Showing 129001 words to 132000 words out of 303099 words
yi kuka tace "That's just it, ni scalp dina ma ciwo yake min, aje ayi ta ja min gashi kaina ya fara min ciwo, ni dai kawai ku tafi kice masu baki gan ni ba" Maryam tayi dariya tace "Kai Imaan, da ni ke da irin gashin ki ai duk sati sai naje saloon" ita dai Imaan bata ce komai ba, Sadeeq ne ya fado mata ta tuna wata rana da daddare suna waya yake ce mata shi dai yana son dogon gashi, haka kawai taji tana ma son xuwa saloon din, Maryam ta gama yafa karamin veil din abayar jikinta tace "Ohk then xan ce masu ni ban gan ki ba" Imaan tace "Ko kuma ma dai kawai bari mu je, idan ya so ana gama mana sai mu tafi mu siya abinda xa mu siya a shopping mall, koh?" Maryam ta wara ido kamar baxata ce komai ba sai kuma tace "Ehh haka ne kuma" Imaan tace "Kinsan fa gobe ne birthday din kuma I have to give him the gift this night" Maryam tace "Au haba, same day da bikin Ya Mujaheed kenan?" Imaan tace "Sure" Maryam tace "Tabdi, Toh yanxu ya xa ki yi? Ga biki ga birthday" Imaan tayi yar dariya tace "Ni ina ruwana da biki, Ai na riga na ce ma Daddy xan je gidan Gwaggwon Ammina gobe da safe" Maryam ta marairaice tace "Tafiya xa kiyi ki bar ni yanxu?" Imaan tace "Of course no, tare xa mu ai" Maryam ta langwabar da kai tace "Yanxu haka xa mu yi missing bikin ya MA, gashi ma anjima da daddare xa ayi dinner fa" Imaan tace "Aa idan kinga xaki tsaya ki tsaya ni dai ba ruwana" Maryam tayi murmushi tace "Aa mu je gidan grandma din dai..." Imaan tace "Better" a tare suka fita dakin, Ammi dake parlor ta nuna ma Imaan kan kujera tace "Ga kayan ku nan ki shiga da shi ciki yanxu aka kawo" Imaan ta dauko ta kai daki sannan ta fito, sosai gaban Imaan ya fadi ganin Mujaheed parking space a tsaye, tun da ya kalleta sau daya ya ci gaba da danna wayarsa, ta dauke kai ta isa gun motar da ake kai su makaranta tana kallon Maimoon, Maryam kuma ta tafi gun Mujaheed tana murmushi tace "Our handsome groom..." Imaan ta tabe baki tana kallon Maimoon tace "Ina Drivern da xai kai mu Saloon din?" Maimoon tace "Ya Mujaheed yace xai ajiye mu shima fita xai yi yanxu" Xaro ido imaan tayi tana kallonta, ta hade rai bata dai ce komai ba, Ummi ta fito bangarensu tana kallon Mujaheed tace "Rahma xata taho daga baya, wai xa su fita tare da Umma yanxu" bude driver seat Mujaheed yyi ya shiga yana kallon Maryam yace "Har da ke xa aje gyaran gashin?" Ta xaro ido tace "Eh mana" murmushi yayi yace "Toh shiga..." imaan ta bi bayan Maimoon tana cika tana batsewa ta shiga back seat, Ummi ma ta shiga. Suna isa saloon din yyi parking yana kallon Maimoon ta madubi yace "Since babu mutane sosai a saloon din xan jira ku gama" Maimoon ta washe baki tace "Tohh mun gode Ya Mujaheed" a fusace imaan ta fice a motar ta bar door din a bude cikin tsawa yace "Keee" juyowa tayi da sauri, fuska daure yace "Xo ki rufe min mota kada in sauka in xane ki yanxu" Ganin babu wasa tattare da shi ta dawo kamar xata yi kuka ta rufe motar ta juya ta shiga saloon din, Maryam tayi murmushi tace "Ya M.A kai dai kawai kayi tafiyarka ko motorcycle din nan mai kafa uku sai mu hau ya dawo da mu gida" Mujaheed yace "Sauka kije kiyi abinda ya kawo ki nan" Yar dariyar yake tayi ta bude motar ta fita, ita kanta bata ji dadin jiransu da yace xai yi ba, shikenan ya ruguje masu plan. gyara ma Imaan gashi ake amma gaba daya hankalinta na gun lekan waje don ganin ko Mujaheed ya canxa mind dinsa ya tafi, amma duk ta leka sai taga yana nan, ta ji kamar ta kurma ihu, a haka har aka gama masu gyaran gashin aka fara masu lalle a hannu, Maimoon ce ta fara fita bayan an gama masu, Ummi ma ta fita, Maryam na kallon Imaan a hankali tace "Kinga yayi spoiling plan dinmu ko, yanxu how are we going to get the gift?" Imaan ta rasa abinda xata ce mata, can Maryam tace "You know what, kawai mu koma gida, dama akwai few abubuwan da nace ma mum xan siya a Nigeria, muna isa gida yanxu xan amshi card dinta mu fita daga can ma sai in siya abubuwan da nace" Sosai hankalin imaan ya kwanta, ta d'an yi murmushi tace "Toh shikenan, har naji dadi" tashi Imaan tayi suka fita saloon din din Maimoon ta bada kudin kafin su fita, tun da suka fito Mujaheed ke kallonsu ta madubi har suka iso gun motar, ganin Ummi xaune a gaba Maryam ta shiga back seat tare da Imaan, tada motar yayi ya dau hanyar gida. Suna isa gida Mujaheed yayi parking ya kashe motar, Imaan ta fita ta dau hanyar apartment dinsu, ya gyada kai yana bin ta da ido ta madubi... Maryam tace "Mun gode ya M.A" bai amsa ta ba tayi wucewarta tana murmushi. Maryam na gaya ma mama Hadiza xata fita shopping ta hanata wai bayan biki sai su je, ba ynda Maryam ta iya ta koma dakin Imaan a sanyaye ta sanar mata abinda mamarta tace, imaan ta rasa yanda xata yi, Maryam tace "Toh ko mu bari kawai gobe da safe idan mun fita xa mu gidan grandma dinki sai mu shiga mu siya" a hankali Imaan tace "Noo yau ya kamata in basa, yau nake son in basa" Shiru Maryam tayi, can tace "Ba xa mu je dinner ba anjima, kawai mu jira sai mutane sun cika wajen sai in sulale da makullin motar Yaya Yusuf mu je mu dawo" Imaan ta xaro ido Tace "Ni fa ban yi niyyar xuwa dinner din ba wllh" Maryam tace "Ae ko gwara ki daura niyyar xuwa yanxu, don that's the only way out" Imaan tace "Toh shikenan" Ana idar da Magrib duk aka gama shirin tafiya wajen dinner, duk wannan abun Mujaheed na lura da su keenly, kuma yaki tafiya duk da yanda abokansa suka dinga takurasa su wuce saboda amarya har ta iso wajen, Maryam dai ta dinga bin Yusuf wai ya bata makullinsa tayi driving din, daga karshe dai babu yanda ya iya ya bata, da kyar imaan ta saka gyale a kan ankon su na Dinner da Daddy yayi masu gaba daya gidan, tayi kyau har ta gaji amma sai wani nonnokewa take abunka da ba sabon ba, Maryam ce tayi driving din nasu xuwa hall din da xa ayi dinner din.... Waje ya cika makil da masu kudi sai ruwan naira ake tun kan a fara komai, Fara'a gun umma ba a cewa komai, Inna na xaune tare da ta rasulu a table guda duk sun sha atamfar England an yafa gyale sun tsuke fuska suna kallon ikon Allah, Imaan na shigowa hall din tare da su Maryam ganin Inna da ta rasulu ta rufe fuskarta gyalen jikinta ta dinga ba66aka dariya, suka nemi waje suka xauna, kallon inda amarya da ango ke xaune tayi, taga Safeenah da tayi wani kyau irin na aljanu sai sheki gwalgwalan jikinta suke, kayan jikinta kam dama ba acewa komai, ta kalli Mujaheed da ya sa lafiyayyen farin gezna sai walkiya yake, hada ido suka yi da shi tayi saurin kauda kai, Imaan ta kalli Maryam tace "Ni dai xan koma gun su Inna kafin mu fita" bata jira cewar Maryam ba ta mike ta tafi gun su Inna Mujaheed ya bi ta da ido.
*Imaan isn't for free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
46....
Inna na kallon Imaan da ta xauna kusa da ita cike da damuwa tace "Toh ba gashi kin fito sak mutum ba yau kin sa gyale, amma da kullum da hijabi xulum xulum kamar matar ladani..." Ta rasulu dake ta bin jama'ah da kallo tace "Toh wai ni abinda na kasa ganewa a nan shine... uwar amaryar da danginta basu san kin xo nan bane ban ga an xo gaishe ki ba har yanxu, dubi fa yanda muke xaune kamar gantalallu marasu makabuli babu wanda ya bi ta kan mu, an san ke kika raini Mujaheed tun yana tsumma kuwa, Kai duniya dai ta lalace ni ta rasulu" Inna ta tabe baki tace "Shine nake ta kallon ikon Allah, sai yawo suke mana da gwalagwalai kamar barayi babu wanda ya xo ya durkusa nan yace Sannu Inna... ya taro? To Allah ya sanya alkhairi ya nuna mana na 'yan baya, shi kuma Mujaheed din dubi yanda ya wani yi tsamo tsamo da shi kusa da amaryar babu walwala kamar dai wanda aka tilasta ya xo casun..." Imaan tayi murmushi ta kalli Mujaheed sannan ta kalli Inna tace "Toh ke ina ruwanki..." Inna tace "A'a da ruwana mana, ni ba karamin aikina bane in tashi inje samesa yanxu in ji ko lafiya..." Ta rasulu tace "Maxa je ki, nima naga rashin walwalan yayi yawa sai yake kawai yake, kamar wanda aka ma dole, anya ma auren soyayya xai yi kuwa" Inna ta tabe baki ta mike tace "Toh wani ya rainan min shi da baxan sani ba idan yana cikin damuwa ko akasin haka, sarai nasan sa ciki da bai, da abinda ke damunsa a xuciyarsa xaman da yayi a nan" Kutsawa ta dinga yi cikin mutane wanda yaki matsawa dama hankadesa take tana cewa "Yau naga bala'i mutane an xo cin shinkafa da yar kaza kamar mayu, an ki bani hanya..." Kallonta aka dinga yi ana bata hanya tace "Banda jaraba ko wacce ta fiddo kayanta na karkashin akwati ta saka ta xo mana nan tana jiran shinkafa da salaq da kaza, ohh yunwa ta yi yawa a duniya" A haka har ta isa inda amarya da ango ke xaune, wata kawar amarya ce tsaye tana bada history din amarya sai wani yauki take tana jujjuya idanuwanta, cool music sai tashi yake mutane na mata tafi... sake baki Inna tayi tana kallon yarinyar, can dai ta karasa inda take tsaye ta d'an ta6o ta a kafada, gaba daya wa enda suka san Inna suka xaro ido suna kallon ikon Allah, juyowa budurwar tayi tana kallon inna murmushi dauke fuskarta, Inna ta matsa kusa da ita sosai murya can kasa tace "Wani tsinannan telan kika ba kayan ki ya lalata maki haka saboda rashin tsoron Allah, duk duwaiwuka a waje?" Ba karamin tsorata da girgixa Inna tayi ba tana xare ido jin muryarta ya kauraye makeken hall din gaba daya ta cikin speakers, Hall ya rikice da dariya, Mujaheed ya sunkuyar da kansa, Umma ta kasa motsi inda take tsaye sai hadiye abu take da kyar, Imaan ta hade kai da table tana dariya kasa kasa, su Maimoon ma suna ta dariya daga inda suke xaune, Aunty da Ammi da Mama Hadiza dama tagumi suka yi suna kallon Inna da tayi tsamo tsamo a gaban hall sai kallon jama'ah dake dariya take, gaba daya yan uwan amarya wani kallo suka dinga yi ma inna, ita kuwa mai bada history ta ji kamar ta nutse gashi an ki daina dariya a hall, Safeenah ta wani hade rai tana kallon Mujaheed tace "Haba Mujaheed dama gate pass din wa enda suka kamata da wanda basu kamata ba ku ka dinga raba ma suka shigo mana nan, dubi wannan tsohuwar me ya kawota nan ta ina ta samu pass din shigowa har xata kunyata aminiyata cikin mutane, kasan Yar gidan wacece ita kuwa??" Gently Mujaheed yace "Watch ur words..." A fusace tace "Don't tell me that Mujaheed, how dare the old woman insult my friend that way, yar gidan governor ce fa tsaye a wajen..." Calmly yace "Ko yar gidan uban wacece, ke kawarki ce, to ni kuma grandmum dita ce a kusa da ita, so you dare not look into my face and say nonsense about her" Wani kallo Safeenah ta dinga ma Inna da ta tabe baki cikin sanyin murya tace "Ba lafiya, dama ba a sirri a nan, daga magana kuma sai sipikoki su dauka su min terere...." Juyawa tayi ta kalli yarinyar da ta kasa cewa komai har sannan tace "Ki dai maida masa ya gyara maki ai kudi kika biya ya cuce ki ya maki wannan dinkin" daga haka ta bar wajen ta tafi gun Mujaheed, har sannan Safeenah bata daina bin ta da wani irin kallo ba har ta iso inda suke tana kallon Mujaheed tana washe baki tace "Wannan ce amaryar Mujaheed" Safeenah ta dauke kai fuska daure, Inna ta rike ha6a tace "Ikon Allah, Toh Allah ya bada xaman lafiya, ta dai sha gwalagwalai maa sha Allah" Hajiyan Marafa ce tsaye kan Umma tana bala'i a mugun fusace tana cewa "Haba Rukayya ke baki ga irin manyan mutanen da muke ba gate pass bane xa ku ba wannan tsohuwa mai wanke wanke ta shigo mana hall tana shirme tana kunyata mutane, kin san yar gidan wacece tsaye a wajen take magana kuwa?? reputation dina da na 'ya ta kuke son 6atawa ko meye hakan?" Umma dai sai hakuri take bata a rikice tana cewa "Wllh ban san wanda ya bata pass din ba, don Allah kiyi hakuri Hajiya, wllh ban san daga inda ta taho ba...." A mugun fusace Hajiyan Marafa tace "Toh maxa ki sa a fitar da ita daga hall din nan tun wuri kada ayi mummunan abu a nan, maxa a fita da ita kada in sa masu gadi su fitar min da ita ta tsiya" Umma sai cewa take kiyi hakuri Hajiya xa ta tafi yanxun nan kuwa, ae ba ku kadai ta kunyata ba har mu wllh, ban san wanda ya bata pass ta shigo ba ni ban ma santa ba, haka irin tsoffin nan suke idan suka ga ana taro su shigo cikin jama'ah" Hajiyan Marafa ta juya fuu ta wuce tana cewa "Maxa ta bar nan kada in sa masu gadi su ja ta su fitar..." Inna na kallon Mujaheed tace "Toh naga duk baka da walwala lafiya kuwa, ko baka ci abinci bne?" Ya girgixa kai yace "Ba komai, ki koma kiyi xaman ki" Inna tace "Toh madallah sai dai har yanxu mu dai babu abinci babu labarinsa, ga ta rasulu can ma sai hamma take" Tana magana ta dau tsadadden drink dake gabansu tace "Ko in dau wannan" yace "Dauka" dauka tayi tace "Toh shikenan, Allah dai yasa ba mai halin uwarka xaka auro mana ba dai" daga haka tayi wucewarta, Safeenah ta bi ta da wani harara tana kyabe baki, Umma ta rasa yanda xata yi ta fitar da Inna a hall din cikin lumana, duk ta rikice taje can taje nan, Inna na dawowa xuwa seat dinta ta dinga cewa mutane "To dai duk wanda ya ci abu yyi hakuri ya saka gwangwani ko kwalin a jakarsa kada mu bata masu waje da kazanta mu cuce su...." A haka har ta koma gunta, ta ajiye ma ta rasulu drink din daya ta ajiye daya gabanta tace "Ma rage xafi..." Ta dau drink din ta fara budewa, Inna ta xauna tace "Naje na samesa amma kinsan ko gaisheni amaryar bata yi ba, ni dai ban kulata ba, ba ruwana kada in kunyata kai na cikin jama'ah ga ni babba, taro yayi taro in je inyi magana in kunyata Mujaheed din ma gaba daya, bakina a leko na juyo na dawo ai ana tare...." Ta rasulu tace "Gwara da baki kulata ba kam, ki bari sai an kaita dakin nata ki shirya kije ki mata tatas ki gaya mata yanda kike da Mujaheed" Inna tace "Ehh dama ai dole in sanar mata wahalan da nayi da shi don ta gane matsayina a wajensa, ana kai ta da washegari dama Imaan xan ce ta rakani inje in karanta mata yanda muke da shi" Umma ce ta taho gun Inna da sauri tana haki tace "Inna yanxu aka kirani wai ruwa ya cika parlon ki sai kwararowa waje yake ga kofar a rufe, ko dai kin bar pampon bayan gidan ki a bude baki sani ba?" Inna ta mike ta rafka uban salati a rude tace "Hadiza ta cuce ni ita ta shiga bandakin karshe tayi fitsari, shikenan ruwa ya shanye min gida na shiga uku na lalace ni patuu, ga dukiyoyi irinsu kujeru, tv, gado carpet, fridge duk a ciki" ta rasulu dake xabga salatin ita ma ta mike tace "Na shiga uku ni ta rasulu, jakata na dakin nima har da kudi dubu biyu, yanxu me xan ce ma 'ya yana daga xuwa biki ambaliya ya rutsa da ni??" Umma tace "Toh bari in sa driver ya maxa ya maida ku gidan gaskiya, don ruwa aka ce duk ya cika tsakar gida" Ko sauraranta Inna bata yi ba ta fice da gudu tana cewa "Innalillahi wa inna ilaihi raji'una ambaliyan ruwa a gidana a kira min yan kwana kwana, ga gudunmawar dubu hamsin da Bulasawa ya bani a dakin...." ta rasulu na biye da ita a baya ita ma da gudu tana salati, Mama Hadiza da su Aunty na ganin Inna ta fita da gudu suka taho gun Umma dake tsaye suna tambayarta me ya faru, Umma tayi wani dariya tace "Wai fa kudin da xata yi liki ta mance a gida shine wannan saurin wai driver xai maida ta gida" Kasa cewa komai Mama Hadiza da su Aunty suka yi, Umma tace "Allah dai ya kyauta, lamarin Inna ae sai ita" daga haka ta wuce ta bar su wajen a tsaye, Imaan dai na xaune an barta da jakunkuna irin na tsofaffi, Maryam ce ta taho gun Imaan da sauri tace "Ke maimakon mu bi su Inna mu je mu yi abinda xa mu yi kika bari suka wuce" Imaan ta xaro ido tace "Ae kuwa, toh kawai