Showing 36001 words to 39000 words out of 303099 words
ina nan" Ya daga kafada yace "Ae shi Abba baxai doke ki ba, fada kuma baya nuna wa a jikin mutum" parking yyi yace "Oya fitar min a mota sai da safe" wasu hawaye na xubo mata ta bude motar ta fita tana kallon sa tace "Duk abinda ya faru daga farko har karshe xan gaya ma Abba baxan boye masa komai ba, tare muka shanye furan kuma kai ka sa na shiga dakin Inna in dauko saboda ta xuba maka kadan" daga haka ta bar wajen da sauri tana kuka ya bi ta da kallo baki bude, tuni ta shige gate ta dinga rabe rabe har ta isa parking space din su Yusuf, a haka har ta shige parlour rufin asirinta ba kowa da gudu ta wuce dakin Anty, Anty dake xaune gaban madubi ta bude baki tana kallonta, Saman gadonta Imaan ta hau ta rufa da duvet, Anty tayi murmushi tace "Ina Mujaheed din?" Imaan ta cire duvet din ta mike xaune kamar xata yi kuka tace "Yace baxai dawo ba yau kuma wllh Anty shi yasa in dauko mata furanta sai ma kinga abinda ya tsammin duk ya shanye sauran" hawaye cike idonta take maganan, Anty tayi dariya tace "Ae ko kun sha jaraba yau, don har yanxu Abba da Ammi na can ana ba Inna hakuri, nima gajiya nayi na taho" Imaan ta turo baki ta koma ta rufe kanta da duvet. Washegari Saturday Imaan na xaune gaban madubin Anty tana shafa mai don har tayi wanka, Anty kuma na xaune kan darduma hannunta rike da hisnul Muslim aka bude kofar dakin, Abba ne tsaye bakin kofar, Imaan ta kusa faduwa saboda rudewa, Abba ya kalli Anty yace "Amina amma baki ce min yarinyar nan na nan ba" Anty tace "Ni ma har na yi bacci na ganta jiya da daddare" Abba ya kalli Imaan yace "Ki sameni parlona yanxu" kamar xata yi kuka tace "Abba to shi yaya fa?" Dakuwa Abba yyi mata yace "Stupid girl, yayan banxa ai duk xa ku gane kuran ku yau" daga haka ya juya ya fita, Imaan ta fashe da kuka tana kallon Anty tace "Kinga ni kadai xa a ma fada yaya ya gudu koh" Anty tace "Ni dai ba kin sani nayi karya ba, maxa fita ki tafi ki samesa ba ruwana" da kyar Imaan ta bar dakin sanye da Hijab dinta, Abba dake parlonsa ya mike ganinta yace "Mu je" bin sa tayi tana goge hawayen idonta suka nufa part din inna, tun daga nesa suka hango Mujaheed yana share mata frontage, Yana ganin Abba ya mike tsaye, Ya gaida Abba da ladabi Abba ya masa banxa ya shiga parlon inna, inna ta fito kitchen tace "Ahmadu ne da sassafe haka" Abba ya xauna ya gaisheta ta amsa, ganin Imaan ta hade rai tace "Ya xaka shigo min da ita parlor Ahmadu, ni da dai ta tsaya daga bakin kofa, tsoronta ma nake ji wllh" Abba ya kalli Imaan yace "Koma can" komawa tayi bakin kofar ta tsaya, Abba yace "Shi yaushe Mujaheed din ya xo nan?" Inna ta xauna tace "Ko minti biyar ba ayi ba, Ashe jiya na shiga alhakin yaron bai ma san me ke faruwa ba baya gidan yana asibiti, sai yanxu da ya shigo nake basa labarin abinda yarinyar ta min, ya taya ni jimami sosai yayi mamaki ainun, shine ya ga xan share waje ya amshi tsintsiyar yake sharewa yanxu duk da dai nasan ba sharuwa wajen xai yi ba amma ai dai ya fi babu" Abba ya sunkuyar da kai yana murmushi, Inna tace "Yanda yarinyar nan ta sa na kwana da yunwa jiya gaskiya Ahmadu idan ba a dau mataki ba xan tafi inje duk inda Allah yayi ko kasar waje ne kuwa, don na gaji da cutata da take, jiya mun dade muna magana da Bukar a waya a kan yarinyar tasa yana ta bani hakuri ni dai ban hakura ba" imaan ta fashe da kuka tace "Wllh yaya ne yasa in dauko masa kwanon furan fa" Abba ya kalli inna da ta bude baki tana kallonta, yace "Ke sai kika yarda da yace maki bai san me ke faruwa ba dama?" A hankali Mujaheed ya ajiye tsintsiyar hannunsa xai bar wajen Abba yace "Don't try that, come in now" Inna ta mike tace "Toh amma ko gaskiya Ahmadu ka haifi abinda ya fi karfin ka, ka haifi tashin duniya, yanxu duk dadin bakin da ya shigo ya min da sa hannunsa a sace min fura da nono, Haba da walakin goro a miya, dama wani Mujaheed ne xai amshi tsintsiya ya min shara, ko da kuwa aiki xai kasheni baxai yi ba wllh, wato xuwa yayi ya yaudare ni ya cuce ni to akwai hisabi ai, ni dama nasan ina imaan ta koyi wani sata idan ba sa ta aka yi ba, ilai ga maganata nan, kuma wllh kaji rantsuwar musulmi ko, to baxan yadda ba sai sun san yanda suka yi aka min furata mai kyau mai kamshi da tsafta irin tawa sannan a siyo min kindirmo mai kyau idan ba haka ba gaskiya abinda xai biyo baya a gidan nan har kai sai ya shafa Ahmadu" Mujaheed ya shigo parlon kansa a kasa, inna na kallonsa da kyau tace "Mugu katon banxa kawai, wllh yau idan na maku Allah ya isa kai da figaggiyar yar nan sai ya bi ku don kun ci da hakkina, ku ka bar ni na kwana da bakar yunwa, to amma ya xanyi, sai dai ku ci albarkacin Ahmadu da Bukar don ni ba abinda na hada da ku, ba dangin iya balle na baba, kawai sai dai ku ci albarka cin 'ya 'yan da na haifa tunda su suka haifo ku duniyar, to banda 6are ma wa xai maka haka, ai 'ya yana baxa su min haka ba, amma kuma Ahmadu ka min iyaka da su kar kato ko figaggiyar da ta sake xuwa bangarena bana bukata Isuhu ya ishe ni rayuwar duniya" Imaan sai hararanta take ta gefen ido, Mujaheed dai kansa na kasa, Abba yace "Toh bana son sake ganin kai ko Imaan a bangaren nan" da sauri Inna tace "Har abada kuwa, don gaskiya idan suka xo sun ja ma kai da Bukar fitina, ita ta tsaya iya bangarensu, shi ma ya tsaya iya nasu, kada wanda ya tsallaka ya yo min nan don xan gudu in bar gidan" Abba yace "Hope u both are apprehending?" Mujaheed yace "In sha Allah" Inna tace " Kuma kafin gobe a kawo min furata da aka yi a kuma siyo min kindirmo nah" Abba yace "Xa su san yanda suka yi in sha Allah" inna ta kalli Imaan tace "Ke kin ma ci halas ya kika kare da ciwace ciwace balle kin dau hakkin mutane, jarababbiya kawai" Imaan ta fashe da kuka Inna tace "Fita can kije ki ma uwar ki Aisha, fitar min a parlor" Juyawa tayi da gudu ta fita tana rusa kuka, Inna ta kalli Mujaheed tace "Kai ma fita, har abada kada ka sake tako min nan, kaje can ka saci furan uwar ka idan ta yi" ta gefen ido ya harareta ya fice a parlon, Abba yace "Ki kara hakuri xan sake ja masu kunne" tace "A'a ni ba ruwana ba dai na gama yanke hukuncin da nake so ba suje can su karata, sai kuma ko wannensu yyi ma uwarsa rashin mutunci ba dai Inna ba" Abba yyi murmushi bai dai ce komai ba. A hanya Mujaheed ya tadda imaan tana kuka bakin rai kamar xata shide, ya tsallake ta yayi wucewarsa. Mujaheed na komawa part dinsu dakin Ummarsa ya nufa, tun da ya shigo take kallonsa ya xauna yace "Ina kwana Umma?" Tace "Ban kwana ba, yanxu duk abinda xaka janyo a xageni a ci min mutunci baka gudunsa ko Mujaheed? Wannan kakar taka wai dole ne sai kaje inda take tunda ita jarababbiya Allah yayi ta, sannan kuma yunwa kake ji da ka dau shegen furanta jiya ta daga mana hankali a gidan nan, ni duk wannan bai wani dameni ba, babban damuwata a nan shine yaushe har ka fara shiri da yarinyar nan Imaan da ku ka dauke furan a tare ku ka sha?" Mujaheed ya bude ido sosai yana kallonta yace "Shiri kuma Umma? Ni bamu wani sha fura tare da ita ba, nine ma na dauke furan na sha" Umma tace "Toh naji tana cewa kai ka tura Imaan daukan furan ku ka raba" ya girgixa kai yace "A'a ba haka bane" Umma tace "Sannan da ake nemanka jiya ina ka tafi, ita yarinyar ma bata gidan a jiya da daddaren" Yace "Ni fa eatry na tafi cin abinci karfe sha daya ya wuce na shigo duk kun yi bacci" tana masa wani kallo tace "Toh ita imaan din ina ta tafi?" Yace "Ban sani ba gaskiya" Umma tace "Mujaheed?" Kallonta yayi tace "Mujaheed?" Yayi Shiru yana dubanta tace "Sau nawa na kira ka?" Ya sauke idonsa kasa tace "Toh wllh idan baka kama kanka gidan nan ba xan sa6a maka, ita kanta innar daga yau na kashe xuwa sashinta, kar ka sake tunda ba kanwar uwata bace ita din, idan kana son gaida kakarka ne sai ka shirya ka tafi katsina uwata na can da ranta" murmushi kawai Mujaheed yyi, tace "Dama tun shekaranjiya akwai maganar da nake son mu yi to da ka dawo gun aiki sai ka tare gun alakakan matar can sai nayi bacci xaka shigo min nan" ya daga kai ya kalleta yace "Toh ina ji Umma" tace "Kasan Hajiya Mansura kuwa?" Ya girgixa kai yace "A'a" tace "Ka santa mana, wata warce ka taba kai ni gidanta a Marafa, ka koma dauko ni da yamma ruwa ya tsuge har tace ka shigo ka ci abinci ka ki ci?" Yace "Ohh na tuna ban san sunanta ba ai" tace "Toh ita ce Hajiya Mansura, dama tana da wata budurwa yar shekara ashirin da daya tana karatu a Malaysia, to ina jin last week suka dawo hutu, baka ganta ba kyakkyawa fara doguwa ga hankali da nutsuwa, shine nake baka shawaran don me baxa ka neme ta ba" Shiru Mujaheed yyi bai ce komai ba, Umma tace "Sunanta Safeena, nasan ma xaka so ta ne coz she have all the qualities, uwa uba ga ubanta mugun attajiri abokin ma d'angote ne aka ce" Murmushi Mujaheed yyi bai dai ce komai ba, Umma tace "Ba batun murmushi bane wannan, dama gashi saura wata hudu ta kare karatun, last week da naje gidan na ganta ta kwanta min har nayi ma Hajiya Mansurar magana ita ma ta ji dadin tunanin nawa don ta yaba da hankalin ka, yanxu abinda nake so da kai ka shirya kaje gidan ko xuwa Sunday tunda baka xuwa aiki da safe, dama xan baka sako ka kai ma Hajiya Masurar nasan xaka ga Safeenar" Murya can kasa Mujaheed yace "Toh, Allah ya kai mu" Umma tace "Ameen son, Allah maka albarka" yace "Ameen, xan je in yi breakfast Umma" tace "Toh shikenan" mikewa yayi ya fita dakin ya kulle mata kofar. Karfe takwas Mujaheed ya fito xai fita kofar gida yaga imaan tsaye jikin mota tana jiran fitowarsu Maimoon su wuce islamiyya, idonta ya kumbura kana ganinta kasan ba karamin kuka ta ci ba, tunda ya fito take kallonsa ta wani cika kiris ya rage ta fashe, Mujaheed ya saci kallonta suna hada ido ya dauke kai, ta fashe da wani matsanancin kuka, da sauri ya kalleta kafin yace komai ta shige gidan da gudu, direct parlon Abba ta nufa, ta samesa kuwa yana kallon news shi kadai, ta xube nan tsakiyar parlon ta dinga rusa kuka kamar xata shide, ya mike da sauri yace "Subhanallah, me ya faru mamana?" Tana kuka sosai tace "Abba Yaya ne ke min dariya, Wayyo Abba" da mamaki yake kallonta, yace "Dariyar me yake maki" ta kara fashewa da kuka tace "Nima ban sani ba wllh Abba" komawa yayi ya xauna yace "Xo nan" mikewa tayi ta koma kusa da shi tana kuka sosai, yayi murmushi ya rungumeta yace "Ya isa haka mamana kiyi hakuri kinji" ta kasa cewa komai yace "To baxa ki daina kukan ba?" Da kyar tace "Xan daina" Ya dau handkerchief ya mika mata yace "Toh goge idon ki kiyi Shiru" tana sauke ajiyar xuciya ta amsa tana goge idonta wasu hawayen na sakkowa, Umma ce ta shigo parlon rike da mug din ruwan Lipton yana turiri, tun da ta shigo take kallon Imaan dake rungume jikin Abba har sannan ta dinga kallonta da wani expression a fuskarta, Umma ta dai ajiye mug din hannunta xata xauna Abba yace "Nemo min Muhammad" Umma tace "Muhammad kuma, lafiya? Ina jin dai ya fita uxurin gabansa ba gwanda a kai ta asibiti ba idan ma ciwon nata ne ya tashi" Abba ya dau wayarsa yayi dialing number Mujaheed, Mujaheed dake xaune gun mai kiosk dake 2 houses away bayan ya siya card ya dinga kallon screen din wayarsa ganin Abba ke kira, ya daga ya kai kunnen kafin yace komai Abba yace "Muhammad ka sameni parlona yanxu" Daga haka ya katse wayar, Umma ta tsaya kallon Abba fuska daure, ba a dau lkci ba Mujaheed ya shigo parlon da sallama, sosai gabansa ya fadi ganin Imaan kusa da Abba ga Umma ma tsaye a parlon, ya sunkuyar da kai ya duka kasa a hankali yace "Abba gani" Abba na kallon Imaan yace "Me kika ce ya maki mamana" cikin rawar murya tace "Dariya ya min ban san ko ya san Ammi ta doke ni bane" Abba yace "Subhanallah ta doke ki kuma, me kika mata" ta fara kuka tace "Wai na sha ma inna fura shine ta mareni ta kuma dokeni a bayana" Abba yace "Aa bata kyauta ba xan je In sameta yanxu kuwa, kai kuma Mujaheed dariyar Uwarka kake mata" Umma ta dinga ma Abba wani irin kallo, Mujaheed ya girgixa kai yace "Abba ni ban fa ganta ba balle in mata dariya" Imaan tace "Wllh ya gan ni ya dinga kallona a sace" tana fadin haka ta fara share hawayen dake sakko mata, Mujaheed yace "To tayi hakuri tunda tace na mata dariya amma ni ban mata ba" Imaan ta turo baki ta dauke kai, Abba yace "Ai kin hakura koh" kin cewa komai tayi Abba yace "Toh kiyi hakuri mamana Aisha kuma zan je in sameta yanxu, maxa tashi ki tafi makarantar kar ki makara" Umma ta fice parlon rai a bace, a hankali Imaan tace "Abba nasan su Maimoon sun tafi yanxu" Abba yace "To mu je in ajiye ki" yana fadin haka ya mike ya dau makullin mota, Mujaheed ya mike yace "Bari in ajiyeta Abba" Abba ya dau dubu biyu ya bata yace "Toh ga kudin lunch din ki" ta rusuna ta amsa.
Alhamdulillah, Thanks to all those that patronize the book *Imaan* Allah bar ku da iyayen ku, My book Imaan is for sale coz I am done with free pages tun friday, ni nasan it will go round as usual, I can't prevent that, but if you should come across it it's not for free, i repeat it's not for free, na siyarwa ne, wllh I am too grown up to say Allah ya isa, but have the fear of Allah SWT in u, don't forget it's my property, hakkina ne, wahalata ce, pay before reading, pay before reading, or you just over look it and smile, have a very good conscience plss, and a good conscience won't read happily without paying, if you want any favor pertaining to d book contact me and let me know, the book is 300 via..... Fcmb 3276052019
Hauwa Bello Jiddah
07087865788 and then u contact me through this digit to be added in the payment groups. Thanks once more for patronizing.
For those saying xa su same shi a banxa yana yawo to gashi... amma fa ba a banxa yake ba wllh, there is power in the tongue, Karamin hakkin da ka raina..... ππ
13.πβimaanβπ
A hankali Imaan tace "Abba nasan idan muka fita kilan xai min fada a hanya" Mujaheed ya kalleta bai ce komai ba Abba yace "Toh ya maki fadan mu ga" Murmushi kawai Mujaheed yayi ya fita parlon, Abba yace "Maxa ku tafi kar kiyi latti mamana" Imaan ta bi bayan Mujaheed tana share idonta, tunda Mujaheed ya fito parlon Abba gabansa ya dinga faduwa, xaune ya ga Umma a main parlor fuskar nan nata a tamke, Mujaheed ya karasa inda take, ita ko bata fasa kallonsa ba, kofar fita Imaan ta nufa, Mujaheed yyi kasa da murya yace "Umma dama Abba...." Katse sa tayi tace "Bana son jin komai, Ban baka izinin fita parlon nan ba in har ni na haife ka Mujaheed, ko da kuwa me xai faru yau" Kallonta Mujaheed ya tsaya yi ba tare da yace komai ba, Anty ta fito kitchen da breakfast a hannunta tayi wani dariya tace "Su haihuwa manya...." Umma ta kalleta ta dakatar da ita da sauri tace "Ke in kina cin k'asa ki kiyayi ta shuri, ki daina min shisshigi a lamari na, ki yi mai fissheki kawai a gidan nan" Anty ta tabe baki tace "Anya akwai wanda ya kai me shiga lamarin d'a da ubansa shisshigi kuwa, kuma naga duk wanda xai ce d'a kada ya bi umarnin mahaifinsa shine mai babban shisshigi a rayuwa kuma bai dauko abinda xai fishshesa ba" Umma ta mike rai bace tace "D'an ki ko nawa? tunda ba wata shegiya ce ta haifa min d'an ba sai kiyi ta kanki ki, ki kuma cire min ido kan d'a na" Anty tace "Na wuce in tsaya ina xance irin na yara da ke, amma bari in baki shawara, domin kin haifi Muhammad ba yana nufin ke kadai ke da iko da shi ba duk ki bi ki takura ma yaro sai abinda kike so xai yi a gidan nan, kina amfani da advantage din ganin yana maki biyayya dari bisa dari...." Cikin tsawa Umma tace "Da ke da shawarar taki Allah kwashe maku albarka..." Dai dai nan Abba ya