Showing 240001 words to 243000 words out of 303099 words

Chapter 81 - Imaan Book 1 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

1683

xuwa Ta Rasulu" Ta Rasulu ta cire Hijab din jikinta ta linke da kyau ta ajiye tace "Ke kuma ina xa ki da gana mas gau?" Inna ta tabe baki tace "Kayana nake hadawa ta Rasulu, sam bani da 'ya yan nuna ma duniya, shine naga gwara kawai in tafi gidan Bala in xauna, duk me xa a min a can xan fi shanyewa tunda nasan ba jinina yyi min ba" Ta Rasulu ta xauna tace "Me kuma suka maki 'ya yan??" Inna tace "Fisabilillahi ta Rasulu ina laifina don nace duk inda xa a nemo min Mujaheed a nemo min shi in ji dalilin da xai dauke min jika ya gudu kamar d'an fashi, ta Rasulu babu lefe babu sadaki babu komai kawai ya samu tsaleliyar yarinya a bagas ya tafi da ita ko uban meye ma'anar haka oho, wato ga sadaka an basa, to wllh ubansa Ahmadu ma yyi kadan balle shi sa karan kada miya, Jikata tafi karfin ayi sadaka da ita, kawai yaro tantiri dai ya shigo min gida ina wankin bandaki ya arce min da jika tsakar dare kawai sbda yana shan wiwi, to ta Rasulu shan wiwin nasa kuma sai ya kare a kai na? Don wannan ni ya ci ma mutunci ba kowa ba wllh, snn ace ayi shiru a xuba masa ido yaje ya lalata min jika? Kinga Hadiza, Ahmadu da Bukar duk gantalallu ne Allah na tuba, sam bbu wanda ya dau wani kwakkwaran akshan a kan batun nan, yanda kika san abun kirki Mujaheed yyi ko kuma shi halitto min jika, idan kika bibiya ma duk sun san inda ya tafi da ita marasu imani, daxu fa har gidansa naje a unguwar dosa basamuden da ya ajiye bakin get yace min ai gidan fanko ne bbu kowa ciki, ni dai ba yarda ba na shiga na gama xagaye na naji shiru bbu alamar kowa shine fa na fito na dawo gida na sa aka siyo min jaka nake xuba kayana, haka kawai yara sun gama rainani sun maida ni shashasha, tsakanin Imaan da Mujaheed fa gantalallen kaza, ni dai ban ta6a ganin ya siyo mata ko da tsinke ne ya bata ba kamar dai yanda wnn yaro d'an albarka Bulasawa ke yi, to wannan mutumi xan dau jika in ba ma, wllh baxata sa6u ba, maxa ya dawo min da Imaan ba yanxu xata tare ba...." Ta Rasulu na girgixa kai tace "Toh shi Mujaheed ko dai hau ne ya fada masa xai aikata wannan barna haka? Ina ya tafi da yar mutane bai bada hakokkin aurenta ba, haka kawai ya cuce ta yyi mata ciki a banxa" Inna ta rushe da kuka tace "Imaan ina ta isa daukan ciki ke kuma ta Rasulu, da kuwa ya cuceta, duka duka nawa take? Ai kamata yyi a xaunar da shi a karanta masa illan hakan, ina laifin ta d'an kara gwabi, to ga dai Safara'u har yau shiru sai dai ta ci tayi kashi, ban gane kan abun ba" Ta Rasulu tace "Yanxu dai kiyi hakuri ki maida kayan nan, tafiya ba taki bace...." Inna tace "A'a gidan Bala xanje gwara inje suyi ta taka ni baxai min ciwo ba don bbu abinda na hada da su na dai san uwarsu kishiyata ce ta aure min miji ban ji ba ban gani ba" Ta Rasulu tace "Asabe nace maki bbu xancen tafiya, ga abun al-ajabi na xo da shi..." Inna tayi shiru tana kallonta, Ta Rasulu tace "Toh dai asiri mummuna aka lafta ma Bulasawa yace ya fasa auren Imaan...." Inna tayi tagumi tana kallon ta Rasulu a hankali tace "Sai aka ce maki wani la'anannen ne yyi asirin Ta Rasulu?" Ta Rasulu ta tabe baki tace "Toh me shi a gidan nan yake tare da ku wllh, ba a dai ambato min suna ba, amma a nan me shi ke kwana yake tashi, amma ke wa kika xarga Asabe?" Inna tace "Allahu Akbar, Rukayyar Ahmadu ce" Ta Rasulu tace "Nima ita na raya" Inna ta bude baki tayi mitsi mitsi da ido tayi shiru tana kallon Ta Rasulu, can tace "Ikon Allah, wato kaikayi ne ya koma kan mashekiya ba shakka, kin lura duk ta fi kowa daga hankali a auren da aka daura da Mujaheed???" Ta Rasulu tace "Wllh kuwa, biri yyi kama da mutum, ni naga ma duk ta rame ta xabge tayi baki, yanxun nan mun hadu da ita xan shigo ita xata fita, wllh duk a birkice take, sai naga ma kamar hadin bauta tayi" Inna ta gyada kai tana wani murmushi tace "Toh Alhmdllh da wnn magana ya fito fili, amma kinsan wani abu? Wllh yanxu a idon Ahmadu, Bukar da Hadiza bbu me tada fitina a gidan nan sai ni, nice dai fitinanniya gantalalliya" Ta Rasulu tace "Ke ma xai wllh ai wannan magana barinsa xa mu yi a ciki mu yi ta kallon ikon Allah, iyaka a tashi tsaye sosai da nema ma yarinyar nan Imaan tsari...." Inna tace "Ke da kika san komai, ai bbu wanda xai fara gwaleni a kan xancen nan sai Bukar, shi Ahmadu dama baxai ce komai ba amma ni nasan kallon jarababbiya yake min baxai dai yi magana ba, ita kuma wannan mata Hadiza sai dai ta xuba min idanu, a takaice dai Bukar ce min xai yi in daina haka shi ba ruwansa, to ya xan masu Ta Rasulu? To wllh tunda Rukayya ta ma jikata haka sbda bakin ciki da hassada tata ta kare duniyar nan gaba daya, kuma kwanaki kadan ya rage mata gidan d'a na wllh, ke dai kawai ki xuba min ido ni kadai na isheta sai ta gwammace kida da karatu, aure jikokina kuma mutu ka raba, ni nasan da tasan auren xai dawo kan Mujaheed da bata san yanda tayi ta hana ba, kuma mutuwa xata yi a banxa idan tace xata raba auren nan...." Ta Rasulu tace "Atoh, kuma fa har yanxun ba wai saduda tayi ba, ance min tana nan tana kokarin raba auren nan, da kyar fitan da tayi yanxu ba gun bokanta xata ba, wllh sai mun tashi tsaye an yi kokarin nisantar da Imaan sosai daga sharrinta, in sha Allahu in dai da ran mu sai ta fito da bakinta tana tona kanta, kada ki kuskura ko da wasa ki gaya ma ko Hadiza tunda lalacewa ta sami yaran naki, mu dai da muka san komai sai mu yi ta kan mu" Inna tace "Dama ba gantalallen da xan gaya ma, iyakata da su su ban kudi in rufa ma jikata asiri, sannan in sha Allahu a gaban Bukar asirin Rukayya xai tonu shi da baya ta6a ganin laifinta..." Ta Rasulu tace "Toh ynxu ya isilin bawan Allahn nan Bulasawa?" Inna ta marairaice kamar xata yi tace "Wai daxu aka sallamesu asibiti inji Ahmadu, ni dai xan shirya in siya lemo ko kwaya biyar inje har gida in duba sa wllh, dama can Imaan ba matarsa bace bani da rabon cin kaji da xabi dai" tana magana tana matsar kwalla, Ta Rasulu tace "Kya ci da kudin ki" cikin rawar murya Inna tace "A'a ki bari Ta Rasulu, wani hanin ga Allah baiwa ne, kuma ni da Bulasawa mutu ka raba har gidansa xan dinga xuwa kai masa xiyara...." Daddy ne tsaye jikin motarsa kofar gidansu Ammi, ya fi minti goma yana jiran fitowarta, jin an bude gate ya daga kai har ta fito, ta gaishesa, yana kallonta yace "Ban san ki da haka ba Aysha, wannan ba halin ki bane, why are u behaving this way pls?" Bata tanka sa ba, yace "Ko ba don ni ba don barrister ya kamata ki hakura haka nan, kar ki manta jininsa fa ya aura ma Imaan, sannan don't forget yayana ne shi din, jinin nasa kuma d'a na ne, beside all this Aysha Mujaheed bai yi deserving haka daga gare ki ba, wai kin mance wanene Mujaheed ne?" Ammi da hawaye ya kawo idonta ta girgiza kai tace "I am thinking of my daughters future, ban san rayuwar da xata yi tare da kishiya da uwar miji warce bata sonta duk da kai ba yarda da rashin son da take mata kake ba, kila sai ranan da xaka gani a xahiri, nasan abinda imaan xata iya jurewa da wanda baxata jure ba, this is too much for her, ga condition dinta...." Daddy ya sauke ajiyar xuciya yace "Baki yarda da kaddara ba kenan, Haba Aysha sai kace ba musulma ba, where is ur faith? All you need to do is wish ur daughter a peaceful and better married life, plss ki shiga kiyi ma gwaggwo sallama we are going home now" Girgixa masa kai tayi tace "No ka tafi gobe in sha Allah xan dawo" yace "Sure?" Tace "In sha Allah" yace "Toh Allah ya kai mu, we will talk later on phone" daga haka yyi mata sallama ya shiga mota ita kuma ta wuce ciki. Mummyn Sadeeq ce xaune makeken parlonta tare da aminiyarta Hajiya Batula, Hajiya Batula tace "To ke wa kike tunanin xai aikata hakan Hajiya" mahaifiyar Sadeeq Hajiya Khadijah, tayi murmushin karfin hali tana gyada kai tace "Ni nasan wacece ita tunda aka ce daga family din yarinyar take, sarai nasan wacece, kuma Billahil azeem xata san ita ce silan heartbreak din d'a na" mikewa tayi ta nufi window fuskarta a murtuke, da mamaki Hajiya Batula tace "Ba shakka, amma koma wacece ita din gaskiya ta xama abar tausayi yanxu, ta rasa wanda xata ma asiri sai Abba? Don me bata bar asirin iya 'yar su ba kadai, Wannan shine biggest mistake of her life, don da ta sani da bata fara ba" Mummy dai murmushi kawai take, aka bude kofar dakin duk suka juya, Sadeeq ne ya shigo dakin, Uwarsa ta dinga kallonsa don ba karamin rama yyi ba, yyi kasa da kai ya gaida aminiyar mum din tasa cikin sanyin murya sannan ya xauna saman kujera yace "Mummy, Ina son xan tafi Uk...." Katse sa tayi tace "Kaje kayi me a UK Sadeeq?" A hankali yace "I need rest Mum..." Shiru tayi tana kallonsa, lkci daya hawaye ya kawo idonta ta dauke kai tana kallon waje ta window.... Mikewa xaune Mujaheed yyi jin ringing din wayarsa, ya dauka yana kallon Screen din, Call din Umma ya gani, ya ji gabansa ya fadi sosai, yyi ta kallon screen din har ya katse, ta sake kira, kasa kin dagawa yyi, ya daga a hankali ya kai kunne yyi shiru, ko sallama babu tace "Mujaheed??" Yyi kasa da murya yace "Na'am, Ina yini Umma" Tace "Kana Ina ne?" Ya d'an yi shiru sannan yace "Ina gida" tace "Wani gidan?" Nan ma yyi shiru, cikin tsawan da ya ji har tsakiyar kansa tace "Baxa ka bani amsa ba ina tambayarka?" A hankali yace "Gidana Umma" strictly tace "Wani gidan naka a ciki?" Yace "Zaria" Tace "Toh" tana fadin haka ta katse wayar kitt, ya dinga kallon phone din xuciyarsa na bugawa, Imaan dai na xaune kan darduma har lkcn ta gama jujjuya shinkafar takeaway din gabanta ta bar sa, kazar ma tunda ya kamata tana ci ta ki ci kuma, sauka yyi saman gadon ya tafi ya bude kofar dakin ya fita, Safeenah na xaune parlor tana waya da Hajiyar su, murya can kasa tace "Haukatar da ita kuma Mummy, A'a gaskiya... idan aka yi haka ai bata kwashi takaicin da ya kamata ba, a dai yi wani abun daban Mummy" Safeenah tayi shiru tana sauraron uwar tata, sai kuma tace "Mummy na fa ce maki babu auren nan wllh, tunda muka xo bai ce min komai a kai ba, sun raba da suka ga bai so...." jin taku a stairs ta katse wayar da sauri, ta gyara xama ta wani hade rai tana kallon tv dake aiki, Mujaheed ya shigo parlon yana kallon ledan abincin da bata ta6a ba ya dauka yace "Ain't you eating?" yi tayi kamar bata ji sa ba, ya tafi kitchen ya wanko plate ya dawo parlon, ido hudu yayi da Imaan dake sakkowa stairs a hankali tana kallon Safeenah dake xaune idonta a kan tv har lkcn....



*Imaan isn't for free* it's 300 via


Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788



85......



Ganin direction din da Mujaheed ke kallo bbu ko kiftawa Safeenah ta juya da sauri tana kallon wajen ita ma, sake remote din hannunta tayi a hankali ta mike tana kallon Imaan da idanuwanta kamar xa su fito, da mugun mamaki da shock take kallon nata, lkci daya ta juya cikin tashin hankali tana kallon Mujaheed xuciyarta na bugawa kamar xai fito, walking slowly ya karasa cikin parlorn ya xauna saman kujera ya bude takeaway din dake cikin leda ya diba abincin a plate ya ajiye sannan ya daga kai ya kalli Safeenah dake kallonsa har lkcn with full shock, sai kawai ta fashe da wani matsanancin kuka jikinta na rawa ta nufesa ta rikosa tace "Tell me, what is she doing in our home Mujaheed? Why is she here? Wa take nema??" Juyawa Imaan da ta hade rai tayi xata koma sama, Mujaheed yace "Don't go back, dawo nan" k'in tsayawa tayi tana ci gaba da tafiyar ta da sauri, cikin daga murya yace "Imaan!!" ta tsaya fuska daure amma ta ki juyowa, har ranta taji xafin ganin Safeenah, ga wani faduwa da gabanta yake yi, Mujaheed ya mike tsaye yana kallonta yace "I said come back here Imaan..." Safeenah na jijjigasa cikin tashin hankali sosai tace "Mujaheed answer my question, ka gaya min me yarinyar nan take a gidana, ka gaya min nace, wa take nema??" Imaan ta juyo walking slowly ta dawo parlon tana kallon Safeenah fuska daure, Safeenah ma ta dinga kallonta xuciyarta na bugawa har lkcn tana rike da Mujaheed, Imaan ta murguda mata baki ta dauke kai tana jiran jin kiran me Mujaheed yyi mata, Safeenah ta nufeta da sauri tana huci bakinta na rawa tace "Me kike yi a gidana??" Imaan ta rungume hannunta tace "Abinda kike yi, and point of correction ba gidan ki bane ke kadai, nima nan gidana ne...." Wani kara Safeenah tayi kamar mahaukaciya jikinta na rawa tace "Karya kike wllh, karya kike, nan gidan mijina ne, gidana ne nan, baki da space a gidan nan yarinya, this is my husband's house" Imaan tayi wani murmushi tace "Koh? To sai ki tambayi mijin ki dalilin da ya sa ya kawo ni nan" Sai kuma ta saci kallon Mujaheed da ya ki kallonsu gaba daya, murya can kasa tace "And here is also my husband's house...." Bata rufe baki ba Safeenah ta wani cakumota da karfi jikinta na rawa, Mujaheed ya taho da sauri ya janye Imaan yana ma Safeenah wani mugun kallo, ya fixgota shi ma cikin tsawa yace "What is this u are doing? Baki da hankali ne xaki fixgota haka? Ciwo xa ki ji mata?" Safeenah na kallonsa with shock ta fashe da matsanancin kuka ta xube kasa tace "Na shiga uku na lalace, Mujaheed kayi ma Allah ka gaya min me take a gidan nan Plss, tell me what brought her to my home" Wani dogon tsaki Imaan ta ja tana hararanta xata bar wajen Safeenah ta mike yi kanta gadan gadan, cikin xafin nama Mujaheed ya fixgota for the second time yana mata wani kallon da ya sa hanjinta ya kada, strictly yace "This should be ur last attempt in this house, I will neva take it likely with you idan kika sake maimaita hakan, Me kike son yi mata da??" Safeenah na kuka sosai tace "Wllh baxan xauna da yarinyar nan ba mutuwa xan yi, ka taimakeni ka gaya min me take yi a gidanmu, wayyo Allah na na shiga ukuuu..." Mujaheed ya saketa, calmly yace "Aure ya kawota gidan nan, ita din xabin mahaifina ne gareni, kamar yanda ke kike xabin mahaifiyata, at that time I've neva for once say no to my mother na karbi auren ki hannu bibbiyu, the only difference btwn my marriage with you and that of Imaan is that, ke naki I was aware and present during the nikka.... Don haka kamar ynda ban ma Mahaifiyata musu a kan auren ki ba, to baxan ma mahaifina musu a kan auren Imaan ba, and I am assuring you that in sha Allah xan xamo mai adalci tsakanin ku, i will try my very best, but Imaan matata ce yanxu kamar yanda kike matata...." Imaan dake tsaye tana jiran ganin abinda Safeenah xata mata, ta kara jan wani dogon tsaki ta wuce sama kamar xata tashi sama, Mujaheed ya bi ta da ido, Safeenah ta sulale kasa ta rushe da wani kuka da karfin gaske, cikin tashin hankali tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, na cuce kai na, don Allah Mujaheed kar ka min haka don kaga Ina sonka, babu mai kishiya cikin 'yan uwana wllh tllh, plsss kar kace min kishiyata ce ita, I can't stand it, xuciyata bugawa xata yi wllh...." Dukawa yyi yana kallonta smiling calmly yace "Kin yi breaking record..." Tun da Imaan ta koma daki ta kasa xaune ta kasa tsaye, ta kalli kofa ya fi a kirga, tsayawa tayi jikin window ta fara kukan da ita ma bata san dalilinsa ba, wani tukuki taji xuciyarta na mata, tana ta tsaye har bayan kusan minti goma, aka bude kofar dakin, juya baya tayi da sauri ta goge idonta tana kallon waje fuska daure, ya rufe kofar yana kallonta yace "She is my wife imaan, aside that kuma ta girme ki sosai, kada ki sake mata tsaki, that's very disrespectful of you...." juyowa tayi tana kallonsa da wani expression, ya karasa kusa da ita kafin yace komai, cike da masifa tace "Wllh sai na mata din, da ta girmeni sai kuma ta haifeni? Ni ina ruwana da ita a gidan nan xaka ce min she is ur wife ko da nace maka ban sani bane? What's my business with that??" Sai kuma ta fashe da kuka ta nufi bathroom da sauri ya rikota yace "No I am only reminding you Imaan" fadawa jikinsa


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login