Showing 132001 words to 135000 words out of 303099 words
mu yi kamar xa mu bi su da jakar su sai mu wuce" Maryam tace "Toh dauko mu tafi" Imaan ta dau jakar Inna ta mika ma Maryam na ta rasulu, kallon Mujaheed tayi taga idonsa na kansu, ta dauke kai tana xaro ido tace "Maryam kin san Yaya kallonmu yake" Maryam ta kallesa taga still kallonsu yake duk da liki da mutane suka taru wajen suke masa da Safeenah, Maryam ta koma ta xauna tace "He is suspecting us Seriously, kin san me xai faru?" Imaan ta girgixa kai, Safeenah ta bude jakarta ta ciro new note din naira dari dari tace "Gashi ki tafi kiyi masu spraying, kafin ki dawo na fita gun mota sai ki sameni da sauri, but before then Bari in canxa seat" Imaan ta nufi can gaban hall din hannunta rike da tulin kudin, su Maimoon, Ummi, Rahma da wasu kawayen Safeenah da yan uwanta da suka sha gold sai cashewa wa suke da wakar jarumar mata da ya cike hall din Lol.... Safeenah ma na tsaye tana rawa gently tana kallon Mujaheed with love, shi ko yana tsaye kamar statue yana jujjuya wayar hannunsa, dance floor din kuwa banda dubu dubu babu abinda xaka gani a kasa sae few five hundred notes, Imaan ta isa kusa da su ta ki yarda ta kallesa tana kallon Safeenah dake rawa ta fara mata likin a hankali, kallon cikin ido Safeenah ke mata haka kawai Imaan taji gabanta na faduwa bata sake yarda sun hada ido ba tana ci gaba da yi mata likin kudin, Bandir din dubu daddaya Mujaheed ya ciro ya nufi gun kanninsa da suka dage sai cashewa suke barin Maimoon, Ya fara manna masu da daddaya da daddaya, Safeenah ta bi sa da wani harara ganin kanninsa kawai yake lika ma, Imaan na lura da abinda tayi haka yasa taki lika mata kudin hannunta gaba daya ta koma gun su Maimoon ta fara masu likin, Mama Hadiza ta xo ita ma tana ma su Maimoon da Imaan likin kamar su kadai ne a wajen tana murmushi, facing din Imaan Mujaheed yyi yana kallonta ya fara xuba mata one thousand naira note din a hankali, kasa kallonsa ta yi kanta a kasa, can kuma a hankali ta fara lika masa na hannunta, Mama Hadiza ta juyo ta dinga xuba masu na hannunta ita ma, Aunty ma haka, da abokansa gaba daya da suka cika wajen lkci daya, Safeenah ta ji kmr ta nutse don ba kowa wajenta sae flowing gown din jikinta, duk aka koma ana ma Mujaheed da Imaan liki, Umma sai xare ido take tana kallon ikon Allah, kowa ya xo sai ya fara ma Imaan da Mujaheed liki kamar ita ce amaryar, don wasu ko noticing Safeenar ma basu yi ba balle su san ba ita suke ma likin ba, Imaan dai ta dawo amarya a wajen duk kunya ya isheta.... Sai da Mujaheed ya manna ma Imaan gaba daya note din hannunsa yana kallonta, ita dai sai kokarin barin wajen take amma saboda yanda aka kewayesu ta rasa hanyar fita, da kyar dai ta samu ta lallaba ta fita taron xuciyarta na bugawa, tana kallon inda Maryam ke xaune taga har ta fita, da sauri ta nufi door din fita hall din ta fice fittt, Maryam na ganinta ta dallo mata fitilar motar ya Yusuf, xata tafi gun motar taji an fixgota, ihu tayi a tsorace ta juya xuciyarta na bugawa.....
*Imaan isn't for free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
Afuwan for the late and short update, am not feeling too well... Thanks in anticipation for understanding.
47....
47. Imaan
Imaan kamar xata yi kuka tace "Ya Yusuf dubi fa yanda ka ban tsoro...." Yusuf yace "Ehh gwara ki ji tsoron, ina xa ku je?" Turo baki tayi tace "Gida mana, mun gaji" yana kallonta da kyau yace "Karya kike yi, ban kuma san lkcn da kika fara karya ba, and I need not to remind you the consequence of lying Imaan" shiru Imaan tayi tana kallonsa, ya d'an hade rai yace "birthday din makaryacin saurayin ki xa ku tafi koh, ke kin san waye Sadeeq kuwa? Kin san irin mutanen da yake abota da? Kinsan abubuwan da xa su faru gun birthday din nan da kika kwallafa rai sai kin je, why all of a sudden kika canxa from the decent Imaan da muka sani kika dawo mara ji?" Fuska daure yayi mata tambayar, kamar xata yi kuka tace "Ni fa ba birthday nace xan je ba, ai ba yau bane birthday din, kuma I only want to get him a gift now coz I know I might not get it tomorrow, ban ce lallai sai na je birthday ba" Kallonta ya dinga yi ta sunkuyar da kai a sanyaye, wayarsa da yyi vibrate ya kalla yyi replying text din da ya shigo sannan ya tafi gun motarsa ta bi sa da kallo, Maryam ta langwabar da kai tana kallonsa, yace "Ke ce ke xugata koh Maryam?" Xaro ido tayi tace "I don't get you" yace "Idan ke baxa ki gaya mata gaskiya ba why encourage her??" Maryam tace "Is there anything wrong with her getting her bf a birthday gift, we are in a civilized world Yaya Yousuf...." Yana mata wani kallo yace "Bani makulli na" Mika masa makullin sa tayi ta fito daga motar, Imaan dai sai kallonsu take ta gefen ido, ya juya ya koma inda take yace "Koma ciki..." A hankali tace "Toh ni gida xan tafi..." Ya daure fuska yace "Koma ciki nace" turo baki tayi ta juya ta koma cikin hall din, Maryam ta wucesa rai bace ta koma cikin hall din ita ma, Imaan na shiga ta tafi inda suke xaune tana kallon Mujaheed dake kallonta ta xauna, Maryam ma ta xauna a fusace tace "Gaskiya guys din nan sun fiye takura mutane, haka suke da sa ido dama, I won't tolerate this shit assuming we are staying together with them" Imaan ta tabe baki tace "I don't even know what's their business with me, sun dameni wllh" Maryam tace "Kece kike nuna kina tsoronsu ai" Imaan kamar xata yi kuka tace "Toh ni yanxu ya xanyi plss?" Shiru Maryam tayi tana kokarin nema masu wani option din, Yusuf dai na xaune d'an nesa da su yana kallonsu lkci lkci, ana fara cin abinci Maryam ta mike ta tafi ta debo masu yar fried rice ta cika nama ta dawo tana kallon Imaan tace "Let eat" Imaan ta girgixa kai tace "Am not eating" Har aka tashi dinner din Imaan bata da walwala, gashi da ta kalli Mujaheed sai ta ga kallonta yake, Tasowa Yusuf yyi ya taho inda suke ya ajiye ma Maryam makulli yace "You two should wait for me..." Daga haka ya wuce, Maryam tayi tagumi murya can kasa tace "Amma gaskiya wa ennan mutanen mayu ne, may be they know what we are up to" Ita dai Imaan bata ce komai ba idonta na kan Safeenah dake tahowa tare da Mujaheed kawayenta na biye da su a baya, hada ido suka yi da ita Safeenah ta wani daure fuska, Imaan ta dauke kai hade da tabe baki, sai da taga sun fita hall din sannan ta mike Maryam ma ta mike tace "Kinga hararan da yarinyar ke maki kuwa, did you know her b4?" Imaan tace "I don't know her fa" fita waje suka yi xuwa gun motar ya Yusuf, Aunty na kallon Yusuf a haraba hall din tace "Ka ajiye Mama Hadiza da su Hajiya Lailah a gida Yusuf..." Yusuf ya d'an bude ido amma bai ce komai ba, da sauri Imaan ta dauke kai tana wani murmushi, xagawa yyi ya budu front seat yana kallonta yace "Xo ki shiga nan" ta d'an xaro ido tace "Ya Yusuf Maryam fa?" Yace "Xata shiga wani motar, bana son musu ki xo ki shiga" Maryam ta hararesa ta dauke kai, A hankali Imaan ta taka ta isa front seat din ta shiga, Mama Hadiza da kawayen Aunty biyu suka shiga back seat, ya shiga motar ya bar haraban hall din. Yana parking a compound Imaan bata ko kallesa ba ta bude motar ta fice xata wuce apartment dinsu ta ji muryar Inna bakin gate tana cewa "Iliya Ahmadun bai dawo ba har yanxu??" Mai gadi da ya bar gate bude ganin motoci har uku dake bin bayan motar Yusuf yace "Ehh bai dawo ba Baaba" Inna na hango Yusuf da ya fito daga mota da Mama Hadiza da kawayen Aunty ta fashe da matsanancin kuka, da sauri Mama Hadiza ta nufeta tace "Me ya faru Inna" cikin kuka tace "Me na ma Rukayya a duniyar nan xata saka min da haka, ni fa na yarje ma Ahmadu aurenta tun tana yar jagaliya, yar yagalgal tana yawo da kodadden zani da yagaggen Hijabi" Mama Hadiza tace "me ya faru" Inna ta sharen hawayenta bata tanka ta ba tana kallon ta rasulu tace "Mu je kawai" ta rasulu tace "Idan ma kika yarda Rukayya ta kwana gidan nan yau Allah ma sai yayi fushi da mu da bamu dau mataki ba, irin wannan cin mutunci da raini haka? Oh oh tun da uwata Mai salati ta haifeni ban taba gani ko jin labarin irinsa ba, waiii.... Ai wannan babban magana ce wllh, ko kotu aka kai kara ba karamin muhimmanci xa su ba maganar nan ba, kuma da kyar idan ba sai an yanke mata hukuncin kare rayuwarta a gidan yari ba" Inna tace "Toh kun ji dai, ke dai mu je kawai wanda ya ajiyeta a gidan xai dawo duk gidan uban da yaje ya same mu, casun kuma da bamu samu ganin yanda xa a kare ba Allah ya isa xa mu hadu gaban ubangiji...." Ta rasulu na biye da ita tace "Ke ma dai wllh, sai ma kin fada?? Ae wannan a rubuce yake Asabe, abinda ba yafewa xa mu yi ba" Mama Hadiza da su Hajiya Lailah dai suka bi su da kallo. Imaan na kokarin saka kayan baccinta bayan ta fito wanka aka bude kofar dakinta, Maryam ce ta shigo ta tsaya tana kallonta tana murmushi, da mamaki Imaan tace "Ina kika je tun daxu kowa ya dawo banda ke??" Maryam tace "Close ur eyes please" Imaan tayi shiru tana kallonta, Maryam ta hade rai tace "Toh ko inyi wucewata" Murmushi Imaan tayi don sai sannan ta lura da hannunta dake boye a bayanta, a hankali Imaan ta lumshe idonta tace "Toh na rufe" Maryam ta isa kusa da ita ta tsaya tace "Bude ki ga gift da xa ki ba Sadeeq din ki" da sauri Imaan ta bude idon taga wani flower mai kyan bala'i da cards Maryam na mika mata tana jujjuya eye balls dinta, Imaan ta saki baki tace "What's this?" Maryam tace "Gift din da xa ki ba sa mana" Dariya Imaan tayi tace "You are very funny wllh, me xai yi da wannan din" Maryam ta xaro ido tace "Me xai yi da shi fa kika ce?matsalar ku kenan yan Nigeria wllh, ke kinsan Value din abun nan dake hannuna kuwa, kin san mu a turai wannan ya fiye mana kudi da wasu abubuwan rayuwa idan aka xo fannin kyautatawa, wllh I am telling you this sai ya fi son wannan akan kudin da xaki basa ko abinda xa ki siya masa, idan kin basa kudi me xai yi da shi bayan yana da fiye da wanda xaki basa, sai dai ma ya bada kudin kyauta tun bai shiga gida ba, idan kika ce xaki siya masa abu me xai yi da shi bayan bai fi karfinsa ba?? Wannan kam kina basa am telling you xa ki ga reaction dinsa..." Tana murmushi ta kare maganar, Imaan dai sai kallonta take nan kuwa a xuciyarta tunani take kuma fa gaskiyan Maryam tunda shi ma a turan ya taso xai so gift din sosai, Maryam ta kai mata flower din hancinta tace "Smell it" lumshe ido Imaan tayi jin wani cool scent da flower din yake, ta amsa tana murmushi tace "It smells nice, I love you Maryam" ajiye flowers din da card tayi gefen gado ta rungume ta. Umma na dawowa daga hall din dinner tare da kawayenta bayan sun sallami mutane gaba daya dama bata yarda ta shiga gidan ba, kawayenta su Hajiya Saude ne kadai suka shiga cikin gidan tunda haka dama suka shirya tun a hanya, Umma ta dau wayarta ta nemo lambar daddy tayi dialing, ba a dau lkci ba ya daga, tayi kasa da murya ta gaishesa ya amsa yace "Lafiya dai koh Hajiya Rukayya" Tana yake tace "Lafiya Baban Imaan, nace kana gida kuwa?" Daddy yace "Ehh na kusa gidan yanxu, driving nake" Umma tace "Toh Ina ma kofar gida, xan jira ka iso" yace "Ohk" daga haka ya katse wayar, Daddy na shigowa layin ya hangota tsaye d'an nesa da gate din gidan, parking yayi kusa da gidan ya fito yana kallonta yace "Lafiya kuwa?" Tace "Toh lafiyar kenan dai..." Yace "Mu shiga ciki toh" da sauri tace "A'a bari dai in maka bayanin a nan" Ya rungume hannunsa yana kallonta yace "Toh ina ji" Tace "Wllh Baban Imaan daxu ne Inna taje wajen da ake dinner...." Da mamaki Daddy yace "Yanxu sai da taje dinner din nan duk abinda muka gaya mata??" Umma ta bude hannu alamar ai shine, tace "Kuma da aminyar nan tata Baaba ta rasulu, wllh Abban Imaan sai kaga abinda taje ta dinga yi" Daddy ya girgixa kai yana kallonta, Umma tace "Wata kawar amarya na tsaye gaban jama'ah tana bada tarihin amarya in gaya maka sai Inna ta tafi ta sami yarinyar ya amshe microphone ta fara xaginta wai wani tsinannen tela ta ba kudi ya mata dinki, Kai maganganu dai babu dadin ji Abban imaan, ai su Mama Hadiza da Hajiya Aisha na wajen ni ba sharri na mata ba, wllh kunya kamar in nutse, dama imu imu ne abun xai xo da sauki amma fa ga dangin amarya sun cika wajen kuma Yan babban gida, bayan ta gama da yarinya mai bada tarihi ta tafi ta kwashe duk abinda aka ajiye ma amarya da ango a gabansu ta wuce ta bar wajen sirara, haka ta dinga ma mutane fada wai kada a xubda datti sun xo cin shinkafa da miya da kaza mayunwata kawai, maganganu dai ga su nan xar kayan kunya xar takaici Abban Imaan, yanxu fisabilillahi hakan ya dace?" Girgixa kai kawai daddy ya dinga yi yana salati, Umma tace "Toh ganin abun sai gaba yake sai naje na sameta nace toh fa ga ruwa can ya cike parlonta ta bar pampon bandaki a bude, shine Inna ta bar wajen ba shiri da kawarta Baaba ta rasulu, yanxu nayi laifi a nan Abban Imaan?" Daddy yace "Aa dai dai kenan" Umma tace "Toh nasan yanxu suna can kila ma ta tara jama'ah ana jirana, kuma ko me xata gaya ma Abbansu Mujaheed wllh yarda xai yi ya xauna a kai, shi sa ma nace bari in maka bayani tukun" daddy ya sauke ajiyar xuciya yace "Toh Allah ya kyauta, kuma hakan da kika yi shine dai dai, don da ba don haka ba baxa su bar wajen ba, kada ki damu nasan abinda xan yi, kiyi wucewar ki ciki" Umma ta d'an yi murmushi tace "Toh ngd Abban Imaan da ka fahimce ni" cikin gidan ya nufa ta bi bayansa bayan ta sauke boyayyen ajiyar xuciya. Inna ce xaune parlonta kan tabarma ta daura kafa daya kan daya fuskarta shabe shabe da hawaye tana fyace majina da hankicin hannunta, ta rasulu dake xaune kan darduma ta girgixa kai kamar xata saki kuka tace "Ni Ahmadu babu abinda ya fi min ciwo irin yanda muka dinga yawo muna xaga garin kaduna a adaidaita sahu muna neman wajen casu bayan mun dawo mun ga karya Rukayya take, daga karshe sai dawowa gida muka yi bamu gane wajen ba, mai adaidaita na bala'i mu ma muna bala'i, haka muka yi asaran dari biyun mu don da kyar mai adaidaitan ya amshi dari biyun wai sai dari shidda xa mu basa, wllh mune har sabon kawo neman wajen casu, babu wajen casu babu labarinsa" Mujaheed dai na xaune parlon sai kallonsu yake, Yusuf ma haka, Aunty da Ammi da Mama Hadiza ma duk suna xaune, Abba dai kansa na sunkuye yana sauraronsu, Cikin kuka Inna tace "Duk a kanmu sanyin daren yau ya kare muna yawo a daidaita neman wajen casu kaman yan iska, kuma ace inyi hakuri saboda ba a san ciwo na ba, ni wllh yau duk sai mu tattara mu tafi Police station, wacece kuma Rukayya da xata min wannan toxarcin, me aka yi aka yi ta, Rukayyar banxa Rukayyar hofi, ni dai wllh Ahmadu na xuba ido yanxun nan in ga matakin da xaka dauka kan katuwar nan, bikin ma ni sai in iya cewa a dage sai an bi min hakkina da na Aminiyata ta rasulu tukun, shkkn haka aka kare casun yau banda mu, ba mu ci Yar shinkafa da kazar da aka raba ba" sai kuma ta fashe da matsanancin kuka, Yusuf ya sunkuyar da kai yana murmushi, Ta rasulu na matsar kwallan da ya cika idonta tace "Ni wllh Asiya bata isa ta min haka ba, don sai dai in sa Muhammadu ya xabi ko ni ko ita...." Sallama aka yi bakin kofa, Inna ta amsa cikin rawar murya tace "Bukar yau dai bamu samu casun bikin Mujaheed ba, Rukayya dai yar iska ce wllh"
*Thanks for the prayers via phone calls and WhatsApp messages fans, Allah bar xumunci, nagode sosai, am feeling a little better in sha Allah*
*Imaan isn't for free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
48.....
Shigowa Daddy yayi parlon yana bin dukansu da kallo, Mujaheed ya mike ya koma kusa da Yusuf, Daddy ya xauna yana kallon Inna yace "Lafiya? Me ke faruwa?" Inna ta fyace majina a hankali tace "Kana ji Bukar?