Showing 213001 words to 216000 words out of 303099 words
Bude kofa aka yi Umma ta shigo ita ma ta dalilin kiranta da Abba yyi, ganinsu Ammi da Aunty, da Mama Hadiza a parlor kawai taji kamar ta saki guda mai xakiii, rumors da ake tayi tsakar gida ya tabbata kenan, Ta xauna da mamaki fuskarta tace "Lafiya kuwa Alhaji, me ya faru?" Ko rufe baki bata yi ba Yusuf ya shigo parlon tare da Inna da ta cakare cikin super abunta an daura dankwali sai xuba kamshi take ta daura mayafi a kan dankwalin, tana murmushi baki har kunne tace "Toh Allah ubangiji dai yasa an daura a sa'a Allah ya kauda idon makiya, ya kuma sa gidan xamanta ne, ku kuma Allah maku albarka ya baku lada" Kawu Bala ne ya amsa da Ameen kansa a kasa, shi dai daddy kansa na jingine da kujera, inna ta nemi kujera ta xauna tace "Toh wani shawarar kuma xa ayi yanxu aka tara mu a nan, ga dai bak'i can na baro" Abba yayi murmushin karfin hali yace "Mujaheed muke jira Inna" Inna tace "Ae dole, shi ne ubanta na hudu a nan ai...." Bude kofa aka yi sai ga Mujaheed ya shigo parlon sanye da shadda fari kal sai walkiya yake, duk suka dinga kallonsa ya nemi gefen Yusuf da kansa ke kasa ya xauna ya gaishe da iyayen nasa gaba daya da ladabi duk suka amsa, Abba ya kalli Aunty a hankali yace "Go and get Imaan immediately" Mikewa Aunty tayi ta fita ita gaba daya ta gama shan jinin jikinta don gani take ba alkhairi yasa aka tara su parlor ba, ba alkhairi xa su ji ba. Aunty na rike da hannun Imaan da ke lullube cikin mayafi suka shigo parlon Abba, ta xaunar da ita gefenta, imaan bata iya ta dago ba balle ta ga mutanen dake cikin parlon gabanta dai sae faduwa yake, Umma dai har ta fara lissafin nawa xata kai ma mutumin nan kyauta don nuna masa farin cikinta, gaba daya ta kasa boye how happy she is ah wajen duk da ynda ta dinga dakewa, tunda Imaan suka shigo da Aunty Mujaheed ke kallonta ko kiftawa babu, Abba ya bude wajen da addu'a sannan a hankali yace "Bbu amfanin tsaya jan xance ko wani boye boye, kuma ina son kowa a nan ya dau abinda ya faru yau a matsayin kaddara wanda aka ce ta riga fata, mu ma ba haka muka so ba, kowa ma ba haka xai so ba, sai dai kawai mu kara gode ma Allah don shi ya san dai dai, a takaice dai bbu xancen auren Fatima da yaron nan Sadeeq yanxu..." Ba sai na fadi irin girgixan da mutanen dake xaune parlon suka yi ba a lkcn, ciki kuwa har da Umma da ta dinga salati tana xaro ido tace "Babu aure Kuma, bbu aure fa kace Alhaji, a kan wani dalili xa a fasa aure gashi mun tara jama'ah ta ko ina, me ke faruwa don know" Inna dai gwalo idanuwa tayi ta mike tana kallonsu Abba jikinta na rawa kamar maxari tace "Mutuwa Sadeeq din yyi Ahmadu?" Imaan ta fada jikin Aunty ta fashe da wani kuka mai ban tausayi, Ammi kam bata iya ta daga kanta ba, nan ko ita ma hawayen take, Aunty dake hawayen ita ma tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, me ke faruwa Alhaji" Yusuf bai iya ya kalli mutanen parlon ba duk jikinsa yyi sanyi ba kadan ba, Mujaheed ya dinga kallon Abba ko kiftawa bbu xuciyarsa na bugawa jin abinda yace, kawu Bala yyi kasa da murya yace "Duk ku yi hakuri, we never saw this coming, and we are in it all together, komai ya samu bawa a duniya dama rubutattce ne, kuma bbu wanda ya isa ya kauce ma kaddararsa, wannan yaro Sadeeq dai da kansa ya xo daxu ya nuna ya fasa auren yar mu, tuni kuma mun maida masu sadakin su lefe kuma ko xuwa anjima in sha Allah xa a mayar, Allah yasa hakan ne mafi alkhairi ga dukkanmu gaba daya...." Inna ta rushe da wani kuka da tsorata mutanen parlon tace "To kuwa yanxun nan xan tafi in nemo gidan Bulasawa in ci ubansa da d'an nasa, Allah ya tsine masu albarka, Allah ya tarwatsa su, Allah ya isa tsakanina da su, Allah yyi yaga_yaga da dukiyar nan tasu ta sata, shegu barayi, mu xa su kunyata a idon duniya ga bak'i mun tara ta ko ins, to in sha Allahu kotu ce xata raba mu da matsiyatan, Shari'a ce mai girma xa mu yi tun a duniya kafin mu tafi gaban Ubangijin mu, yau xan tafi in shigar da kara a kotun Habuja...." Abba yace "Don Allah ki sauraremu Inna, dama an taba aure dole?? bbu ruwan ki da su balle aje wani shari'a kawai mu sa a ranmu fasa auren nan shine mafi alkhairi ga 'yar mu, kuma basu kunyata mu ba don bamu bar masallaci ba sai da na tabbatar na fitar da d'an uwana kunya na daura ma 'yar sa aure da nawa d'an da nake da iko da...." lkci daya gaba daya mutanen parlon suka daga kai suna kallon Abba with full shock, ko allura ya fadi a lkcn sai kaji karansa, Imaan taji kamar numfashinta na mata gardama ta dinga kallon Abba xuciyarta na wani bugawan da bai ta6a mata ba, Umma ta hadiye abu da kyar tana kallon Yusuf da kansa dai ke kasa, ji tayi wani xufa na keto mata don wannan shine anyi ba ayi ba, yanxu Yusuf aka makala ma yarinyar nan, Mujaheed dai sai kallon Abba yake xuciyarsa kamar xai fashe sabida yanda yake harbawa, Abba ya mike yana kallon Inna da ta cire mayafin kanta tana kikkifta ido tana kallonsa, yyi kasa da murya yace "Na hada auren Imaan da Mujaheed yau, saboda ina da yakinin xai ma fi Sadeeq din rike min 'ya ta da amana...."
*Table_shaker/Media shaker* 🙄✍🏻
*Imaan isn't for free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
76.....
Kusan a tare Ammi da Umma suka mike tsaye a parlon suna kallon Abba da wani irin shock, can Ammi ta kalli Daddy xuciyarta na bugawa lkci daya hawaye suka dinga sakko mata tana girgixa kai, Tuni Umma ta isa gaban Abba cikin kidimewa bakinta na rawa haka ma ko ina na jikinta tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, la ilaha ilallahu Muhammadur rasulillahi sallallahu alaihi wassalam, ban fahimce ka ba Alhaji? Ban gane ba wllh tllh, Wani Mujaheed din ka hada da Imaan??? Wani Mujaheed din kake nufi, wai d'a na kake nufi?? Ka min bayani don girman Allah Alhaji, wani Mujaheed ne wannan??" Aunty ta kasa rufe bakin da ta bude tana kallon Abba a mugun sanyaye ko motsi ta gagara yi daga xaunen da take, Mama Hadiza tayi tagumi tana kallon Inna da bakinta ke hangame tana kallon Abba a tsorace da alama magana dai ya makale mata gaba daya, sai a sannan Imaan ta gama fahimtar abinda Abba ya fada few seconds ago, don tun bayan maganarsa taji komai na kanta ya kwance ta kasa apprehending, da kyar ta gano me yake nufi bayan maganganun Umma, ja baya ta dinga yi a hankali tana jin wani sanyi na ratsa ko ina na jikinta numfashinta ya dinga sama sama kamar xai dauke, can ta juya a hankali ta kalli inda Mujaheed yake xaune, kan kneels dinsa ta gansa ya rufe fuskarsa da both palms dinsa.... wani ihun da yasa duk mutanen parlon suka juya kallonta ta fasa da karfi, sai kuma ta mike da gudu ta fice daga parlon kamar mahaukaciya, Umma ta durkusa kan gwiwowinta bibbiyu duk jikinta na 6ari ta rushe da wani matsanancin kuka mai cike da tashin hankali ba na wasa ba tace "Alhaji ka min bayani yanda xan gane don girman Allah, ko akwai wani Mujaheed din ne banda nawa a gidan nan, ka fahimtar da ni fisabilillahi, don nasan Mujaheed guda ne a gidan nan kuma d'a na ne, kuma da matarsa... Wani Mujaheed din ka hada da Imaan???" Ammi da ta kasa controlling kanta ta fashe da kuka sosai tashin hankali karara muryarta tace "Abubakar ban amince da auren nan ba, ban yarda ba, nace ban yarda ba, warware auren nan xa ayi, ban amince da shi ba...." tana fadin haka ta fice parlon da sauri tana kuka, Muryar Inna suka ji da karfi tana xaga parlon tana cewa "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'una, la ilaha ilallahu Muhammadur rasulillahi sallallahu alaihi wassalam, hasbunallahu wa ni'imal wakeel, la ilaha illa anta subhanaka innee kuntu minazzalimin, wayyoo Allah ni patuu, Naga abinda ya isheni waye kuma Mujaheed?? Lalacewa ta samu Bukar da Ahmadu, Allah ka yo min agaji naga abinda ya isheni kankat a duniya yau, jama'ah waye kuma Mujaheed, daga ina kuma aka samosa??" Umma dake durkushe ko ina na jikinta na rawa ta dinga gyada kai kamar idanuwanta xa su fito tana kallon Inna ganin abinda ta dinga yi a parlon, gaba daya a birkice take don bata ma san tana gyada kan ba, Mikewa Aunty tayi tana goge hawayen idonta ta fice daga parlon duk jikinta a sanyaye, daga Abba har Daddy da su kawu Bala kallon Inna dake ta xagaye parlon suke, har daga karshe ta tsaya cak waje daya ta juyo tana kallonsu, sai kuma ta rushe da matsanancin kuka tana nuna su tace "Amma Allah ya hada ni da gantalallun 'ya ya, waye kuma Mujaheed Allah na tuba, to wllh kafin in tada gidan nan cikin minti kalilan a warware auren nan don jikata ba rasa manema xata yi ba, ban amince da auren nan ba, kun cuce ni, kun ci amanata kun ja mana fushin Ubangiji a gidan nan yau, lalacewa ta sami 'ya yana ni Asabe...." sai kuma ta fashe da kuka tace "Tunda uwata ta haifeni ban taba ganin haka ba" Umma ma ta fashe da kuka mai ta6a xuciya tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, na shiga uku na lalace ni Rukayya, dama Mujaheed dina ake nufi ban sani ba, dama d'a na aka hada aure da Imaan, na mutu na lalace kuwa" kuka take sosai ba na wasa ba ta daura hannu a ka ke kya ce uwarta ce ta mutu, Ba Abba kadai ba har Daddy was so shocked at reaction din kowa a parlon, Abba ya sunkuyar da kansa ya ma rasa abinda xai ce, Inna ta xauna kan kujera ta kara fashe da wani sabon kukan tace "Idan ba a raba auren nan ba yanxun nan ni dai xan ce na bar ku da Allah inyi tafiyata kano Ahmadu da Bukar, Bala da d'an tsut" Abba ya dago yana kallonta, lkci daya gaba daya mood dinsa ya canxa ganin yanda Inna ke kuka, Umma na jin abinda Inna tace ta tsayar da kukan da take har sannan jikinta na 6ari tana kallonsu Abba taji me xai ce, a hankali Mujaheed ya xame hannunsa daga fuskarsa da ya rufe yana kallon Umma da idanuwansa da suka rine, Mikewa Abba yyi ya wuce bedroom dinsa without thinking twice, Mujaheed ya bi sa da kallo, lkci daya ya mike ya fice daga parlon without anybody noticing him except Mama Hadiza da ta bi sa da kallo, sai ga Abba ya fito daki rike da takarda da biro, tunda Umma take bata ta6a sanin akwai abu wai shi relieve ba sai a wannan lkcn da taga abinda ke hannun Abba, ko da relieve din na ciwo ne tasan bai kai wannan da taji dadi ba yanxu, Abba ya kalli inda Mujaheed ke xaune kafin ya wuce daki yace "Ina Mujaheed din??" Da sauri Umma ta juya tana kallon direction din tace "Gashi nan Alhaji" Xaro ido tayi ganin babu shi a wajen, da karfi Umma tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un.... Ina yake??" sai kuma ta mike kusan a guje ta fita parlon, Inna ta fashe da kuka tana kallon inda yake xaune kafin ya fita tace "Toh me yasa ya fita ga takarda da biro ka dauko me yake nufi da tafiyar da yyi da auren yar mutane a kansa?? To wllh sai ka bi sa Ahmadu, maxa ku bi sa" Abba dai ya kasa cewa komai har sannan yana tsaye da takarda da biro a hannu yana kallon bakin kofa da mamakin fitan da Mujaheed yyi.... Safeenah na xaune compound ana ta hadin salad sai murmushi take ita kadai tun bayan da taga Imaan ta fito parlor ta wuce apartment dinsu da sauri kamar warce aka kora, sai dai fuskarta a rufe yake bata ga expression din fuskar ba, can kuma taga Ammi ma ta fito ta wuce apartment din nasu, ita ma dai ba wani ganin fuskarta tayi sosai ba don saurin take, sai kuma ga Aunty ma ta fito babu walwala ta nufi apartment din su Imaan ita ma, lastly sai Mujaheed, kansa a kasa ya nufi gate, ta mike ta bi bayansa da sauri fuskarta dauke da damuwa tace "Dear wai me ke faruwa ina ta jin kananun rumors wai kamar an fasa auren Imaan, what's happening?" Bai tanka ta ba tafiyarsa kawai yake, da sauri ta dinga binsa tana kallon idonsa da mamaki tace "Did you cry Mujaheed?" Murmushin da bata ta6a sanin sa da shi ba ya sakar mata a hankali yace "Not at all, ki je ki ci gaba da aikin ki" sosai taji dadin murmushin Mujaheed dinta, coz ita dai tun da suka yi aure da kyar idan ta ta6a ganin ko da murmushin sa, ta mayar masa da murmushin tace "Toh dear, amma akwai bikin kuwa har yanxu? Naji sai kananun xance fa ake wai kamar Sadeeq din yace ya fasa??" Still walking yace "Akwai biki, kije ki ci gaba da abinda kike" bai jira cewarta ba ya fice daga gate din gidan kamar dai wanda ake jira a waje sbda saurin da yake, ya shige motarsa yyi zoom off ya nufi main road, Safeenah ta bi motarsa da kallo tana murmushi sannan ta juyo ta dawo cikin gidan, Umma ta hango tana tahowa kusan a guje, a rikice Umma ke kallonta tace "Safeenah ya fita gidan nan ne? Kin gansa?" Da mamaki Safeenah ke kallonta tace "Lafiya? Me ke faruwa? Waye ya fita" Gaban Umma yyi mugun faduwa ta yi still tana kallon Safeenah xuciyarta na bugawa, Safeenah tace "Wai me ke faruwa ne?" Cike da karfin hali Umma tace "A'a dama sako xan basa...." Safeenah tace "Ya wuce a mota ai yanxu" Umma ta saki wani salati ba tare da ta san tayi hakan ba ta fita gate din da sauri, Safeenah ta bi ta da kallon mamaki, har titi sai da Umma ta tafi bbu hijab ko xata ga Mujaheed, amma babu alamar sa, nan ta fashe da matsanancin kuka cikin tashin hankali tace "Toh ina kuma ya tafi bai tsaya ya rubuta takardan ba ni Rukayya..." Sai kuma ta juya da sauri ta koma gida tana goge idonta, wayar Safeenah dake xaune tsakar gidan ta amsa ta xaga bayan gidan da sauri, Safeenah dai sai bin ta take da kallo, a xuciyarta kuwa tunani take to me ke faruwa kuma da matar nan ta rude haka ko dai an daura auren ne bayan full assurance da aka basu baxa ayi ba kuma su ma sun ga alamar hakan, ita duk ba wannan ba murmushin da Mujaheed yyi mata ne ya tsaya mata a rai, ta d'an yi murmushi tana tunanin what to cook for him today, Umma na xagawa tayi dialing number Mujaheed hannunta na rawa, Mujaheed dake driving ya kasa controlling tears dake sakko masa har lkcn ya kalli wayarsa, ganin Safeenah ya d'an yi murmushi ya dau wayar ya katse sannan ya kashe phone din gaba daya ya ajiye, salati umma ta rafka jin waya a kashe da ta sake kira, ta fashe da kuka tace "Ai ni na shiga uku na banu na lalace, me hakan ke nufi ko ba shi da caji ne?" Hannunta na rawa ta sake kira amma a kashe, tayi xaman dirshan a kasa tana shessheka tace "Kila dai ba shi da caji ne, amma da yasan takarda Abba yaje daukowa a daki da baxai wuce ba sai ya tsaya ya rubuta masu, nasan bai sani bane" cikin rawar murya take maganar tayi dialing number Hajiya Saude da har ta haddace lambarta ta kai kunne, Hajiya Saude na dagawa umma ta sakar mata wani kuka da karfi tace "Saude na shiga uku, abu bai yi ba, Saude da nasan xa ayi haka da na bar d'an Bulasawa ya auri tsinanniyar nan, wllh ni yanxu ma sai in taho ki rakani mu koma gun mutumin ya warware abun yaron ya dawo hankalinsa ya xo su yi auren, Saude da yaron yace masu ya fasa auren sai wai Ahmad ya sa aka daura da Mujaheed dina, Mujaheed fa Saude, da d'a na Mujaheed aka daura auren, Mujaheed aka daura ma aure da sauran ciwo, yar wajen Aisha Saude...." Cikin rikicewa da tashin hankali Hajiya Saude ta dinga cewa "Mujaheed kuma, Mujaheed fa kika ce, Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Mujaheed din ki??? La ilaha ilallahu Muhammadur rasulillahi sallallahu alaihi wassalam, mun shiga uku Rukayya, Mujaheed kuma" Umma na kuka sosai tace "Wllh shi Saude, ko Safeenah ban yarda na gaya ma ba ban san ya xata dau wannan labarin da nake ji ya ma fi mutuwata ciwo ba, wllh da auren nan da Ahmad ya daura da d'an cikina da ma mutuwa nayi hakan bai faru ba, wayyo Saude xama bai gan ni ba, gani nan fitowa mu koma gun mutumi a warware komai na hakura duniya da lahira in ma Bualsawan da kansa ke son auren Imaan wllh tllh na hakura Allah ya basu xaman lafiya da xuri'a dayyaba, gani nan fitowa Saude ai lkci bai kure mana ba, da sauran lkci" Bata jira cewar Saude ba ta katse wayar tana kuka kamar ranta xai fita ta daura hannu a ka, da ta tuna Safeenah sai taji xuciyarta ya tsinke har ranta take jin da ma da gaske mutuwa tayi