Showing 243001 words to 246000 words out of 303099 words

Chapter 82 - Imaan Book 1 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

1688

tayi tana kuka sosai tace "Ni wllh Yaya bana son gidan nan, I don't want to stay here, na tsane ta da gaske, baxan xauna ina ganinta ba kullum, I don't like her, bayan ta gama xagi na saura kadan to dokeni kuma kaje kana ta bata hakuri tun daxu fa.." tana fadin haka ta kara rushewa da kuka har da shessheka tana shigewa jikinsa, rungumeta yyi yana sauraronta da mamaki, sai kuma yyi murmushi a hankali yace "Toh ya kike son ayi?" Cikin rawar murya tace "Ni dai mu tafi wani gidan kuma kar ta bi mu wllh..." Yace "Kin hakura xa ki xauna da ni kenan yanxu?" Still tayi da farko, lkci daya kuma ta janye jikinta daga nasa da sauri ta juya masa baya tana imagining abinda ta fada, murmushi kawai yake yana kallonta, ta turo baki tace "Ni baxan xauna da kai ba" daga haka ta wuce cikin bathroom da sauri ta rufe kofar, juyawa yyi ya fita dakin still smiling. Lallashi bbu irin wanda Mujaheed bai ma Safeenah ba domin a rayuwarsa ta duniya ya tsani kukan mace, kukan ma wai sabida shi, amma kamar yana dada tunxurata, da ta tuna biye ma Umma ya ja mata wannan masifa da tashin hankali sai ta kara rushewa da kuka tana tunanin me xata ma Umma taji dadi a ranta, gani take kamar ta kusa farkawa da mummunan mafarkin nan da ke neman fasa mata xuciya, sai lkcn ta san meye kishin abinda kake so, gashi ta kasa ko da kiran Hajiyarta ta sanar mata ai fa kishiya na nan daram, tsoro take kada tace mata ta dawo gida don har xuciyarta take jin baxata iya rabuwa da Mujaheed ba har abada, rabuwa da Mujaheed mutuwar ta kenan a ganinta, ta rikosa tana kuka sosai tace "Wllh ina sonka Mujaheed, Ina son kasancewa da kai amma baxan iya xama da yarinyar nan ba idan ma record din gidanmu xan yi breaking ba da wannan yarinyar ba gwara ka saketa ka auri wata na yadda, Allah da gaske ban son ganinta ko na second daya, yanxu kana nufin kun hada gado da yarinyar nan?" Mujaheed ya saketa ya mike yace "Baki son ganina kenan idan baki son ganinta, don she is me" Bai jira sauraronta ba ya shige toilet din dakin yin alwala, har ya fito kuka take tayi dai dai a kasa kamar warce uwarta ta mutu, ya nufi kofa ya fita dakin, bedroom din sa ya nufa ya bude a hankali yana kallon ciki, fitowar Imaan kenan daga bathroom ta dauro alwala ita ma, ta wani hade rai ta dau hijab dinta ta sa tana shimfida darduma, cire makulli yyi ta ciki ya kulle dakin da makullin sannan ya tafi masallaci bayan ya saka makullin a aljihu. Mujaheed na dawowa masallaci ya shiga dakin da Safeenah take, kamar yanda ya bar ta haka ya dawo ya sameta, Yana tsaye dakin yace "Baki ma yi sllhn ba kenan?" Banxa tayi masa tana kuka sosai, ya tabe baki yace "Xa mu fita in siyo mata few wears coz gaba daya kayanta na gida" Safeenah ta mike da sauri tana xaro ido tace "Xaku fita fa kace Mujaheed??? Har xaka fara walakanta ni kenan kake nufi, xaku fita kake ce min fa" yace "You heard me right, we are going to the market, kuma don't forget cikin one week dinta muke..." Kallonsa kawai Safeenah take kamar idanuwanta xasu yo waje xuciyarta na bugawa, yace "Her one week started from yesterday" Bai jira cewarta ba ya fita dakin ya kulle kofar, imaan na xaune saman darduma ta hade kanta da gado ya sameta, Yana kallonta yace "We are going out now" Ta dago da sauri tana kallonsa tace "I am going no where plss" Yyi shiru yana kallonta, sai kuma yace "Ohk dama shopping xamu je ki yi, bari mu je da Safeenah tayi maki kawai" Mikewa tayi da sauri tace "Tayi mani a kan me? What's my business with her? Ko ita xata sa kayan da xata min shopping??" Bata jira cewarsa ba ta nufi kofa ta fice, murmushi yyi ya bi bayanta, waje ya sameta tsaye jikin motar, ya bude lock din motar ta bude front xata shiga suka yi ido hudu da Safeenah dake lekosu ta window tana kuka kamar ranta xai fita, Imaan ta ji dadin hakan har ranta, ta kalli Mujaheed sai kuma ta nufe sa da sauri tace "Toh ai baka gama saka buttons din ba" Bata jira cewarsa ba ta fara buttoning din masa shirt dinsa, kallonta yake da mamaki, ta turo baki taki yarda su hada ido har ta gama sannan ta juya ta koma gun motar ta shiga ta rufe tana satan kallon windown dakin Safeenah tana d'an murmushi, Mujaheed ya bude gate sannan ya dawo ya shiga driver seat yana kallonta murya can kasa yace "Kema bari in gyara maki Hijab din ki" Bai jira cewarta ba ya jawota kusa da shi yana gyara mata hijab duk da bbu abinda ya samesa, xata turasa sai kuma ta tuna kila Safeenah na nan tana kallonsu, hakan yasa ta tsaya ta matsa kusa da shi amma bata yarda sun hada ido ba, unexpectedly taji bakinsa cikin nata, ta xaro ido a mugun tsorace xata kwace kanta ya ki saketa. Siyayya ba na wasa ba Mujaheed yyi ma Imaan, duk ita ke daukan kome taga yyi mata, tun daga inner wears, dogayen riguna, kananun kaya, amma fa gaba daya fuskarta a daure yake sbda abinda yyi mata daxu, da ta tuna sai ta goge bakin, sau dayawa sai ta dau kayan da yyi mata kyau sai ta juya gunsa da sauri tana nuna masa kayan tace "Yaya wannan xai min kyau koh??" sai kuma ta tuna sabon relationship dinsu, a hankali take juya masa baya tana turo baki bar wajen fuska daure, shi dai sai dai yyi murmushi yana biye da ita, bayan sun gama da boutique suka shiga shopping mall, gun turarruka ta nufa shi kuma ya tafi gun kayan shayi don siya masu, Tana cikin daukan turare suka yi ido hudu da farida dake duba wani turaren a wajen ita ma, xaro ido imaan tayi da mamaki ta nufeta da sauri tace "Anty Farida" Rungume ta Farida tayi cike da murnan ganinta tace "Imaan, what are you doing in Zaria?" Imaan na murmushi sosai tace "Ni da Yaya ne Aunty Farida, dama Zaria gidan ki yake?" Farida da lkci daya fara'arta ya d'an ragu, a hankali tace "Ehh nan nake, me kika xo yi nan din ke?" Lkci daya fara'ar da ke fuskar imaan ya bace ita ma jin tambayar da ta mata, sai kuma da sauri tace "Lahh ni da Yaya ne Aunty, bari in kirasa ku gaisa" Bata jira cewar Farida ba ta bar wajen da sauri, Farida ta bi ta da kallo sannan ta sauke idonta kasa a hankali, Mujaheed na duba blue band sanin Imaan na son ci sosai, ta iso inda yake, daga kai yyi yana kallonta, ta wara ido tace "Yaya I just met Aunty Farida now" da mamaki yace "Farida? Where is she?" Imaan tace "Wajen perfumes" sai kuma ta kamo hannunsa kamar xata yi kuka tace "Don Allah Yaya don't tell her that we are married plsss" da mamaki yake kallonta trying hard not to laugh yace "Why???" Hankali tashe tace "Wlh abun kunya ne wannan Yaya, ya xa ayi ace wai kai mijina ne bayan kowa ya san kai yayana ne, don Allah kar ka gaya mata wllh xan ji kunya sosai" Murmushi yyi yace "Toh na ji, mu je...." Tana rike da hannunsa suka tafi inda Farida take, shi dai bin ta kawai yake yana kallonta har suka iso wajen, Imaan na kirkiran murmushi tace "Aunty ga yayan, shi ma yyi aure few months ago, wajen matar ma na xo in mata kwana biyu"




*Imaan isn't for free* it's 300 via


Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788



86.....



Farida na murmushi tana kallon Mujaheed tace "Ina yini Dr?" Mujaheed ya mayar mata murmushin yace "Lafiya lau Farida, kwana da yawa?" Tace "Alhmdllh ya aiki" yace "Lafiya lau, dama Zaria kike?" Tace "Ehh a nan nake" Ya gyada kai yace "Maa sha Allah, toh ya mai gidan?" Tace "Yana lafiya lau, tare muke yana waje" Mujaheed yace "Toh maa sha Allah" Imaan dai sai kirkiran murmushi take tana kallon Faridar, Farida tace "Yaushe kika ce xa ki koma kaduna?" Imaan ta wara ido tace "Nan da sati daya idan Allah ya yarda" Farida tace "Amma xa ki xo gidana ai koh?" Imaan tace "Ehh xan ce Yaya ya kawo ni, ki ba mu address" Farida na murmushi tace "Toh bani number wayar ki" Imaan tace "Na bar sa a gida, bari ki bani naki inyi saving a wayar Yaya" daga haka ta karbe wayar hannun Mujaheed ta mika mata, Farida ta amsa ta sa number ta sannan ta mika ma Imaan, Imaan ta amsa tayi saving number da Aunty Farida sannan tace "Nagode Aunty sai kin ganni soon" Farida na murmushi tace "Toh nagode Imaan" daga haka tayi mata sallama, tayi ma Mujaheed ma sallama sannan ta bar wajen, Imaan ta ci gaba da daukan turarrukan da take so, Mujaheed na bin ta da ido har ta juyo, suna hada ido ta turo baki tayi gaba ta bar sa a wajen, murmushi yyi ya bi bayanta, suna isa counter ya biya kudin abubuwan da suka siya gaba daya aka kai masu mota, har suka isa gida babu wanda yace komai cikin motar, Yyi parking yana kallonta yace "Ke baki ji kunya ba da kika ce mata wajen matata kika xo?" ko kallonsa Imaan bata yi ba ta dau ledan turarruka da body cream sai toothbrush da toothpaste dinta xata fita motar yace "Xa ki san hutu kika xo yi gidana" ita dai bata tsaya ta sauraresa ba ta wuce ciki, ya fita motar ya tafi ya kulle gate ya shiga cikin gidan, direct sama Imaan ta wuce ta tadda Safeenah tsaye corridor idonta yyi jajir sbda kuka, da alama dai jiran haurowanta sama take, tun da suka hada ido Imaan ta dauke kai fuska daure, Safeenah na kallonta da kyau tace "Mijina kika yadda aka aura maki dai koh???" Imaan ta juya tana kallonta tace "Mijin mu dai malama...." Tana fadin haka tayi maxa ta shige dakin ta sa makulli, xuciyar Safeenah ya dinga tafarfasa tana tunanin me xata ma Imaan taji sauki, wani murmushin takaici tayi ta juya ta koma ciki, Mujaheed na shiga parlor ya fiddo wayarsa dake ring, ya d'an yi jim yana kallon Screen din don number Daddy ne, xaunawa yyi saman kujera sannan ya daga ya kai kunne murya can kasa yyi sallama, Daddy amsa daga daya bangaren yace "Ya ku ke Muhd?" Mujaheed yace "Alhmdllh Abba, Ina yini?" Daddy yace "Lafiya lau, su Hadiza xa su kai ma Imaan kaya can gidan naka, how about the key to the house?" Mujaheed yace "In sha Allah xan kawo makullin Abba" Daddy yace "Alright, Hadiza tace baka daukan kiranta why?" mujaheed yyi murmushi sai dai bai ce komai ba, Daddy yace "Kar ka damu ka dauka kaji me xata ce maka, may be Sunday ma su je tare da Inna" Mujaheed yace "Toh Allah ya kai mu, nagode" Daddy yace "Ba matsala dai koh?" Mujaheed yace "In sha Allah" Daddy yace "If there is any you let me know, amma kasan Ummar ka an kwantar da ita asibiti kuwa?" Mujaheed yyi shiru da farko, sai kuma yace "Not at all Abba" Daddy yace "Ohk, Alhmdllh da sauki sosai, later xa a sallamosu" Mujaheed yace "Toh Allah ya sauwake, nagode Abba" Daddy yace "Madallah" daga haka ya katse wayar, mujaheed yyi dialing number Umma, bayan wani lkci ta dauka, a hankali ya gaisheta ta amsa, yace "Ashe baki ji dadi ba Umma?" A takaice tace "Wannan ba matsalar ka bace Mujaheed, kuma shirun da kaji na maka ba yana nufin na hakura da aurenka da tsinanniyar sauran ciwon nan bane, in sha Allahu ina kara jin sauki xan taho zariar ayi ta ta kare duk uban da xai faru sai dai ya faru amma wllh baxa kayi aure da yar Aisha ba in dai ina numfashi a duniya, kai koma bbu raina baxa ka yi ba wllh, don ma kaji da kyau, kwata kwata ban amince ka hada daki da ita ba...." Tana gama fadin haka ta katse wayar kitt, Mujaheed ya fi minti goma xaune kansa a jingine da kujera ya lumshe ido, a hankali ya mike daga karshe ya wuce sama, dakin Safeenah ya shiga, ya sameta tana xuge jaka bayan ta ciro Hijab, ko kallonsa bata yi ba ta saka hijab din, ta daga trolley dinta tana ja ta nufi kofa, yace "Ina xa ki" ganin bata da niyyar tsayawa balle ta basa amsa ya fixgota, ta fashe da matsanancin kuka kamar jira take tace "Let me Mujaheed, gidanmu xan wuce don wllh baxan xauna da yarinyar nan ba, I can't stay under the same roof with her, na tsaneta, na tsaneta...." Katse ta yyi yace "Kin tsane ni kenan, good and fine, you dare cross this house da sunan wucewa gidanku to a bakin auren ki wllh, kin ji na rantse" daga haka ya saketa ya fice daga dakin, ta bi sa da kallo baki bude, lkci daya ta xube kasa ta dinga kuka kamar ranta xai fita. Bayan Magrib da takeaways din abinci Mujaheed ya shigo gidan, ko kadan bai yarda damuwar da ke tattare da shi ya bayyana fuskarsa ba, sama ya wuce ya sa makulli ya bude kofar dakin da Imaan take, ya sameta saman darduma ta idar da sllh, ya ajiye mata leda daya yace "Daxu baki sha drugs din ki ba why?" Shiru tayi masa, yace "Imaan" ta dauke kai tace "Am not sick" ya fi second goma yana kallonta sannan ya juya ya fita, mikewa tayi da sauri ta nufi kofarta ta kasa kunne, ta ji ya bude kofar dakin Safeenah ya shiga, tabe baki tayi ta koma ta xauna gefen gado fuska daure. Xaune ya samu Safeenah kasan dakin ta jinginar da kanta da gado ga wayarta a gefenta, kana ganinta kasan ta gaji da kuka, ya ajiye ledan hannunsa ya karasa ya xauna gefen gadon yace "Kin yi sllh?" Bata ko kallesa ba balle ta amsa, yace "Let talk Safeenah...." Still bata ce komai ba wasu hawayen na xubo mata, yayi kasa da murya yace "Yanxu ya kike son ayi Safeenah?" Ta daga kai tana kallonsa cikin rawar murya tace "Am very serious Mujaheed baxan iya xama da yarinyar nan ba a gidan nan" Ya d'an yi shiru sannan yace "Mind u, sunanta Imaan ba yarinya ba" A mugun fusace ta mike tace "What ever" ya dauke kansa yace "Idan baxa ki iya xama da imaan ba baxa ki iya xama da ni ba kenan ae" Wani kuka ta sakar masa tana kallonsa, ya mike ya isa gabanta ya kamo hannunta a hankali yace "I have decided in raba maku gida, ke sai ki xauna nan, ita kuma....." Ta wani xaro ido da karfi tace "Ka raba mana gida?? Ka raba mana gidan don ka ji dadin cutata, to wllh baxai yiwu ba" Bai san lkcn da yyi murmushi ba yace "To baxan raba ba, don kada in cuce ki, amma Ina son don Allah ba don ni ba ki kwantar da hankalin ki, mu xauna lfya gaba daya, I will neva give imaan space din raina ki... Plss Safeenah kiyi hakuri ki kwantar da hankalin ki, wannan kaddaranmu ne gaba daya, bana son kina kukan nan don I am feeling guilt inside me, gaba daya we never saw this coming, ain't you proud being my first? Kowa xata shigo gidan nan fa a bayan ki take kin sani, so why disturb ur self, kuma duk yanda kika ce ayi haka xa ayi, don haka kiyi hakuri wife...." Rungumesa tayi tana kuka sosai tace "Wllh kishin sharing dinka da wata mace nake Mujaheed, ji nake kamar xuciyata xata fashe saboda kishi" ya rufe bakinta yace "Aa baxa ki yi sharing dina ba..." Da haka dai Mujaheed ya dinga lallaba Safeenah har ta d'an hakura ta ci abincin da ya shigo mata da shi, jin lkcn isha yyi ya mike ya fita dakin xuwa masallaci, for once xae huta da koke kokenta ko hankalinsa xae kwanta ya samu relieve, he hate it when a lady cries..... Yana dawowa masallaci ya sameta parlor tayi jigum, shi dai ya san yana tausayinta sosai, kuma babu abinda ya fi unexpected kishiya ciwo, kishiyar kuma warce tun asali basa shiri, ya karasa parlon ya xauna saman kujera kusa da ita yace "Kin yi sllhn" shiru tayi bata ce komai ba fuska bbu walwala, ya kalli movie din da ake a tv ya dau remote yace "Bari in kai maki wannan series din naki da kike kallo kullum...." Daga haka ya canxa tashar ya jawota jikinsa a hankali, wani sabon hawaye ne ya fara sauka idonta, yace "I don't like this tears plss Safeenah, yanxu baxa ki hakura ba for the sake of the love you are having for me??" Cikin rawar murya tace "Ae nace maka na hakura" yyi pecking goshinta yace "Toh kar ki sake kukan nan" daga masa kai kawai tayi, tayi lamo jikinsa, suna ta xaune a haka har kusan karfe goma, jin footstep a stairs Mujaheed ya daga kai da sauri suka yi ido hudu da Imaan, dauke kai Imaan tayi, Safeenah na jin tafiyarta ta kara shige masa, Imaan bata sake kallonsu ba ta wuce kitchen rike da takeaway din da ya kai mata daki, tana ajiye ledan hannunta ta jingina da cabinet din kitchen din xuciyarta na bugawa, tafi minti biyar sannan ta fito ta wuce sama da sauri ba tare da ta yadda ta sake kallonsu ba, Mujaheed ya bi ta da kallon gefen ido... Sha daya saura Mujaheed ya tafi sama tare da Safeenah bayan an gama series din, ya bude mata kofar dakinta yana kallonta yace


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login