Showing 69001 words to 72000 words out of 303099 words
to kuma meye baxai yi ba yanxu?" Imaan na daga kwance sai dariya take da kyar, Ammi dai ko kallon Inna bata yi ba tana fiddo ma imaan kayan da xata sa, inna tace "Toh Allah dai ya kiyaye gaba yyi maki tsari da shi, amma gaskiya imaan ki guji duk inda Mujaheed yake, idan kun dawo asibitin xan xo dubaki idan Allah ya yarda, tafiya dai ta sha ruwa" daga haka ta fita dakin, Ammi tace "Kin tashi kin shirya ko xaki kwanta nan kina dariyar walakanci ne?" Imaan ta tashi ta saka kayan da Ammi ta fiddo mata, Inna na fita taga Abba tsaye a waje, tace "Ahmadu tafiya dai ta sha ruwa koh?" Yace "A'a xa su wuce tare da Yusuf yanxu, shi Mujaheed xa su je asibiti da Imaan" inna tace "Toh madallah, hakan ma yayi, to ko in bisu asibitin ne" Ta gefen ido Mujaheed ya kalleta da sauri, Abba yace "Ehh to xa ki iya bin su" Tace "Toh bari in kulle dakina kada a barsa a bude gaskiya" daga haka ta wuce sashin ta, Mujaheed ya nufi motarsa don fitar da motar waje, Abba ya bi sa da kallo har ya isa parking space ya shiga motar, Imaan ta fito sanye da Hijab har kasa, da kyar take tafiyar, Abba yace "Sannu mamana, Allah ya sauwake" a hankali yace "Ameen" yace "Mu je can kofar gidan, ban gane fita da motar da yayi ba" tare suka fita compound din, Ya bude ma Imaan front seat ta shiga, Abba na kallonsa yace "Inna na tahowa yanxu, tare xa ku tafi" yace "Ehh na sani" Daga haka Abba ya koma cikin gida, Mujaheed na ta kallon gate har sai da yaga inna ta fito tana washe baki sannan ya ja motarsa yayi zooming off, Imaan ta xaro ido tana kallonsa, yana isa titi ya kashe wayarsa ya ajiye ya dau hanyar asibitin da yake aiki, Sai da suka yi nisa fuska daure yace "Ni kika je kika hada da mamarki koh?" Tace "Ko dai ita taga ina kuka" ya gyada kai yace "Xa ki gane kuran ki" Ta turo baki ta jinginar da kanta da kujera, Suna isa asibitin bayan yayi parking ya juya yana kallonta yace "Sauko min a mota" Bude ido tayi da sauri, ya bude door din motar ya fita, a hankali ta ta bude side dinta ta saukar da kafafuwanta kasa, xagayowa yyi ganin bata fito ba yace "Baxa ki sauka ba" kamar xata yi kuka tace "Wllh jiri nake ji yaya" Wani harara ya watsa mata yace "To daukan ki xan yi?" Bata ce komai ba ta sauko motar, ya rufe ya kama hannunta suka shiga cikin asibitin. Yana xaune office misalin sha daya bayan ya kunna wayarsa kiran Abba ya shigo wayar, murmushi yyi ya daga ya kai kunne, Abba yace "What's taking you people too long Mujaheed" yace "Drip aka sa mata Abba, jikin da sauki sosai, she is fast asleep now" Abba yace "Toh Allah ya sauwake, why did u left inna behind?" Yace "Abba Kasan yanda take abinta, xuwa xata yi tayi ta fada every slight mistake" Abba yace "Haka ne, da yaushe xa ku dawo kenan" yace "Nan da azahar in sha Allah" yace "Toh Allah ya kai mu" Mujaheed yace "Ameen" daga haka Abba ya katse wayar, Mujaheed ya juya yana kallon Imaan dake kwance kan gadon duba pregnant women tana bacci, mikewa yyi ya isa kusa da ita yana kallon ruwan da ya kusa rabi, Hannu ya kai forehead dinta yaji da dumi har sannan, ta bude ido a hankali, daure fuska yyi yace "How are you feeling now?" Yamutse fuska tayi tana son mikewa xaune yace "Lie still and answer my question" murya can kasa tace "Kai na yana min ciwo" yace "Shi kadai?" Tace "And am hungry" ya kalli abincin da ta ki ci da yawa daxu kafin a mata alluran a sa mata drip ya dauka ya bude ya ajiye kusa da ita ya daga ta xaune, xaro ido tayi tace "Yaya abincin daxu kuma??" yace "Kin taho da abinci daga gida ne" ta hade rai tace "Ni dai baxan iya ci ba bayan ya huce kuma an ajiye k'ura ya gama shiga ciki" wani kallo ya mata yace "Toh sai ki tsaya da yunwar ki ai, wannan abincin dake rufe meye ya samesa da baxa ki ci ba, Bayan har ynxu ma da dumi abincin" yana fadin haka ya dau cokalin ya debi abincin ya kai baki, ta tabe baki ta dauke kai tace "A'a ni dai bana so, tun da safe fa, ko ta gefe gefe ai dust xai iya bi ya shiga, sai dai kai ka cinye a kawo min wani" Yace "Toh xaki ga wani kuwa" daga haka ya kai abincin table dinsa ya xauna ya fara ci, ta dinga kallonsa kamar xata fashe da kuka, ganin ko kallonta bai yi ba tace "Ni dai ka bani waya in kira Ammina ta kawo min abinci" yace "Baxan bayar ba" komawa tayi ta kwanta ta fara kuka har bacci ya sake xuwa mata, mikewa yyi ya rufe sauran abincin da bai cinye ba ya fita office din. Wani takeaway din ya fita ya siyo mata na abinci, yana dawowa ya tasheta ya ajiye mata abincin a gabanta sannan ya juya ya fita, ta mike xaune ta bude abincin ta fara ci a hankali, har ya dawo dakin bata gama cin abincin ba, ya xauna kan office chair dinsa, tana kallonsa tace "Yaya ni baxan iya cinyewa ba" bai tanka ta ba hankalinsa na kan laptop din gabansa, ya gama abinda yake sannan ya juya yana kallonta ya ga ta ajiye abincin ta kwanta, mikewa yyi ya karasa kusa da ita ya dauke abincin ya ajiye ta bude ido tana kallonsa tace "Yaya ina son xan yi magana da Ammina" yace "Baxa kiyi ba" yana fadin haka ya koma table dinsa, ta turo baki ta juya masa baya. Karfe biyu Imaan ta bude ido jin an kama hannunta, ya karasa cire mata drip din yace "How are you feeling?" Ta mike xaune da kyar tace "Da sauki, I want to go home" Yyi disposing roban ruwan ta sakko saman gadon, da sauri ya rikota ganin xata fadi duk da ita ma ta kama gadon, kamar xata yi kuka tace "Wllh jiri nake ji yaya" Ya saketa yace "Toh ni nace ki sakko?" Komawa saman gadon tayi ya fita dakin, ba a dau lkci ba ya dawo ya dau wayarsa da car key yace "Mu je" ta xaro ido tace "Idan na fadi fa?" Yace "Sai ki tashi" daga haka ya nufi kofa, sauka tayi saman gadon ta tsaya na kusan minti daya har ta ji ba jirin kuma sannan ta nufi kofa a hankali kamar mai counting steps dinta ta bude kofa ta fita, tsaye ta gansa yana jiranta, ya mata wani kallo yace "Da kin bari na sake shiga office din ki gani" daga haka ya wuce ta bi bayansa, sallama yyi da co workers dinsa suka fita asibitin, a Wani pharmacy ya tsaya ya sauka ya siyo mata drugs da aka mata prescribing sannan ya dawo ya shiga motar suka bar wajen, sai da suka kusa gida a hankali tace "Yaya baxa ka siya min kaza ba plss" yace "A'a sai dai in siya maki akuya" murmushi tayi tace "Toh siya min" A waje yyi parking yace "Sauka..." Ta bude motar ta fita sai da ta shiga gate ya ga ledan maganin da ya siya mata" fitowa yyi motar rike da ledan ya wuce ciki da sauri, ganin har ta kusa apartment dinsu ya wuce nasu bangaren kawai, Babu kowa parlon, ya haura sama dai dai fitowar Anty dakinta tace "Ya jikin Imaan din?" Ya saci kallon kofar Umma kafin yace "Da sauki, Umma bata nan ne?" Anty tace "Ehh tun da ta ji kai ka kai Imaan asibiti ta fice gidan tun safe bayan ta gama bambaminta" Mujaheed ya xaro ido ya jingina da bango yace "Wa ya gaya mata Anty?" Anty tace "Abban ku, tunda ba tsoron ta yake ba" Ji yayi xufa na keto masa, Anty ta wuce ta bar sa wajen tsaye, da kyar ya ja kafafuwansa ya wuce dakinsa. Ammi ta hada ma imaan ruwan xafi a bayinta ta fito tace "Ga ruwan ki shiga, saura ki salance ruwan" Tashi Imaan tayi ta wuce dakin nata. Wanka Mujaheed yayi ya shirya jin lkcn Asr yyi yayi alwala ya fita gidan, yana dawowa masallaci dama part din inna ya nufa don Allah yasan yana tsoron haduwarsa da mahaifiyar tasa Inna ta fito daga daki jin an bude kofar parlor ganinsa tace "oyaa Alale, fitar min parlor kada in tara maka jama'ah, uban me ka xo min??" Mujaheed yayi dariya yace "Haba dai mai gidan kuma kike kora yau inna?" A fusace tace "Yana kabari, tun raina bai baci ba Mujaheed ka fita" Mujaheed yace "Abba ne fa yace kada mu tafi dake Inna" ta buda baki tana kallonsa tace "Kai haba?" Yace "Xan maki karya ne" xauna wa tayi tace "Ikon Allah, shi Ahmadun yace ku tafi ku bar ni kenan, to ya ma kansa kuwa, shine har da shi a bani hakuri da masu gadi a tsakar gida daxu, har hawaye fa sai da na xubar" Mujaheed yyi murmushi ya kwanta kan kujera, Inna tace "Toh ae shikenan, ya jikin Imaan din?" Yace "Da sauki" inna tace "Kuma da gasken bata da lafiya Mujaheed? Naga kamar don kar aje kauyen da ita yasa ta langwabe fa" Mujaheed yace "Ni dai akwai abinci?" Tace "Gashi can wanda Aisha ta kawo min ne daxu, bai wuce shinkafa da miya ba, Idan kuma biskit xa ka ci ga su can iri iri a daki wanda aka kawo ma Imaan, Kazan ma daxu na dumama na karasa cinyewa..." Mikewa xaune Mujaheed yyi yana kallonta na kusan second goma, can yace "Wa ya kawo mata?" shiru Inna tayi kanta a kasa, can ta saci kallonsa suna hada ido tace "Yo wa gareta banda Bukar??" tana fadin haka ta mike ta shige daki.... Imaan ta fi minti biyu tsaye bakin kofar bedroom din Ammi ta kasa shiga don bata san me xata ce mata ba, bude kofar dakin aka yi ta ja baya da sauri, Ammi ta dinga kallonta tace "Meye haka kike yi a bakin kofa ta?" Ta fara kame kame ba tare da ta kalli Ammi ba, Ammi tace "Imaan" daga kai tayi ta kalleta kamar xata yi kuka, Ammi tayi kasa da murya tace "Tell me what you want" tana jan fingers dinta a hankali tace "Ammi dama... Dama Sadeeq ne yace min yana waje ya xo gaisheni" Ammi ta dinga kallonta tace "Waye Sadeeq" ta sunkuyar da kai tace "Abokin ya Muhsin" Ammi ta yi shiru, can tace "Toh kar ki dade" Ta d'an yi murmushi tace "Toh nagode Ammi" daga haka ta saka Hijab dinta ta fito don tun da aka yi la'asar Sadeeq ke waje amma ta rasa yanda xata sanar ma Ammi ta fita, sosai hankalinta ya kwanta ganin ba motar Mujaheed a parking space, kamar mai tausayin kasa ta fita kofar gida, Tsaye ta ga Sadeeq jikin motarsa ya rungume hannunsa, as usual sanye da spec dinsa, dogon hancinsa da cute millionaires belt dinsa shine first abinda xaka fara noticing a fuskarsa daga nisa, Ta sunkuyar da kanta har ta isa inda yake tsaye, kallonta yake daga cikin glass din idonsa ko kiftawa babu, murya can kasa tace "Ina yini?" Yyi murmushin da ya bayyan dimples dinsa ya cire glass dinsa yace "Lafiya lau Imaan ya jikin?" A hankali tace "Na ji sauki" yace "Sure??" Ta gyada masa kai, yace "Toh Allah ya kara lafiya, hope kin sha dosage na afternoon, I mean ur drugs?" Ta gyada masa kai tace "Na sha" yace "Good, ya mama fa?" Tace "She's inside" ya langwabar da kai yace "Yaushe xan xo gaisheta pls" ta xaro ido tace "A'a xan ce kana gaisheta" cikin sanyin murya yace "Ke dai baki son yan gidanku su san ni koh?" xata yi magana aka bude gate, Inna ce tsaye bakin gate din tana kallon mai gadi tace "Kai iliya kake ko ilu, Kasan kan waya kuwa? Hadiza xa a kira min duk ba kowa gidan sai mai laluran can kuma nasan tana can tana bacci yanxu haka, yaran duk sun tafi kauye sai gobe xa su dawo" Imaan tayi stiff inda take bayan gabanta yayi mugun faduwa jin muryar inna, Mai gadin ya mike da sauri ya amshi wayar yace "Toh Hajiya...." Buda baki inna tayi tana kallonsa tace "Eh lallai baka da da'a, banda barbada kace ma matan gidan Hajiya nima kace min Hajiya, to bari kaji ko wa enda suka dauke ka aiki ma inna suke ce min balle kai, bar gani na haka xuciya mai kyau da rikon gaskiya da amana yasa ka gan ni har yanxu da kyau na, amma wllh da kyar idan ban girmi wanda ya haifi kakanka ba ma" yayi kasa da kai yana murmushi sosai yace "Yi hakuri Baaba tuba nake" inna tace "Kaji min yaro dai" Imaan dai ta kasa tsaye waje daya tayi backing din inna xuciyarta sai bugawa yake, murya can kasa Sadeeq yace "Ur grandmum?" ta gyada masa kai a hankali, kamar ance inna ta daga kai ta gan su, sake baki tayi ta kalli mai gadin tace "Kai wancan ba Imaan bace nake gani a tsaye?" Yace "Ita ce Baaba" Sadeeq yace "Let me go and greet her tunda ta gan mu" imaan dai kasa cewa komai tayi, ta ji kamar ta fashe da kuka, ae kuma shikenan.... Sadeeq na isa gun Inna dake ta kallonsa ya risina ya gaidata da ladabi, tace "Kai ne sabon saurayin nata?" Murmushi Sadeeq yyi ya kasa cewa komai, Inna tace "Ikon Allah, Kai ni fa na haifi ubanta Bukar, jikata ce fa, ita kenan Allah ya ba Bukar fa, a hannuna fa aka haifeta wllh, yanxu d'an nan da ban fito na gan ku ba shikenan, kai a garin ku haka ake yi?? ko bata ce maka kakarta na da rai bane, ita tunda bata da hankalin cewa ka shigo ka gaisheni kai baxa ka yi tunani ka shigo ba, dubi fa yanda ta ji kunya ta kasa juyowa kamar warce ruwa ya cinye" Sadeeq dai sai murmushi yake yace "Dama ai xan shiga in gaida ki kaka, kiyi hakuri" inna tace "Ni dai ba ruwana a dinga abu saboda Allah, tunda dai na kama ka mu je ciki" Yana murmushi ya bi bayanta suka shiga compound din ta rufe gate, tana nuna masa bangaren su Mujaheed tace "Kaga wancan katon ginin?" Yace "Na gani kaka" tace "Toh na wan ubanta ne, barrister suke ce masa, a India yayi karatun lauyancin sa, matansa biyu sai 'ya ya bakwai, Mujaheed shine d'an sa na fari, ina tsaye bakin kofar asibiti aka haifesa, yana nan xaka gansa wani lafcece dogo, da yake ada yana daga wannan karafunan turawan, to da kyar dai Ahmadu ya raba sa da su, nima na dinga rokon Allah har ya daina, a gabana fa ya girma, tun yaye yake wajena iyayen suka bar min, yana gama sakandari dama babansa ya biya masa kudin karatun likita a turai, ai ko in gaya maka babu irin fitsarar da bai koyo a can ba gaskiya, ni dai lkcn da ya dawo ma tsoron sa nake ga wani uban gashi da ya tara, buduwar da xai aura ma yar hayi ce, to sai kaninsa Yusuf, xaka gansa shi kuma wani lagwai lagwai kamar ya karye malam, da ma muka samu ya d'an yi kauri yanxu, sai kaga yanda aka haifesa d'an fiyot, to sauran kuma duk mata ne" Murmushi kawai Sadeeq ke yi yana bin inna, inna ta nuna masa part din su Imaan tace "Toh kaga wannan bangaren na su Imaan ne, Ubanta a can Habuja wajen neman abincinsa yake, ita kadai Allah ya basa a duniya, to dai ya fi babu d'an agwai da bak'in da, uwarta na nan wata bafillatana sai kirki, toh ni kuma kaga akurkin da suka gina min nake rayuwa ciki" ta fadi haka tana nuna masa nata part din.
*The book Imaan is not free, you read for free ur cup of coffee*🤷🏻♀️
It's 300 via Fcmb 3276052019
Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp digit 07087865788 to be included in the payment group.
_23. Imaan
Am bringing this to the notice of my fans, idan xaku biya book din *Imaan* in dai ba digit din nan 👉🏻 07087865788 wato lambata kuka yi ma magana ba to Wllh ba ni kuka biya ma kudi ba, lambata guda daya ne kacal kuma gashi can a sama na rubuta, sannan ni bana amfani da wani kati idan ba Airtel ba, don haka duk wanda ya biya ta wani lamba daban wllh ya karanta hakkina without paying coz every page sai na sa number na da account number amma sai ku tsallake ku tafi kuna biya a gun wa enda ban sani ba ban san da su ba, ni kadai nake harkata a bangaren rubutu bni da wani xae ce ku tura masa xai turo min, talk to me directly through my WhatsApp digit 👉🏻 07087865788, su kuma masu siyar min da littafi har da hada document Billah na bar su da Allah, we shall surely meet in the hereafter in dai hakkina ne in sha Allah. Sannan masu *forwarding* ma su ci gaba there is power in the tongue_
Dariya Sadeeq yayi yace "Haba wannan ai ba laifi kaka" ta tabe baki tace "Mu je dai tukun" suna isa bakin kofa tace "To dai ka gani..." yana murmushi ya shafa kansa yace "Wannan ai ya fi duk sauran kyau kaka, ga shi ba hayaniya ba komai" Inna ta kara tabe baki ta bude kofar tace "Toh Allah ya masu albarka da suka gina min ai dai yafi babu" bin bayan ta yayi cikin parlon dake ta kamshin turaren wuta ta bude fridge