Showing 84001 words to 87000 words out of 303099 words

Chapter 29 - Imaan Book 1 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

1669

ci mutuncin ta..." Da sauri ya dakatar da ita yace "Wllh bata sani ba, baki ga ita ma duk ta ki sakin jiki ba" Ammi tace "Ni dai ka cuce ni, har kasa naje ina ce masa mai gida" Shi dai bai fasa mata dariya ba, ta gama xuba abincin tace "Ai sai ka daukar maku, ni kam na wuce daki" bata kara sauraransa ba ta fita kitchen din ta wuce bedroom dinta, Muhsin ya ci abincinsa ya koshi, Sadeeq kam ruwa kawai ya sha ya mike yace "I am waiting for you outside" duk yanda Muhsin ya so tsayar da shi kin saurarensa yayi har ya fita, nan Muhsin ya kira Ammi a waya yace "Toh ya dai fita Ammi ki fito mu yi sallama" Ammi ta fito parlon tace "Bai ci abincin ba kenan" Muhsin yace "Ae baxai ci ba, Ammi Abbansu Mujaheed ne fa ya kirasa yana nemansa shine muka taho tare" Ammi tayi shiru tana kallonsa da mamaki, can tace "Toh ya aka yi da ku ka je?" Muhsin yace "Ba wani matsala wllh, Ai nasan daddy xai maki bayanin komai idan ya shigo, yanxu dai xan wuce kinga yana can waje yana jirana" Ammi tace "Toh shikenan ka gaida Hajiya da Hajjo" Yace "In sha, kice ma Imaan ta fito mu dai mun wuce" daga haka ya fita parlon yana murmushi, a can kofar gida ya tadda Sadeeq xaune cikin mota yana jiransa, Muhsin ya bude motar ya shiga yana kallonsa yace "Kai dai ka rage munafurci Sadeeq duk rashin jin ka don ka xo gaban surkai sai kayi ta wani sinne kai" Murmushi kawai Sadeeq yyi ya saka glasses dinsa ya tada motar yace "I will have ur time later" daga haka ya fara reverse suka bar layin. Kamar yanda Muhsin ya fada hakan ne ya faru don daddy na shigowa bayan Magrib ya yi ma Ammi bayanin duk abinda ke faruwa, Ammi tayi shiru duk jikinta yyi sanyi, A hankali tace "Toh yanxu ya ake ciki yallabai?" Ya sauke ajiyar xuciya yace "Ina imaan din, taje can barrister na kiran ta" Ammi tace "Ni dai Yallabai da dai a dakatar da yaron gaba daya, imaan har nawa take don Allah" Daddy yace "So kike ki ja mana matsala gun inna kenan, did you know maganar da ya dawo dani weekend kenan, ke kin ga abubuwan da inna ta dinga fadi a parlor kuwa jiya?" Ammi dai bata ce komai ba, Daddy ya girgixa kai yace "Fatanmu mu rabu da ita lafiya, gaba daya ta rikice ne yanxu" murmushi kawai Ammi tayi, Daddy yace "I don't even know me yasa xa ki ba Imaan fuskar kula saurayi at the first place, ko me xaki ce min baxan ta6a yarda baki san da xancen yaron ba, kuma ki wani ce min nawa Imaan take?" Ammi tace "A'a ko da baxa ka yrda ba I have to tell you I know nothing much about the boy, of recent naga tana waya shi ma sai da na mata fada, kai sai kace baka san yar taka bace da nuku nuku" Daddy yace "Wannan ba hujja bace, kina tare da ita 24/7 a gida...." Ammi ta dakatar da shi tace "Toh duk ba wannan ba ita innar da ta kirkiro abun sai a fada mata ta gaya ma yaron lalurorinta... If he wish to be with her like that shikenan, idan kuma baxai iya ba gwara tun wuri a san haka, I don't want my daughter's heart to be broken or anything of such..." Daddy ya dinga mata wani kallo ta mike ta wuce kitchen, yace "Wato you are even in support of the silly thing the girl did, dama nasan kinsan komai ai, tunda aure take so fine I will give her the best wedding ever" Imaan ta marairaice tana kallon Ammi tace "Toh me yasa yake kirana Ammi?" Ammi tayi banxa da ita, a hankali ta mike ta nufi kofa, Ammi tace "Kuma kiyi maxa ki dawo idan ya sallameki ki xo ki kai ma Inna abinci" to kawai tace ta fita parlon. A hankali Imaan ta bude kofar parlorn hade da sallama ta shiga ciki, Umma ce xaune parlor sai Ummi da Rahma, ta dauke xata wuce parlon Abba Umma ta dakatar da ita ta hanyar daka mata tsawa, Imaan ta tsaya amma bata juyo ba, Umma ta mike tana mata kallon tsana karara tace "Uwarki tayi ajiya parlon ne ta aiko ki kixo ki dauka?" Imaan taki cewa komai sai ma dauke kanta da tayi, Xagi Umma ta kunduma mata tace "Kin matsa bakin kofar nan ko sai na faffalleki da mari"


27.....


Imaan dai bata tanka ta ba ta nufi stairs, Umma tace "Ragowar ciwo kawai" Sai da Imaan ta isa stairs ta turo baki ta wuce sama, sai kuma ta fashe da kuka, dai dai corridor suka hadu da Mujaheed ya fito dakinsa, ya bi ta da ido har ta shiga dakin Aunty, Karasawa stairs yyi yana lekan downstairs ganin Umma xaune ya dawo da sauri ya bude kofar dakin Aunty ya shiga ya kulle, Aunty na tsaye kanta sai tambayarta me ya faru take hankali tashe, Imaan da ta xube mata nan tsakar dakin ta dinga kuka ta ki cewa komai, Aunty tace "Kinga iskancin nan naki ne bana so, baxa ki bude baki ki min magana ba, me kika yi ma Ammin?" Still ta ki cewa komai, Mujaheed ya karasa kusa da su yana kallonta yace "Baxa ki bude baki ba ana maki magana?" Ta hade kai da gwiwa cikin rawar murya tace "Ko ba Umma bace take xagina ni ban mata komai ba har da ce min ragowar ciwo" Aunty ta ja tsaki tace "Shine xaki xo ki tada min hankali a nan? Sai me don ta ce maki ragowar ciwo? Xa kuwa ta ga ragowar ciwo a xuri'arta wataran, domin ita ta gama haihuwa ai yanxu su kuma 'ya yanta xa su fara...." Juyawa Mujaheed yyi ya nufi kofa, Aunty ta bi sa da harara har ya fita, Aunty tace "Banda shashanci shine xaki xo kina ma mutane kuka, yau ta saba gaya maki haka?" Ita dai Imaan bata ce komai ba sai share idonta take, Anty tace "Aiko ki Ammi tayi ko me?" Ta dago ta kalleta a hankali tace "Abba ne ke kirana" Aunty tace "Tashi mu je, yana parlon sa ai" mikewa imaan tayi ta bi bayan Aunty suka fita, Umma ta dinga bin su da wani kallo, Aunty ta nufi parlon Abba tana cewa "Ae ba mahalukin da ya isa raba ki da ubanki, sai dai a ganki a kyale bbu ynda aka iya da ke" Aunty ta bude mata kofar tace "Shiga" Imaan ta shiga parlon Aunty ta rufe kofar ta koma sama, Abba na xaune yana kallon news Mujaheed ma na parlon, sallama Imaan tayi ta xauna kasa ta gaida Abba dake kallonta, yace "Lafiya lau Mamana sai yanxu kika xo?" Kai kawai ta gyada masa, Abba yace "Toh yayi" bai kuma cewa komai ba, Imaan ta saci kallon Mujaheed taga kallonta yake, suna hada ido ya hade rai, turo baki tayi tana fidgeting fingers dinta, Bayan few minutes Abba yace "Imaan ai kin san wannan yaron Sadeeq koh?" Shiru tayi bata ce komai ba ta kuma kasa kallon Abba, Abba yace "Ina saurarenki" ta gyada masa kai tace "Uhm" Abba yace "Kar fa ki boye min komai I am ur father, ki gaya min meye tsakaninku" dauke kai tayi ta ki cewa komai, Abba yyi murmushi yace "Baxa ki gaya min ba kenan" Nan ma dai ta ki cewa komai, Abba yace "Toh tunda ni kunyata kike ji sai ki gaya ma Mujaheed meye tsakanin ku" Xaro ido tayi tana kallon Abba, Abba ya mike yace "Xan dawo yanxu, let me make a call outside, sai ki gaya masa kafin in dawo shi kuma ya gaya min" daga haka Abba ya fita ya kulle kofar, tun da Abba ya fito Umma ke binsa da kallo har ya fita main parlor, ta kalli kofar parlon sa.... Imaan dai ta kasa xaune waje daya bayan fitar Abba, jin shiru ta d'an saci kallon Mujaheed, ganin irin kallon da yake mata xata mike yace "Koma ki xauna" ta marairaice tana dubansa tace "Ni fa ruwa xan je in sha in dawo" ya dawo kusa da ita ya xauna yana kallonta da kyau cikin husky voice dinsa yace "Me nace ki ce ma Abba?" Ta 6ata fuska kamar xata yi kuka a hankali tace "Yaya ba ka riga ka gaya min jiya ba, ai xan gaya masa...." Sai kuma tayi shiru, ya hade girar sama da ta kasa yace "I will slap you idan baki gaya min abinda xaki gaya masa ba" Tace "To ba cewa kayi ince ban san sa ba...." ya dinga kallonta fuskarsa daure, a hankali ta mike da nufin fita parlon ya fixgota ta fado jikinsa, xaro ido tayi tace "Yayaa" bude kofar parlorn aka yi yyi saurin janyeta jikinsa, Kallonsu Aunty ta dinga yi daga inda take tsaye bakin kofa, Mujaheed duk ya daburce ya mike tsaye, Imaan ta zamo kasan kujeran kamar xata yi kuka, Aunty tace "Meye hakan" Mujaheed yace "Aunty kawai daga mata magana shine xata fado kaina" Aunty ta tabe baki har sannan tana kallonsu, juyawa tayi xata fita sai ga Abba, ta basa hanya ya shigo parlon, Anty ta fita waje, Abba na kallon Mujaheed bayan ya xauna yace "what did she say about him?" Mujaheed ya xauna saman kujera yana shafa kansa a hankali yace "Tace ba komai tsakaninsu, bata ma wani sansa ba kawai shine ke kiranta a waya..." Imaan ta kallesa da sauri, Abba yace "Haka ne Imaan?" Kamar xata yi kuka tace "Abba ni dai bance masa haka ba, frnd dina ne fa, kuma yana koya min karatu ta waya wani lkcn, ina ganewa kuma" Mujaheed ya kasa kallon Abbansa, Abba ya kafe sa da ido, can ya d'an yi murmushi mara sauti yace "Toh shikenan mamana, tashi ki tafi" mikewa tayi ta nufi kofa, xata fita ta d'an saci kallon Mujaheed da ya ki dago kansa ta fita. Bata damu da irin kallon da Umma ke mata ba har ta fita parlon ta wuce part din su. Abincin inna ta dauka ta tafi kai mata, sallah ta sameta tana yi a parlor ta ajiye abincin xata fita, inna ta dinga gyaran murya alamar ta tsaya, imaan tayi kamar bata ji ba tayi wucewarta da sauri, a hanya ta tadda Yusuf rike da ledan fruits xae kai ma inna, ta gaishesa tana kallonsa, sama sama ya amsa mata ya wuce, ta tsaya ta bu sa da kallo har yyi nisa, turo baki tayi ta bar wajen, har ta gama shirin kwanciya kiran Sadeeq ya shigo wayar ta, ta kashe fitilan dakin ta hau saman gado ta rufe har kanta da duvet sannan ta daga kiran, murya can kasa ta amsa sallamansa yace "Kin fara bacci ne?" Ta girgixa masa kai tace "A'a" murmushi yyi yace "Toh ya kike?" Tace "Alhmdllh, ya aiki?" Yace "Lafiya lau..." A hankali tace "Shine daxu baka ce min xa ku xo da ya Muhsin ba koh?" yyi murmushi yace "Shi yace kar in gaya maki" tace "Toh yanxu da kun sameni ban sa Hijab ba fa?" Ya wara ido yace "Yea sai in ganki da kyau, ai ba laifi bane don naga abinda nake so ba hijab" ta xaro ido tace "Uhnnn?" Yace "Yess" murmushi tayi bata ce komai ba, Yace "Ya Ammi fa?" Tace "Tana lafiya" yace "Maa sha Allah, kinje gun kaka yau?" Tace "Ehh na je kai mata abinci" yace "Ina son in samu time in xo mu yi hira sosai da ke da kaka" ta xaro ido tace "Ai ita bata hira, bata fiye son magana ba ma" Dariya Sadeeq yyi yace "Really?" Kamar xata yi kuka tace "Ehh" yace "Uhm to shikenan, yaushe xan xo mu yi hiran mu biyu kadai, I want to tell you lot of things Imaan" Murmushi tayi tace "Ae Daddyna na gari bai koma ba tukun" Yace "Toh baxa ki gidan gwaggo ba mu hadu can?" Ta d'an yi shiru, murya can kasa yace "Are you there Imaan?" A hankali tace "Toh gobe xan ce ma Ammina xan je can dama ai saura kwana uku bikin Anty Halima kilan idan na je sai bayan bikin xan dawo gida" yace "Toh shikenan idan kin shirya goben sai ki kirani" ta xaro ido tace "But ai sai Ammi ta amince in je, kasan ba a son ina fita ni kadai" yace "Toh Allah yasa ta amince" Tace "Ameen" da sauri Imaan ta cire duvet din kanta jin kamar ana bude window, ganin farin abu tayi ya fadi kasan dakin, ta sauka gadon ta nufi windon da sauri ta bude labule har sannan waya na kare kunnenta, Mujaheed ne tsaye kusa da window din, ta xaro ido tana kallonsa, yana mata wani kallo ya juya ya bar wajen, ta rufe window din ta durkusa ta dau takardan tana kallo, muryar Sadeeq taji a kunnenta yace "Are you there?" Tace "Yea ina ji" yace "Ko kin fara jin bacci ne" murmushi tayi tace "Um" don so kawai take ta bude takardar ta ga content dinsa, yace "Toh shikenan, sleep like a baby dear" murmushi tayi tace "Toh nagode, good night" daga haka ta katse wayar ta ajiye ta kunna fitilar wayar ta warware takardan tana haska rubutun kai, xumburo baki tayi ta cukwuikuye takardan ta jefar ta kwanta kamar xata yi kuka tace "Ni dai ba ruwanka da ni"

Mikewa tsaye Aunty tayi tana kallon Yusuf dake xaune gefen gadonta, shi kam bai yarda ya kalleta ba, Tace "What are you saying Yusuf?" Still ya ki cewa komai, aunty ta dinga kallonsa ko kiftawa babu, can ta ja stool ta xauna tace "Ka daga kai ka min magana malam" Sai a sannan ya daga kai ya kalleta, tace "Are you serious with what you are saying, or should i say are you on ur right senses?" Cikin sanyin murya yace "Sure Mum" Tagumi Aunty tayi tana kallonsa with much surprise, can ta girgixa kai cike da damuwa tace "Kai ma kasan wannan ba abu bane da xai yiwu, ba abu ne mai sauki, haba Yusuf me yasa ka yarda xuciyarka ta yaudare ka da son abinda kasan da wuya ka samu, ko da kuwa kana tunanin xaka samu mai yasa baka tsaya kayi naxarin irin matsalolin dake tattare da samun ba? Wait tukun toh ita Hafsat din fa?" Ya girgixa kai cikin low voice yace "Ku ke tunanin ina son Hafsat, she is just a frnd, bani da intention na auranta...." Aunty ta xaro ido tana kallonsa, can tace "Ikon Allah, i really don't know what to say to you now Yusuf, ban san me xance ba gaskiya, amma ni da xaka bi shawarata ka bar wannan xancen it's something that isn't and will neva be possible, forget this pls son" Yana kallonta da mamaki yace "Why Mum?" Tace "Look Yusuf, Imaan is my daughter, her mother is my very close frnd as well, infact childhood frnd dita ce Aisha, don ta dalilinta na hadu da mahaifin ku har muka yi aure, but... ni xan fi son mu ci gaba da xumunci da Hajiya Aisha as just the frnds we are, and marrying into same family, I mean relationship din mijinta da mijina, amma bana son xumuncin mu ya koma na in-laws, its somehow, that aside Yusuf, kusancin inna da Imaan.... don't misunderstanding me plss son, kai ma inna kakar ka ce, amma gaskiya akwai matsala daga bangaren inna ka bar ni ma in ji da headache daya...." Yusuf ya girgixa kai yace "Kiyi hakuri Mum, I don't think all this u are saying is enough da xai sa ki hanani auren Imaan" Aunty ta bude baki tace "Ni nace xan hana ka aure Imaan Yusuf, idan Allah yyi Ita din matar ka ce ni na isa in hana? Don't quote me wrong plss, amma kai kasan kana son ta me yasa ko sau daya baka taba nuna alamar haka ba?" Yace "That's bcos she is still young, har yanxu Imaan bata san meye rayuwa ba, bata san kanta ba har ynxu, I was thinking idan ta fara jami'a ta d'an yi hankali sai in fito da intentions dina toward her" Aunty tace "Toh Allah ya kyauta, I think it's best ka je ka samu abbanku, amma ni nasan da kyar ne...." Yusuf yyi kasa da kai a hankali yace "Ni dai ki daina cewa haka plss mum, support me sannan ki min addu'a" a sanyaye tace "Toh na daina cewa haka, Allah yayi maku xabi mafi alkhairi Yusuf" yace "Nagode mum" daga haka ya mike ya nufi kofa ta bi sa da kallo har ya fita, Tagumi tayi tana furta innalillahi.... A xuciyarta. Sake baki Abba yyi yana kallon Yusuf with surprise, shi dai Yusuf bai yarda ya kallesa ba, bayan few seconds Abba yace "Yusuf" Sai a sannan Yusuf ya daga kai da kyar yana kallon Abban nasa, Abba yace "Kana nufin Imaan kake so?" Yusuf ya sunkuyar da kai a sanyaye yace "Ehh Abba" Abba yace "Ikon Allah" Shiru ne ya biyo baya na kusan minti biyu, can Abba ya daga wayarsa yyi dialing number Mujaheed har ya gama ring ba a daga ba, Abba ya ajiye wayar sanin yana gun aiki, Abba yace "I am happy hearing this son, but at the same time I am disturbed coz I made a promise to someone earlier, all the same don't worry, Allah xai shige mana gaba, tashi ka tafi" Mikewa Yusuf yyi ya nufi kofa Abba ya bi sa da kallo yana murmushi. Ko minti goma ba ayi da fitar Yusuf ba sai ga Umma ta shigo parlon Abba cikin shirin fita, har sannan Abba was still pondering at what Yusuf told him, kuma har ransa yake jin xai fi kowa murna da wannan hadin, Auren d'an sa da tillon 'yar d'an uwansa, tunanin yanda xai fara billowa al'amarin yake, first ya fara kiran D'an uwan nasa ya


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login