Showing 294001 words to 297000 words out of 303099 words

Chapter 99 - Imaan Book 1 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

1625

kai da kanta kawai, Inna na xaune Parlor ta sa tuwonta a gaba tana ci, Ta dinga bin Ammi da kallo har Ammi ta xauna ta gaisheta, Inna ta amsa tace "Yar ki kika xo dubawa kenan, ai har na kullaceki nayi xaton baxa ki xo ba don kece ta farko da na fara kira" Ammi tayi murmushi ta ajiye abincin hannunta tace "Ga danwake nan na kawo" Inna tace "Toh gata can, malaria ne ya kusa mata illa Ahmadu yace ba sai na kai ta asibiti ba an riga an kai ta" Ammi tace "Toh Allah ya sauwake" Inna tace "Ameen, mijin ya dai cuce ta jeki ki ganta" mikewa Ammi tayi ta wuce dakin, karasawa tayi kan gadon tana kallon imaan ta cire blanket din jikinta, Imaan ta bude ido, da sauri ta mike ganinta tace "Ammi" sai kuma ta rungumeta, Ammi tayi murmushi lkci daya jikinta yyi sanyi ganin yanda ta rame, Imaan tace "Ammi Ina yini" dago kanta Ammi tayi tace "Ya jikin?" Imaan tace "Da sauki" Ammi tace "Mu je parlor ki ci danwaken na kawo maki" Ta marairaice tace "Ammi ina son inje can bangarenmu mu" Ammi tace "A'a kiyi xaman ki a nan" Inna ce ta shigo dakin tace "Toh ta fito ta ci danwaken tun daxu babu abinda ta saka a baki" Ammi ta mike tana kallon Imaan tace "Sakko mu je ki ci" A plate Ammi ta xuba mata danwaken, Imaan dai sai kallon abincin take, ta dau fork da Ammi ta sa mata ta dau daya a hankali ta kai baki, Ammi ta koma saman kujera ta xauna, Inna dai sai kallon Imaan take tace "Toh ni dai ko wancan mayyar da ya saka ce ta kama jikata ba a sani ba...." Ko rufe baki Inna bata yi ba Imaan ta mike tayi hanyar daki da gudu tana yunkurin amai, Inna ta mike da mamaki tace "Yau naga tsiya, naga jaraba, meye kuma amai amai kamar me ciki? Aman meye kuma wannan take yi?" Mikewa Ammi tayi ta bi bayanta, Inna tayi shiru kamar me naxari, can ta bi bayansu ta shiga dakin da sauri tana xare ido tana kallon Ammi da ta dago Imaan tana mata sannu, tace "Mun shiga uku, Astagafirullah Aisha ko dai ciki ne da Imaan din?" Ammi dai bata kalleta ba kuma bata ce komai ba, Inna dai sai xaxxare ido take tana kallon Imaan dake sauke numfashi Ammi ta karasa shiga bandaki da ita. Inna ta saki salati tana tafe hannu dai dai shigowar Aunty dakin, Inna tace "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un, ta cuce kanta wllh, kanta ta cuta ba ni patuu ba" da mamaki Aunty tace "Me ya faru Inna?" Hawaye cike idon Inna tace "Yanxu sbda rashin tsoron Allah Amina sai da yarinyar nan ta amince da wannan mutumi har ya kai ta ya baro babu kayan aure, cikin d'an mutum ne da ita fa Amina, wllh tllh danyen ciki ne shataf da ita, ni naga yarinya tayi wani haske kamar danyen nama, sai kirji da suka cicciko, to sai kuma ga amai naga ta kirba daxu a bandaki daga tayi ido hudu da tuwo, yanxu kuma daga uwar ta kawo mata danwake da mai da yaji ta kai loma biyu baki sai amai shaaaa duk karni, kaiiii Amina lallai sai dai a kyale yaran yanxu, amma ba a ta6a kunyata ni irin yanda Imaan ta kunyata ni ba yau" Aunty dai sai kokarin danne Dariyarta take tace "Haba Inna, yarinya da mijinta kuma...." A fusace Inna tace "Ke dalla rufe min baki, Mujaheed ne har xa a kira miji, dama jira kawai yake yyi mata ciki ashe ni ban sani ba, ita kuma jarababbiya kawai, oh oh toh ba ruwana ya xo ya tattara ta ya mayar da ita gidansu su je can su karata da aman su ba da ni ba xa ayi wannan gagarumin kazantar ko 'yar cikina Hadiza lkcn da take da cikin d'an ta na farko ban amince ta xauna da ni ba sbda amai da yawu balle wa ennan kareren, duk kawai a bata min gida da k'arnin aman ciki, Aa wllh duk inda yake ya xo ya dauketa ko kuma uwarta ta maida ta bangarensu suje can su karata wllh wllh ba ruwana, ba dani ba, duka duka yaushe aka yi auren har ta yadda da shi ciki ya shiga idan ba fitina ba" Aunty ta fita dakin tana girgixa kai tana murmushi, Ammi dai ta gama gyara mata jikinta a bandaki ta fito da ita dakin tana rike da hannunta Inna ta basu hanya da sauri fuska daure, Ammi ta fita dakin, ta dau cooler din danwaken suka bar parlon ta wuce part dinta da yar ta.



*Imaan isn't for free* it's 300 via


Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788



*Albishirinku 'yan uwa*

Shin ko kun San zaku iya magance mafi yawan cututtukan da suka addabi al'umma yanzu cikin sauki?
Sinadarin _Stemcell total care_ yayi fice wajen magance matsalolin diabetes, BP, asthma, sickler, cancer, stroke, rashin haihuwa, fibroid, infection da duk wata matsala da ta danganci lafiyar Al'umma.
Ba wannan kadai ba, akwai coffee na double root Wanda ke inganta duk wani abu da ya shafi rayuwar aure ga maza da Mata, inganta qwayoyin haihuwa da dai sauransu.
Akwai sinadarin rage tumbi da dai sauransu.

*Domin neman qarin bayani ku tuntubi wannan lambar 07068136856*
Sai an gwada akan san na kwarai.






105.....







Da daddare Ammi na tsaye dinning tana debar ma Imaan kunun da ta dama mata a flask aka bude kofar parlor, rufe flask din tayi tana kallon kofar Abba ya shigo da sallama, amsa sallamar tayi har suka karaso cikin parlon Mujaheed na biye da shi a baya, Abba ya xauna saman kujera yace "Sannu da gida Hajiya" Ammi ta karaso parlon tana murmushi tace "Ina yini Alhaji" Abba yace "Lafiya lau, ya mai jikin ta kara ji?" Ammi tace "Da sauki, Alhmdllh" Abba yace "Toh Allah ya bata lafiya" Ammi tace "Ameen" shi dai Mujaheed kansa na kasa bai kalli Ammi ba yace "Ina yini Ammi" tace "Lafiya lau, ya aiki?" Yace "Alhmdllh, ya mai jiki" Ammi tace "Da sauki tana ciki" Abba ya mike yace "Bacci take ne?" Ammi tace "A'a ina jin idonta biyu" Bedroom din Imaan Abba ya nufa Mujaheed ya mike ba tare da ya yarda ya kalli Ammi ba ya bi bayansa, idonta rufe suka sameta dakin ta rufe duk jikinta da bargo, Abba ya tsaya yana kallonta yace "Ta koma baccin kenan" Shi dai Mujaheed na tsaye sai kallonta yake bai ce komai ba, Abba ya girgixa kai yace "Allah ya bata lafiya, I will check on her tomorrow" daga haka ya juya ya nufi kofa, Mujaheed ya bi sa da kallo har ya fita sannan ya isa kusa da ita ya xauna ya sauke blanket din jikinta ya kai hannu forehead dinta yace "Imaan" Bude ido tayi tana kallonsa, ya sakar mata lallausan murmushi ta kamo hannunsa cikin sanyin murya tace "Yaya" ya dagota ta xauna yace "Kanwata" shiru tayi tana kallonsa, yace "Are you feeling pain anywhere?" Ta jingina da gado tace "Ina jin xaxxabi da tashin xuciya, kuma my leg is aching me now" yace "Toh xan taho maki da magani yanxu, but me kike son ci kanwata?" A hankali ta girgixa masa kai tace "Amai xan yi" da damuwa yace "No baxa kiyi ba sweet, tell me what u want to eat let me get it now" ta d'an yi shiru kamar me naxari, can tace "Beans" ya wara manyan idanuwansa yace "Ke da ba ki cin beans baby?" Turo baki tayi tace "Ni dai xan ci yau" murmushi yayi yana shafa cikinta a hankali yace "Babynmu beans yake so kenan?" Kallonsa ta tsaya yi, ya ja hancinta yace "Ko ba haka ba?" Ta 6ata fuska tace "Wani babyn?" Ya kashe mata ido yace "Na mu mana sweet" turo baki tayi kamar xata yi kuka, ya ja hancinta yana murmushi yace "Salon ki haifo min baby me turo baki koh?" Rufe fuskarta tayi da pillow, ya mike yana murmushi yace "Xan dawo anjima kadan" Ita dai bata ce komai ba ya nufi kofa ta dago kanta a hankali ta bi sa da kallo har ya fita, Ammi na tsaye dinning rike da cup din kunu tana jiransa ya fito, Bai iya yace mata komai ba duk da ya so ce mata xai dawo anjima, har dai ya nufi kofa ya fita ya kulle kofar sannan Ammi ta nufi dakin. Abba na fita part din Inna ya nufa, ya shiga parlon da sallama jin ta a kitchen ya xauna, sai ga ta ta fito tace "Ahmadu ne" yace "Ni ne, Ina yini Inna" tace "Lafiya lau, aiki nake a kitchen, baka ji bayana ba wllh kamar xai balle in huta" D'an murmushi yayi yace "Me kike girkawa kuma da daren nan Inna, ba an kawo maki abinci ba?" tace "Me nake girkawa kuma? Wannan yarinya me laulayi nake ma faten tsaki, wai daxu daga nace tana jin amai da sai ta min magana in kai ta waje tayi a can sbda kar mu xama kazamai tunda a daki bandakin yake, kada kazanta ya ra6e mu, na dai mata magana ta fahimta Ahmadu, shkkn in gaya maka sai matar nan Aisha ta kullace ni ta taho ta dauketa ta tafi ba kunya ba tsoron Allah, suka bar ni tsaye baki sake ina kallonsu, ni abun ma mamaki ya bani wllh, baka ji ba duk jikina yyi sanyi qlau, nace to meye kuma daga magana dai mata ta figi hannun yarinya ta wuce, to kaga agwai?? To ka ji tsoronsa, ni dai nayi shiru ban ce mata komai ba, to ni dai bana bi ta mata bafillatana in ki kyautata ma jikata ba, daxu na kira ta Rasulu ta aiko min jikarta da tsakin masara ko garin acca in yi mata fate mai kyau da lafiya, shine nake yi tun daxh..." Abba yace "Ai kam kin kyauta Allah ya bada lada" Inna tace "Ameen, amma da don ta Aisha ce wllh baxan yi ba don bata da kirki Sam, ni dai ba ruwana inyi magana Bukar ya kullace ni, ita kuma Imaan kaga ikon Allah daga auren sai ga rabo ko Ahmadu, ni dai nayi murna nayi murna, na gode Allah, na gode Allah, na kuma yi addu'ar Allah ya raba lafiya, in sha Allahu sae ta cika parlon ubanta da jikoki, tass sai ta haife kanninta muna nan da ku... Da kyar kuma idan ba mace xata haifa ba don ita ce aka ce ko da bala'i sai ta je gidan ubanta, Kai Alhmdllh, uwarta fa sai da tayi shekara kusan sha biyar ta haifeta ita kuwa dubi daga shiga sai ga rabo" Abba dai sai murmushi yake, can yace "Toh Allah ya raba lafiya" Inna tace "Toh Ameen, Allah ya bata da sauki naga kamar irin mugun laulayin nan take irin dai wanda uwarta tayi, ni tsorona ma kada ta xama k'ashi da rai dama gata ba lafiyayya ba" Abba ya mike yace "Toh bari in je Inna sai ki ci gaba da abinda kike" Inna tace "Toh Allah maka albarka, amma gudun kada a tada rigima gwara kawai in ci girma in bar Aisha da halinta sai ta karata da 'yar ta ni kuma kullum sai in yi ta sintirin xuwa dubata koh Ahmadu?" Abba yace "A'a in sha Allahu xata dawo wajen naki, xan je ynxu..." Da sauri Inna ta katse sa tace "Lalala kar ka fara Ahmadu, a bar ta a can kawai ta xauna, ni kadai nasan irin halin Aisha, bar mata yar ta kawai su karata, gani take baxan iya kula da ita ba, bar su a can kawai ni babba ce baxan kulata muyi tashin hankali ba" Murmushi kawai Abba yyi ya fita, Inna tayi wucewarta kitchen murya can kasa tace "kawai kawai ina ganin irin aman da take kirbawa, ta ina xan fara ni ba kamfanin hypo da omo ba, ni ba boyi boyi ba, A'a wllh uwarta na da rai ai" Inna na gama faten ta juye a cooler ta fito kai ma Imaan, dai dai balcony suka hadu da Mujaheed da warmer a hannunsa da leda, tana ganinsa ta hade rai, ya kalleta yana murmushi... Yace "Kishiyar ki kika ma girki kenan" Wucewa ciki tayi tace "Ni dai ba ruwana, in sha Allahu a kanka ciwon da jikata take xai kare, kuma sai Allah ya saka mata, lefe kuma ni dai ko na mutu ban yafe ba ehe" bin bayanta yyi yana dariya yace "Sai dai ciwon ya kare a kanki" Mikewa Ammi tayi bayan Inna ta shigo dakin, Inna dai bata kalleta ba ta nufi Imaan dake kwance tace "Sannu takwara, ga faten tsaki me tsafta na maki, xai gyara maki baki, ta shi in xuba maki ki ci" Tana fadin haka ta fita xuwa kitchen dauko plate da spoon, mujaheed dai na xaune parlor, ta dauko plate din ta koma dakin ta bude ta dibar mata faten da ya ji kayan hadi da ganye mai yawa ta nufi Imaan tace "Tashi xaune" Imaan ta mike xaune tana kallon plate din da kyar tace "Meye wannan?" Inna tace "Fate ne mana...." Imaan ta amshi plate din tana rike numfashinta sai kuma ta ajiye ta dauke kai, inna ta bude baki tace "A'a ni fa ba wahalalliya bace, kuma ba asararriya bace, cefanen dari biyar kenan kike gani wllh, babu abinda xai maki sai ma gyara maki ciki da baki da xai yi" ita dai Ammi na tsaye, Imaan ta juya a hankali ta dau spoon din ta debi abincin ta kai baki, Inna ta xauna gefen gado tace "Dama banda ke wa xan ma haka? Ko Hadiza wllh bata samu haka ba, baki ji maganata ba an dai cuce ki kawai" juyawa Ammi tayi ta fita dakin, Imaan ta dinga cin abincin a hankali sbda tsamin yyi mata dadi a baki, sai da ta ci kusan rabin plate din sannan ta ajiye, Inna tace "Ya aka yi?" Ta girgixa kai tace "Na koshi" Inna tace "Toh sai ki ci sauran anjima" tana fadin haka ta mike tace "Gashi har kin d'an marmaro, amma a bar ki haka ba kula kila tun safe babu abinda Aisha ta baki kika ci, ni dai na tafi idan na gama sllh ko cikin dare ne xan shigo in duba ki" daga haka ta fita, Mujaheed ya bi ta da kallo bayan ta shigo parlor yace "Toh ni nawa abincin fa" Inna ta nufi kofa tace "Wanda uwarka Amina ta dafa kenan" yyi murmushi yace "Ehh shi" bata tanka sa ba ta fita, ya mike ya dau warmer da ledan drugs da ya siya ya wuce dakin, imaan da ta kife kanta da pillow ta dago tana kallonsa, ganin yanda ta 6ata fuska ya karasa cikin dakin yace "What happened?" Kamar xata yi kuka tace "Amai" ajiye abin hannunsa yayi ya xauna kusa da ita yace "Sorry dear, baxa ki yi ba" bubbuga bayanta ya dinga yi a hankali, tayi lamo jikinsa ta rufe ido, Bayan wani lkci ya dago kanta yace "Are you okay now?" Ta gyada masa kai, yace "Toh in xuba maki waken?" da sauri ta girgixa masa kai tace "Na koshi" yace "Toh ga magani ki sha" kamar xata yi kuka tace "Aa idan na sha yanxu xan yi amai" yace "Toh anjima Ammi xata baki ki sha, xan je in yi sllh yanxu" kwantar da ita yayi ya manna mata kiss a forehead yace "Allah maki albarka sweet" lumshe idonta tayi, ya ja mata blanket ya mike yace "I will come in the morning in sha Allah" gyada masa kai tayi ya juya ya fita dakin. Haka Imaan ta ci gaba da xama part dinsu tana laulayi gun Amminta dake bata kulawa yanda ya kamata, har wanka Ammi na taimaka mata idan jikin ya matsa mata sosai, throughout kuma Ammi na dakin to make sure she is fine, komai tace tana so Ammi na kokarin ganin ta yi mata, Aunty ma a rana ta kan shigo kusan sau hudu dubata, ita ma once in a while tana girki irin na gargajiya ta kawo mata, dama ana idar da sllhn asuba Inna ke rafka masu uban sallama a bakin kofa da cup din kunun ta a hannu, baxa kuma ta bar part din ba sai in Imaan ta kirba amai kamar yanda take cewa, to ko second daya bata karawa xata yi gaba tana yamutse fuska, Duk irin yanda Mujaheed ke son ganin wife dinsa a ko da yaushe kasa shiga yake sbda Ammi, nauyi da kunyarta yake ba kadan ba, kwata kwata bai iya shiga, haka nan xai wuce gun aiki da safe da tunanin wife din tasa, a gun aikin ma gaba daya rabin hankalinsa na gun Imaan, gashi yyi ta kiran wayarta bata dagawa sbda ko da yaushe silent wayar yake bata son ringing din, sai dai kuma babu abinda ya rage su da, don every week sai ya siya kayan shayi, duk da Ammi ta gaya ma Maimoon dake kawowa tace masa ba fa wani sha Imaan ke yi ba, hakan bai sa ya fasa siya ba, Magungunan ta ma duk ya san lkcn da xai kare ya siya ya bada a kai mata, once in a while idan Abba xai shiga da daddare shine xai bi sa su shiga tare, duk Friday Yusuf kan shigo dubata shi ma, ya kan dade dakin yana mata hira duk sai dai tayi murmushi tana kwance, a haka har cikinta yayi wata uku, laulayin ya d'an mata sauko tayi wani kyau na musamman ta kara haske, gaba daya Mujaheed ya kagu Abba yace ya wuce da matarsa gida amma shiru Abba dai bai ce komai ba, yau Saturday da yamma kamar ko da yaushe Inna na bakin tap dinta tana gurje gurjenta taji footstep, daga kai tayi, tayi mitsi mitsi da ido tana kallon mai tahowa, lkci daya ta dauke kai ta ci gaba da abinda take....



*Imaan isn't for free* it's 300 via


Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login