Showing 174001 words to 177000 words out of 303099 words
yaron nan, gaskiya wannan karan bana son magana da yawa sabili da kar raina ya baci, ga abinda nace in dai kuna tsoron Ubangijin ku, meye kuma wata daya da rabi Ahmadu? Shi auren ake gudu kuma yanxu ana rirrike boko hannu biyu, Me yasa ku ke haka?? Ni dai idan na isa da ku gwara a hada bikin ma da na wannan yaron Isuhu tunda an ma kusa kai sadakinsa" Mujaheed dake kallonta har sannan yace "Don dai an jira wata daya da kwanaki ban ga wani damuwa ba, hanxarin me yake??" Inna tace "Amma gaskiya idan xan yi maganar arxiki Mujaheed ya daina shigo min parlona, a daina xuwa min da shi" wani kallo Mujaheed ya dinga mata, tana kallon Abba da karfi tace "d'an bakin ciki ne fa Ahmadu, ya xai yi aurensa yaje can yana morewa da figaggiyar matar sa amma ya dinga yi ma yar Uwarsa bakin ciki, haka yake so tayi ta xama a gida kamar ba mashinshini?" Mikewa Abba yayi yace "Toh shkkn, xa mu ba yaron ranan da xai turo magabatan nasa in sha Allah" a fusace Inna tace "Yaushe?" Abba yace "Nan da ko kwana uku in Allah ya yarda sai a hada bikin da Yusuf yanda kika ce" Inna tayi murmushi tace "Toh Allah ya kai mu lafiya ya maku albarka" kallon Abba da ya nufi kofa kawai Mujaheed yake har ya fita yana amsa maganar Inna da Ameen, can ya kalli inna da ta mike ta fara kakkabe kujeru, yace "Kin kagu ta bar gidan kenan??" A fusace tace "Ba ruwan ka, wai ma dai meye hadina da kai Mujaheed??? Ni dai nasan na haifi Ahmadu amma wllh da babu abinda ya hada mu gwara kayi ta kanka, kiri kiri ka dinga nuna ma jikata bakin ciki??" Yana murmushi ya mike yace "In sha Allahu wannan auren da kike ta 6arin jiki a kansa baxa ayi ba, kuma har tsayuwar dare sai na yi akan hakan" salati Inna ta saki tana kallonsa, sai kuma ta fashe da kuka tace "Baxa ayi ba?? Ehh lallai ka zama dan iska Muhammad, ita yar Bukar kake ma bakin ciki?? Me ta maka xaka mata wannan fatan" ko sauraranta bai tsaya yyi ba ya fice daga parlon, a hankali yake tafiya don shi kansa bai ma san lkcn da ya fada mata hakan ba. Abba na komawa dama ya kira Daddy ya gaya masa yanda suka yi da Inna, Daddy dai bai iya yace komai ba, Abba yace "So yanxu na yanke ranan Sunday as ranan da xa ace ya turo parent din nasa, kai kuma sai ka dawo Saturday or Friday" Daddy ya sauke ajiyar xuciya yace "Toh shkkn Allah ya kai mu, Allah yasa hakan ne mafi alkhairi" Abba yace "Ameen" daga haka suka yi sallama ya katse wayar. Washegari Abba ya kira Sadeeq ya kuma basa izinin turo magabatan sa ranan lahadi, Sadeeq was so happy, farin cikin da bai taba yin irinsa ba duk tsawon rayuwarsa ya dinga yi ma Abba godiya kamar ya masa albishir da aljanna, Mujaheed dai na xaune parlon shi ma don tun safe Abba ya kirasa, amma banda danna wayarsa babu abinda yake, lkci daya ya dago yana kallon Sadeeq suna hada ido ya dauke kai, ya mike ya kai wayarsa kunne yyi excusing kansa ya nufi kofa hakan yasa Abba ma ya bi sa da kallo kamar yanda Sadeeq yyi.
*Imaan isn't for free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
62....
Ranan lahadi kamar yanda Abba ya tsara hakan ce ta faru, don Mahaifan Sadeeq a ranan suka xo gidan nema masa auren Imaan, Bulasawa ne sai kanninsa biyu, da abokansa biyu, da kuma wani kawunsa suka taho gidan, shi dai daddy baya cewa komai don har ransa bai son aurar da only child din tasa a lkcn, a da ya dau burin sai ta kusa gama University amma yanxu gaba daya Inna ta gama ruguje plan din, kuma babu yanda ya iya, dubu dari biyar iyayen Sadeeq suka bayar kudin gaisuwan da akwatuna har guda takwas da sauran abubuwan da ake badawa a al'adance amma triple triple suka kawo komai, sannan suka ajiye ranan da xa su dawo a saka rana, Umma tunda ta sami labarin shigowar su gidan ta kasa xaune waje daya ta dinga safa da marwa a daki, can dai ta kira Hajiya Balaraba duk ta sanar mata abinda ake ciki, Hajiya Balaraba tace "Toh meye abun daga hankali Hajiya Rukayya, ke fa an gama baki tabbacin babu auren nan, ba abu bane da xai taba yiwuwa, to meye abun damuwa kamar baki yarda da bawan Allahn nan ba...." Hankali tashe Umma tace "Nasani Hajiya Balaraba ba wai ban yarda bane, na ji fa har ynxu shiru shiru ba alamar komai, ko xuwa gidan ma wllh yaron ya daina, ita kuma yarinyar gaskiya bbu wani linkage tsakanin mu, bbu ta ynda xa a hadu har yau ban yi yanda aka ce min ba, ga lkcn na ta wucewa..." Hajiya Balaraba tace "Bata tahowa bangaren ku ne?" Umma tace "Sae ta yi wata ma bata shigo ba idan ba uwar bace ta aikota, shi ma iyakarta dakin Amina" Hajiya Balaraba tace "Ke dai baki da dubara wllh, ga dai wajen da take xuwa kullum wajen Hajiya Asabe, ke baxa ki hada wani dubaran ba daga can" Umma ta d'an yi shiru kafin tace "Toh shkkn xan duba, can din ma ni ba haduwa muke ba ko na je gaishe da tsohuwar, xa dai mu yi waya xa a shigo min daki...." katse wayar tayi da sauri jin an bude kofa, Aunty ta shigo da farin ciki sosai tace "Hajiya an kawo kudin gaisuwan Imaan dubu dari biyar, kayan na gani Ina so kuma akwatuna takwas daga gidan Alhaji Bulasawa...." Umma ta dauke kai ta mike ta fara kakkabe gadonta tace "Toh Allah dai yasa ba yaudara bane, mu dai namu ido, wani kudin auren kirki ne har dubu dari biyar ba ma sadaki ba kamar xa a siyar da ita" Juyawa Aunty tayi ta fita dakin, Su Bulasawa na barin gidan Abba ya sa su Ummi da Rahma da Maimoon su kwashi kayan su kai part din Inna, Inna ta saki baki tana kallonsu suna shigo da kayan tace "Meye haka kuma?? Meye wannan din" Maimoon na murmushi tace "Na Imaan" Inna ta mike da sauri tace "Wa ya kawo?" Maimoon tace "Daga gidan su Sadeeq" tuni Rahama da Ummi suka fice parlon xuwa dauko sauran, Inna ta saki wani kabbara sai kuma ta xaro ido tace "Yaushe suka xo?" Maimoon tace "Basu dade da tafiya ba" Xaunawa Inna tayi ta fashe da kuka tace "Allah sarki Bukar, ita kenan fa garesa, ita kenan Allah ya basa gashi yanxu xai raba sa da ita... Yanxu ya xai yi da ran sa" Shigowar Abba yasa tayi shiru tana share hawayen idonta, Abba ya xauna ya gaisheta, ta amsa cikin rawar murya tace "Yanxu shkkn raba Bukar xa ayi da Imaan ni patuu??" Abba dai bai bata amsa ba ya ajiye ledan hannunsa a kusa da ita yace "Kudin gaisuwar da suka bada kenan" Inna ta xaro ido tana kallon ledan kudin tace "Nawa?" Yace "Dubu dari biyar" Inna ta saki salati tace "Toh dama ku siya mata dankareren gwal ku ajiye kar a ta6a mata ko biyar tunda ba wani xai mata xaman auren ba Ahmadu" Abba dai bai ce mata komai ba ya mike yace "Xuwa anjima xa mu shigo da Abubakar" daga haka ya fita parlon, Inna na murmushi ta daga hannu sama da karfi tace "Alhmdllh, Alhmdllh, takwarata tayi goshi ni Asabe, Allah na gode maka Allah, Allah na gode maka, ka bar min rai da lafiyar kai ta dakinta da hannuna in sa mata albarka" sai kuma ta fashe da matsanancin kuka, Maimoon ta tabe baki ta ta fita xuwa debo wasu kayan. Bayan Magrib Inna na share parlonta don ba a dade da fitar Aunty da frnd dinta sai frnds din Ammi biyu ba sun shigo ganin kaya, Yusuf ne ya shigo parlon bai dai xauna ba yana kallon Inna daga tsayen da yake yace "Ina yini" ta mike ta ajiye tsintsiyar hannunta tace "Lafiya lau Isuhu, sannu da xuwa bari in bude maka kayan, wllh babban akwatin babu atamfar kasa da dubu hamsin, gaba daya Holland da England suka xuba mata, ba fa lefe ne kayan sun gani sun kyasa ne..." Xata fara sauke sauke yace "A'a ba sai kin bude ba, dama Allah ya sanya alkhairi na xo maki, Allah yasa ayi muna da rai da lafiya" Inna tace "Atohh, Ameen dai, dama ganin kaya ai sai mata, kuma ai rana daya xa ayi bikin da naka idan Allah ya yarda, kai ka angwance kanwar ka ita ma haka" shi dai bai ce mata komai ba ya nufi kofa yace "Sai anjima" tace "Mu jima da yawa, Allah maka albarka, Ina nan ina lissafin wa enda suka shigo yi ma jikata barka, har yan anguwar nan ina xuba ido in ga wa enda xa su shigo da wa enda baxa su shigo ba, mutane uku dai sun shigo daxu, amma kaga Rukayya da Aisha ko keyarsu ban gani ba kuma xan ji dalili gobe da safe, ita Imaan din ma ban ganta ba yau gaba daya" shi dai tuni ya fita. Inna na xaune tana cin abinci aka bude kofa, Mujaheed ne ya shigo parlon ta mike da sauri ta shige daki sai ga ta ta fito da katon bargo ta rufa ma akwatin har tana neman faduwa, shi dai kallonta kawai yake, ta tabbatar ko kalan akwatun ba a gani sannan ta koma ta xauna tana ci gaba da cin abincinta tace "Wa alaikumussalam" Yana tsaye yace "Ina yini" tace "Lafiya lau" Bai kuma ce mata komai ba ya juya fita parlon ta mike ta rufe kofar tace "Gaskiya xan kira Ahmadu ya ja ma mutumin nan kunne ya daina shigo min nan, yaje can ya ji da xabiyar matarsa, kwata kwata xuciyarsa ba shi da kyau, hassada bakin ciki duk sun taru sun masa yawa, hooo ni patuu Allah ya ba ma Ahmadu Ya ya, sai dai Allah ya raba mu da su lafiya" Imaan ta fito wanka kenan daure da towel taga wayarta na haske, ta tafi gaban mirror ta dauka tana kallon screen din, pick din kiran tayi ta kai kunne tana murmushi, shi yyi sallaman ta amsa a hankali, yace "Why ain't u picking sweetheart" ta wara ido tace "Ina parlor ban jima da shigowa ba" Yace "Ohk, ya gida?" Tace "Lafiya lau" yace "Kayan sun maki dear?" Ta d'an yi murmushi ta sunkuyar da kai kamar yana gabanta tace "Ai bn gani ba" da mamaki yace "Why?" Nan ma dai murmushi kawai tayi bata ce komai ba, murmushin shi ma yyi yace "Ina fa mancewa bafillatana xan aura, to ya xa ki yi da ni da kunyar ki Imaan" ta turo baki tace "Nima bn sani ba" Yar dariya yyi yace "Xa ki sani ne ma" ita dai bata ce komai ba, yace "I can't wait imaan, in gan ni tare da ke as married couple" tace "Uhm ina son in shirya, I just took my bath now" yace "You need a helping hand?" Ta xaro ido tace "Noo, sai anjima" Bata jira cewarsa ba ta katse wayar, d'an murmushi tayi ta fara goge jikinta. Umma ce xaune parlon gidan Mujaheed tare da Safeenah dake danna waya tana mata sannu da xuwa, bayan sun gaisa tace "A kawo maki ruwa Hajiya?" Umma tace "A'a Alhmdllh, ai daga gida nake, Mujaheed din na nan?" Tace "Yana gun aiki" Umma tace "Toh madallah, na xo don Allah xa mu yi wata magana da ke ne mai muhimmanci" Safeenah na kallonta tace "Toh ina ji Hajiya" Umma ta d'an yi shiru sai kuma tace "Wannan yarinyar da tayi sauka kwanaki Imaan na xuwa gidan ki kuwa?" Safeenah na yatsine fuska tace "Yauwa dama don Allah Ina son kawo maki wani kara Hajiya, kinga ni dai da Mujaheed xai aureni ba wai ance min cousins dinsa xa su dinga xuwa min without good reasons ba kuma ba tare da sanina ba, don haka, don Allah a dakatar da wannan yarinyar daga xuwa gidana bana so, kada Watarana abu ya 6aci, sannan wannan kakar tasa ita ma kusan kullum sai ta xo, don tare ma suke xuwa da cousin din tasa" Umma ta xaro ido tace "Haba dai, kice suna xuwa nan sosai" Safeenah ta tabe baki tace "Ai kam, ni dai na gaji, sannan idan Yarinyar ta xo tayi ta nuna min isa da gadara a gidana ko gaisheni fa bata yi" Umma tayi dariya tace "Toh ai a kanta ma na xo gidan nan yanxu haka, Kinga kenan faduwa ya xo dai dai da xama" Safeenah ta bude ido sosai tana kallonta tace "Toh Ina ji" Umma ta gyara xama tace "Kin san d'an gidan Bulasawa??" Safeenah ta d'an yi shiru sai kuma tace "Gaskiya a'a, ina dai following din yaransa mata a Twitter" Umma tace "Toh d'an sa na fari ne ke neman Imaan din da aure, jiya aka kawo gaisuwa dubu dari biyar, da akwatuna takwas da sauran tarakace me yawa, wllh da kinsan abinda uwar yarinyar nan ta min a rayuwar duniya da kin tausaya min ke ma ki taya ni bakin ciki da auren nan" Safeenah dake gwalo ido tace "D'an Bulasawa fa?? Me ya gani tare da ita yake sonta?" Umma tace "Toh wllh sauran ciwo ce ma, yau ciwo gobe lafiya tunda sickler ce" Safeenah na gyara xama tace "Tabb, Shi sa take ma mutane wani gani gani kenan???" Umma tace "Wllh don haka yanxu kawai so nake kada auren ya faru, ni dai ba shige shige nake ba balle ace, ba ruwana da boka ko malam, kawai dai da yan dubaru xa a raba su, kema kuma dole sai kin bada contribution" Safeenah tace "Toh ta yaya?" Umma tace "Ba kince tana xuwa gidan nan ba, dama nima naji labarin suna xuwa da kakar, shi yasa nace bari in xo in same ki" Safeenah tace "Ba dai ko da yaushe su ke xuwa ba sai jefi jefi" Umma tace "When last suka xo??" Safeenah tace "xai yi kusan wata daya, Umma tayi tagumi tana naxari, can ta kalli Safeenah da ita ma tayi shiru xuciyarta fal takaicin wanda Imaan xata aura, wai yaron Bulasawa, Umma tace "Kinsan me xai faru yanxu Safeenah" Safeenah ta kalleta tace "A'a" Umma tace "Ki jira sai Mujaheed din ya dawo sai ki ce masa kwana biyu baki ga Inna ba, yaushe xata xo?? Ko kuma kyalesa kawai bari in baki lambar Innar ki kirata sai bayan kun gaisa sai ki tambayeta kwana biyu shiru shiru baki ganta ba yaushe xata xo??" Safeenah tayi murmushi tace "Koh?" Umma tace "Ahaf jikinta na rawa xata xo, ai ita tana son a dinga nuna ana ji da ita, kuma in xata xo da wuya ta xo ita kadai, Dole da Imaan din take fita kinga shikenan Allah ya kawo mana ita har gida amma kar ki yarda ki gaya ma Mujaheed kamar yanda nace da farko don akwai sa da kwakwalwa, nan da nan xai gano ki" Safeenah tace "I thought as much, ga wayar ki sa min lambarta" Umma ta amsa wayarta ta saka mata lambar Inna daga nata wayar sannan ta mika mata, Safeenah ta amsa ta kai kunne, Inna na dagawa ta rafka sallama, Safeenah ta amsa tace "Ina yini Inna?" Inna tace "Lafiya lau, waye don Allah, ni dai aiki nake ta yi na bude ma mutane akwatuna tun safe suna shigowa gani, kinsan duniya ba gaskiya yanxu sai a samu rikakken barawo da xai boye abu ya wuce da shi shi sa nake sa ido" Safeenah tace "Safeenah ce Inna" Inna tace "Waye Safeenah kuma?" Safeenah ta tabe baki tace "Matar Mujaheed" Inna tace "Ayyo, Safara'u ce, Toh sannu kin ji labarin an kawo kaya kenan?" Safeenah tace "A'a ban ji ba" Inna tace "Atoh wa xai gaya maki dama d'a bakin ciki uwa bakin ciki, wllh har yanxu ban ga keyar Rukayya ba, Mujaheed kuwa tunda ya shigo ya gaggasa min magana ban kara ganinsa ba sai jiya da aka kawo kaya, bakina a leko na shiga daki da gudu na dau katon bargona na rufe ma yarinya kaya da shi tun bai kai ga gama kirga guda nawa bane, akwatuna takwas ne da kyar ake xuge xif din, Toh me xance banda in gode Allah, har da gwal na dankunne guda biyu da xobuna biyu fa a ciki, ni dai ba ruwana duk me ma jikata bakin ciki Allah shi yasan yanda xai yi da shi, ko ke wllh baki samu haka ba shi sa Mujaheed ya fito kiri kiri ya nuna bakin cikinsa a fili, kwana nayi Ina al-ajabin abinda ya gaya min ranan wllh, isuhu kuwa har nan ya xo ya min Allah sanya alkhairi...." Safeenah da Umma sai sauraronta suke don a hands free Safeenah ta sa wayar, Umma ta wani kankance ido tana kallon wayar, Safeenah ta tabe baki tace "Toh Allah ya kyauta, yaushe xa ki billo Inna kwana biyu shiru" Inna tace "In billo a yashe ma yarinya kaya in shiga uku Safara'u, ai ba xancen billowa sai na kai Imaan dakinta, sa ido yayi yawa gwara in mike tsaye kyamm, toh ke baxa ki xo ganin kayan bane kike jira in billo?" Safeenah ta kalli Umma, Umma ta gyada mata kai da sauri alamar tace xata xo, Safeenah ta tabe baki tace "Toh xan shigo in sha Allah" Inna tace "Atoh, sai kin xo, sai kiyi sauri don xuwa anjima xa a kai ma kakarta ta wajen uwa ta ga kayan ita ma, sannan a maido min inyi gadin kayana" Safeenah tace "Toh sai anjima sai na xo" Bata jira cewar Inna ba ta katse wayar tana kallon Umma da tayi tagumi, Safeenah ta ja tsaki tace "Ai nima sai inda karfina ya kare wajen