansa. Sai da suka yi nisa ya juya yana kallonta da kyau yace "Baxa ki gaya min kukan me kike ba" tace "It's just mood swings" Bata jira cewarsa ba tayi wucewarta ya bi ta da ido, can dai ya bi bayanta, Xaunawa parlon Abba tayi bata yadda sun hada ido ta Abban ba ta gaishesa ya amsa yace "What did you want for ur Qur'anic graduation?" Shiru ta d'an yi, can tayi murmushin karfin hali tace "Abba kawai a min abinda aka ma su Maimoon" yace "To maa Sha Allah, you can go" Mikewa tayi ta masa sai da safe ta nufi kofa Mujaheed ya bi ta da ido har ta fita, wanka imaan tayi bayan ta koma part din su, tana saka kayanta text ya shigo wayarta ta kalli screen din, dauke kai tayi ganin Sadeeq ne ya turo sakon ta karasa shirinta ta bar wayar nan gaban madubi ta kashe wutan dakin ta kwanta, ta jima bacci bai xo mata ba sai juye juye take daga karshe dai baccin ya dauketa. Washegari Friday duk da ynda imaan ta dinga jin ciwon kai haka ta shirya ta wuce islamiyya, karfe sha daya kuma ta dawo gida, har sannan dai bata wani dawo normal ba don scene din abinda ya faru jiya ya ki barin memory dinta da ya fado mata kuma sai gabanta yayi mugun faduwa, sai dai tana ganin motar daddy a parking space alamar ya dawo taji dadi har ranta. Tana fitowa wanka ta dau wayarta da ta boye a press ta bude, missed calls din Sadeeq taga ni har uku da text biyu bayan na jiya da daddare da bata bude ba, ta ki bude text din tayi lock din wayar ta mayar cikin press dinta ta gama shiryawa sannan ta fito parlor, Tana murmushi ta karasa ta gaida Daddy da ya fito parlor, daddy na kallonta yace "Lafiya lau Mamana, are you okay" ta buda ido tace "Sure daddy, ya hanya?" Yace "Alhmdllh, ya shirin walima" tayi yar dariya tace "Daddy Ina yi" Ammi dake jera ma Daddy abinci a dinning sae hararanta take, Daddy yace "Ga tsaraban ki can Ammin ki ta sa maki a fridge" cike da jin dadi tace "Toh nagode daddy"
Da yammacin ranan Imaan ta tafi kai ma Inna abinci, sallama tayi ta shiga parlon, Daddy ne xaune parlon sae Kawu Bala, ga Umma ma xaune ta sha xumbulelen hijab kanta a kasa, ga wasu kawunnanta har biyu su ma a parlon, Inna dai na xaune kan tabarma tayi tagumi tana sharban kuka, ganin imaan ta shigo cikin rawar murya tace "Wllh bata fi wannan yarinyar muka aurota ba Talle" imaan ta gaishesu ta ajiye abincin hannunta ta fita.


*Imaan isn't for free* it's 300 via


Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788



58.....


Daddy ne xaune parlon Inna bayan su kawu Bala, Umma da kawunnanta sun fita, Inna ta tace "Wlh wllh Bukar ka ji rantsuwar musulmi ko, to Rukayya ta ci albarkacin ka ne, don ina jin kunyan ka ainun, amma idan ta sake ko da min kallon banxa ne a gidan nan to aurenta da Ahmaduna ya kare ba ruwana, xan nuna mata ni na haifesa ba wani shegen ya haifa min shi ba, yanxu ma ni wllh darajar ka da na Mujaheed ta ci, tunda ni nayi wahala da shi kuma yana min biyayya, kai ma kuma kana min biyayya, matar da ma ba wai son matar ka take ba amma ka dinga tsayawa tsakanin ka da Allah kan lamuranta, ita bata ki ba ma ta cutar da Aisha ba wllh, kai kuma duk ka damu da lamarinta, duniya dai ba gaskiya" Shi dai daddy bai ce komai ba yana sauraranta, tabe baki tayi ta mike tace "Ni dai ba ruwana, kawai mata ta wani taho min da rubabbun mutane su ban hakuri, wllh ta ci albarkacin Mujaheed da sai na masu koran kare ba kunyar kowa xan ji ba, ba ruwana, matar da ba tsoron Allah gareta ba balle a raga mata" Daddy dai ya bi ta da kallo har ta shiga daki sai ga ta ta fito ta xauna tana kallonsa tace "Kana ji na Bukar, ni dai duniyar nan kaf ba wanda bai san imaan takwarata bace, kuma kowa yasan ita kenan Allah ya baka, ita kenan jikata a wajen ka, Toh ya dai fi babu ai, sabili da haka gaskiya ni dai ga dubu ashirin dina da nake ta tarawa a samo tikeken rago da ya kusa d'an mariki a yanka mata na saukan nan, Allah kuma yasa na tsoron Allah xata yi, yayi mata albarka ya hada ta da mijinta na gari wato wannan yaro Bulasawa...." Shiru Daddy yayi yana kallon kudin da take mika masa, tace "Haba ka amsa mana yaro, ka bar min hannu a sagale" d'an murmushi yayi yace "Amma Inna kin fa san ba ita kadai xata yi sauka a gidan nan ba" tace "Toh ai shi sa nace takwarata" ya girgixa kai yace "Ai Ummi ma takwarar ki ce" Bude Baki tace "Yau naga abinda ya isheni, ji Bukar da wani xance, to cewa nayi ban sani ba, ai xuciya ma na son mai kyautata masa, Ummi ko gaisuwar kirki tana min a gidan nan balle in dinga tuna cewa takwarata ce, ni dai ba ruwana a dinga jin tsoron Allah, yanxu meye ma'anar hakan da kafada salon Ahmadu ya ji ya kullace ni, ni dai gashi ka tafi bakin ka a leko ka siyo mata tikeken ragon da nace a kawo mata" mikewa Daddy yyi yace "Toh Allah ya saka da alkhairi, sai anjima" tace "Toh kai dai ka ja bakin ka kayi shiru, abinda naman ma duk xa a tsakura ma kowa da kowa a gidan" shi dai daddy bai ce komai ba har ya fita. Washegari asabar da wuri aka tashi a gidan aka fara girke girke, Ammi da Aunty ne ke girkin a nan bayan kitchen din su Aunty, abinci kala uku xa suyi, sae soye soye, tun daren jiya dama Ammi tayi samosa da spring rolls, Aunty kuma tayi cakes da doughnuts, Umma sai kai wa da kawowa take kamar dai me neman abu fuska a daure, ta shiga ta fita, babu dai wanda ta ce ma sannu da aiki cikinsu, su ma babu wanda ya kalleta, Maimoon ne da Ummi suka shigo kitchen ko wanne sanye da Sabbin dinkin da Daddy yayi masu na atamfa gaba daya su uku masu saukan har da imaan, da Hijab dinsu ash colour yana jan kasa, sosai suka yi kyau, Aunty tace "kun yi kyau sosai, amma kuna kallon agogo dai koh" Ammi tace "Allah ya sa ita wancan ta gama shiryawan" Maimoon tace "Shayi kawai xa mu sha sai mu je mu kirata" Muryar Umma suka ji bakin kofar kitchen din tana kallon Ummi cike da masifa tace "Kin wuce kin cire kayan nan na jikin ki ga lace can na dinka maki ko sai na 6ata maki rai???" Ummi ta kalli atamfar jikinta sannan tace "Lace umma?" Xagi umma ta kunduma mata tace "Don uwarki xo ki fita ki cire kayan nan, ko ubanki ne yayi maki" Ummi ta nufi kofa ta fita, Ammi dai sai aikinta take, Aunty ta tabe baki ita ma ta ci gaba da aikinta, tsaki Umma ta ja ta bar bakin kofar kitchen din, Maimoon ta hada masu shayin cup biyu ta fita, karfe bakwai da kusan rabi Imaan ta taho part din su Maimoon sanye da nata atamfar da well ironed hijab dinta har kasa, sosai tayi kyau Aunty tace "Iyye daughter tayi kyau sosai, amma ko yar powder baxa ki shafa ba Imaan" Yar dariya Imaan tayi ta gaida Aunty, Aunty ta amsa tace "Ki tafi daki ki dau powder Maimoon ki shafa kin ji?" Tana murmushi ta juya ta fita ta wuce sama, dakin su Maimoon ta shiga ta dau powder dinta dake gaban mirror ta shafa, ta goga chappete a lips dinta mai two colour, sosai tayi wani sanyayyen kyau kamar warce tayi wani kwalliya, juyawa tayi ta fita dai dai fitowar Umma dakinta, Sosai gaban Imaan ya fadi ta sunkuyar da kai har xata wuce maganan Sadeeq ya fado mata, a hankali tace "Ina kwana" Umma na mata shegen kallo tace "Kin sa6a gaisheni a gidan nan ne ko kuma gulma da kinibibi irin na uwar ki, to ko da mistake kika sake gaisheni a gidan nan wllh sai na gaura maki mari munafuka kawai sauran ciwo" Ita dai Imaan bata ce komai ba ta dinga sauka stairs, Umma ta bi ta da kallon tsana karara, har wani tafarfasa xuciyarta yake... Imaan na komawa kitchen Aunty tace "Ba gashi kin kara kyau abin ki ba, don kana da kyau kuma baxa ka kara da wanka ba" Imaan dai murmushi kawai tayi, Aunty tace "Kin dai karya koh?" gyada mata kai tayi, Aunty tace "Toh maxa ki tafi suna jiran ki a mota, sai mun xo in sha Allah" Imaan har ta nufi kofa ta juyo ta marairaice tace "Aunty xa ku taho da Inna?" Aunty ta d'an yi dariya tace "Tabb, to ban dai sani ba, amma kila mu taho tare" Ammi dai sai kallonta take ganin yanda ta rame kamar warce tayi ciwo na sati daya, Imaan tayi masu sallama ta fita kitchen din, ta tadda su Maimoon har sun shiga mota suna jiranta, ita ma ta shiga motar aka wuce da su islamiyyar su, Imaan dai sai Muraja'ah take a xuciyarta har suka iso islamiyyar tasu, Da yake islamiyyar sananne ne, kuma duk yawanci yaran masu shi sosai ne a makarantar, manya manyan mutane ba na wasa ba ne suka halacci taron waliman saukan, ciki kuwa har da 'yan gidan Bulasawa gaba daya, da shi kan sa Bulasawan, duk da yaran second wife dinsa kadai ke xuwa islamiyyar wato su


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login