Showing 189001 words to 192000 words out of 303099 words
tace "Atoh, banda mai sonka wa xai kawo maka haka har gida, yanxu xamani ya lalace mutane basu son fadin gaskiya ga ta nan dai kiri kiri ana ganinta, wllh bbu wanda bai san abubuwan nan da na gaya maki ba amma sai mutune su yi gumm su xuba ido, to mu ba mu gaji haka a xuri'ar mu ba gaskiya" Hajiya Saude tace "Wllh ko a gaban uwar yarinyar ce xa mu iya fadin abinda Hajiya Rukayya ta fada maki a nan tunda ba tsoronta mu ke ba, gaskiya ne dai sai mun fada, sam matar bata da hali, makirace ba ta wasa ba, yanxu haka ita gani take ta ci nasara tunda bbu wanda ya isa ya fito ya fadi aibunta duk ta rufe bakin kowa...." Mummy tace "Na ce maku xan yi shawara ai koh?" Umma tace "Toh Allah ya baki ikon yin wanda baxa ki dawo kina da kin sani ba wataran, Allah kuma nuna maki duk abubuwan da muke fada da idon ki, kai ko spy mace ne xa ki iya biya ta dinga shigowa gidan namu taga wainar da ake toyawa, wllh wllh duk ta mallake gidan......" Daga haka ta mike tana murmushi tace "Nagode da lkcn da kika bani Hajiya, Allah ubangiji ya mana xabi nagari..." Tana nuna Safeenah tace "Yar wajen Hon Usman Basiru ce wannan... Kuma surkata ce d'ana na fari ke aurenta, yanxu haka sun kusa wata uku da aure" Mummy na kallon Safeenah tace "Maa sha Allah, that's nyc, Allah ya bada xaman lafiya" Safeenah ta mike tana amsawa da Ameen, Hajiya Saude ma ta mike nan suka yi ma Mummy sallama, Mummy tace "Toh nagode, sai anjima" Umma tace "Mu jima da yawa Hajiya" kofa suka nufa kafin su isa kofar Sadeeq ya shigo parlon, kallon Umma ya dinga yi da mugun mamaki da su Safeenah, Umma ta sunkuyar da kai ta fita parlon su Hajiya Saude na biye da ita, Sadeeq na kallon Mummy ya karasa cikin parlon ya xauna har sannan fuskarsa na dauke da surprise yace "Mum what is she here for??" Mummy tace "It's not necessary you know Sadeeq" ya mike cike da damuwa yace "Why will u say so mum, don Allah ki gaya min me ta xo yi?" Mummy ta mike tace "Nace maka it's not necessary Sadeeq, I am busy upstairs pls" daga haka ta wuce ya bi ta da kallo, a hankali ya koma kan kujera ya xauna ya jinginar da kansa jikin kujeran ya rufe ido xuciyarsa na bugawa.
Bayan kwana biyu Sadeeq ya shigo part din mum dinsa ya ganta da sisters dinta da few frnds a parlor suna xuba lafiyayyu kuma tsadaddun kayan lefen da aka yo daga Dubai cikin boxes set shidda sau biyu, sosai boxes din suka yi kyau sannan they look sooo unique kana gani kasan ba da kudin wasa aka siye su ba, Mummy na kallonsa tace "Perfumes da kace xaka Karo fa??" Yana dai tsaye yace "Ohk suna wajen Aunty" ta masa wani kallo tace "Wajen Aunty Kuma?? Me ya kai su can?" Shiru yyi bai ce komai ba, Kawar Mummy Hajiya Farida tace "Toh Aunty ce ta nemo maka mata da xaka bata kudin siyan turarurruka, kai sai samm baka san ciwon kanka ba Sadeeq, kila ma har ka hada yarinyar da ita Auntyn koh?? tunda ga kanwar uwarka" Shi dai bai ce komai ba, ya juya ya fita, Mummy ta bi sa da harara, Hajiya Farida tace "Ni fa ban ji dadin da tasan yarinyar tun a asibiti ba wllh, Bai kamata ta san komai ba a maganar auren nan"
Imaan na xaune dinning misalin karfe sha daya na safiyar lahadi tana answering past questions din gabanta kasancewar gobe xa su fara waec, aka bude kofar parlor.... Inna ce ta shigo parlon da sallama Imaan na kallonta har ta karaso ciki tana tabe baki murya can kasa tace "Ko turaren wuta bana jin an sa ma parlon nan yau, dama fa tsafta sai wanda Allah ya so da Rahama yake ba ma, mu dai mun gode masa....." Imaan tace "Toh ba sai ki sa mana ba tunda ba mu sa ba" da sauri Inna ta juya ta kalleta, Bata dai ce komai ba ta xauna saman kujera, Imaan ta ajiye pen din hannunta ta shigo parlon tace "Ina xa ki je da sassafe haka?" Inna tace "Ina xan je kuwa da ya wuce gidan Mujaheed, wa gare ni banda Allah sai shi, jiya fa haka ya xo bashi da isasshen lafiya duk ya rame sai 'yan idanuwa, ya xama wani tsololo da shi sai tsayi kamar pal waya, ni dai ba ruwana wllh, Mujaheed da ko ciwon kai da kyar ka ji yana yi sai gashi duk ya xabge haka kamar ana cin namansa, ni ko nace anya matar nan ba mayya bace aka lika masa ya aura kuwa?? Tun fa da aka yi auren yake a haka yau lafiya gobe babu, toh ni dai yanxu gidan xan tafi idan ma Safara'u mayya ce muna hada ido xan gane, mayu kuma wasu iri ne ba mu kara da su ba a duniya, Ni wllh har dambe nayi da mayya, kuma da kyar idan Safara'u ba mayya bace" Imaan dake kallonta da mamaki tace "Mayya kuma Inna" Inna tace "Oh oh Allah, to idan ba mayya bace mecece, ce min yayi fa bai san me ke damunsa ba da na tsare sa jiya, wllh da barbajin gaskiya a xancena, ni dai duk abinda ya samu Mujaheed ni ya sama kuma baxan xuba ido haka ba, a kan Mujaheed sai duk in tada gidan nan Al-quran, ni bai fiye min kowa sau dubu dari biyar ba aka ce maki, idan xa ki tafi ki shirya ki tafi ki shirya mu tafi gidan yanxu in san abun yi, dama kuma ki taho da takadda da biro duk yanda muka yi da shegiyar matar xa ki rubuta min, don tambayoyi xan mata na dangin uwa da uba, a nan xa a gano tushen abun...." Xaunawa imaan tayi tana kyalkyala dariya sosai, Inna ta wani hade rai tana kallonta tace "Amma ke kam baki da da'a, Meye abun dariya a nan jikana na can rai a hannun Allah, Toh ni fa wllh a kan Mujaheed sai ince a fasa kawo kayanki da sadaki yau ba ruwana, haka kawai jikana ba lafiya xa a cika ma mutane gida da jama'ah... Bari ma in je in sami Ahmadu yanxu tunda ke matar banxa ce baki da mutunci" wani kallo Imaan tayi mata tace "Toh ni ce bani da lafiya da xa a fasa kawo kaya???" Inna ta saki baki tana kallonta, can ta mike tana kwalo ma Ammi kira, Ammi ta fito da sauri tana amsawa, rai bace Inna na nuna mata Imaan tace "Wllh jaraba kika haifa Aisha, mu dai kaf danginmu babu butulu wllh ban dai san ya naku yake ba, gaskiya imaan butulu ce, banda haka kiri kiri ta fito ta nuna ciwon d'an uwanta bai dameta ba saboda tana 6arin jiki tayi aure, baki ta6a xaunar da ita kin bata labarin irin bakar wuyar da Mujaheed ya sha da ita tun tana tsummarta bane wai? Ni dai wllh a dinga jin tsoron Allah, wllh baki xaunar da ita kin sanar mata ba da baxata fifita aure kan d'an uwanta na jini ba, idan ban sa an fasa kawo kaya ba gidan nan yau a kan Mujaheed ace ba ni bace, lefen banxa da hofi jikana ya fi lefe ne, wllh jiya baccin kirki ban yi ba sai da safe bacci ya kwashe ni, ban tashi ba sai daxu na shirya a gurguje na taho ta raka ni gidansa in ga abinda yake ciki, nace to ko ma matar ce mayya xan je in ga" Imaan ta tabe baki tace "Ba fa inda xan je gobe Ina da jarabawa, ko kuma ni likita ce da xan biki...." Inna ta fashe da kuka ta nufi kofa tace "Eh lallai Imaan ta xama jarabar duniya, Bukar ya haifi jaraba, Allah ka mana iyaka da Butulu duk inda yake.... Bari naje in samu Ahmadu ai na fi ki tsiya yau" daga haka ta fice daga parlon, Imaan na turo baki ta juya xata koma dinning Ammi tace "Wuce ki shirya ki bi ta ku tafi" ta juyo da sauri kamar xata yi kuka tace "Ammi karatu fa nake, ni wllh bana son xuwa gidan Yaya..." Ammi ta hade rai tace "Musu xa ki tsaya yi da ni kenan?" Lkci daya hawaye ya kawo idonta ta wuce dakinta, atamfa riga da skirt ta fiddo ta saka bayan ta feshe jikinta da turare, ta goga chappete a bakinta ta sa gogaggen Hijab dinta har kasa ta fito parlor rike da wayarta da karamin jaka, Ammi dake xaune parlor ta bi ta da ido, a hankali tace "Ammi sai mun dawo" Ammi tace "Allah ya kiyaye, you pray before leaving" Imaan ta gyada mata kai ta nufi bakin kofa tana karanto addu'ar fita gida a ranta. Part din su Maimoon ta nufa ta bude parlon ta shiga a hankali, ko karasawa cikin parlon bata yi ba ta dinga jin Muryar Inna a parlon Abba tana cewa "Gaba daya Imaan ta banu ta lalace, sam bata da kirki yanxu, amma abinda ya ban tsoro shine yanda aka boye mata wuyar da Mujaheed ya sha a kanta, bata fa yarda da kowa a lkcn sai shi sai uwar, duk ta fitsare masa jiki, har uban nata Bukar tsoron sa take... Toh meye kuma lkci daya sai yarinya ta xama jarababba mara Imani, ni ka ma kira min Bukar din in ji ko su ke koya mata, dariya fa ta dinga ba66akawa daga nace mata Mujaheed ba lafiya xan je gidansa, ni wllh na gaji da imaan a gidan nan" shi dai Abba bai ce komai ba kansa na kasa yana sauraranta, ta tabe baki tace "Ni dai ba ruwana, shi kuma Mujaheed gaskiya sai mun tashi tsaye kansa don idan aka rasa sa ni nayi asara ba wani ba, idan ma auren ne bai so gaskiya sai a raba yau yau din nan, ba ruwana a kai ni a baro in shiga uku" Sai a sannan Abba ya kalleta yace "Xaxxabi fa kawai yake, amma ai yana jin sauki yanxu..." Tsaki Inna ta ja tace "Tunda ba jikin ka bane ba dole kace yana jin sauki ba Ahmadu, gansamemen mutumi da ya dinga min rawan sanyi jiya sai da na rufa sa da katon bargo shine xaka ce yana jin sauki, ku dai ku dinga jin tsoron Allah, wlh ku ji tsoron Allah, tunda ba wani ya min wahala da shi ba to ni xan je yanxu inji abinda yake ciki, idan ma matar ce mayya duk xan gani" Da mamaki Abba yace "Subhanallah, haba Inna ya kike irin wannan magana haka, wannan fa babban magana ne ka ce ma mutum maye...." A fusace Inna tace "Na ce mata mayyar, idan ba mayyar bace ina dawowa ai xan ce ba mayya bace, tsoron ubanwa aka ce maka xan ji banda Allah, shi kadai ne abun tsoro dama, kuma ni da shi nayi imaani" dai dai shigowar imaan parlon, kanta a kasa ta gaida Abba, Abba ya amsa yana tambayarta jiki domin jiya yini tayi ciwon kafa, Inna tace "Ya jiki?? Ce maka aka yi bata da lafiya, Ga dai bawan Allah me ciwo can a kwance xaka tambayi lafiyayyar mata ya jiki" tana fadin haka ta tabe baki ta mike tace "Toh yanxu xa ka kirasu ka sanar masu d'an ka na fari ba lafiya a bar kawo lefen da kudin aure sai wani satin koko?" Da sauri Imaan ta kalleta, Abba yace "Haba Inna, ae wannan bai shafi ciwon Mujaheed ba, Ina ruwansu da wannan, shi Mujaheed din yaro ne, don Allah ki yi hakuri ki bar xancen nan Inna bai ma kamata ba, ga yanda dai muka yi da mutane kuma ki kawo wata magana daban" Inna tace "Atoh ni dai duk abinda ya sami jikana Allah ya isa wllh...." Daga haka ta fice daga parlon a fusace, Imaan tace "Abba sai mun dawo" ya gyada mata kai kawai ta bi bayan Inna, har suka isa titi Inna bala'i take idan abu ya sami Mujaheed ya sami kowa, ita dai Imaan sai turo baki take tana tsaye gefenta, Inna ta tsayar da adaidaita ta shige yana tambayarta inda xata a fusace tace "Don Allah ka rufa min asiri yaro ka ja mashin dinka mu je, meye kuma Ina xanje kamar yar yarinya, jikana ne fa ba lafiya rai a hannun Allah gidansa na can unguwar dosa ana ma kyautata xaton matar ce mayya, kuma kana ta cewa ina xan je" Mai adaidaitan bai tanka ta ba, Imaan ta hade rai ta shige adaidaitan. Har suka isa gidan Mujaheed mita take ita kadai daga imaan har mai napep babu mai ce mata komai, suna sauka kafin ta fiddo hamsin ta mika masa Imaan ta basa dari biyar din hannunta don bata ma son dogon xance, ya ciro dari biyu ya mika mata, Inna ta saki salati tace "Nawa ka cire bawan Allah?" Imaan tace "Toh ai ba kudin ki bane Inna, kayi wucewan ka kawai" Mai adaidaitan ya ja napep dinsa yyi gaba Inna ta dinga jaraba tana kiransa barawo tuni imaan ta shige cikin gidan ta bar ta tsaye a bakin gate, dai dai balcony ta tsaya ta rungume hannu tana jiran shigowarta, Can sai ga ta ta shigo compound din tana cewa "Babu abinda kudin Bukar xai masa a rayuwar nan ta duniya, iyaka ma ya gudu ne da wahala da Bala'i tunda bamu basa ba" bata ko kalli Imaan ba ta murda kofar parlon ta bude ta shiga, Imaan ta turo baki ta bi bayanta, Umma ce ta leko daga kitchen tana soya kwai da dankali, Inna ta rike ha6a tana kallonta a hankali tace "Wacece wannan?" Umma dake sanye da hijab har kasa ta gaisheta a dakile ta koma kitchen din, Safeenah ce ta sakko parlor sanye da doguwar riga na material hannunta rike da tray na cup, ganin Inna ta dauke kai ta hade rai hade da tabe baki tace "Sannu da xuwa" Inna tace "Ina Mujaheed din???" Safeenah tace "Yana sama an sa masa drip" Inna tace "Ai ni na shiga uku, abun har ya kai an fara sa drif... Toh aniyar kowa xai bi sa wllh babu abinda xai sami jikana" Kallon Imaan tayi tace "Ke mu je in gansa..." Imaan ta nufeta, da sauri Safeenah tace "Inna a can dakinsa yake fa...." Inna ta juya tana kallonta tace "Dakinsa kuma? Toh da ina nace maki xan je banda dakin nasa? Ko nace maki dakin ki xan shiga Safara'u?" Safeenah tace "A'a da naji kince ku tafi, idan ma tafiyar ne ke da kike matsayin kakarsa ai sai ki tafi dakin" Inna ta gyara tsayuwa tace "Toh ita Imaan din fa??" Safeenah ta d'an hade rai tace "Wannan ba hurumin ta bane gaskiya shiga dakin mijina, bata da wannan hurumin, dakinsa sirrina ne da nashi" Salati Inna ta xabga ta xauna kan kujera tayi tagumi tace "Naga abinda ya isheni ni Asabe... Safara'u kinsan me kike cewa kuwa, wani sirrin ku ke da shi ke da Mujaheed da ba mu sani ba, kinsan wacece kike kokarin hana shiga dakin nasa kuwa???" Umma ta fito kitchen bbu yabo bbu fallasa tace "A'a inna, xancen gaskiya ayi ta, dakinta ne da na mijinta fa kuma kice wata daban ta shigar masu, a kan wani dalilin?? sai kace dai a garin ga6a ga6a muka taso, ko a musulunce ai hakan haramun ne ma wata ta shigar maki turakan miji..."
*Imaan isn't for free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
69. Imaan
Mikewa Inna tayi ta bude baki tana kallon Umma tace "Rukayya ita imaan din ce wata a gidan Mujaheed?? Ita Imaan din?? Ehh lallai ba shakka kin xama mahaukaciya, to wllh tllh Imaan ta fiye ma Mujaheed Safara'u sau dubu dari, wacece kuma Safara'u Allah na tuba?? Sannan yaushe kika san Allah da kike kokarin min wa'azi wai kar ta shiga daki ta duba yayanta? Toh kwanciya tace maki xata yi a dakin idan ta je?? Ko ko ce maki tayi bata da kwakkwaro kamar ki ne?? Ni dai na ga abinda ya isheni, ba kunya ba tsoron Allah kin kwaso jiki xalalo xalalo kin xo gidan surka kina girki a kitchen ita kuma tana sama wajen miji, anya Rukayya?? A'a tunda uwata ta haifeni ban taba gani ko jin haka ba wllh, Toh ni duk ba wannan ba, don bai dameni ba... Babban magana a nan shine gaskiya ban gane kan ciwon jikana ba, don wannan ciwo ba na Allah bane, tunda ya auri wannan mata Safara'u yayi bankwana da lafiya, yau ciwo gobe lafiya, yau fari gobe tsumma, To a kan me? Ita Safara'un yar wace gari ce in ji tukun kafin in san abun yi" Umma ta dinga mata wani kallo tana jin kamar ta tanka ta amma wata xuciyar na bata hakuri, fuska daure Safeenah tayi wucewarta kitchen tana kas kas da cingam ta bar su nan tsaye, Inna ta gyada kai tace "Toh kya ci uban ki kuwa ba dai jikana ba don kurwarsa daci ne da ita yarinya, in sha Allahu sai dai ki ci uwarsa da ta jajibo ki ba shi ba, kuma xaman ki saura kiris a gidan nan" daga haka ta ja hannun Imaan dake tsaye gefenta suka wuce sama tana huci, Umma ta bi su da wani kallo xuciyarta na tafarfasa tasan dai ko hauka take baxata tanka Inna ba, Inna ta bude kofar parlon dake sama ta shiga, Ganin Imaan ta ki shigowa ta fixgota a fusace ta nufi dakin Mujaheed da ita, Imaan dai sai bin ta take, kwance Mujaheed yake saman gado idonsa rufe, Inna na kallon empty robber din drip dake sakale ta rike ha6a tace "Ka ji jarababbu mayu, wai an sa masa ruwa yana daki, alhalin ga