Showing 207001 words to 210000 words out of 303099 words

Chapter 70 - Imaan Book 1 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

1680

a parlor ta tadda imaan mai lalli na mata lallin, Inna ta matsar da kujerunta gaba daya ta lullube su, ta kwashe carpet dinta kada a goga mata lalli a cuceta kamar yanda tace, Xaunawa Maryam tayi tana kallon Imaan, lkci daya taji tausayinta ba kadan ba ya kamata, kawai mikewa tayi ta fice daga parlon daga karshe.... Sai kusan Magrib Imaan ta wanke lallenta da yyi kyau ba kadan ba ta tafi part din su dauko Hijab don Inna ta wanke mata gaba daya wanda ta taho da, Shirye shiryen Mothers day da xa ayi gobe kawai ake yi a gidan, bata ga kowa part din su ba ta wuce daki ta dauko hijab ta fito, Muryar Maryam taji tace "Imaan" da sauri ta kalli direction da taji muryata ta ganta xaune ita kadai a dinning, karasawa tayi tana kallonta tace "Me yasa kika ce baxa ki yi lallen ba?" A takaice Maryam tace "Nothing" Imaan tace "Amma fa jiya kince xa ki yi" Maryam tace "Fasawa nayi, xauna mu yi magana Imaan" Imaan ta ja kujera ta xauna tana kallonta, Maryam ta d'an yi shiru sai kuma tayi kasa da murya tace "You know what imaan?" Imaan ta girgixa mata kai gabanta na faduwa, Maryam tace "Plss ina son ku xauna da Inna kiyi mata magana yanda xata fahimce ki, ki ce mata don Allah tayi ma su Abba magana a daga bikin nan xuwa wani lkci" Kallonta kawai imaan ke yi, Maryam ta girgixa kai tace "This is not the Sadeeq you know before imaan, ki rufa ma kanki asiri ki yi ma Inna bayani ita kadai xata iya ma su Abba magana su daga bikin nan, wllh idan kika auri wannan Sadeeq din you are going to live a miserable life in his home, gaba daya gadara yake yana ganin ya gama samun ki, dama boye maki real him yyi tun farko, kinsan yanda muka yi da shi a waya daxu da na kira in ji dalilin Change of attitude dinsa?" Imaan da har hawaye ya kawo idonta ta girgixa mata kai a hankali, Maryam tace "Ce min yyi ince maki idan kin isa ki fada ma su Abba kin fasa auren a dawo masa da sadakinsa" Sosai gaban Imaan ya fadi ta dinga kallon Maryam xuciyarta na bugawa, Maryam ta girgixa kai cikin sanyin murya tace "I am not in support of you marrying Sadeeq any longer Imaan, ba shi da mutunci ko kadan, hallaka ki kawai xai yi Imaan, kiyi hakuri ko min son da kike masa ki samu Inna ki gaya mata abinda ke faruwa a san abun yi tun da sauran lkci..." Imaan ta fara kuka a hankali, cikin sanyin murya tace "But I love him Maryam, shi ma yana sona, I just don't know what came over him..." Sai kuma ta fashe da kuka sosai ta hade kanta da dinning cikin rawar murya tace "May be stress yasa yake jin haushi haka, ni dai nayi masa uxuri, this is not the Sadeeq I use know, nasan idan munyi aure xa mu koma yanda muke da in sha Allah...." Da mugun mamaki Maryam ke kallonta tace "Are you on ur right senses Imaan, Ina gaya maki ga abinda mutumi yace kice idan kunyi aure xa ku dawo yanda ku ke da???" Imaan ta dago tana kallonta hawaye na sakkowa idonta tace "Ina sonsa a haka Maryam, kawai ki taya ni da addua Allah ya maida sa yanda yake da, beside bayan duk bak'in da suka taho from different places sai ace an fasa aure, idan shi bai fito ya fada masu ya fasa ba I see no reason why I should do so Maryam" Mikewa Maryam tayi tana mata wani irin kallo tace "Baki da hankali wllh" Imaan ta tashi da sauri tace "Plss this should be between us, ban ga dalili me karfi da xai sa ince na fasa auren nan ba, don Allah forget you even called him, ai ni xan xauna da shi ba ke ba, I know he loves me, nima kuma Ina sonsa, so plss mu bar maganan nan a nan" daga haka Imaan ta bar dinning din Maryam ta bi ta da kallo baki bude. Daren ranan Imaan bata yi bacci ba, gaba daya she is just disturbed nd restless, ta mike xaune daga karshe ta kalli Inna dake sllh kamar dai yanda ta saba duk dare, kallon agogo tayi taga biyu da minti biyar, wayarta ta dauka tana kallo, sai kuma ta shiga text message, cikin minti goma ta gama rubuta ma Sadeeq text, da farko tambayarsa tayi ko tayi masa wani laifi ne ya gaya mata, daga karshe kuma ta basa hakuri cikin tausasan lafazi ta tura masa, tagumi tayi tana kallon wayar duk da bata expecting reply don tasan bacci yake at that time, text taga ya shigo wayar nata gabanta ya fadi sosai, ta dinga kallon wayar kafin ta dauka ta bude text din tana kallon content dinsa, "if you think you notice any change of behavior da bai maki ba a tattare da ni, ki yanke hukunci da kika ga is the best, wanda xai yi suiting din ki" ta karanta text din ya fi a kirga amma ta kasa apprehending, can ta yi dialing numbersa har ya gama ring bai dauka ba, ta kuma kira bai dauka ba, ta tura masa text na cewar ya dau call dinta don Allah, ba a dau lkci ba reply ya shigo yace "Good night" Ta dinga kallon reply din sannan ta ajiye wayar ta mike ta shige bathroom ta rufe kofa, kuka ta fara yi a hankali tana jin xuciyarta na mata xafi, tayi kukan da ta dade bata yi ba amma maimakon taji d'an sanyi a ranta sai k'una da radadi, bubbuga kofa Inna tayi tace "Me kike yi a bandaki tun daxu Imaan, lafiyan ki??" Imaan ta fara wanke fuskarta da sauri, Inna bata fasa bubbuga kofar ba hakan yasa imaan ta bude kofar kanta a kasa, Inna ta gwalo ido tace "Kukan uban me kike? Ni fa bana son a gigitani gaskiya, ni ba karamin aiki na bane ince ki bi dare ki koma gidan ku, lafiya kike kuka a bandaki" Imaan bata tanka ta ba ta fara alwala, Inna tace "Naga jaraba, don xa a maki aure kuma sai ki shige bandaki kiyi ta kuka salon cuta ta kama ki" inna na tsaye tana kallonta har ta gama akwala ta fito ta sa hijab dinta ta hau saman darduma, Inna ta tabe baki tace "Ni dai ba ruwana" daga haka ta tafi ta xauna ta ci gaba da addu'o'in da take. Washegari tun sassafe Umma ta bar gida ana girke girke, ko danginta daya babu a cikin mutanen da suka cika gida, Ummi da Rahma ma duk ta sa sun shirya sun bar gidan, Aunty mamaki ta dinga yi na irin xuciyar umma, tunda take bata taba ganin mata mai nuna bakin ciki kiri kiri a fili irin Umma ba don cikin anko hudu da suka yi da Ammi ko daya ta ki yi, su Ummi ma ta ki barin su dinka nasu da aka masu. Mama Hadiza ce xaune parlon Inna tare da Aunty misalin tara na safiyar ranan Thursday din, Inna na kallonsu tace "Toh dama so nake ku rufa min asiri ku tattara 'yarku ku maidata can bangaren ku, tun daren jiya take kuka ga idanuwa can sun kumbure, toh ina dalili wani abun ya sameta a bangarena, dama aure hauka ne, wannan mata mai gyaran jiki ba irin lallashin da bata mata ba amma kamar ana tunxurata, to tunda uwarta ta sallama maku ita shi sa na kira ku, ku tafi da ita can nayi kokari haka kuma Allah ya gani" Aunty ta mike ta tafi dakin inna tana kallon Imaan dake kwance, murmushi tayi ta xauna kusa da ita ta dagota tace "Haba daughter, kuka kuma haka?? Ko kina da damuwa ne?" Imaan bata ce komai ba ta sunkuyar da kanta, Aunty tace "Kiyi hakuri kar ki sake kuka kinji, it's always like this for every lady Imaan" Imaan ta fara wani sabon hawayen, Aunty ta rungume ta tana lallashinta, Mama Hadiza ta shigo dakin ita ma ta dinga kwantar mata da hankali, sai da suka tabbatar tayi shiru gaba daya sannan suka fita dakin, Aunty ta hado mata shayi mai kauri ta kai mata.




*Imaan isn't for free* it's 300 via


Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788




74.....



Bayan azahar mai make up da aka yi hiring ta xo tayi ma Imaan very light make up da ya fito da ainahin kyanta na 'yar fillo, ta saka wani lace mai tsadan gaske da Daddy yyi mata da head din da xata saka, ko tsinke ba a taba ba a lefenta dama, gaba daya kayan da xata yi fitan biki Daddy ne yyi mata su, tayi kyau har ta gaji barin ita da dama bata make up, kowa sai kallonta yake cike da sha'awa, Aunties din Sadeeq da Step mum dinsa duk sun xo gun mother's day din, Mariya da frnds dinsu na islamiyya da boko duk sun xo suma, da Ammi da Aunty ankon lace suka yi, ko kai ka gansu sai sun burge ka, karfe uku da wani abu Umma ta dawo gidan ita ma ta shirya cikin tsadadden lace ta shigo cikin jama'ah ana ta gaisawa, sosai hakan ya ba Aunty mamaki sai dai bata ce komai ba, bayan kusan awa daya sai ga Safeenah ta xo gidan cikin shiga ta alfarma da sisters dinta biyu, can kuma sai ga wasu daga kawayen Umma, gida ya cika da frnds din Aunty da Ammi masu ji da kansu cikin ankonsu na mothers day da Aunty ta fitar, irin rawan da Safeenah tayi sai abun ya baka mamaki, don xagewa tayi ba kadan ba kamar dai bikin masoyiyarta, sosai hakan ya ba Imaan mamaki, ita dai tana xaune ana ta abubuwa a wajen, duk Ammi na lura da imaan throughout the program bata da walwala kana gani kasan tana da damuwa, biyar da wani abu Ammi ta samu ta kebe da ita a backyard din apartment dinsu tana kallonta tace "Imaan ba nace ki kwantar da hankalin ki ba, or do you have any problem da baki son fada min ne" Imaan ta girgixa mata kai cikin sanyin murya tace "Ba komai Ammi...." Sai kuma ta sunkuyar da kanta hawaye ya fara taruwa idonta, Ammi tayi tunanin kila duk fargaban da ko wace amarya ke yi da xulumin barin gida ne ke damun yar tata, hakan yasa ta jawota kusa da ita ta shiga kwantar mata da hankali cikin taushin murya, Imaan dai sai gyada mata kai take hawaye na sakko mata, Ammi ta rungumeta tace "Bana son wannan kukan Imaan, today is ur happy day, ki saki ranki pls" a hankali imaan tace "Na daina" Ammi tace "Good ki shiga ciki ki xauna, karfe nawa yace xa ku tafi dinner din?" ta girgixa kai tace "Ban dai sani ba kila bayan Magrib" Ammi ta bude mata kofar kitchen tace "Go in and get some rest before then, or are you feeling pain anywhere?" Imaan ta girgixa kai tace "A'a" Ammi tace "Toh shiga ciki ki xauna" shiga kitchen din tayi sai kuma ta juyo a hankali tace "Ammi Daddy na fa?" Ammi tace "Ya dawo two days ago ai, don kina part din Inna ne" Imaan tace "Toh" daga haka ta wuce dakinta, wayarta da ta sa a jaka ta fiddo tana dubawa taga text na Sadeeq, sosai gabanta ya fadi ta bude message din tana kallon content dinsa, "I am sorry to let u know that... tonight dinner isn't going to hold anymore due to some reasons, ki sanar ma mutanen gida, thanks" ta karanta message din ya fi sau biyar sannan ta ajiye wayar a sanyaye, lkci daya ta ji wani hawaye me xafi na xubo mata, xaunawa tayi gefen gado ta cire head tie dake kanta, Maimoon ta kira a waya daga karshe ta sanar mata babu dinner din ta gaya ma su Ammi don a sanar ma mutane da xa su tsaya sbda dinnern, Maimoon tace "What?? Sbda me??" A hankali Imaan tace "Ke dai ki gaya masu kawai ni ina daki yanxu" daga haka ta katse kiran, Aunty ce ta shigo dakin tana kallonta tace "Imaan shi Sadeeq din yace maki babu dinner kuma?" Imaan ta kalleta trying her best to look alright tace "Ehh daxu yyi min text Aunty, he said he is sorry for the inconvenience" Aunty tayi shiru tana kallonta can tace "Toh shkkn Allah ya so babu wanda ya tafi can din ma" daga haka ta fita dakin, kowa a gidan yayi mamakin me yasa aka ce an yi canceling dina, ciki har da Umma dake tsakar gida tace "Ahhh gaskiya mu dai ba a kyauta mana ba, mu da muka sa ran mu yi yanda muka ga dama yau abu namu maganin akwabe mu, ni fa har na hango an dire ma kowa full chicken a table da lemon masu kudi, gaskiya an shiga alhakin mutane da yawa..." Safeenah tace "Ikon Allah, to bari mu san inda dare ya mana dama dinner din nake xaman jira a tafi, ni ban ma taba jin inda aka fasa dinner ba sai a bikin gidan nan" Ammi dai ko kallonsu bata yi ba tana sallaman wasu frnds dinta da gifts da aka raba na mothers day, Mama Hadiza tace "Toh ai gwara hakan, Allah na tuba meye abun birgewa a dinner, albarka ake so a aure dama ba tsiya ba, dinner sai kace fadan Allah, ai ni wllh ya burgeni da yace bbu dinner kowa sai ya ci kajin a gidansa...." Umma dai bata kalli inda take ba ta shiga sallaman neighbors dinsu da xa su tafi, Mama Hadiza ce ta tafi sanar ma Inna babu Dinner don suna can ana shiri da ta Rasulu da taxo da yamma, Inna ta gwalo ido tana kallon Mama Hadiza tace "Subhanallahi shi Bulasawan wiwi ya sha da xai ce an fasa shagalin?" Mama Hadiza dai bata ce mata komai ba ta fita, Inna ta kalli Ta Rasulu da har ta fiddo kayan da xata saka da mayafi tace "Yau naga gantalallen mutumi ta Rasulu, wai ki ji ba casu" Bayan isha Imaan na xaune can karshen gado tana ta bin frnds dinsu da Mariya dake ta hira a dakin da kallo, ko kadan bata san abinda suke cewa ba don gaba daya she is absentminded, Maryam dai na xaune one side tana danna wayarta amma gaba daya mood dinta wasn't good, Maimoon ce ta shigo dakin ta nufo Imaan ta mika mata wayar hannunta, Imaan ta amsa a hankali tace "Waye?" Maimoon tace "Ya M.A" Imaan ta kai wayar kunne tayi sallama, cikin sanyin murya Mujaheed ya amsa mata daga daya bangaren, tace "Ina yini Yaya?" yace "Lafiya, can you pls come out now?" Tace "Kana Ina?" Ya d'an yi shiru sai kuma yace "Ki sameni bayan apartment dinmu" tace "Toh" daga haka ya katse wayar, ta mika ma Maimoon wayarta ta sauka daga kan gadon ta dau hijab dinta har kasa ta saka, Maryam na kallonta tace "Where are you going to?" Imaan tace "Yaya ke kirana" daga haka ta fita bayan tace ma su Mariya tana xuwa, ta kitchen dinsu ta fita, ta dinga tafiya kamar mai tausayin kasa har ta kai Bangarensu Maimoon, tsaye ta gansa yana facing bango har ta iso kusa da shi bai juyo ba, a hankali tace "Ga ni Yaya" juyowa yyi yana kallonta, lkci daya ya sauke idonsa, ya fi minti biyu bai iya yace komai ba, sai kuma cikin sanyin murya yace "Sure I was suppose to ask you what u want for ur wedding but I didn't Imaan, but I don't know if you will appreciate this little that I have for you..." Imaan dai sai kallonsa take, wani round box mai kyau dake hannunsa ya bude yana kallonta ya fiddo bracelet sai kyalli yake kana gani kasan na menene ya kamo hannunta a hankali ya saka mata a wrist cikin sanyin murya yace "Am hoping you will love it lil sis" lkci daya hawaye ya kawo idonta ta fada jikinsa tana shessheka tace "Nagode Yayana" rungumeta yyi cikin breaking voice yace "I am... wishing u all d very best in ur marriage lil sis, Allah ya ba ku xaman lfya, but.. but i want to let you know this Imaan....." Sai kuma ya kasa ci gaba ya runtse ido, saketa yyi ya janyeta jikinsa ya juya xai bar wajen tace "You want to let me know what Yaya?" Bai juyo ba sbda bai son taga hawayen idonsa yace "I want to let you know that, kiyi ma mijin ki biyayya, be the best wife you can..." Daga haka ya wuce ta bi sa da kallo tana goge hawayen idonta tace "Toh nagode Yaya" a hankali ta juya ta koma apartment dinsu hawayen da take ta gogewa ya ki tsaya mata. Kamar Daren jiya wannan Daren ma Imaan bata yi baccin kirki ba, sai kallonsu Mariya da Maimoon da Maryam dake ta baccinsu take, daga karshe ta tashi ta dauro alwala ta dinga sllh har sai da taji bacci ya xo mata, nan kan darduman ta kwanta nn da nan kuma bacci yyi awon gaba da ita. Da asuba Ammi ta shigo ganinta kwance kasa ta tada ta tana kallonta tace "A kasa kuma Imaan maimakon ki tafi dakina?" Imaan ta mike xaune tana murxa ido tace "Sllh nayi ne daxu" Ammi tayi shiru tana kallonta, can tace "Toh ku tashi ku yi sllh lkci yyi" daga haka ta fita dakin, Da safe gida ya xamo ba masaka tsinke duk inda ka bi jama'ah ne, tun asuban fari dama ake ta girki a gidan don Aunty tace da kansu xa su yi abinci ba sai an wani kira masu yi ba, Umma ma dai na cikinsu, da ita aka dinga yin komai tun asuban, Ba karamin tilasta Imaan Ammi tayi


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login