Showing 201001 words to 204000 words out of 303099 words

Chapter 68 - Imaan Book 1 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

1653

dai kasa da shi" murmushi Safeenah tayi ta mike ta fita dakin dai dai fitowar Mujaheed daga bedroom dinsa, rungume sa tayi tana shigewa jikinsa tace "What should make for breakfast sweetheart?" Tabe baki yyi ya kauda kai. Sosai Imaan tayi wani fresh tayi kyau ta dalilin gyaran da aka fara mata, har wani sheki da glowing skin dinta yake, duk ta gifta ka dama kamshin da xaka ji na musamman ne, a haka kuma take fita tayi jarabawa kullum, tun biki na saura sati biyu dama wayarsu ya ragu sosai da Sadeeq, yawanci kuma ita ke kiransa ma, shi ko sai dai ya bi miss call dinta. Yau Wednesday Imaan na dawowa daga exam bayan tayi wanka ta sauya kaya Inna ta xubo mata abinci da yaji nama ta ajiye mata a kusa da ita tace "Ni dai wai yaushe xa ku gama wannan kaddararren jarabawan ne ki nutsu waje daya a maki gyaran nan cikin kwanciyar hankali, wannan ae fitina ne ana gyara yana bin iska tunda kullum sai kin fita..." Imaan na kallon abincin da Inna ta ajiye mata tace "Ni fa bana jin yunwa" Inna ta kalleta da sauri tace "Ni dai na shiga uku da wannan 'ya ta Bukar, ko kumallon kirki fa baki yi ba daxu, a haka xa a kai ki gidan Sadeeq din nan da sati biyu a rame duk k'ashi a wuya?? Ni dai ba ruwana bari Amina ta shigo tunda Aisha ta sallama mata ke gaba daya" Imaan ta tura abincin xata kwanta kan kujera a fusace Inna tace "Ni fa bana son a dameni gaskiya sai ince ki tattara kayanki ke da mata mai gyara ku koma bangaren ku yanxu nan, ya xan dinga maki magana kina walakanta ni, dama katuwar mata mai gyaran jiki ce tace ki ci abinci kafin ta dawo taje siyo wasu kayayyaki a kasuwa ta dawo, to idan ta dawo ba ki ci ba fa..." Imaan tace "Inna to ko dai yaya ba shi da lafiya ne har ynxu?" Bude baki Inna tayi tana kallonta da mamaki, can ta xauna tayi tagumi a hankali tace "Naga abinda ya isheni ni Asabe, waye kuma Yaya??" Imaan ta turo baki ta dauke kai, Inna tace "Wai akwai abinda ya hada ki da Mujaheed ne bayan kasancewar Ubansa wan ubanki? Akwai wani dangantaka tsakaninku ne dama da ban sani ba? Wato kwana biyu shiru bai shigo ya takura ki ba shine duk kika damu tunda ke gantalalliya ce, toh sai ki tashi ki tafi gidansa, Toh wai ma ina ruwanki da wani yaya ke da xa ki yi aure nan da kwana sha biyar? Ko dai akwai ajiyar ki a gunsa ne bai baki ba kafin a kai ki daki in kirasa ya baki?" Imaan ta wani hade rai tace "Toh kawai daga tambaya? Naga ya dade bai xo ba kuma ba haka yake ba" Inna tace "Toh idan lalacewa yyi ya fara hakan fa?? Ko idan ya xo me xai bani banda ya tsokane ki ya cuce ki ya wuce don ma naga tunda yayi aure yyi hankali ya daina sa ki kuka, Ke dai ki dinga jin tsoron Allah kiyi ta kanki ba ruwana, to ni ko shekaranjiya na sa Ummi ta kira min shi katon ya ki dauka, wa ya sani ko fushi yake na daina xuwa gidansa, sai kace gidan aljanna Allah na tuba, ni dai ba ruwana wllh" daga haka Inna ta shige daki, imaan ta bi ta da harara ta jinginar da kanta da kujera bata ce komai ba.... Ana saura kwana 7 biki Imaan ta gama jarabawa kasancewarta science student, Maimoon da Mariya kuma nan da kwana shidda xa su gama jarabawan don art class suke, yau kusan kwana hudu basu yi waya da Sadeeq ba, bai kirata ba ita ma bata kirasa ba, tana bedroom din inna bayan la'asar hannunta rike da hisnul Muslim wayarta ya fara ring, daukar wayar tayi tana kallon mai kiranta, ganin number Sadeeq ta daga ta kai kunne tayi shiru, shirun shi ma yyi na kusan second goma sannan yace "How are you?" Murya can ciki tace "Am good" yace "Ina waje" ta kalli agogo bata dai ce komai ba, yace "Or are you busy?" Tace "Ni ba bari na ake ina fita ba..." Ya d'an yi shiru sannan yace "What did you mean?" Tace "Bana fita" yace "Ohk gida ake biyo ki da papers din ki kenan?" Turo baki tayi tace "Waye ubana da xa a biyo ni gida da papers?" Yace "What exactly are you trying to say?" Kin cewa komai tayi, Yace "Ohk then kar ki fito..." Xai katse wayar frnd dinsa Saleem dake tsaye gefensa jikin motarsa ya amshi wayar ya kai kunne yace "Haba amarcy ba dadewa fa xa kiyi ba, ki d'an fito pls, just few minutes" a hankali Imaan tace "Toh" Saleem ya katse wayar yana kallon Sadeeq yace "Amare fa lallaba su ake basa laifi Dr" Sadeeq dai bai ce komai ba yana rungume da hannunsa, Saleem yyi murmushi yace "To saki ran kafin ta fito mana" Nan ma dai Sadeeq bai tanka sa ba, Hijab Imaan ta saka sai dai ba har kasa ba, ta fito parlor ta sanar ma Inna sadeeq na kiranta a waje, Inna dake xaune parlon tare da mai mata gyaran jiki suna hira sai kallon takwarar tata take, can a hankali cikin sanyin murya tace "Ashe dama haka kike da kyau ban sani ba Imaan?" Dariya sosai mai gyaran jiki ta shiga yi tana kallon Inna dake sa ta nishadi tun xuwanta, kwata kwata bata gajiya da fadan Inna da labaranta masu kai da marasu kai, ga uwa uba tsaftarta, komai na Inna burgeta yake, Imaan bata san lkcn da tayi murmushi ba bata dai tanka Inna ba ta nufi kofa ta fita, Inna na kallon mai gyaran jikin tace "Allah kuwa yar nan, dubi fa yanda take walkiya da kyalli, ga kamshi kaca kaca ta ko ina a jikinta, duk inda ta gilma sai ya kamu da kamshin da take yi, ni dai xan kara maki dari biyu da tsinkin sabulu a kudin da xa su biyaki, gaskiya kin fito min da jikata, kai har dambun nama xan maki ni dai" Matar dai sai dariya take tana ma Inna godiya, Imaan na isa part dinsu ta shiga don daukan hijab mai tsayi, Ammi ta fito daga kitchen jin an bude kofa, Imaan ta gaisheta sannan ta nufi dakinta, Ammi ta bi tada ido, ba a dau lkci ba ta fito sanye da hijab har kasa, tana kallon Ammi a hankali tace "Ana kirana a waje ne..." Shiru Ammi tayi tana kallonta, hakan yasa Imaan ta sunkuyar da kanta, Ammi ta karaso kusa da ita ta sa ta xauna saman kujera ta xauna kusa da ita tace "What's wrong with you Imaan?" Imaan ta kalleta da sauri tace "Ba komai fa Ammi" Ammi tace "Noo there is something kar ki ji komai ki gaya min..." Imaan ta girgixa mata kai a hankali tace "Da gaske ba komai Ammi...." Ammi tace "Toh shikenan, but don't forget baki da wanda ya wuce ni a duniya, idan baki gaya min damuwar ki ba ban san wanda xa ki gaya ma ba" Imaan ta sunkuyar da kai tana murmushi tace "Idan akwai xan gaya maki ai Ammi" Ammi tace "Toh ki kwantar da hankalin ki and keep praying, kar ki gaji da addu'a, kuma ki dinga cin abinci sosai kin ji" murya can kasa Imaan tace "Toh nagode Ammi" Ammi tace "Ko me kike bukata ki kirani a waya ki sanar min" Imaan tace "Toh bari in je ana jirana" Ammi tace "Toh ki kame kanki" mikewa Imaan tayi ta nufi kofa Ammi ta bi ta da kallo har ta fita ta kulle kofa. Tunda Imaan ta iso part din su Maimoon Umma dake xaune tare da Hajiya Balaraba kan fararen kujeru take kallonta ko kiftawa babu, ta sunkuyar da kai ta gaishesu a hankali Hajiya Balaraba ce kadai ta amsa a dakile, tuni kamshin da take ya daki hancinsu gaba daya, har ta fita gate basu daina kallonta ba, Da ba don Saleem da ya ki barin sa ba da tuni Sadeeq ya bar wajen ganin har bayan minti goma bata fito ba, tana fitowa sau daya ya kalleta ya ci gaba da danna wayarsa, Saleem ya mata murmushi har ta iso inda suke ta tsaya a gefe a hankali tayi masu sallama sannan ta gaishesu kanta a kasa, Saleem ya amsa yace "Hope an gama exams lfya?" Tace "Alhmdllh" Sadeeq ya maida wayarsa aljihu yana kallonta ta cikin glasses din idonsa a takaice yace "Wani shirin xa ku yi a nan gida?" Shiru tayi da farko, sai kuma ta kallesa taga wani direction yake kallo daban, tace "Nima ban sani ba" yace "Ohk then, on Thursday xa ayi dinner...." Yana magana ya bude mota ya fiddo hadadden IV mai yawa sosai ya mika mata ta risina ta amsa, shi dai bai yarda sun hada ido ba, yace "I think that's all, dama sbda IV din na xo, if there is anything I will call and let u know" daga haka ya bude driver seat ya shiga, ita dai sai kallonsa take, Saleem na mata murmushi yace "Toh mun gode amarya, ki shiga ciki xa mu koma" tayi murmushin karfin hali ta juya ta nufi gate, Saleem ya xaga ya shiga front seat, Sadeeq ya tada motar suka bar layin, suna hawa kan titi Saleem yace "Plss ka rage wnn xuciyar Sadeeq... I don't like the way u treated her gaskiya" Sadeeq dai sai driving dinsa yake bai ce masa komai ba, Saleem ya tabe baki ya fiddo wayarsa yana dannawa, Sadeeq yace "Raina min hankali take" Saleem yace "Meye abun rainin hankali" a d'an fusace Sadeeq yace "Baka ji abinda tace ba kenan, wai bata san abinda xa su yi ba a gida na biki, wato babu events da xa su yi kenan take nufi, which is a lie" Saleem ya tabe baki yace "Duk wannan xumudin da ka dinga yi kwanki kafin a saka bikin duk naga babu shi yanxu Sadeeq" Sadeeq ya rage gudun da yake yana shafa kansa a hankali bai dai ce komai ba....




*Imaan isn't for free* it's 300 via


Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788




72......



Ranan lahadi da karfe sha daya Mama Hadiza ta iso gidan tare da autar ta Maryam, a part din su imaan suka sauka as usual, sai bayan azahar sannan suka taho part din Inna, Inna dake xaune ta gama hada ma Imaan kwadon rama da ya ji kayan hadi a bowl kenan tayi masu kallo daya ta dauke kai ta rufe bowl din raman ta ajiye a gefe, Maryam ta tabe baki ta xauna tana kallon TV, Mama Hadiza ta xauna kusa da Inna tana murmushi tace "Sannu Innata" ba tare da Inna ta kalleta ba tace "Yauwa, a rufe min kofata kada k'uda su biyo bayan ku su shigo min parlor" Mama Hadiza ta mike ta rufe kofar ta dawo ta xauna tana murmushi tace "Ina yini Inna? Fatan mun same ku lafiya" Inna tace "Lafiya lau, ai naji labarin tun sassafe ku ka shigo nan dai ne ba ku xo ba sai yanxu" Mama Hadiza tayi dariya tace "Mun d'an kintsa ne Inna, ya shirye shirye?" Inna tace "Atoh suna can suna yi, ko shawara ma basa yi da ni wllh ban ya ake ciki da maganan bikin ba, nasan dai ta Rasulu xata gayyato kawayenmu gaba daya sai a kafa mana katon rumfan nan da kujeru mu xaxxauna a tsakar gida" Mama Hadiza ta sunkuyar da kai tana murmushi, Inna na kallon Maryam tace "Toh ita wancan har yau ba manema ne yarinya ta xama sangamemiya ban ji ana batun aure ba Hadiza, kina gaba tana biye da ke fa a baya" Maryam ta hade rai ta gaisheta, Inna tace "Lafiya lau, baki da samarin ne?" Maryam dai bata ce komai ba ta dauke kai, Mama Hadiza dai sai murmushi take tana kallon uwartata, Inna ta tabe baki tana gyara daurin dankwalinta a hankali tace "Ni dai ba ruwana" Mama Hadiza tace "Toh Ina amaryar, ango dai shi ya dauko mu airport daxu?" Inna tace "Isuhu ai ya lalace ya daina shigo min nan kwata kwata sai dai mu ci karo a tsakar gida, Ita kuma Imaan suna can bandaki tare da mata mai gyaran jiki, ke kya ce canja mata fata xata yi, ni kada garin neman ido a rasa gira a kona min jika in shiga uku, iyayin matar yyi yawa wllh, gashi duk tayi ta ajiye min kaya ta ko Ina kamar tababbiya, ni ko in tattara in jibge mata su a kan katuwar jakarta, ni dai na gaji wllh" Dariya Mama Hadiza ta dinga yi, can tace "Mujaheed fa inna?" Inna ta kalleta tace "Ai Mujaheed ya daina xuwa gidan nan, ni na fi wata ma ban gansa ba, ba laifin xaune balle na tsaye ban san me na masa ba ya dauke kafa" Mama Hadiza ta fiddo wayarta a jaka tace "Toh yanxu ai dole ya xo, jiya ma mun yi waya da shi kafin in taho..." Tana magana tayi dialing number Mujaheed, har ya gama ring bai dauka ba, Inna tace "Atoh, ko dai an sace wayar tasa ne, nima har na gaji da kira ba a dauka fa" Imaan ce ta fito daki sanye da Hijab har kasa, ta wara ido ganin Maryam ta nufeta da sauri ta rungume ta cike da jin dadin ganinta, Maryam ta wara ido tace "Waoww sis kinga yanda kike glowing kuwa? Wllh kin yi kyau sosai" Imaan na murmushi ta koma gun Mama Hadiza ta durkusa ta gaisheta, Mama Hadiza ta jawota jikinta smiling broadly tace "Maa sha Allah, my daughter kinyi kyau sosai, ya shirye shirye" Imaan ta boye fuskarta jikinta a hankali tace "Lafiya lau mama" Inna tace "Ai dama ita Imaan da kyanta, wannan gyaran kyanshi dama Ummi, ita ce mummunan gidan, gaskiya ban san inda Rukayya ta samo ta ba..." Dariya Mama Hadiza tayi tana kallon Inna, Inna tace "Allah kuwa" Mama Hadiza na kallon Imaan tace "Toh tafi ki goge jiki ki shirya" Imaan ta mike tana murmushi ta wuce daki Maryam ta bi ta da kallo don kyau ba na wasa tayi ba. Imaan na xaune tare da Maryam a bedroom din Inna bayan la'asar, Maryam dake ta kallonta a hankali tace "Kina nufin ba events da xa ayi Imaan?" Imaan ta bude hannu tace "Nima ban sani ba sai dai ki tambayi Maimoon, daxu dai ya kawo IV, su xa suyi dinner" Maryam tace "Toh dress code fa? Kuma wani kayan yace xa ki sa?" Imaan tace "Oho ni bai gaya min ba" Maryam tace "Kamar ya, ba ku shirye shiryen tare ne?" Imaan ta tabe baki kamar baxata ce komai ba, sai kuma tace "Ni ko waya fa bama yi" da mamaki Maryam tace "Saboda me?" Imaan tayi shiru tana kallonta, Maryam ta kamo hannunta tace "Talk to me, what's happening?" Imaan ta sauke idonta tace "Nima ban sani ba, baya kirana sai dai in ni na kirasa, kuma ba xuwa yake ba" Maryam ta xaro ido tana kallonta da mamaki, Imaan ta d'an yi murmushi tace "In xubo mana abincin ynxu?" Maryam tace "Plss mu yi magana ki ajiye batun abinci, toh ke kina ga babu abinda kika masa Imaan?" Imaan ta girgixa kai a hankali tace "Ba abinda na masa wllh, he just changed all of a sudden, I don't know why...." Sai kuma tayi shiru lkci daya hawaye ya kawo idonta, Maryam ta kasa daina kallonta lkci daya jikinta yyi sanyi, can cikin sanyin murya tace "Kuma kin tambayesa abinda kika masa? Kila kin yi offending dinsa baki sani ba" Imaan tace "That doesn't warrant him to change his attitude, ko don yaga few days ya rage a daura mana aure shi sa yake min haka" sai kuma ta fara kuka a hankali, Maryam taji gaba daya hankalinta ya tashi ta rungumeta tace "Plss kar kiyi kuka, we have to find out why d sudden change of attitude, be strong plss" Imaan dai bata ce mata komai ba, bayan wani lkci ta mike a hankali tace "Bari in xubo mana abinci" daga haka ta fita dakin. Bude Ido Sadeeq yyi don ganin wanda ya shigo masa bedroom dinsa that is almost out of bound for everybody except his mum, Mikewa xaune yyi yana kallonta, Mummy tace "Sai yaushe xaka kai masu kayan da ka bari parlor na ga lokaci na ta wucewa Abba, today is Tuesday, or do they have any other alternative?" Yace "Mum xan ba Mariya ta kai anjima" Da mamaki Mummy tace "Mariya kuma, kaga ina involving din su a harkata a gidan nan?" Sadeeq ya koma ya kwanta yace "Kawarta ce fa Mum, ta san gidansu ai, I don't think I am going out today" Mummy tace "You tell me what's wrong with you this days Sadeeq, meye matsalar ka" Mikewa xaune yyi yace "Mummy frankly speaking gaba daya naji bana son auren nan kuma, am I even supposed to get married now? Isn't it too early? Sure Ina sonta amma bana son auren ynxu gaskiya" Wani kallo ta dinga masa, kafin tace "You are stupid..." tashi yyi ya wuce bathroom ya rufe kofar gbam, ta fi minti biyar tsaye dakin mamaki fal xuciyarta kafin ta juya ta fita. Sadeeq ne xaune parlon Dad dinsa da yammacin ranan, tun shigowar sa parlon bai yarda ya daga kansa ba, Mummy ma na xaune parlon sai kallonsa take, Alhaji Ahmad Bulasawa dake tsaye ya gama duk fadan da xai yi kamar xai ari baki daga karshe ya xauna yana kallon Sadeeq da kyau yace "If you think I have a son that will tarnish my image here in my mother's land... you are mistaken Abubakar, ban haifi wannan d'an ba, kindly get out from my sight now, aure ba fashi tunda ba wani ya nema maka yarinyar ba, kuma ba wani yace


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login