Showing 261001 words to 264000 words out of 303099 words
Sadeeq ce..." Mikewa Inna tayi da sauri tana kallon Hadiza tace "Wacece mahaifiyar tasa?" Mama Hadiza ta nuna mata, inna ta saki kabbara tace "Sannu baiwar Allah, lallai kin iya haihuwa, ynxu ke ce mahaifiyar wnn yaro me kirki da mutunta babba? Eh lallai Allah ya baki..." Hajiya Khadijah ta gaida ta with respect, frnds dinta ma duk suka gaisheta, Inna ta amsa tana washe baki tace "sannun ku da xuwa bari in debo maku ruwa" daga haka ta wuce kitchen ta dau faranti ta daura lemo biyu da ruwa biyu ta kawo ta ajiye masu tace "Gashi ku dau daddaya ku sha, Allah ya maku albarka" Hajiya Khadijah tace "Toh mun gode Kaka, dama gun mai gidan na xo bai nan, shi ma mahaifin Imaan din yana Abuja aka ce min" Inna ta d'an yi shiru, sai kuma tace "Lafiya kuke nemansu?? Ba an mayar maku da kaya kunce a bar shi ba, to gasu can dai a daki ko tsinke ba a ta6a ba har ynxu a ciki" Hajiya Khadijah tace "A'a ba wannan ya kawo mu ba Kaka" Inna ta sake fuska tana murmushi tace "Toh madallah, me ya kawo ku kenan?" Hajiya Khadijah tace "Xuwa nayi, ga ni ga matar gidan nan, ga Mai gidan, ga mahaifin Imaan da mahaifiyarta su tambayar min ita ko mai ni da Sadeeq muka ta6a mata xata shiga ta fita ta hana aurensa da Imaan, idan kuwa tace babu... to Billahil Azeem xan dau mummunan mataki a kanta, in dai ina numfashi maganan nan baxai tafi a haka ba sai ta san ita ce silan bakin cikin d'a na, kafin in dau mataki nace bari dai in xo ku tambayar min ita ko Sadeeq ya ta6a mata wani abun ne...." Inna dake wurga ido tace "Ban fahimce ki ba 'yar nan? Wace matar gidan a ciki kike nufi??" A takaice Hajiya Khadijah tace "Uwargidan wan mahaifin Imaan, ita nake nufi" Inna tayi wani dariya murya can kasa tace "Toh Alhmdllh, ke ma dai an gano maki ita ta raba auren d'an ki da Imaan kenan? To na ji dadin xuwan ki gidan nan, na kuma ji dadin yanda kika tsaya kan d'an ki ba wasa, yanxu abinda xai faru 'yar nan hakuri xa ki yi har xuwa ranan lahadi duk inda uban Imaan yake dama xan kirasa ya dawo don a kan idonsa xa ayi komai, sannan Ahmadu ma bbu inda xai je ranan, duk xa mu hadu, ga ni, ga ki, ga autata Hadiza, ga uban Imaan, ga bafillatana uwar Imaan, ga ita matar da ku ka xo nema ga kishiyar ta, to sai ayi magana me ma'ana gaban kowa, da kanta xata bude baki ta fadi me tayi har yasa aka fasa wannan aure mai albarka kaca kaca..." Hajiya Khadijah tace "Toh nagode Kaka, Allah ya kara girma" Inna tace "Ameen yar nan" mikewa Hajiya Khadijah tayi ta ma Inna da Mama Hadiza da ta kasa cewa komai sallama ta nufi kofar, frnds dinta ma suka masu sallama duk suka fita, Inna na murmushi tana kallon Mama Hadixa tace "Toh Alhmdllh ba a bakina aka fara jin wannan xancen ba, Rukayya dai ta shiga uku ta lalace in matar nan ta fallasa ta gaban kowa har shi Bukar, sai kuma in xuba ido in ga matakin da Ahmadu xai dauka, shi kuma Bukar xan ga da wani bakin xai yi magana idan ya ji wannan abun al-ajabin" sai kuma Inna ta fashe da kuka sosai tace "Rukayya dai ta cuce mu, ta cuce mu, ta cuci jikata yanxu wannan mata da ta fita da ita ce surkar Imaan fa" Mama Hadixa ta sauke ajiyar xuciya ta dai kasa cewa komai duk jikinta yyi sanyi, a nan ta gane dalilin da yasa Umma ke ta sauri daxu. Tun da Umma ta shiga daki take kuka kamar ranta xai fita banda bugawa babu abinda xuciyarta ke yi, ta leka compound daga windown dakinta ya fi a kirga amma bata ga alamar mahaifiyar Sadeeq da Mama Hadiza ba, tasan kila suna can bangaren Inna, tunanin hakan yasa cikinta ya kara hautsinewa, don tasan shkkn mahaifiyar Sadeeq ta gama fada masu har gida ta je ta sameta ta 6ata Imaan da mahaifiyarta, sai xaga dakin take tana salati hawaye na bin idonta, da ta tuna ai sai dai su Abba su ji a bakin Inna ba dai directly daga bakin uwar Sadeeq din ba sai hankalinta ya d'an kwanta, gwara innan ta fada masu da bakinta, sun kuma santa da karin xance ko xa su yarda ba duka ba... Ammi ta dinga kallon Imaan bayan ta shigo parlor da mamaki tace "Daga Ina kike?" Imaan ta karasa da sauri ta rungumeta tana murmushi tace "Daga gida Ammi, Ina yini" Ammi ta daga kanta tana kallonta tace "Ina Mujaheed din?" Imaan tace "Tare muke, ya shiga gida" Ammi ta dinga kallonta sannan ta saketa tace "Toh sannu da xuwa" Imaan ta xauna saman kujera still smiling tace "Nayi missing din ki Ammi, Daddy yana Abuja koh" Ammi tace "Ehh yana can, bari in sauke abinci" daga haka ta koma kitchen, mikewa Imaan tayi a hankali ta nufi dakinta. Bayan Magrib Imaan na xaune tana cin abinci sai dai gaba daya hankalinta yayi kan Mujaheed ta rasa dalilin da yasa hakan, may be don ta san he is still sad ne and there will be no one to console him, a hankali ta dinga cin abincin duk da yanda tayi missing girkin Ammi amma turawa kawai take bbu appetite, Ammi ce ta fito parlor daga dakinta rike da wayarta tana kallonta ta karaso cikin parlon ta xauna tace "Imaan what's happening?" Imaan ta kalleta da sauri tace "Na me Ammi?" Ammi tace "Me yasa ku ka taho gida?" Imaan ta d'an Bude ido tace "Ya kawo ni ne kawai Ammi fa" Ammi tace "Ya kawo ki kiyi me?" Imaan tace "Ba komai, anjima xa mu koma" Ammi tace "Yanxu daddy ya kirani wai Inna ta kirasa ya taho gida ranan lahadi" Shiru Imaan tayi tana kallonta, dai dai shigowar Mujaheed parlon da sallama Imaan ta kallesa, ya karaso parlon yana kallon Ammi ya xauna kansa a kasa yace "Ina yini Ammi?" Ammi tace "Lafiya lau, sannu da xuwa" yace "Ya gida" tace "Alhmdllh" Yace "Abba yana Abuja" tace "Ehh ya tafi" yace "Toh Allah ya dawo da shi lafiya" Ammi tace "Ameen" daga haka Ammi ta mike ta koma cikin daki, Mujaheed ya kalli Imaan dake ta kallonsa, sunkuyar da kanta tayi tace "Have you eaten?" A hankali yace "Yeah" ta kallesa tace "Nasan baka ci ba" ya d'an yi murmushi yana shafa kansa yace "Na ci mana" kallonsa ta dinga yi, ya mike yace "Dama Ammi na shigo gaidawa" Imaan tace "Xa kaje wajen Inna ne?" Girgixa mata kai yayi ya nufi kofa, ta d'an saci kofar dakin Ammi sannan ta mike da sauri ta bi bayansa. Har ya sauka balcony tace "Yaya" juyawa yayi ya kalleta, ta isa kusa da shi tana kallonsa, a hankali tace "Plss in debo maka abinci ka ci??" Ya matso da ita kusa da shi ya ja hancinta yace "Wanda na ci fa?" 6ata fuska tayi tace "Wllh baka ci ba, ni dai ka jira in debo maka" murmushi yayi a hankali yace "Toh debo min" Da sauri ta juya ta koma ciki, ya bi ta da kallo, direct kitchen ta shiga ta bude warmer din da Ammi ta xuba shinkafar da ta dafa, duk da bashi da yawa sosai haka ta debar masa ta sa masa stew da nama hudu, ta rufe warmer din ta juya xata fito taga Ammi tsaye bakin kofar kitchen din, ji tayi kamar ta nutse kasa kawai ta huta, Ta kasa kallon Ammi ta fara kame kame bakinta na rawa tace "Dama, dama abinci xan kai masa, Ammi shi ya tambayeni" Ammi bata ce komai ba ta karasa cikin kitchen din, Imaan bata yarda ta kalleta ba har ta fita kitchen din da sauri, tana shigowa parlor ta duka kusa da plate din abincinta ta dau nama biyu ta kara a nasa tana satan kallon kofar kitchen din sannan ta mike ta fita, bata gansa a waje ba, ta dinga bin compound din da kallo amma babu alamar sa, part din su ta nufa kamar me counting step dinta ta shiga parlon da sallama murya can ciki, babu kowa sai Tv dake aiki, taji dadin hakan sosai, sama ta wuce ta nufi dakinsa tana kalle kalle ta bude kofar, xaune ta samesa gefen gado yana danna wayarsa, daga kai yayi yana kallonta, ta shiga ta kulle kofar dakin ta karasa kusa da shi ta ajiye masa abincin ta hade rai tace "Shine ka wuce koh?" Jawota yyi jikinsa a hankali yace "Ba gashi kin kawo min har daki ba" Tana kokarin mikewa tace "Xan tafi kar Ammi ta dinga nemana" ya ki saketa yace "Ai a nan xaki kwana" xaro ido tayi ta kallesa sai kuma tayi dariya tace "Tabdi, ni dai ka sakeni in wuce Yaya" yace "Toh wuce da abincin ki baxan ci ba" shiru tayi tana kallonsa, sai kuma ta 6ata fuska tace "Ni wllh sai ka ci" yace "In dai ba nan xaki kwana ba kuma ki bani abincin a baki to baxan ci ba" xaro ido tayi tace "Toh babu spoon din bari in je in dauko a kitchen" ya matseta yace "Guduwa xa ki yi" tace "Ae nasan idan na gudu baxa ka ci ba, spoon xan je in dauko in dawo" yace "Toh je ki dauko" mikewa tayi ta nufi kofa sannan ta juya ta kallesa ta wara masa manyan idonta tana dariya tace "Kai ma ka xo part dinmu ka kwana mana" daga haka ta fice dakin.
*Imaan isn't for free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
93.....
Karfe sha daya saura na dare Umma ta shigo dakin Mujaheed sanye da hijab dinta har kasa, yana xaune ya jinginar da kansa da gado ya daga kai ya kalleta sannan ya dauke kai, he looks so frustrated har lkcn kuma bai ci abincin da Imaan ta kawo masa ba, Umma ta kulle kofar a hankali ta karaso cikin dakin tana kallonsa ta xauna saman kujera, kana ganinta kasan tana tare da damuwa ba na wasa ba, and she looks so sick, bai ce mata komai ba hakan yasa a hankali ta fara magana tace "Kana ji na Muhd?" Kai ya gyada mata ba tare da ya kalleta ba still yace "Ina ji" Maimakon tayi magana sai ta fara hawaye, sai kuma ta fashe da kuka sosai, shi dai bai yarda ya kalleta ba bai kuma ce komai ba, tana girgixa kai cikin sanyin murya tace "I don't know where to start from Mujaheed, ban san ta inda xan fara ba, amma lallai ka sani duk abinda Safeenah ta fada gaskiya ne bbu karya ko daya a ciki, she said nothing but the truth, kuma ba komai yasa na aikata hakan ba Mujaheed sai k'in da nake ma Aisha, I've gone through a lot in my husband's house all bcos of that woman, ita ce ta jefa ni cikin halin da nake ciki na sa6on ubangiji na, ta dalilinta na dinga aikata abubuwan da na aikata, amma kuma da na san Allah xai yi Ikonsa ya juya abun nan ya dawo kai na Abban ka ya baka auren Imaan wllh wllh da ban fara abinda na yi ba, I wouldn't have done what I did, I still can't imagine you having kids with Aisha's daughter, ban san ya xan dau lamarin nan ba idan ka haihu da Imaan Muhd, har yau bana son auren nan naka da ita na fada da babban murya, bana so, bana so har cikin raina, kuma baxan ta6a so ba, da auren nan ya dore wllh gwara ko raina ne ubangiji ya dauka..." Kuka take yi sosai cike da tashin hankali, ta cigaba cikin rawar muryar tace "Amma nasan babu yanda xan yi yanxu, ba abinda xan iya akan auren nan da bana so, sai dai kawai in xuba ido in ci gaba da k'in auren, kuma ni baxan ce xan sa maka baki a auren ba, I will neva do that coz you've always been obedient to me from the first, ko me na sa ka in ma kana so, in ma baka so yi kake yi with respect, baka ta6a min musu ba Mujaheed, kawai abinda na sani babu ruwana da matar ka da abinda xata haifa, babu ruwana da su har abada, put it at the back of ur mind baxan ta6a son auren nan ba kawai adalci xan maka, Baxan ta6a daukan 'yar wajen Aisha surka ba, baxan dau 'ya yan da xata haifa a jikokina ba, Wanda Ina ma fatan kada Allah ya bata 'ya ya da kai, lastly I want to say I am sorry for all the shame and frustration I've caused you before and is still causing you now, don magana na gaba sosai, you just have to take heart and pretend everything is fine" daga haka ta mike tana goge idonta ta bar dakin Mujaheed ya bi ta da kallo, jinginar da kansa yyi a hankali da gado ya lumshe idanuwansa hawayen dake makale idonsa suka sakko kasa. Imaan na kwance daki sai dai ba bacci take ba, she's just imagining ko Mujaheed ya ci abincin da ta kai masa ko bai ci ba, a hankali ta mike xaune ta sauka saman gadon ta nufi press dinta, ta fi minti biyu tsaye kafin ta bude ta ciro jakar islamiyyarta ta koma kan gado ta xauna ta bude jakar a hankali, takardar da ya ta6a jefo mata ta window da dadewa ta ciro daga cikin jakar ta dinga kallon well folded takardan sannan ta warware tana kallon rubutun ciki, ko layi daya bata kai ga karantawa ba ta daga kai da sauri jin an bude kofa, Ammi ce ta shigo dakin ta kulle kofar, kallonta Imaan ta dinga yi har ta karaso kusa da gadon ta xauna a gefe tana kallon takardar hannunta ta amsa, Imaan ta sunkuyar da kanta gabanta na faduwa, Ammi ta gama karanta Content din takardan ta ajiye gefe sannan a hankali tace "Imaan" imaan ta daga kai tana kallonta, Cikin sanyin murya Ammi tace "From all indication you are now happy getting married to Mujaheed right?" Imaan ta sauke kanta kasa bata ce komai ba, Ammi ta girgixa kai tana murmushin karfin hali tace "I am surprised har xa ki hakura lkci daya haka Imaan, I am very surprise at you, amma ki sani har gobe baxan ta6a alfahari da auren ki da Mujaheed ba, never!" Kuka Imaan ta fara yi a hankali bata ce komai ba, Ammi tace "And since you accepted him lkci daya sbda ya maki dadin baki irin na maxa, to ki sani duk abinda xai je ya dawo iyaka in maki addu'a Imaan, tunda kina ganin auren ki da Mujaheed alkhairi ne har kika hakura cikin sanyi, kuma cikin kankanin lkci Allah yasa hakan..." Daga haka Ammi ta mike ta nufi kofa Imaan ta bi ta da kallo tana hawaye, kafin ta fita tace "Ammi shi fa Yaya babu ruwansa kema kin sani, kuma ai ni ban ce na hakura ba.." Ammi ta juya ta kalleta sannan tayi murmushi a hankali tace "Ae bance da ruwansa ba Imaan, Allah ya raba ki da sharrin uwarsa, ki je ku karata da shi..." Daga haka Ammi ta fita dakin. Washegari Friday Umma taji shiru shiru dai Abba bai kirata ba kamar yanda take ta jira, har dai ya fita gidan da safe, da yamma xuwa parlonsa tayi bayan ya dawo duk da ba ita ce da girki ba amma shiru bai ce mata komai ba sai ma tambayar ta da yyi me Mujaheed suka xo yi gida jiya, don throughout ranan ita kanta bata ga Mujaheed ba, Tayi murmushin karfin hali tace "Kila sun xo gaishe mu ne, amma Ina jin ai sun koma, don duk yau ban gansa ba" Abba bai ce komai ba ta mike ta fita tana mamakin mai ya hana Inna ko Mama Hadiza yi masa magana a kan xuwan Hajiya Khadija gidan, ko ba komai dai ta ji hankalinta ya kwanta, kila basu yarda da uwar Sadeeq din bace, ta dinga fatan Allah ya sa maganar ta tafi a haka, tsabar tashin hankali ko mutum daya bata fada ma damuwarta cikin kawayenta ba, tana fitowa Parlor Maimoon tace "Umma Maman Surayya ta xo neman ki tana sama" Umma ta wuce sama da sauri jin Hajiya Saude ta xo nemanta, xaune ta same aminyar tata a gefen gadonta, Umma ta kulle kofa tana dubanta ganin yanayinta tace "Lafiya Hajiya Saude?" Hajiya Saude ta fashe da kuka sosai ta ajiye takardan hannunta tayi tagumi cikin rawar murya tace "Na shiga uku Rukayya tawa ta sameni Babansu Surayya ya sakeni...." Umma ta xaro ido tace "Ya sake ki kuma Saude? Garin Yaya, me ya faru?" Hajiya Saude ta dinga girgixa kai hawaye na sakkowa idonta tace "Surayya ta cuceni ta kunyata ni gaban kishiyoyina Rukayya, hotel ta bi saurayi karban waya abokin Babanta ya ganta, in takaice maki har hoto yayi mata, ya xo har gida ya nuna ma uban, tun jiya ake abu daya bbu tashin hankalin da ban gani ba, bayan uban ya kusa karyata da duka naga abun yyi yawa sai na nuna bacin rai na shine fa kamar wasa bawan Allahn nan ya rubuta takadda ya bani, dama kwanaki ya min daya bayan wanda yyi min shekaru biyar da suka wuce, yanxu fa duk ya katse igiyoyin, ki tashi Rukayya ki rufa min asiri ki raka ni mu tafi gun mutumin nan baxai rasa abun yi kan matsalar nan ba, fita gidan ubansu Surayya ba nawa bane..." Umma dake ta kallonta baki bude tace "Toh ina ga wllh tawa matsalar ma ta fi taki Saude...." Nan Umma ta kwashe duk yanda aka yi daga jiya xuwa yau ta labarta ma Saude tana matsar kwalla ita ma, tana girgixa