Showing 216001 words to 219000 words out of 303099 words

Chapter 73 - Imaan Book 1 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

1624

da wnn bakar rana da take gani, Wai only son dinta da take ji da take alfahari da aka daura ma aure da yar makiyiyarta sauran ciwo...." Hade kai tayi da kasa tana kuka tana cewa "Ya Allah kasa mafarki nake ba gaske ba, Allah ka warware wannan auren kada in mutu, wayyo Allah ka dubeni" sai kuma ta mike kamar mahaukaciya ta shiga gidan ta kitchen, kanta a kasa ta wuce sama ta dau hijab a daki ta saka har da nikab sannan ta fito ta sake bi ta kitchen ta fice daga gidan ta nufi titi da shegen sauri tana hadawa da gudu tana cewa "In sha Allahu, xa a warware komai na hakura in ma uban Sadeeq ne Imaan ta aura ba komai"



_Hajiya Sadiya Chamo wakar biki yyi sweeeet😉 Mujaheed yace ince maki ki turo account number, amma fa su a duniyar su basu da banks irin na Naija, to ko ya xa ayi wannan abun?? Ya dai ce ince ki turo...._🥰

*I really appreciate the prayers and well wishes yesterday fans soyayyata gare ku babu mix wllh🙅🏻‍♀️, masu Ihisani😍 ina godiya kwarai Allah ya kara budi da daukaka, Allah ya sa ku gama da duniya lafiya, Allah ya raya kids ya raba ku da iyayen ku lfya...*

_If you are yet to patronize Imaan... Do so for the love u are having for the book and the writer for the sake of Allah.... nima sai in ji dadi_😃🥰
it's just 300 via....
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah.

Next Update around 9 or so in sha Allah. Tnx.



77.....




Duk yanda Maryam tayi da Imaan ta gaya mata abinda ya faru ganin yanda take kuka kamar ranta xai fita tun shigowarta kin ce mata komai Imaan tayi, Maimoon da hankalinta ya tashi ba kadan ba ta cire mayafin da Imaan ta rufe fuskarta da shi tace "Wai meye haka Imaan, what's happening, talk to us plsss" Fadawa kan gado imaan tayi ta kara rushewa da wani kukan tana shessheka, Maryam ta dinga kallonta tana fatan Allah yasa ba tunanin da take bane ya tabbata wato Sadeeq yace ya fasa auren, lkci daya jikinta yyi sanyi ta xauna gefen gadon ta ma rasa abinda xata ce tayi tagumi tausayin Imaan ya cikata, Hawaye Maimoon tafara yi tana dago Imaan tace "Don Allah me ya faru Imaan ki gaya mana, wani abu ya sami Sadeeq din ne? Ki mana magana don Allah" Mikewa Maryam tayi ta fita dakin a sanyaye hawaye na sakko mata. Aunty ce tsaye bedroom din Ammi ta jingina da bango ta rungume hannu tana kallon Ammi gaba daya ta rasa abun cewa, Ammi dai na xaune gefen gado ta ci kukanta har ta gode Allah tayi tagumi, cikin sanyin murya Aunty tace "plss I don't want you to react again Ummi Imaan, kiyi hakuri and keep calm ki ga next action da xa a dauka, bana son ki sake cewa komai" Ammi ta kalleta tana girgixa kai tace "I should keep calm fa kika ce Amina?? Why will I?? am sorry to say this duk da Mujaheed ba shi da wani aibu kuma shi din tabbas namijin aure ne amma aurensa da Imaan will be the last thing I could imagine on Earth, Amina kin mance wacece uwar Mujaheed? Kin manta wacece Rukayya? Me yasa su Alhaji xa su yanke hukunci haka babu knowledge dinmu, why will they do such, me yasa xa a aura ma 'ya ta Mujaheed bayan ba rasa masoya xata yi ba, duka duka nawa Imaan din take ma gaba daya, me yasa xa su min haka...." Hawaye sosai Ammi ke yi tana girgixa kai tace "Yau da ba Rukayya ta haifi Mujaheed ba da xan fi kowa farin ciki da wannan hadin nasu, I will be happy Amina, amma a wannan circumstance din na fi kowa jin takaici da bakin ciki, I hate the thought of my daughter been an inlaw to Rukayya, fatana kada 'ya ta ta kwana yau a gidan nan da auren Mujaheed a kanta, Mujaheed ya fi karfinta, Rukayya xata iya karasa kashe min 'ya ta ne idan aka bar wannan auren, don Allah Amina ki min favor din fahimtar da Abba illar wannan auren da ya hada" Ammi na kuka sosai tace "she is all I've got a duniyar nan, idan na rasata shkkn that's just the end, ya xan yi Amina? wannan karan wllh baxan yi shiru a cutar min da Imaan ba, auren nan babu alkhairi babu alamarsa Mujaheed ya sakar min 'ya ta ko kuma in dauketa mu bar gidan nan, ba matarsa bace Imaan" kuka sosai Ammi ke yi tana jin xuciyarta na mata xafi, Aunty ta kasa cewa komai ita ma hawayen na sakko mata, Mama Hadiza ce ta shigo dakin ta tsaya tana kallonsu kafin ta karaso calmly tace "Aisha I never expect ur reaction a parlon yayana ba, ban taba xaton ko a mafarki xa ki yi abinda kika yi ba, you look into my brothers face and tell him baxa ki iya barin d'an sa yyi xaman aure da 'yar ki ba, ko da kuwa Rukayya shaidan ce a siffar mutum don nasan saboda ita kika yi wannan furuncin wllh bai kamata ki yi ma Ya Ahmad haka ba, bai kamata ba, bai kuma cancanci haka daga gare ki ba, kuma ni kin ban mamaki don ba Ahmad kadai ba har ni da Ya Sadeeq kika ci ma fuska don Mujaheed d'an mu ne, kuma ko albarkacin abinda Mujaheed yyi ma Imaan a rayuwa ba gori ba bai cancanci ki rufe ido a gabansa yana xaune ki nuna baki son hadin nan ba, ita Inna dama bana ma kawota a lissafi don nasan wacece ita amma kiri kiri ki kunyata d'an uwana da yake tunanin yana da iko da Imaan kamar yanda Ya Sadeeq ke da iko da ita" Ita dai Ammi bata ce komai ba hawaye kawai take don gaba daya ba wani sauraron Mama Hadiza take ba, ta dade bata jita cikin tashin hankalin da take a lkcn ba, Cikin sanyin murya Aunty tace "Mama Hadiza put ur self in her shoes, she spoke out of frustration, kiyi hakuri ko wace uwa iyakar abinda tayi xata yi wllh, bbu wanda bai san Rukayya ba bbu wanda bai san halinta ba, wace uwa ta gari ce xata so Rukayya a matsayin surkar 'yar ta, think of it mama Hadiza..." Mama Hadiza tace "Don't tell me that Amina, Imaan ba da Rukayya xata xauna ba, wllh da Yaya Ahmad yyi breaking min news din nan nayi farin ciki ba kadan ba, amma me?? lkci daya farin cikin nawa ya koma ciki tuna uwar Mujaheed da nayi, ni ina da yakinin wllh tllh nan gaba sai kun fi kowa murnan hadin nan da ya Ahmad yyi yau, barin ma ke Aisha..." Mikewa Ammi tayi tana goge idonta tace "Kiyi hakuri Mama Hadiza bana tunanin xan amince da wannan auren na fi ku sanin wacece uwar Mujaheed, na kuma san abinda xai faru, Kar ki ce na maki rashin kunya but Imaan is all I've got sannan ga condition dinta, baxan so wani abu ya samar min ita ba, da wanne xata ji? Kishiya ko Uwar miji, wanda ba sai an fito fili an fada ba kowa yasan kishiyar nan ba mutunci gareta ba har ke kin shaida, imaan is too young and sick for this, don Allah kiyi hakuri ki ma yayinnanki magana a warware auren nan they are not meant for each other, Allah ubangiji ya mata wani xabin mafi alkhairi" Ammi na magana hawaye na sakko mata ta shige bathroom, Aunty ta lumshe ido ta bude tana jin tausayin aminyartata da 'yar ta, Mama Hadiza ta fi minti biyu a tsaye kafin ta juya ta fita dakin. Kawu Bala dake ta girgixa kafa daga inda yake xaune parlon Abba bayan fitar Inna da kusan minti goma yace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, where are we to start from now??" Shi dai Daddy ya jinginar da kansa da kujera tun xamansa parlon har sannan bai ce uffan ba, Kawu Audu yace "Masalha daya shine a warware auren nan kawai shine kwanciyar hankalin kowa don Asabe ba kyau... ayi hakuri kawai a warware auren Allah yasa hakan yafi alkhairi" Abba dai sai kallon Daddy yake da ya ki cewa komai ya rungume hannu, Abba ya mike yace "Sadeeq tun a lkcn da na baka sadaki a masallaci ya kamata ka fito fili ka nuna min baka son na hada auren 'yar ka da d'a na, bai kamata ka min shiru a lkcn ba, da ka fito da abinda ke ranka da duk abubuwan dake faruwa yanxu bai faru ba, but anyway yanda na hada auren nan haka xan rabasa ba da jimawa ba in sha Allah, ka tashi ka tafi ka ba uwarka hakuri, kai ma kuma ina baku hakuri da matarka, in dai a kan na aura ma Imaan son dina ne xa a raba auren yanxu sai kowa ya saki ransa...." Kallonsa kawai Daddy yake ya kasa cewa komai, Kawu Bala yace "A'a bai kai haka ba Ahmad.... Don't misunderstand him plss" ko saurarensa Abba bai yi ba ya nufi kofa ya fice yana dialing number Mujaheed, Daddy ya bi sa da kallo, Kawu Bala yace "Haba sadeeq idan ma baka yi na'am da auren nan ba bai kamata ka fito fili ka nuna ba, Ahmad yyi iya kokarinsa ne na ganin ka fita kunyan jama'ah da aka tara, ko shawara bai yi da d'an sa ba yana ganin ya isa da shi ya yanke hukunci amma kuma a samu matsala daga bangaren ka" Daddy ya sauke ajiyar xuciya kamar baxai ce komai ba sai kuma ya girgixa kai yace "Noo, not at all...." kawu Audu yace "Banda abin ka xumunci bai kara karfi ba hakan da aka yi?? jini daya wasa ne Sadeeq? ita Asabe fa dama ba a saiti take ba wani lkcn sai dai Allah ya gyara mana ita, don me xaka dau maganganunta ka kunyata D'an uwan ka, shi Mujaheed da aka ma aure without his consent dubi fa yanda ya nuna kamar ba komai amma sai ku Sadeeq, to Allah na tuba ina laifin wannan hadin banda rikicin Asabe da yawa yake?? Ku kan ku xa ku yi farin ciki da auren nan nan gaba, Mujaheed bayan hankali da natsuwa da sanin ya kamata ga ilimin muhammadiyya ga boko, uwa ba ya rike ibada ba da wasa ba, ai ya xo wajena na gani, haba wnn ai abun kunya ne kuke sai kace ba jini ba, kuma duk Asabe ce daburtattciya, kai Asabe dai ba kyau" Daddy ya girgixa kai a hankali yace "Ko kadan ni ban ga aibun hadin nan ba, Mujaheed d'a na ne, na kuma san waye shi, na kuma san tarbiyarsa, infact tarbiyata ne Mujaheed, but 6acin ran fa?? You all can see the reaction displayed by his mum ga kuma maganganun da Inna ke yi tana cewa ta bar mu da Allah, for what?? Ni tun a masallaci nasan xa ayi haka, Yusuf da ya fito ya nuna yana so ma ga abinda ta mana balle wannan?" Mikewa yyi yace "Am coming" daga haka ya fita ya bi bayan yayan nasa. Ta Rasulu ta rike haba ta hangame baki tana kallon Inna da ta gama tsara mata sa6on da su Ahmadu da Bukar suka yi tana sharban kuka sosai, tsofaffin parlon suka dinga salati ana nanatawa ana tafe hannu, cikin rawar murya Inna tace "Allah ya isa tsakanina da Sadeeq da ya yaudari jikata ya kuma ja mana rudani a gida har ya kai ga Ahmadu da Bukar da su d'an tsut suka tafka babban sa6o suka aura ma Imaan Mujaheed wai a fita kunya, basu san kunyar aka shiga ba tsumu_tsumu, da wani idon xa mu kalli jama'ah" Ta Rasulu tace "Ikon mai mana ruwan sama, to yanxu kice duk uban kayan da muka tafi muka mata jere a rusheshen gidan Bukari komawa xa mu yi mu kwaso a kai gidan Mujaheed kenan?" Gwalo ido Inna tayi tana kallonta, sai kuma ta fashe da kukan takaici tace "Ke dai Allah kadai yasan yanda xai yi dake, kuma gaskiya na yafe kawancen nan namu, waye kuma Mujaheed, me Imaan xata yi da shi fisabilillahi ta Rasulu? Anya kinsan Allah kuwa" Ta Rasulu tace "Al-quran baki son gaskiya Asabe, yau ko Bala ne ya haifi Mujaheed baxa ki tambaye ni wanene shi ba balle Ahmadu ne ya haifesa, to ita Imaan din wacece da Mujaheed baxai aureta ba Allah na tuba, wllh ban taba ganin shegen gantalallen xumunci irin naku ba, 'ya 'ya uwa daya uba daya ki dinga nuna bambanci haka, daga an rufa ma yarinya asiri kada aji kunya an lika ma Mujaheed sai ya xama laifi??" Inna tace "Gaskiya Allah ya isa sanin ki da nayi a duniya Ta rasulu, Allah kuma ya saka min...." Ta Rasulu ta mike tace "Oho dai gaskiya ce sai na fada, Bulasawan da ya so kunyata ku ma ba don...." Inna ta katse ta da sauri tace "Waye kuma Bulasawa Ta rasulu? Tsinannu xa ki ce manyan barayin duniya, uban waye bai san sata suke yi ba? Waye bai san abinda Bulasawa yyi a Nigeria ba, an fa sha kamasa dumu dumu yana sata wllh, ni dai Allah ya dubi jikata ya rufa mata asiri da aka fasa auren, da ina xan shiga idan aka aura mata d'an gagarumin barawo, mu ma duk kallon barayin xa a dinga mana kawai, in sha Allahu sai naje na ci uban yaron a gidan satan su da suka gina, bari dai komai ya lafa a sakar min jika wllh wllh sai na je" Ta Rasulu tace "Dama idan xa ki tafi sai ki rike kudin satan da ya dinga baki kina boyewa ki mayar masu da abun su" Inna ta saki salati tayi tagumi tace "Duka duka nawa ya ban, sau uku fa kadai ya ban dubu uku sai shegen iron dinsa gashi can ko budewa ban yi ba, ance maki ni gantalalliya ce mara tsoron Allah??" Shigowar Ammi yasa Inna tayi shiru, Ammi ta xauna parlon kanta a kasa, Inna ta share guntun hawayen idonta tana kallonta, cikin sanyin murya Ammi tace "Inna xan tafi gidanmu tare da Imaan...." Inna ta katse ta da sauri tace "Akan me??" Ammi tace "Idan aka raba auren in sha Allah xamu dawo, amma yanxu...." Inna ta katse ta mike tace "Yau naga fitinanniyar bafillatana, don an aura ma Imaan Mujaheed sai kice xaki tafi gida da Imaan, meye da Mujaheed din kamar warce aka aura ma barawo, jikana ne fa shi ma?? Ni fa na haifi Ubansa na haifi Uban Imaan.... yau naga ikon Allah, to wllh kiyi ta tafiyar ki amma bbu inda xaki da jikata don an aura mata d'an uwanta, wahalan da yyi da ita ko ke kinyi idan ba rashin tsoron Allah ba??"



*Imaan isn't for free* it's 300 via


Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788




78......



Mikewa Inna tayi ta shige daki tana cewa "Ni dai ba ruwana, kiyi tafiyar ki ke kadai amma bbu inda imaan xata je, kawai Allah ya rufa mana asiri mu kuma mu ki rufa ma kanmu?? kaji min mata dai" Ta Rasulu na kallon Ammi tace "Haba Shatu, ke ma fa Mujaheed din nan d'an ki ne, ko yana da wani mugun hali ne wanda ke kika sani ba mu sani ba??" Inna ta leko daga daki tace "Ina fa ta Rasulu kawai samun waje irin na bafillatani, mai mugun hali ai a bayyan 'yar ta imaan yake, ni wllh sai ince ma cutar Mujaheed aka yi da aka hada sa da Imaan bayan ga matarsa Safara'u, Imaan fa ko girki bana jin ta iya, banda Mujaheed din wanene xai iya da ita, kuma daga an rufa ma juna asiri sai ki nemi ki tona mana, ni dai ba ruwana kiyi ta kanki Aisha, ko kinfi Ahmadu da Bukar sanin abinda suke ne, kawai mata kina nema ki lalata mana xumuncin mu sbda rashin tsoron Allah" Mikewa Ammi tayi ta fice daga parlon, Inna ta rike ha6a tace "Yau naga bafillatana dai..." Ta Rasulu ta tabe baki tace "Ni dai ban taba ganin irin wannan xumunci ba tunda uwata mai salati ta haifeni, gida duk ya rikice daga hada aure na xumunci" Inna tace "Wllh idan xuciya ta debeni sai in iya ce ma Mujaheed ya ki sakinta mu ga ta tsiya, idan an bi komai a hankali kuma Allah ya dora mu kansa ai sai ya saketa tunda a gaskiya Imaan ta fi karfin sa sai irin su Bulasawan dama, amma mata kya xo kice min xa ki tafi da Imaan...." Ammi na komawa part dinsu ta shiga dakinta ta sa Hijab ta dau purse ta fito ta bude dakin Imaan, Mama Hadiza ce xaune dakin ta rungume Imaan dake kuka kamar ranta xai fita cikin tashin hankali take cewa "Yayana ne shi fa Mama, ya xa ayi ace wai an daura mana aure da yaya, wayyo na shiga uku mama dama Yaya na auren kanwarsa?? don Allah ki gaya ma su Abba Yaya na ne, wllh ni dai yayana ne...." Mama Hadiza ta kasa ce mata komai, jin har jikinta ya dau xafi sosai ta dago kanta tana kallonta fuska daure tace "Wato ban isa ince kiyi shiru kiyi ba koh?" Maryam dai na xaune dakin tayi tagumi, Maimoon sai hawaye take duk jikinta a sanyaye tana kallon Imaan da duk ta fice hayyacinta, Mama Hadiza ta sake Imaan ganin Ammi ta mike ta fita daga dakin, Ammi ta karasa cikin dakin tana kallon 'yar tata tace "Dauko Hijab din ki" tashi Imaan tayi ta dau hijab dinta tana shessheka tace "Ammi plsss kice ma Daddy su yi hakuri wllh yayana ne shi, ba aure tsakanin mu, don Allah kar su ce sun daura mana aure" Fixgo hannunta Ammi tayi suka fita daga dakin trying hard to control her tears, Imaan ta dinga bin ta tana kuka sosai har suka fito compound dake cike da jama'ah


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login