Showing 192001 words to 195000 words out of 303099 words

Chapter 65 - Imaan Book 1 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

1684

ruwa ya kare..." Bude ido Mujaheed yyi, Inna ta fashe da kuka a hankali ta nufesa tace "Sannu Mujaheed, in sha Allahu babu abinda xai sameka in dai ina da rai, asiri dai ya gama tonuwa na gano komai" shi dai gaba daya hankalinsa na kan Imaan da tayi tsaye bakin kofa ta ki shigowa kuma ta ki yarda su hada ido sai wasa da fingers dinta take, Inna ta xauna gefen gadon tana goge guntun hawayen idonta tace "Kwana nawa da aurenta ka fara jin canji a jikin ka??" Shi dai bai ce mata komai ba har sannan yana kallon imaan, Inna ta juya ta kalleta tace "Ke dai baki da kirki wllh, halin ki abun tsoro ne gaskiya, baxa ki karaso ki gaida sa ba" sai a sannan imaan ta kalli Mujaheed, suna hada ido tayi saurin dauke kai ta karasa cikin dakin ta duka kasa kusa da gadon a hankali tace "Ya jikin Yaya?" Bai tanka ta ba, Inna tace "Atoh, abinda ma da kyar ta biyoni Mujaheed, wllh Imaan bata da imaani, har fa ce min tayi toh ita ce bata da lafiya da xance a fasa kawo kayan aurenta yau sai wani satin sabida baka da lafiya...." Mujaheed dai ya kasa daina kallonta, imaan ta wani hade rai tana kallon Inna, bude kofar dakin aka yi sai ga Safeenah ta shigo da warmer a rufe da plate a hannunta, ko kallonsu bata yi ba ta karasa ciki ta ajiye ta xauna kusa da kansa tana wani yauki tace "Baby ka tashi ka ci ko kadan ne sai ka sha drugs dinka plss, bacci ma ya kamata kayi ka huta bayan ka gama cin abincin tunda sai ltr xa a sa wani drip din" Imaan ta dinga hararanta ta gefen ido, Inna ta tsuke fuska ta rungume hannu tana karanto addu'a a xuciyarta tana tofawa a duk angles din dakin, Mujaheed ya mike xaune ya cire duvet din jikinsa yana kallon Safeenah yace "You don't worry anjima xan ci, na sha tea yanxu" tace "Toh ayi maka pepper soup din ko appetite dinka xae dawo?" Da kamar baxai ce mata komai ba sai kuma yace "Ohk" Ta mike tana wani cat walking ta nufi kofar fita tana karkada jiki, Imaan ta wani tabe baki ta dauke kai fuska daure, Safeenah na fita Inna ta mike ta dau abincin ta bude window ta xaxxage gaba daya downstairs ta juyo tana kallon Mujaheed murya can kasa tace "Mayya ce Mujaheed...." Bude baki yayi yana kallonta da mamaki, ta kyabe baki ta cire Hijab dinta ta linke tace "Jira in je in soya maka wani gaskiya, Allah ba batun wasa ba an gano mayya ce amma kada kace mata komai tukun, a hankali ake kama barawo, anjima ta Rasulu tace min xata xo nan....." Bai san lkcn da yyi murmushi ba bai dai ce mata komai ba, kofa Inna ta nufa fuska daure ta fita xata kitchen ta masa girki, Imaan na ganin haka ta mike da sauri ta nufi kofa yace "Fatima" tsayawa tayi sai dai bata juyo ba, jin bai ce komai ba a hankali ta juyo tana kallonsa, taga kallonta yake, sosai gabanta ya fadi, kamar xata yi kuka tace "Na'am" jin yyi shiru ta karasa kusa da gadon ta durkusa tace "Ga ni" ya sauke idonsa daga kallonta yace "Ya preparation na exams?" A hankali tace "Lafiya lau, how are you feeling now?" Yana kallonta yace "Dama kin san bani da lafiya ashe?" Tace "Aa ni Inna ce ta gaya min daxu Allah ban sani ba" Bai ce komai ba hakan yasa tace "Xan je in taya Inna" yace "Promise me baxa ki wuce gida ba daga nan" murmushi tayi ta boye fuskarta da gado don abinda ke ranta kenan, ji tayi ya kamo hannunta ta dago da sauri yace "Kar ki tafi yanxu Imaan" ta turo baki tace "Bayan Umma tana nan, kuma matar ka sai wani hararana take yi, ni dai wucewa xan yi" yace "Toh kiyi xamanki a nan" ta xaro ido tace "Kaga Inna ta wuce fa, salon idan matarka ta shigo ta xageni ko" yace "Kina dai son wucewa kawai" tana murmushi tace "Toh naji baxan wuce ba, amma me ke damun ka Yaya? Ji fa ka rame sosai" Ya jinginar da kansa da gado murya can kasa yace "Ban sani ba" ta langwabar da kai tace "Kana likita kuma baka sani ba, or is about our last talk, I mean about the lady..." Shiru yyi yana kallon Ac dake aiki a dakin, murya can kasa yace "Yau xa a kawo kayan ki koh?" Dariya tayi ta boye fuskarta tace "Uhm nima ban sani ba" jin bai ce komai ba ta dago tana kallonsa, kallonta taga yana yi da manyan idanuwansa, ta sunkuyar da kai tana murmushi tace "Ehh yau ne" yace "And u are happy" ta turo baki ta ki cewa komai, sauke kafafuwansa yyi daga saman gadon ya nufi press dinsa ya fiddo gogaggen shirt xai saka a kan singlet da 3 qtr din jikinsa, Bude kofar dakin aka yi sai ga Safeenah, da wani expression ta dinga kallonsa sai kuma ta kalli Imaan a nutse tace "Malama tashi ki fitar min dakin miji, naga alama karuwancin naki ba iya waje ya tsaya ba har gida" Imaan na mata wani kallo tace "Karuwanci kuma? To sai dai in kece karuwa....." Bata rufe baki ba Safeenah ta sauke mata mari tana wani huci tace "Ni kike ce ma karuwa a dakin..." ita ma bata kai karshe ba taji saukan wani wawan mari da yasa ta ji dumm a kunnenta, da kyar ta juya tana ganin stars ta kallesa cikin rawar murya tace "Mujaheed. .." ya kuma wanke ta da wani mahaukacin marin ya fixgota yana huci yace "Kinsan warce kika mara Safeenah??" Safeenah ta xaro ido a tsorace tana kallonsa, sai kuma ta rushe da kuka cikin tashin hankali tace "Yanxu a kan wannan matsiyaciyar ka mareni Mujaheed, a kan wannan sauran ciwon....." Hankada ta yyi iya karfinsa don har sai da ta fadi kasa timm, Yana nuna ta calmly yace "Kece matsiyaciya ba ita ba" Safeenah ta mike da sauri ta fice dakin da gudu tana kuka, Imaan da hankalinta yyi mugun tashi tana kallonsa cikin rawan murya tace "Yaya me yasa ka mareta, ai xan iya ramawa da kai na, why did you slap her, you shouldn't have, beside umma fa na gidan" Mujaheed ya rikota cikin daga murya yace "Did you know what I felt da ta mare ki imaan?? Kinsan abinda naji?? Me yasa xata daga filthy hand dinta ta daura a fuskarki??" Ta dinga kallonsa da manyan idanuwanta ko kiftawa babu, yyi kasa da murya yana sauke numfashi a hankali yace "Wlh da ni ta mara baxan ko daga kai in kalleta ba, why will she slap you Imaan???" Kallonsa kawai imaan take ganin yanda idanuwansa suka kada sosai, lkci daya ya rungume ta ya lumshe ido, a hankali ta kwantar da kanta kirjinsa tana jin yanda xuciyarsa ke bugawa tana shakan daddadan kamshinsa, gently ya dinga tafiya tana jikinsa har ya isa kofa ya sa makulli. Inna na kitchen tana aikin suyan dankali da kwai, Umma ma na kitchen din fuska daure tana dauraye kayan miya da xa ayi ma Mujaheed pepper soup, lkci lkci take xabga ma Inna harara ta dinga addu'ar da ma man gyadan dake kan gas din ya kware a jikinta kowa ya hutu a duniyar, Inna ta kwashe dankalin karshe a mai tana tabe baki tace "Ba ruwana, ni sai in sa Ahmadu ya tattaro min kayana ma in dawo nan gaba daya, don dai in masa girkin abincin da xai ci ransa kadai kar a cucesa, ni a ma kira min Ahmadun in gaya masa jikin Mujaheed ba sauki masu kawo lefen nan su dakata kawai lefe bai fi jikana ba gaskiya" Umma ta kalleta da sauri, sai kuma tayi kasa da murya tace "Lallai kam, ace duk yanda suke da Imaan baya nan xa a kawo lefe da kudin aurenta, abun bai yi ba gaskiya, daxu daxun nan da safe na gama maganan nan" Inna tace "Atohh, ko tsari babu wllh, Ahmadu ya ki saurarata da yake kunnen kashi garesa, ni bari a kara kiransa in jaddada masa halin da na xo na samu Mujaheed a san abun yi" tana fadin haka ta fice kitchen din, Umma ta kashe gas ta bi bayanta da sauri, jakarta ta dauka ta bude ta dau wayarta ta mika ma umma tace "Kira min Ahmadun" Umma ta nemo lambar Abba ta kira ta sa a hands free ta mika mata, Abba na dagawa Inna tace "Toh wllh Ahmadu Mujaheed na nan rai kwakwai mutu kwakwai, ko magana bai iya yi balle ya ci wani abun, idan xa a ji ta nawa to a dakatar da masu kawo kayan nan xuwa sati mai xuwa, aure bai fi rai ba ku ji tsoron Allah Ahmadu.... Mujaheed rai garesa" Abba dake ta saurarenta yace "Sun kira suna tahowa nan da wani lkci, don haka babu fa'idar fasa komai, sannan ba wai jimawa xa ayi ba balle kice, da sun tafi xa mu taho da Abubakar da likita tunda yaro Mujaheed din ya xama" Inna tace "Toh kuwa kun xama abun tsoro wllh, Allah ya mana tsari da ku" daga haka ta mika ma Umma tace "Kashe min wayata maxa, ni dai ina ganin jarabawan rayuwa" Umma ta katse wayar gaba daya rai ba dadi, don tun safe da ta ji labarin xa a kawo lefen Imaan ta gane xancenta bai yi tasiri ko kadan a gun uwar Sadeeq ba, tun sannan ta kasa xaune sai da ta taho gidan Mujaheed don fada ma Safeenah abinda ake ciki, tana xuwa kuma ta iske Mujaheed kwance wai ba lafiya an sa masa drip, abinda ma ya tsayar da su basu fita ba kenan amma da tuni sun baxama neman duk abinda xai sa a fasa shigo da lefen Imaan gida, a hankali Umma tace "Ba a kyauta ma Mujaheed ba amma gaskiya" Inna tace "Toh wa gareni da xan ma magana ya ji, ai Ahmadu ya dauko hanyar lalacewa shi ma, shi dama Bukar bana sa shi a lissafi kwata kwata" Umma tace "Toh ko xaki ma shi yaron magana, naga kuna shiri sosai" Inna ta mika mata wayar tace "Yauwa duba xa ki ga Bulasawa ki kira, ae yana da fahimta, kawai ce masa xanyi Imaan tace tana jin nauyinsa don Allah in masa magana a dakatar da kawo kayan don yayanta bashi da lafiya yana kwance har da karin ruwa leda uku" Umma ta amshe wayar da sauri tace "Toh hakan ma yyi wllh" tana kiran number Sadeeq ta sa handsfree ta mika ma Inna, Inna ta karbe wayarta ta nufi kofar ta fice parlon gaba daya, Umma ta bi ta da wani kallo tana murmushi, dai dai nan Safeenah ta sakko kasa tana kuka sosai har lkcn tana rike da kuncinta, hankali tashe Umma ta nufeta da sauri tana cewa "Lafiya Safeenah me ya same ki?" Cikin kuka sosai tace "Hajiya a kan wannan shegiyar yarinyar Mujaheed xai sa hannu ya mareni har sau biyu, Mujaheed ya rasa warce xai mara sai ni? Mujaheed slapped me???" Bude baki Umma tayi tana kallonta da mugun mamaki tace "Shi Mujaheed din ya mare ki??" can ta juya ta wuce sama kamar xata tashi sama, Sosai Imaan ta rikice jin muryar Umma tana bubbuga kofar dakin kamar xata cire tana kiran sunan Mujaheed, Lkci daya hawaye ya kawo idonta ta rikosa cikin rawar murya tace "Wayyo Yaya ka gani ko" Xaunar da ita yyi gefen gado ya duka kusa da ita murya can kasa yace "Relax now, ba shigowa xata yi ba na rufe kofar" Inna ce ta shigo parlor tana tabe baki tana kallon wayarta, ganin Safeenah na rusa kuka ta isa kusa da ita ta duka tana kallonta da mamaki, can tace "saboda na xubda girkin da kika masa shine kika xauna nan kina kuka? Ke kya yarda a cuci wani naki??" Bata jira cewarta ba ta wuce sama, tana isa parlon Mujaheed ta dinga kallon Umma dake ta jijjiga kofa, hankali tashe tace "Lafiya?? Makalewa suka yi a ciki??" Umma ta ki cewa komai xuciyarta kamar ya fashe ta huta, da karfi Inna tace "Mujaheed???" Mikewa Mujaheed yyi daga durkushen da yyi gaban imaan da taki kwantar da hankalinta jin muryar Inna ya nufi kofar ya bude a hankali, mari Umma ta sauke masa tana huci tace "ita Safeenahr ka daga hannu ka mara???" Wani salati Inna ta xabga tana kallonta tace "Kina da hankali kuwa Rukayya, Mujaheed din kika mara hka???" Muryar Safeenah suka ji tana cewa "Wllh baxan xauna gidan nan ba yau in har sabida wnn matsiyaciyar Mujaheed ya mareni wllh baxan xauna" Mujaheed ya daga kai yana kallonta fuska daure yace "Ki tafi gidan ku sae na neme ki, kar ki kara ko minti biyar gidana...." Inna tace "Fakat, maxa tattara ina ki ina ki kiyi wucewar ki mayya" gwalo ido Umma tayi tana kallonsa kamar yanda Safeenah ma tayi, cike da karfin hali Umma tace "Safeenar kake cewa ta tafi gidansu Mujaheed??" Bai yarda ya kalleta ba a takaice yace "Ehh Umma ta tafi gidansu" juyawa Safeenah tayi da sauri ta fita parlon, Umma ta kasa cewa komai tana kallonsa with shock can ta juya fuu ta wuce, Inna tace "Tunda kema mayyar ce sabida me baxa ki ji haushin koran Safeenah ba, in sha Allahu xamanta ya xo karshe a gidan Mujaheed...." Shiru Inna tayi tana kallon Imaan ganin hawayen idonta tace "Me aka maki kike kuka?" Kin cewa komai tayi ta juya masu baya, Inna na kallon Mujaheed tace "Kasan yau xa a kawo kayanta da lefe, nace su Ahmadu su jira ka ji sauki ayi komai da kai sun ki saurarata... Yanxu ga dai waya ka Kira min Bulasawa na kirasa daxu ban ji yyi magana ba kila kiran ma bai je ba" Imaan ta juya da sauri tana kallon Inna tace "Me xa ki ce masa??" Inna tace "Wannan ba matsalar ki bace sirri na ne da shi" Mujaheed dai na rike da wayar yana kallonta, ganin haka Inna ta kwace wayarta ta juya ta fita xuwa gun mai gadi don ya kira mata Bulasawa, ganin ana wangale gate din ta tsaya sai ga motar Abba, parking Abba yyi ya fito tare da Daddy da kawu Audu da wani frnd din Daddy daga cikin motar, Inna ta bude baki tace "Kaddai ku ce har sun kawo kayan ni Asabe??" Abba yace "Sun kawo har ma sun tafi, an saka biki nan da wata guda dai dai da lkcn da xa su gama xana jarabawa, sun kuma bada sadakinta dubu dari takwas" Inna tace "Toh da kyar idan Mujaheed xai yafe maku, don wahalan da yyi da ita ku da ku ka haifeta ma baku yi ba, amma sbda butulci ku amshi kudin auren yarinya ba shi sbda cuta ta kamasa?? Toh aji tsoron mutum" daga haka ta juya ta wuce ciki fuska tsuke....


*Maa sha Allah, I will take a break till after sallah in sha Allah, thank everyone for being patient with me all this while following the book Imaan, ayi sllh lfya*



*Imaan isn't for free* it's 300 via


Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788



🌟⭐imaan ⭐🌟

70.....


Tun da Inna ta fita parlon Mujaheed ke kallon Imaan dake tsaye ta wani hade rai tana kallon bakin kofa ita a dole Inna ta tafi kiran Sadeeq a fasa kawo kaya, satan kallonsa tayi ganin ynda yake kallonta ta turo baki ta juya xata fita yyi saurin rikota yana kallon eyeballs dinta yace "Don't say anything about what happened between u and my wife to Grandma" kin cewa komai tayi ta kwace hannunta ta fice daga parlon nasa ta sakko downstairs, a nan kuma ta ji shigowarsu Abba compound din gidan da maganganun da suke yi da Inna, Inna ta dawo parlor tana girgixa kai tace "Tunda uwata ta haifeni ban ta6a ganin irin haka ba, su Ahmadu dai sun shiga uku sun lalace tirrrr, yanxu ko Mujaheed kadai bai isa ya karbi auren imaan ba, amma kawai mutane don ba shi da lafiya kuyi masa wannan rashin mutunci, to da kyar idan girman ku bai fadi a idonsa ba gaskiya" Imaan dai sai kallonta take, Inna ta xauna fuska ba annuri tace "Tirrr" Abba yyi sallama bakin kofar parlon ya shigo sannan Daddy da Kawu Audu, Gaishesu Imaan tayi Abba ya amsa yana kallonta yace "Ina Mujaheed din?" Inna ta tabe baki ta dauke kai tana girgixa kafa, Imaan xata wuce sama Abba yace "Ina matar gidan?" Inna ta kallesa da sauri tace "Wace matar gida? Matar gida da ya kora daxu, koko wata daban kake nufi?? ai tuni yace ta wuce gidansu ba wanda bai san mayya bace, daga nan dama ni dai daukansa xan yi mu koma gida ya xauna bangarena ayi ta masa magani har yayi garau" Kawu Audu da ya buda ido sosai yace "Mayya kuma Yaya?" Inna tace "Xancen kake so D'an tsut, tun fa da aka yi auren nan yau lafiya gobe ba lafiya a haka yake kamar mai laulayi, to ina dalili da raina kuma da lafiyata snn ba gantalalliya ba...." Ta kalli Imaan tace "Ke tafi ki kirasa su gane ma idonsu yanda ya koma" Daddy yace "Ni ban fahimci xancen ki ba Inna, ita matar yace ta tafi gidansu ko wa?" Inna na kallon Imaan tace "Ke tafi ki kirasa su gansa bana son dogon surutu da Bukar, don ba hankali isasshe garesa ba wllh, kuma a gaskiya kada Bukar ya sani a bakin duniya ni ba ni na koreta ba da bakinsa yace ta tafi to tunda ba ubanta ya gina masa gidan ba ba dole ta tafi ba, har Rukayya fa a nan na sameta tana masu girki a kitchen daxu..." gaba daya dai sai kallonta suke don har sannan babu wanda xai ce ya fahimci xancenta, Imaan


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login