Showing 198001 words to 201000 words out of 303099 words
ce ta Rasulu, waye kuma Mujaheed da xa ki ce ya aurar min Imaan in shiga uku in lalace, Ina Imaan xata kai sa, ke dai wllh fitinanniya ce tirrrr" Mikewa Imaan tayi ta wani hade rai ta nufi kofa, Inna ta hade rai tace "Atoh maxa yi tafiyar ki Imaan kada a sa min ke a bakin duniya, Toh ni dai tunda kin gama ganin kaya tashi kiyi tafiyar ki ta Rasulu ba ruwana kar ki kawo mana rudani a lamarin mu, tunda ke rudaddiya ce, tashi ki tafi haka a gaida su Muhammadu" Ta Rasulu tace "Toh banda Mujaheed din dama wa xai iya da ciwace ciwacen Imaan Allah na tuba, ni fa tunda Uwar Bulasawa ta kore ni da d'ana ta hanamu abinci na tsaneta har yau" Inna tace "Toh ae ba ni da Ahmadu ta kora ba ta Rasulu, kuma ko da ni ta kora ma xuciyata me kyau ce fesss na yafe mata duniya da lahira, ke dai kawai kiyi ta kanki ta Rasulu, bikin ma ni bance lallai sae kin xo ba kar ki kunya ta ni don Allah ki rufa min asiri kiyi xaman ki a gida kin ji???" juyawa Mujaheed yyi ya fita parlon, Inna ta bi sa da harara tace "Waye kuma Mujaheed da xan hada jikata da?? Kai Allah dai ya isa da wannan tunanin naki gaskiya" Washegarin ranan Imaan suka fara jarabawan waec, karfe biyu saura suka tafi yin first paper dinsu, xuwa hudu da wani abu suka gama suka fito, tunda suka fito Maimoon ke kallon Imaan da ta nemi dakali ta xauna, Maimoon ta karasa kusa da ita tace "What happened Imaan?" Imaan ta kalleta a hankali tace "Kamar bana jin dadi" Maimoon tace "Toh sannu yanxu driver xai xo sai mu wuce gida" Mariya ta nufo su tace "Amaryar mu how was today's paper?" Imaan tace "Alhmdllh" Mariya tace "ki taso ku gaisa da Ya sadeeq yana waje, yace in kira ki" Imaan ta d'an turo baki tace "A'a ni dai kice masa baki gan ni ba plss" Mariya tace "C'mon ki taso mu je plss how will I say ban gan ki ba" Maimoon ta dago Imaan tace "Mu je kila ma Driver ya xo" Maimoon na rike da hannunta suka fita wajen gate din makarantar, a hankali Imaan ke tafiya har suka isa gun motar Sadeeq ta tsaya, ya dinga kallonta daga glasses din idonsa yace "What's wrong?" Mariya tace "Nima na tambayeta daxu tace ba komai" bude motar yyi ya fito yana kallonta daga sama har kasa yace "Me ke damun ki?" Kamar xata yi kuka tace "Ina yini?" Yace "I said what's wrong?" Ta sunkuyar da kai tace "I am not feeling fine" Back seat ya bude mata yace "Shiga in ajiye ki gida" ta buda ido sosai tace "Driver dinmu na xuwa" kallonta kawai ya tsaya yi, hakan yasa ta kalli Mariya, Mariya tace "Ki tafi xa mu taho yanxu" Sadeeq yace "Kema shiga mu je may be baxata yi tunanin guduwa xan yi da ita ba" dariya Mariya tayi tace "Toh kuma driver yana hanya, ku tafi kawai xa mu jira shi da su Ummi" ta fadi haka tana nuna masa Ummi dake can tsaye sai kallonsu take suna kallon direction dinta kuma ta dauke kai da sauri, a hankali Imaan ta shiga bayan motar, Mariya kuma ta shiga front seat, ya rufe motar ya xaga ya shiga maxaunin Driver ya tada motar suka bar kofar makarantar, tun da suka dau hanya yake kallonta ta madubi, ita ko ta jinginar da kanta ta rufe ido, har suka isa gida, parking yyi bakin gate yana kallonta ta madubi still, can ya bude motar ya fito ya dawo baya ya xauna, sai a sannan yasan bacci take da gaske, ya kai hannu forehead dinta ta bude ido da sauri ta koma baya, yyi kasa da murya yace "Ina ke maki ciwo?" Ta sunkuyar da kai tace "Ina jin xaxxabi" yace "Tun yaushe??" Tace "Da safe" shiru yyi bai ce komai ba, can ya sauka motar yana kallonta yace "Come down" a hankali ta fara sakkowa motar ya kama hannunta don taimaka mata, xata kwace hannun ya ki saketa, Bata yarda ta kallesa ba ta fito motar, yana kallonta yace "Anjima xan xo maki da drugs" tace "Toh nagode" saketa yyi ta juya xata shiga gate suka yi ido hudu da Mujaheed dake kallonsu yana xaune gun mai kiosk dake layin, ta dauke kai da sauri ta shiga gate din, duk da hada idon da Sadeeq yayi da Mujaheed shigewa motarsa yyi ya tada ya bar layin.
Thanks for d call and text fans...
Allah maimaita mana.... Ameen.
*Imaan isn't for free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
71......
Da daddare Imaan na parlon Inna a kwance ta dalilin kiranta da Sadeeq yyi xai kawo mata magunguna ita kuma bata son fita kofar gida shi sa ma ta taho part din Inna ya sameta a nan, ko tsinke Inna bata bari a parlonta ba cikin kayan da aka kawo na Imaan gaba daya ta kai su daki, dakin ma makulli take sa masa sai in xata shiga ta bude idan ta fito kuma ta kulle ta daure makullin a ha6ar xaninta, Inna dake xaune ta gama cin abinci kenan ta daura kafa daya kan daya ta ta6e baki tace "Ni dai da ki tashi ki lallaba ki koma can bangaren ku ki jirasa, bana son wannan juye juyen da kike min kamar macijiya gaskiya, ni bana son abinda xai gigitani da daddaren nan, Bukar kuma ba kirki ne da shi ba tsaf xai iya cewa a parlona ciwon ya tashi in shiga uku" Ita dai Imaan bata kulata ba, dai dai nan aka yi sallama kofar parlon, Mikewa Inna tayi tana amsawa tace "A'a Bisimillah Bukar, sannu da xuwa" Sadeeq ya shigo parlon, inna ta kinkimo lallausan carpet dinta da ta nade saboda masu shigowa kallon lefe kar su 6ata mata ta shimfida masa, yana murmushi ya xauna ya gaisheta, ta amsa tace "Tun daxu take xaxxabi nace ta tafi gidansu iyayenta su sani ta ki, to dama wannan mutumin Mujaheed da yana nan ne yasan kan xaxxabin, to ban gansa ba kuma nasa Maimuna ta kira min shi nace ga kanwarsa ba lafiya amma shiru bai xo ba, ita kuma lkcn da ba shi da lafiya har cewa tayi a fasa kawo lefenta da kudin aure sai ya ji sauki, su Ahmadu dai ne basu yarda ba, kowa da imaninsa kawai a rabu da shi, shi ya sani...." Sadeeq dake fiddo drugs da ya kawo bai dai ce komai ba, can ya kalli Imaan da ta juya masu baya, Inna tace "Atoh, tsorona daya kada uban yace a nan xaxxabin ya tasar mata kuma ni daxun nan ta shigo min wllh" a hankali yace "How are you feeling?" Shiru Imaan tayi bata ce komai ba, Inna tace "Idonta biyu wllh" Imaan ta hade rai ta juyo sannan ta mike xaune, ledan maganin ya nuna mata yace "Ur drugs with prescription, sai ki sha yanxu" Inna ta tafi kitchen ta dauko ruwan gora da cup tace "Toh tashi ki sha" Sadeeq yace "Ni xan koma Kaka" Inna tace "A'a abinci fa? uwarta ce tayi, da ke ni dama idan ba girkinta ba bana cin na kowa sai in Amina, tuwo ne da miyar agushi yaji kayan hadi, sai kamshi yake xubawa in xubo maka?" Yana d'an murmushi yace "Naci abinci kafin in taho kaka" tace "Toh ko in juye maka ka tafi da shi?" yace "Ai kuma ni da abinci sai gobe idan Allah ya kai mu" Inna tace "Atoh, haka naga Mujaheed ma yake yi, shi in dai karfe tara yyi bai ci abinci da daddare ba to ya gwammace ya kwana haka bai ci komai ba, kaji fa abinci ma sai an masa ka'ida, Ni ko nace aikin banxa, yo ko tsakar dare cikina ya bukaci hakkinsa bana tashi in san yanda nayi na sallamesa ba? Wlh akwai hisabi mai tsanani tsakanin mutum da yan hanjinsa, in dai ka cuce su to ranan gobe kiyama abun baxai maka kyau ba, shi sa ba ruwana ko biyun dare ne naji yyi kugi xan tashi in san abun yi, abinda ga kayan shayi kaca kaca a gidan" Sadeeq ya mike yana murmushi yace "Sai da safe kaka, xa a kiyaye" tace "Toh Allah ya bada ikon kiyayewa" Yana kallon Imaan yace "Sleep tight, Allah ya kara sauki" a hankali tace "Ameen, amma ba wanda xai sani bacci coz I am having 10 o clock paper tomorrow" yace "Not at all, xa ma ki iya tashi cikin dare kiyi karatun ki" daga haka ya nufi kofa Inna tace "Toh baxa ki tashi ki daddage kiyi masa rakiya ba Imaan?" yace "A'a ta sha magani ta kwanta kaka, sae da safe" Inna tace "Atoh, Allah ya tashe mu lafiya, ka gaida iyayen naka, Allah yayi albarka" yace "Ameen kaka nagode" daga haka ya fita parlon ya rufe kofar. imaan sun fara jarabawa da sati guda aka fara shirye shiryen biki a gidan kasancewar biki biyu ne da nata sai Ya Yusuf... yau Friday Imaan na dawowa exams karfe sha daya ta tafi part din Inna, bakin tap ta sameta tana wanke gaba daya buckets dinta da iron sponge da detergent, Imaan ta shiga parlor ta xauna, Sai kusan sha biyu Inna ta shigo tana cewa "Haka kawai, naga bokitai suna son komawa kamar takashin kare, Allah ubangiji ya min tsari, na wanke su tass na shanya kayana ni dai, kuma duk Maimuna ce me min amfani da abokitai gashi sun dauko hanyar dafewa, gaskiya xan kira ubanta ya mana iyaka, idan nata xai siya mata to sai ya siya mata ta rabu da nawa..." Tana kakkabe kujerunta tace "Toh ya jarabawan yau?" Imaan tace "Alhmdllh" Inna tace "Toh Allah ya baku sa'a, sai kiyi kokarin ganin kin cinye jarabawan kin fi kowa, to kin ci abinci kuwa?" Imaan tace "Ni bana jin yunwa" Inna ta tabe baki jin yanda take amsa mata ta gama kakkabe kakkabenta ta dauko tsintsiya, Imaan na kallonta tace "Inna Yaya yana xuwa?" Inna na gyara tsintsiyar hannunta tace "Yaya? Waye kuma Yaya?" Imaan bata ce komai ba, Inna ta tabe baki ta fara sharanta tace "Wai Yaya, to ajiyar Yaya kika bani Imaan? Ina xan ga wani Yaya mutumi na gidansa, ni har na mance rabon da ya tako min nan ma, toh mutumi ya fara sanin dadin aure me xai xo ya min kuma? A'a ni kam kusan sati kenan ban gansa ba" Imaan dai sai kallonta take, Inna ta kalleta tace "Sako xaki bada a ajiye masa?" Imaan ta turo baki tace "A'a kawai na daina ganinsa ne" Inna ta tabe baki tace "Toh ba sai ki shirya ki tafi gidansa ba ko akwai wanda xai hanaki? Ni dai har abada in taka cikin gidansa tunda iyayensa ba so suke ba, to me Mujaheed xai bani wanda Allah bai ban ba? A'a ba ruwana ta kai na nake yanxu, ni ko naje gidan nasa fa ko yar kudin motar nan baya bani, kullum a gantale nake dawowa idan naje wllh, to sai kace uwata tace min je ki kya gani" Imaan tace "Toh ki kirasa" Inna ta kalleta da sauri tace "In kirasa? Ke uban me ya hanaki kiransa, gafara xai min Mujaheed din koko?" Imaan ta hade rai bata ce komai ba, Inna ta ci gaba da sharanta tace "Ni dai kar ki dameni don Allah, waye kuma Mujaheed Allah na tuba" can kuma ta mike ta dauko wayar ta mika mata tace "Toh kirasa dai mu ji" Karban wayar Imaan tayi, tayi dialing number sa ta sa handsfree ta ba Inna, har ya gama ring bai dauka ba Inna ta ajiye wayarta ta ci gaba da abinda take. Ranan lahadi warce Anty ta kira domin yi ma Imaan gyaran jiki ta iso gidan duk da bikin saura sati uku, sati ukun kuma xata yi tana gyara Imaan, kudi ba na wasa ba Aunty xata biyata, matar ta so ace Imaan ko fita baxata dinga yi ba during the period amma hakan baxai yiwu ba sbda exams da take, Tunda Umma taga sananniyar mai gyaran jikin da aka dauko hankalinta yayi mugun tashi, duk gaba daya she is soo confused, sun koma gun mutumi kamar yanda Hajiya Saude tace amma ita fa taga abu sai gaba yake ga biki saura sati uku har xa a fara gyara amarya, tsabar yanda ta sa abun a rai har wani rama tayi abincin kirki bata iya ci, hatta bacci gagaranta yake yi ynxu, ga uban kayan abinci da drinks da aka fara jibgewa a gida na bikin... Anty ce xaune parlor tare da mata mai gyaran jiki tana sake jadadda mata irin gyaran da take so tayi ma Imaan, Matar tace "Baki da matsala Hajiya, ni tsakani da Allah nake aiki na" Anty tace "Toh sai abu na biyu, a wajen kakanta xa a ke gyaran, amma fa kinsan yanda tsoffi suke sai ana yi ana hakuri da kauda kai don Allah..." Dariya matar tayi tace "Ae muna da su Hajiya wannan ba damuwa bane in sha Allahu" Umma dake kitchen ta shirya xata fita amma ta kasa fita duk tana saurarensu, Anty tace "Toh mu je in raka ki bangaren kakar tata..." Mikewa matar tayi rike da Babban jaka, Anty ta dau mata dayan suka fita xuwa part din Inna, sai a sannan Umma ta fito tana danna wayarta, ta kai kunne, Mujaheed dake bedroom dinsa ya fito wanka yana shiryawa ya kalli wayar Safeenah dake gaban mirror yana ring, karasawa yyi ya dau wayar yana kallon screen din, har kiran ya katse kallon wayar yake ganin number Ummarsa, can ya ajiye wayar sai gashi ta sake kira, dauka yyi ya nufi kofa suka kusa cin karo da Safeenah xata shigo dakin, karbe wayar tayi a hannunsa tace "Ka gaji da kwanciyar kayi wanka kenan..." Bai tanka ta ba ya juya yana ci gaba da buttoning din shirt din jikinsa, ita kuma ta fita dakin ta koma nata don daxu da ta shigo ganin ko ya tashi ne ta bar wayar a dakinsa, ta daga kiran ta kai kunne tace "An tashi qlau Hajiya?" Umma tace "Lafiya lau, ya jikin Mujaheed?" Safeenah ta tabe baki tace "Ya warke fa kawai yana pretending ne sbda bai son ina xuwa inda yake tunda ina takurasa sai ya ci abinci ko makamancin haka, wllh har yanxu na rasa gane kan Mujaheed, gaba daya ya ki gaya min damuwarsa duk da dai da sauki yanxu, in dai ya fita aiki ne baya dawowa sai nayi bacci..." Umma tace "Ke ki rabu da shi haka nan yake ba a taba gano inda ya dosa, wani lkcn kuma tsabar miskilanci ne, ni da na haifi kayana kuma, kema ki fita harkansa kawai idan kika ga yana shan kamshi sai ki ga kun dawo dai dai..." Safeenah ta tabe baki tace "Ni ko ina xan sha masa kamshi ya hango wata a waje, gwara inyi ta lallabasa a haka...." Umma tace "Toh ni ba wannan ba, Safeenah shirye shirye dai sai gaba yake a gidanmu don yau ma aka dauko mai gyaran jiki xata fara mata gyara..." Safeenah tace "Saura sati uku fa Hajiya, ba sai a xuba ido ba a ga ikon Allah, idan fa mutum ya fiye axar6a6i da kyar ya dinga ganin abubuwa yanda yake so, ke dai kawai ki xuba masu ido ki daina damun kan ki, auren nan ance ko an daura bai fi na minti goma ba in ma an daura kenan to me xai dameki, ni ban cika yarda da irin mutanen nan ba amma gaskiya mutumin nan da alama yana da gaskiya sosai, duka duka nawa ya amsa wajen mu..." Umma ta sauke ajiyar xuciya tace "Ban son in sakankance ne da maganar mutumi a xo ayi abun nan Ina ji Ina gani, wllh da na shiga uku, shi sa gwara in buga nan in buga can, yanxu ma xan je gidan Hajiya Balaraba" Safeenah ta tabe baki tace "Toh ni dai sai mun yi waya xan hada ma mijina breakfast ya tashi" Bata jira cewar Umma ba ta katse wayar ta ajiye ta ja tsaki tace "Ance maki ba don abinda Mujaheed yyi min sbda yarinyar da irin rainin da take min xan bata lkcina a kan abinda ya dame ki ne, nima ta kaina nake shi sa na xage" shiru tayi tana imagining ace da gaske d'an Bulasawa ya auri Imaan, Tabb har takasu ma xata iya dinga yi ita surkar Bulasawa, kawai wataran sai a wani xo da motoci kusan biyar gidanta a sunan Imaan ce ta xo gaida Yayanta, ta sakko daga motar da gwalagwalai iri iri tana yatsine yatsine tana mata kallon banxa, tabbb, da sauri Safeenah ta kauda tunanin a ranta tana cewa Allah ya kiyaye hakan ma baxae faru ba, in sha Allahu talaka bawan Allah xa ki aura ki xo gidana in taka ki yanda nake so in walakantaki, murmushi Safeenah tayi wai ta hango imaan ta xo ce ma Mujaheed basu da abinci a gida shi kuma yace ta debo mata a nasu ta bata, Safeenah ta tabe baki tace "Ae Kyawunta ma baxai bari wannan mafarkin nawa ya xamo gaskiya ba, Allah dai yasa idan an rabata da yaron Bulasawan ba wani mai kudin xai kuma xuwa mata ba don wannan shine anyi ba ayi ba...." Safeenah ta d'an yi murmushi a ranta tace muna wargaza auren nan xa mu yi mata maganin bakin jini in sha Allahu, ita da aure sai dai taga wasu na yi, shiru tayi tana tunanin to kada kuma fa ta rasa miji wataran iyayen suce a hadata da yayanta tunda da aure tsakaninsu.... sosai gaban Safeenah ya fadi ta xauna gefen gado da sauri xuciyarta na bugawa, lkci daya ta girgixa kai tace "A'a gwara dai a rabata da d'an Bulasawan kawai, duk tsiyarta kuma baxata sake samun kamarsa ba sai