Showing 147001 words to 150000 words out of 303099 words
jiya nace mata ta shirya da safe xa mu tafi tare tunda wannan yarinya Maryam dangin ubanta sun xo sun tafi da ita jiya da magariba... Kai ku dai baku da tsari gaskiya... Meye kuma baccin safe??" Shi dai Daddy bai ce komai ba, Ammi ta fito daga kitchen ta gaida Inna sannan ta tafi dakin Imaan ta tasheta... Inna na ta xaune parlor ta tsuke fuska har imaan ta fito bayan kusan minti talatin cikin atamfa riga da skirt na biki da aka masu bata sa ba, sosai kayan suka amsheta, Inna tace "Ki dauko mayafi mu tafi idan munje can kya karya gaskiya...." Ammi da Daddy suka kalleta, can Ammi tace "A'a inna da dai ta karya ai bata da 6ata lkci wajen cin abinci, ta je gidan mutane da sassafe...." A fusace Inna tace "Ke dai Aisha ki daina haka, ki dinga jin tsoron Allah, Gidan Mujaheed din ne gidan mutane idan ba walakanci ba, gidan Mujaheed ne fa, ni dai ku dinga tsoron Allah sai kace wanda xata gidan 6are? Ke dauko hijabinki mu tafi, shi gidan yayan nata xaki ce ma gidan mutane saboda baki da mutunci..." Tana fadin haka ta nufi kofa a fusace, Daddy ya tabe baki bai dai ce komai ba, Imaan ta sa hijab ta dauko takalminta da wayarta tana kallon parent din nata a hankali tace "Sai mun dawo" Daddy kadai ne yace "Allah ya kiyaye" Ammi kam bata ce komai ba sai aikin gabanta take.
*Imaan isn't for free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
52.....
Suna fitowa compound Inna ta kalli Imaan tace "Toh ko dai in je inyi ma Ahmadu magana ya sa direba ya kai mu?" Imaan dai bata ce komai ba, Inna tayi tsaki tace "Ayi ta maki magana kina ma mutane shiru idan ma baccin ne bai isheki ba idan munje gidan Mujaheed din ba sai a baki daki daya ki kwanta kiyi ta yi ba, ai can ma gida ne" Daga haka ta nufi part din Abba imaan na biye da ita, Aunty ce parlor tana goge goge da su Maimoon, Aunty ta xauna ta gaida Inna, su Maimoon ma suka gaisheta, Inna ta amsa tace "Gidan shiru ba wannan mata Rukayya koh" Ita dai Aunty bata ce komai ba, Inna tace "Toh Ahmadu nake nema ya kira wannan mutumi me jan mota ya kai mu gidan Mujaheed, tun asuba na gama shiryawa Imaan ta bata min lkci" Aunty tace "Toh xauna Inna ki jira driver din an aike sa yanxu" Inna ta xauna tace "So dai ake in makara kawai, Banda haka ni fa tun Asuba nayi wanka na" Imaan ta xauna a parlon bayan ta gaida Aunty tana kallon series din da akeyi, ba a dau lkci ba driver ya dawo, Aunty na kallon Inna dake xuba gyangyadi tace "Toh ya dawo fa inna..." Inna ta bude ido da sauri ta mike tace "Toh tashi mu je imaan, shi Ahmadun baya nan ne?" Aunty tace "Bacci yake" Inna tace "Ni dai ba wajena suka gaji baccin safe kamar rubabbu ba gaskiya" daga haka ta fita imaan na biye da ita, a waje suka tadda driver da mota, imaan ta bude ma Inna motar ta shiga tana amsa gaisuwar driver din sannan imaan ma ta shiga, sai da suka hau saman titi Inna na kallon Imaan tace "Toh kin gaya masa anguwar ne" Drivern na murmushi yace "Ae na san gidan kaka" Inna ta washe baki tace "Ashe har ku kunje kun sa ma gidan albarka ku ma" Shi dai bai ce komai ba yana murmushi, tafiyar kusan minti ashirin suka yi suka iso gidan Mujaheed, Inna na kallon driver da yayi parking a waje tace "Kai ya haka ka danna han a bude maka gate ka shiga mana, gidan jikana ne fa" Horn driver yyi mai gadi ya fito yana kallonsa, can ya karaso gun motar yace "Daga ina?" Rike baki Inna tayi da mamaki tana kallonsa tace "Naga abinda ya isheni, kai gidan jikana ne fa kake tambayar daga ina? Na shiga uku wai ni yake tambaya daga Ina, ko in sauko in bude get din da kai na ne" Mai gadin yyi kasa da kai yace "Yi hakuri Baaba" daga haka ya tafi da sauri ya bude gate din, Inna ta ja tsaki tace "Mutane dai ba tsoron Allah... wai daga Ina, ke ki ji fa gantalalle amma ba laifinsa bane na Mujaheed ne da bai sanar masa kakarsa na da rai ba" Ita dai Imaan bata ce komai ba driver ne ke bata hakuri, yana gama parking imaan ta bude motar ta fito, Inna na kallon driver din tace "Toh yi wucewar ka yaro, mu da gida kuma sai bayan isha in sha Allah" Yace "Toh baaba ku dawo lafiya" Inna ta nufi entrance din shiga gidan tana washe baki, Imaan dai na biye da ita, Bubbuga kofa Inna ta shiga yi da karfi tana cewa "Salama alaikum" Imaan tace "Kai inna kiyi a hankali mana..." Matsawa Inna tayi ta bude baki tana kallonta, Imaan ta turo baki ta danna bell tace "Kawai kiyi ta bubbuga ma mutane kofa da karfi" Inna xata yi magana aka bude kofar, Inna ta washe baki tana kallonsa tace "Mujaheed...." Kallonsu kawai yake yana tsaye bakin kofar sanye da jallabiya, Inna ta rike haba tace "Ashe da gaske ba ku tashi ba kenan" rabawa tayi ta gefensa kamar yar yarinya ta shige parlon, Imaan ta juya tana murmushi, can dai ta juyo a hankali, kallonta taga yana yi, ta sunkuyar da kai tace "Ina kwana Yaya" Muryar Inna suka ji a parlor tace "Ina amaryar??" Mujaheed ya juya ya koma parlon, Imaan ta bi bayansa, Xaunawa yyi yana kallon Inna yace "Ina kwana?" ta washe baki tace "Lafiya lau Mujaheed, tun asuba da na tashi nayi wanka wllh, Banda imaan da ta bata min lkci da tun gari bai gama wayewa ba xa ku gan ni" shafa kansa yyi bai dai ce komai ba, Inna na kallon pillow da aka ajiye kan lallausan sabon rug din parlon tace "Cewa nayi ina amaryar" Mujaheed yace "Tana sama...." Yana fadin haka ya tashi ya wuce sama, Inna ta kara kallon pillow dake parlor murya can kasa tace "Toh waye kuma ya kwana a parlor ni patuu" Imaan tayi murmushi tace "Toh ke ina ruwan ki" Inna tace "Atohhh, ba ruwana kuwa" Cire Hijab Inna tayi ta linke tana kallon parlon tana murmushi tace "Sabon gida ba dai sha'awa ba" Mikewa tayi ta nufi wani kofa ta bude tana lekan ciki ta karasa ta ajiye hijab din nata a ciki ta fito ta rufe tace "Dakinsu Hansai ne, shi ma sun xuba lafiyayyun kaya a ciki wllh masu tsada...." tabe baki tayi ta tafi ta bude kofar kitchen tana lekan ciki ta xaro ido tace "Waiii.... Ai kitchen din ma ba masaka tsinke da kayan kitchen na xamani, Ashe dai ba gwalagwalan karya aka dinga yawo da shi ranan casu ba" Imaan dai ta hade rai sai kallonta take... Mujaheed na haurawa sama ya bude dakin da Safeenah ke ciki, bacci ya sameta tana yi, ya shiga ya kulle kofar ya karasa kan gadon ya d'an bugi gadon yana kallonta, sai da ya buga gadon da karfi for d second time sannan ta bude ido ta mike xaune tana kallonsa da wani expression, yace "Kin ma yi sllhn kuwa?" D'an tsaki tayi tace "Haba don Allah sai ka wani buga gado ka tsorata ni kamar xaka tada kato??" Daga head har toes yake kallonta, ta tabe baki ta kalli agogo tace "Sllh dai dole inyi ko karfe nawa ne" da mamaki yake kallonta yace "A gidan ku haka kike kai wa har karfe tara baki yi sllh ba Safeenah?" A fusace tace "Toh gajiyan bikin fa? Plss Mujaheed that's not how to treat a new bride you are not romantic, haba don Allah sai kace mun ta6a rayuwa gida daya...." Wani kallo kawai Mujaheed yake mata, strictly yace "Look Safeenah I won't tolerate this, gidana ba na kafurai bane, tun asuba na shigo na tashe ki kiyi sllh shine har yanxu baki yi ba, is this ur home training?" Yar dariya tayi tana kallonsa daga sama har kasa tace "Kai ko kunya baka ji ba don Allah??" tana kwaikwayonsa tace "Wai wani tun asuba na shigo na tashe ki.. ban taba jin labarin ango irin ka ba sai yau da nake gani a xahiri a gidana, wai ka shigo min da asuba, ain't you ashame of ur self plss" murguda baki tayi ta sauka daga saman gadon da yar figigiyar rigar baccinta ta nufi bathroom, ya bi da kallo kafin ta shiga bayin yace "Ki sameni downstairs yanxu idan kin yi sllhn" daga haka ya juya ya fice daga dakin, Tv ya tarar Inna na kokarin kunnawa tana cewa "Toh sai me idan Baki kunna min ba kamar yau na saba hada kayan kallo kuma... Gidan Mujaheed kuma baxa ki saki jiki kiyi yanda kike so, ban da shi wa gare ki da xa ki je gidansa ki sake jiki dama, ni dai ba ruwana, ki dinga abu domin Allah Banda munafurci" Imaan dai sai kallonta take fuska daure, Inna na ganin Mujaheed ta mike tace "Wai ka ji daga nace ta hada min kayan kallo shine xata ce min daga xuwa gidan mutane, su waye kuma mutane, Mujaheed din koko Amaryar da bata fito gaisheni ba har yanxu, ni dai ba ruwana, idan ma xa ki cire Hijabin nan na jikinki ki linke ki ajiye ki tsayar da ranki waje daya ki saki jiki kamar kina gidan Bukar to gwara ki cire don da kyar ma ba kwana xamu yi a nan ba gaskiya, ga dai dakuna na kirga har hudu ranan" Mujaheed ya karasa ya kunna mata tv din yace "Xata sakko yanxu ta gaishe ki ai" Inna ta koma kan kujera ta xauna ta tsuke fuska tana kallon Tv, Xaunawa Mujaheed yayi kan kujera ya kalli Imaan ta gefen ido, Sai turo baki take, Mujaheed ya kalli Inna yace "Amma kuma sai ki yi irin wannan sammako Inna" Inna ta kallesa da sauri tace "Ni dai Ahmadu ne yace in taho da sassafe, bayan jiya ya shigo da daddare mun yi magana" Imaan ta xaro ido tana kallon Inna, Murmushi Mujaheed yyi yana gyada kai, Jin taku a stairs ya juya, Safeenah ce ke sakkowa sanye da doguwar riga damamme, Still tayi tana kallonsu, Inna ta kankance ido tana kallonta da kyau ita ma, Safeenah ta hade rai ta karasa sakkowa ta shigo cikin parlon, Mujaheed ya kalleta yace "Meet my grandma and my lil sis Imaan...." Inna na washe baki tace "Sannu Amarya, da fatan dai an tashi lafiya" dauke kai Safeenah tayi ta tabe baki murya can ciki tace "Ina kwana" Inna tace "Lafiya lau, sai dai ko sunanki ban sani ba" Mujaheed yace "Safeenah" Inna tace "Toh madalla, to safeenah Mujaheed dai gashi nan a gabana aka haifesa, kuma ni nayi wahala da shi tun yana tsummarsa, ke wahalar da nayi da shi wllh kare baxai ci ba, Tabb banda nakudarsa me Rukayya tayi???" Hade rai Mujaheed yyi yana kallonta, Safeenah tace "Toh maa sha Allah, ina d'an yi abu ne a sama Hajiya...." Xaro ido Inna tayi kafin tace komai Mujaheed yace "Mind you, Inna is what we call her..." Safeenah ta d'an tabe baki tace "Toh xan je in yi abinda ke gabana a sama Inna" Inna tace "Ba xancen kije kiyi abinda ke gaban ki ba Yar nan, ko karyawa fa ba mu yi ba, Imaan ma ina jin ko wanka bata yi ba don da naje ma bacci na tarar tana yi...." Imaan na kallon Inna tace "Ni bance maki ban yi wanka ba inna" wani matsiyacin kallon Safeenah ta jefa mata sannan ta kalli inna bluntly tace "Ba a kai ga sauke min gara na daga container da ya kawo ba, ba komai yanxu haka s gidan" Wani kallo Mujaheed ya dinga mata trying hard to control his temper, inna ta rike ha6a tana kallonsa tace "toh me ku ke ci a gidan ba a sauke gara ba ni 'ya su?" Safeenah tayi wucewarta sama, Mikewa Mujaheed yyi ya bi bayanta, yana shiga dakin ya kulle kofar yana nunata da yatsa cikin tsawa yace "Let me give you this warning Safeenah, idan baki son na fito maki da the other side of me you've got to respect that woman to the fullest, she is my grandma kuma albarkacin ta yasa kike gidana, wllh wllh xan yi taking action din da xai baki mugun mamaki idan baki maida hankalin ki ba, sannan breakfast ni nace ki tashi ki fita kije ki girka masu yanxun nan...." A tsawace ya kare maganan yana kallonta, Gaba daya ta gama tsorata sai kallonsa take tana komawa baya, lkci daya hawaye ya kawo idonta sai kuma ta fashe da kuka tace "Is this the real you dama Mujaheed?? me yasa tun farko baka yi encourage dina wajen ganin nayi kokarin hakura da kai ba, you are always telling me xaka koyi sona I shouldn't worry, dama ka aureni ne to make life a living hell for me, kasan irin mutanen da na ki amincewa da nace sai kai?? Kasan mutanen da na watsa ma kasa a ido nace sai kai, dama laifine son mutum da xuciya daya?? Tun da aka kawo ni gidan nan ka ki ko da xama na minti ashirin a dakina balle ka kwana, wllh ina sonka Mujaheed, ban aure ka saboda komai ba sai saboda Ina son kasancewa da kai, ka dai san irin gidan da na fito balle kace saboda wani abu naka na aure ka" dauke kai Mujaheed yyi xuciyarsa na bugawa, right from time a rayuwar sa na duniya ya tsani ganin hawayen mace, a hankali ya karasa inda take ya xauna gefen gadon ya jawota jikinsa cikin sanyin murya yace "I won't make my home a living hell for you Safeenah, and sure I will create a soft spot for you soon, but you've got to respect my family, duk abinda nace bana so kuma plss try to avoid that, Kinga ke yan uwanki baxa su xo in masu gaisuwar walakancin da kika ma grandma dita ba...." lamo tayi jikinsa tace "Amma kana ganin wannan yarinyar fa bata gaisheni ba ma" Shiru ya d'an yi, Sai kuma yace "Mind you sunanta Imaan, and kar ki damu xan mata magana" tace "Step sis dinka ce?" Ya girgixa kai a hankali yace "She is my cousin sis" daga kai tayi tana kallonsa, ya gyada mata kai, tabe baki tayi bata ce komai ba, yace "Toh for my sake kiyi hakuri ki hada breakfast din even if it's just Irish and egg, sai ki dafa ruwan shayi" Shiru tayi masa yace "Xa ki yi?" A hankali tace "Toh" murmushi yyi ya manna mata kiss a goshinta, ta lumshe ido don ba kadan ba taji dadin hakan, ya mike yace "Come out soon" daga haka ya nufi kofa ta bi sa da kallo, Allah yasan so ba na wasa ba take ma Mujaheed, Bata taba yi ma d'a namiji irin son da take masa ba, kuma xata iya yin komai a kansa. Mujaheed na dawowa parlor ya tadda Imaan kadai tana kallo, tun da ta kallesa sau daya ta dauke kai, ya isa kusa da ita yace "Me yasa baki gaida Safeenah ba?" Ta turo baki ta ki cewa komai, ya dafa kujeran da take xaune yana kallonta da kyau yace "Look, duk kika xo gidan nan ko kika ganta a wani waje dolenki ki gaidata coz she is my wife... Kin ji abinda nace??" Ta hade rai tace "Toh ai ita ma ba da respect ta gaida Inna ba da ta sakko, so why will I greet her, why??? beside she is suppose to tell me... Sannu da xuwa kafin in gaisheta, amma ko kallona bata yi ba so nima naki gaisheta din ai ba wajenta muka xo ba...." Kallonta kawai yake ganin yanda take maganar cike da tsiwa tana xare masa ido, ya dauke kai ya d'an yi murmushi, can dai ya mike ya nufi kitchen jin muryar Inna kasa kasa ita kadai tana magana, tsaye yyi bakin kofa yana kallonta tana duke tana fere dankali tana cewa "Idan ba jaraba ba da safen ma ya wani bi figaggiyar mata kamar xabiya daki bayan kwana da yayi a dakin daren jiya, to meye xasu shige daki kuma da safe bayan nace masu ban karya ba ga 'yar mutane na taho da ita, ita ma bata karya ba, dama da ya iyayenta suka yarda ta biyoni, ni dai ba ruwana..." Dariya sosai ta basa, tana ganinsa tayi shiru tace "A'a har ka fito Mujaheed" yace "Dankali kike ferewa da kanki kuma?" Inna tace "Yo baxan fere ba tunda na kwaso yunwar cikina Mujaheed, ga Imaan ma bata karya ba da kyar Bukar ya yarda ta biyo ni... Abu dai da raina da lafiya ta, ita wancan matar dake xaune parlor tace ba ruwanta baxata shiga kitchen din mutane ba, ni ban gane ma wannan abun ba gaskiya" ya shafa kansa yace "Yanxu Safeenah xata xo ta hada maku kayan karin" inna ta ajiye wukar tace "Toh amma anya ka ce mata nice na raine ka kuwa...." Safeenah na sakkowa parlor ta dinga yi ma Imaan wani kallo sak na tsana tana tafiya, suna hada ido Imaan ta tabe baki ta dauke kai.... Tsayawa Safeenah tayi tana kallonta xuciyarta na tafarfasa tace "Beware a gidana kike.... you had better respect ur self ki maida hankalin ki" Kallonta Imaan tayi da sauri tace "Gidan ki ko gidan yayana? Gidan ku na can kin baro sa malama don haka baki isa ki min warning a gidan Yaya ba...." Da sauri Inna ta karasa fitowa kitchen jin muryar imaan, Mujaheed ma ya fito ya tsaya kallonsu da mamaki, Inna tace "Lafiya?? me ya faru??" Imaan tace "Wai inna ki ji ce min take in shiga hankalina wai nan