Showing 87001 words to 90000 words out of 303099 words

Chapter 30 - Imaan Book 1 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

1644

sanar masa sannan su tafi gun Mahaifiyar su ita ma su sanar da ita, yasan Daddy xai yi farin ciki da hadin shi ma, don fargabarsa a ko da yaushe gidan da only child din tasa xata fada da sunan aure, yasan Daddy na son imaan fiye da tunanin me karatu, he can do anything bcos of his only child, Umma Ta karasa cikin parlon tace "Alhaji kasan Mujaheed ya tura min kudi xan fara hada masa lefe, to yau xan fara shiga kasuwa" Abba na kallonta da mamaki yace "What? Lefe kuma? But he told me nothing about that" Umma ta d'an bude ido tace "Toh ba sae an gama hadawa ba xa a kinkimo maka ka gani, kar ya fada maka kayi tunanin ko so yake ka basa wani abun, wllh ban son ya daura maka ko wani nauyi ne kaga ba a dade da hidimar seeyama ba, tunda Allah ya hore masa xai iya komai shi sa kawai nace kada ya gaya maka sai na gama hada kayan a kawo maka ka gani, ba laifinsa bane shi ma ya so sanar da kai na hanasa, amma idan hakan ya bata maka rai kayi hakuri don Allah" Abba yace "Toh Allah ya rufa asiri..." Umma tace "Ameen, tun jiya naga kamar abu na damun ka, shine nace to mai kuma ya faru, idan ma inna ce don Allah a dinga hakuri, uwa ce... Sai ayi ta fatan a gama lafiya da ita, ya ci ace duk abubuwan inna ya xame maka jiki yanxu..." Abba yace "Haka ne" Umma ta xauna ganin maganganunta sunyi tasiri xuciyar Abba, murya can kasa tace "Toh me kuma take so Alhaji?" Abba yace "A'a wannan mun shawo shi tare da Sadeeq, Yusuf ne dai ya xo min da wata magana yanxu da ya kulle min kai... Am still trying to find a way out ne har yanxu" Da mamaki Umma tace "In ji dai lafiya??" Abba yace "Lafiya lau, yar uwarsa Imaan yake so da aure wai" Mikewa Umma tayi da mugun mamaki baki bude tana kallon Abba, can tace "Aure kuma Alhaji??" Abba yace "Kwarai, yanxu ma ya bar parlon nan" Umma tace "Ikon Allah.... Aure fa???" Juyawa tayi ta nufi kofa tace "Toh Allah yayi mana mai kyau dai, ya xaba abinda ya fi alkhairi, ae imaan yar uwar sa ce, Imaan ta mu ce..." daga haka ta fice, direct sama ta wuce ta bude dakin Yusuf ganin baya ciki ta shiga dakin Aunty, xaune ta samesa tare da Aunty, Umma tace "Amma Yusuf kayi asara wllh, ka kuma samu tabin kwakwalwa mai wuyar ganowa balle ayi maka magani, yanxu ka rasa warce xaka je kace ma Ubanka kana so sai Imaan, Yusuf me ya same ka ni Rukayya?? ina ita Hafsar da kake nema take??" Yusuf dake kallonta yace "Umma ni Hafsat ba aurenta nace xan yi ba" Salati Umma ta saki tace "Amma Allah ya isa tsakaninmu da kai, mu xaka ka ma bakin ciki Yusuf?? ka bar 'yar attajiri ka dawo kace mai lalura iri iri kake so? Anya akwai lafiya kuwa, mu xaka kwaso wa mugun iri, irin ciwo a xuri'ar mu? Yarinya mutu kwakwai rai kwakwai?? Toh wllh tunda an asirce uwarka ta kasa cewa komai ni kam ba a asirce ni ba sai inda karfina ya kare in sha Allahu, yanda xan ma Mujaheed haka xan maka don duk daya ku ke a gu na, in sha Allahu sai naje na gano tushen abun nan... Ba wanda ya isa ya ci nasara a kanka kamar yanda aka ci a kan kanin Ubanka, uban kuturu yyi kadan wllh balle na makaho" daga haka ta fice a dakin kamar xa ta tashi sama, Aunty da ta bude baki tana ta kallonta tace "Ikon Allah ya fi gaban haka...."
Daddy couldn't help it but laugh bayan Abba ya xo har part dinsa ya sanar masa intention din Yusuf a kan Imaan, Daddy yace "Ikon Allah, nayi farin ciki sosai sai dai kar ka mance da alkawarin da kayi a baya barrister, ko ya xa mu yi?" Abba yace "Sure ina sane, shi ma ba wai xa a dakatar da shi bane Sadeeq din, abinda xai faru yanxu kawai mu fara xuwa gun Inna mu je ta bakin ta kafin a yanke ko wani decision" Daddy yace "Gaskiya ne wannan" Part din inna suka tafi a tare, Inna ta fito daki tace "Tun safe in gaya maku nake aiki ban xauna ba, ku leka bandakina ku ga ko tuwo ya xube kasa xa a iya xaunawa a cinye tass, ba ku ji bayana ba kamar ya balle ni dai in huta" Murmushi duk suka yi suka xauna, Daddy yace "Gwara dai ki dinga hutawa haka inna, gashi kince baki son mai aiki balle a samo maki ko yar dattijuwa ce" Inna tace "Ni ko ina xan so masu aiki mutane duk wari, sannan su cinye ma mutum abinci, A'a ba ruwana ni ko da rarrafe ne xan yi aikina, 'ya yanku ne sun xama abun tsoro banda haka Imaan ko Maimoon ko Ummi baxa su dinga xuwa min d'an share share ba banda karshen duniya da lalacewa ta xo" Abba yace "Inna ke fa kika ce baki so, ai da suna xuwa..." Inna tace "Ehh ni nace bana so, don ba abinda suka iya gaskiya, basa min yanda nake so, ni dai nace na yafe su daina xuwa" Duk suka yi shiru basu ce mata komai ba, ganin ta dauko tsintsiya Abba yace "Inna daxu Yusuf ya sameni kan wata magana da naga ya dace mu sanar maki kafin mu yanke hukunci...." Ajiye tsintsiyar tayi ta xauna kan kujera da sauri tace "Me ya faru kuma??" Abba ya d'an yi murmushi yace "Wai yar uwarsa Imaan yake so da aure...." Inna ta gwalo ido ta saki baki tana kallonsu, saukowa kasa ta yi a hankali ta xauna kan rug ta fashe da matsanancin kuka tana tafe hannu tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, LA haula wala kuwata illa billahil Aliyul Azeem, la ilaha ilallahu Muhammadurrasulillahi sallallahu alaihi wassalam, hasbunallahu wa ni'imal wakeel.... Na ga abinda ya isheni ni patuuu" Daga Abba har Daddy kallonta suka dinga yi da mamaki, inna ta dakatar da kukan da take tace "Toh da kyar idan Imaan bata ta6a shan nonon Amina ba ma, yo ta ma sha ne kawai... Idan xa kuyi ta kanku kuyi ta kanku"




*The book Imaan is not free, you read for free ur cup of coffee*🤷🏻‍♀️

It's 300 via Fcmb 3276052019
Hauwa Bello Jiddah

Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp digit 07087865788 to be included in the payment group.


28.....

Girgixa kai Daddy yayi yace "Hakan bai ta6a faruwa ba Inna, ko kin manta ba gida daya muke lokacin ba" Inna ta mike a fusace tace "Yau naga jaraba ni Asabe, ka fi ni sanin abinda nake ne Bukar, so nawa idan matarka xata fita gantalinta na makaranta take kai ma Amina Imaan, kuma babu wanda bai san irin kukan banxa da shagwaban da Imaan tayi tana jaririya, bata kuma yarda ta sha komai sai nono, shi sa ma bana son a kawo min ita ba ruwana, kuma kace min 6ata ta6a shan maman Amina ba?? karya xan xauna in giggilla maku da tsufa na?" Sai kuma ta fara kuka ta xauna tayi tagumi tace "Shkkn karshen duniya ta kama....." Abba ya sauke ajiyar xuciya yace "Toh bari a kira Aminar a tambayeta" Kuka kawai inna take bata tanka su ba, Abba ya dau waya ya kira Aunty, bayan ta daga yace "Ki taho part din inna yanxu, it's urgent" tana tambayarsa abinda ya faru bai bata amsa ba ya katse wayar, Aunty tayi jigum dama ita irin abinda take gudu kenan, haka dai ta sa Hijab ta fita xuwa part din inna, Daga Abba har Daddy sai kallon inna dake sharban kuka suke, da daddy yayi kokarin bata hakuri a fusace tace "Rufe min baki, naki hakura, ko dole ne?" Haka yasa duk suka ja bakinsu suka yi shiru, da sallama Aunty ta shiga parlon inna, Abba da Daddy kadai suka amsa mata, banda Inna dake hararanta ta gefen ido, Aunty ta durkusa tace "Ina kwana Inna?" Inna tace "Sai yanxu garinki ya waya da xaki ce min ina kwana? Ina ce ana idar da sllhn asuba nan ya kamata ku yo ku gaisheni amma ke da Aisha sai rana tayi gauuu sannan ku yo min nan wai kun xo gaisheni, ni dai ba ruwana a dinga jin tsoron Allah" Aunty dai ba ta ce mata komai ba sai gaida Daddy da tayi ya amsa, Abba yace "Amina wai kin ta6a ba Imaan mama?" Da mamaki Aunty ke kallonsa tace "Imaan kuma?" Abba yace "Ehh" Aunty tace "Ta ya hakan xai faruwa kuwa? A'a ni ban taba ba..." mikewa inna tayi, tayi mitsi mitsi da ido tace "Toh bari ku ji... da ki bata mama da kar ki bata duk uwarsu daya ubansu daya a wajena... in dai da rai na a duniya to wllh Isuhu baxai auri Imaan ba, harammm, ga dai d'an Bulasawa da ya riga sa sbda ku ba yan gaskiya bane shine ku ke son yi masa fin karfi, to ni 'yar gaskiya ce, kuma ba a cin amana da ni, na kuma yi ma yaron alkawari Imaan ta sa ce, don haka duk ku yi ta kanku munafukai kawai, shi isuhun tun da can bai san yana sonta ba sai da ya ga bulaswa sbda bakin ciki da hassada kar jikata ta huta, to aniyarsa ta bi sa, to wai ma ina figaggiyar budurwarsa da har xai ce sai jikata sbda rashin tsoron Allah, to ni ba ruwana ya cire idonsa kan jikata na riga na mata miji" sai kuma ta fashe da kuka ta rike kai tace "Innalillahi Wa inna ilaihi raji'un, wayyooo ubangijina, su dai yan gidan nan basa tsoron Allah na rasa me yasa haka, basa tsoron axaban Allah, xaman gidan nan ya haramta gun mai tsoron Allah iri na, ni dai idan xuciya ta kwasheni ma sai in tafi Habuja gun shegen Balan can inyi xamana, don wani lkcn ma gwara 6are da naka" Mikewa Daddy yyi ya nufi kofa ya fita parlon, Aunty ta tashi ta bi bayansa, A hankali Abba yace "Toh kiyi hakuri an bar maganar in sha Allah inna" Ta kunce habar xaninta tana share idonta tace "Ni dai ba ruwana, tunda haka isuhu ya xama dama kar ya sake tako min nan, gwara min Mujaheed sau sittin a kansa, shi Mujaheed baya haka, xuciyar sa mai kyau ce, kuma ni duk wanda ya sake tada maganar nan gaskiya xan ja masa Allah ya isa" Mikewa Abba yayi yace "Sai anjima" ko tanka sa bata yi ba har ya fita ya kulle mata kofar. Abba ne xaune parlonsa da Daddy sai Aunty, Yusuf ma na xaune kansa a kasa, a hankali Abba yace "Kayi hakuri Yusuf, Allah ya sa hakan shi ya fi maka alkhairi" Yusuf ya daga kai ya kallesa yace "Ameen" Daddy kam kasa cewa komai yayi, Aunty ta mike ta fita parlon.
Misalin karfe goma da rabi na safiyar ranan Imaan ta fito parlor bayan tayi wanka ta shirya cikin atamfa an mata dinkin riga da skirt da ya amsheta sosai, gaida Daddy dake parlon a xaune tayi, he was still tensed at what happen safiyar ranan, bai taba tunanin Inna xata yi masu haka ba, gaba daya bai ji dadi ba, don ko da ace yau Yusuf bashi da hali bai ci tayi haka ba sbda shima jikanta ne, balle Yusuf is perfect in every aspect, ko Ammi daddy ya kasa gaya ma, ya kalli Imaan ya amsa gaisuwar da tayi masa, ta mike ta wuce kitchen gun Ammi, Ammi tace "Ki dau nose mask ki sa ki tafi ki share balcony din nan ki goge it's too dusty ni kuma xan tafi unguwar rimi yanxu ina sauke girkin nan" Ta marairaice tace "Ammi toh ai nima can xanje fa yau, gashi har na shirya" Ammi tace "Me xaki je kiyi biki saura kwana uku???" Kamar xata yi kuka tace "Don Allah Ammi ki bar ni in je, Anty Halima fa kawata ce kawai don dai ta girmeni ne, plss Ammi let me go" Ammi tace "A'a ba ruwana sai daddy ya bar ki, yanxu ki tafi ki share min inda na sa ki" A Hankali ta juya ta fita kitchen din ta tafi daki ta dauko thick nose mask dinta ta dau sweeper xata fita daddy yace "Ina za ki?" Tace "Xan share waje ne" Daddy yace "Xa ki share waje kuma? Ina mamar taki?" Ammi dake jin su a kitchen ta leko tace "Gani!!" Daddy yace "Ta share k'ura fa kika ce madam" Ammi tace "Ga dai nose mask nace ta sa ae, toh wai yallabai idan tayi aure ni zan bi ta ina share mata gidan ko kuwa haka za ta bar gidanta ba tsafta sbda tana da asthma??" Daddy dai bai ce komai ba, Imaan ta juya ta fita, daddy ya juya yana kallon Ammi yace "Ba lallai tayi aikin gida ba idan tayi aure, I will get her a housemaid that's capable" murmushi Ammi tayi tace "Lallai kam, to idan mijin yace bai son Housemaid fa?" Mikewa daddy yyi yace "Sae a fasa auren, I know what I am saying...." daga haka ya wuce dakinsa, Ammi ta tabe baki ta juya ta koma kitchen, Imaan na share tiles din dake shimfide a babban balcony din nasu lkci lkci xata mike ta d'an huta idan ta ji breathing din nata na sarkewa, kamar ance ta juya taga Mujaheed kai kana ganinsa kasan daga asibiti yake, mikewa tayi tsaye ta jingina da pillar tana sauke numfashi a hankali, Mujaheed ya tsaya yana kallonta coz she looks so tired, fuska daure yace "Wa ya sa ki shara?" Ba tare da ta kallesa ba tace "Ammi" d'an jim yyi sai kuma yyi wucewarsa part din inna, Xaune ya tadda inna a parlor fuska a tsuke, ya tsaya bakin kofa yace "Me ya faru kike kirana??" Tace "Baxan kiraka ba Mujaheed, naga xama bai gan ni ba na tashi naje na sami mai gadi ya nemo min lambarka ya kira min kai, ni dama kai ne nawa, da kai muke kashe komai mu rufe, tunda ga irin 'ya yan da Allah ya jarabce ni da samu, ni ba din ba din ba ma sai ince banyi dacen 'ya ya ba, samm Bukar da Ahmadu ba yaran nunawa bane" Kallonta kawai Mujaheed yake, can ya karasa cikin parlon ya xauna yace "me ya faru?" Ta fara matsar kwalla tace "Wai kaji fa Isuhu ya fito masu da cewar yana son Imaan da aure" a hankali Mujaheed ya mike yana kallonta da manyan idanuwansa, Inna tace "Maimakon su tsigale sa su masa tatass, tunda ga yaro d'an kirki na nemanta da aure, in gaya maka sai yaran nan suka biye sa, suka kwaso jiki suka yo min nan suna washe min hakora a can" ta fadi haka tana nuna masa kujeran da su Abba da daddy suka xauna, A hankali Mujaheed yace "Sai kika ce masu me?" A fusace tace "Me kuwa xan ce masu Mujaheed?? Balbalesu nayi nace ko bayan raina bulaswa xa a ba ma imaan, don ni yar gaskiya ce ba a cin amana da ni, kai kaji bakin ciki irin na d'an uwanka fa?? Shi mai daukan albashin da bai wani taka kara ya karya ba xai ce xai auri jikata taje ta mutu in shiga uku in lalace? Dududu albashin nasa ya wuce dubu dari biyu da wani abu?? A'a ba ruwana, ni dai nan na binne maganar nace bana son a sake tada ta ko inyi Allah ya isa, Imaan ta Bulasawa ce idan Allah ya yrda, shine abun ya min ciwo na fita na kiraka ina kuka a waya, ko kai ya ka gani?" Mujaheed ya sauke wani boyayyen ajiyar xuciya ya xauna yace "Haka ne, tunda ya riga sa" Inna tace "Atohhh... kai dama duk ka fita daban a jikokina, kai d'an gaskiya ne kamar ni, nasan kuma kai baxa ka ta6a irin wannan kazamin tunanin ba wai xaka auri Imaan, kai kaji wani sa6o don Allah a ja mana fushin ubangiji, toh Isuhu dai ya xama abun tsoro, har abada kar ya sake yo min nan don xan tsallake in gudu gidan bala" Mujaheed dai bai ce komai ba don har sannan gabansa bai daina faduwa ba ya rasa dalili, Inna tace "Ahmadu da Bukar dai sun xama shashashai yan cin amana, Allah ya shirye su, kuma su gaggauta tuba ga Allah ni ba ruwana" Mujaheed ya jinginar da kai da kujera ya lumshe ido a hankali, inna tace "Baka rufe ido ba wannan abun takaicin Mujaheed, Wllh yanda kake ji haka naji nima daxu, naji kamar ince wayyoooo Allah, kawai na fashe da kuka bayan fitar su, haka kawai suje su ja mana girgixan kasa a gidan" Mikewa inna tayi tace "Har naji sanyi da na gaya maka wllh, ni dai bari in kada shayina in sha, ba ruwana da wahala" Daga haka ta shige kitchen, Mujaheed ya dafe kansa, lkci daya ya dago yyi murmushi, da cup biyu ta fito tace "Ko kai ma in kada ma ka shayin ne?" Mujaheed ya kalleta yace "Toh"
Imaan ta gama goge balcony din ta tafi cikin parlor tana cire mask din bakinta, Breakfast Ammi ta mika mata a tray ta ajiye ma Daddy a dinning table, karasawa tayi ta amshi tray din tana ajiyewa dinning sai ga Daddy ya fito, imaan na kallonsa ta marairaice a hankali tace "Daddy xan je gidan gwaggwo yanxu, sai in dawo bayan bikin Aunty Halima" Daddy ya ja kujera ya xauna yace "A'a sai dai ku dinga xuwa kuna dawowa da mamarki" Ammi tace "Sae kace handbag, kawai ka barta ta tsaya can har bayan bikin mana" yace "kin dai fi ni sanin condition dinta, so I don't need to talk much" Ammi tace "Imaan fa ba yarinya bace yallabai, she can take very good care of her self" daddy


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login