Showing 156001 words to 159000 words out of 303099 words

Chapter 53 - Imaan Book 1 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

1657

tana dariya a hankali, kallon ta ya dinga yi yana jin xuciyarsa na wani tukuki, a hankali ta dago tana kallonsa, ganin yanda ya daure fuska ba shiri ta shiga taitayinta strictly yace "Sai kika bude masa kaya ya maki allura yana kallon ki right?" Sosai ya bata dariya amma bata yi ba tana komawa baya a hankali tace "Ni a cinya nace ya min, kuma a nan ya min fa yaya, bari in nuna maka wajen ma" tana fadin haka ta dage gown din jikinta a hankali tana nuna masa lap dinta, a hankali ya sauke idonsa yana kallon fresh lap din nata, lkci daya yaji ransa yayi wani mugun baci xuciyarsa na tafarfasa, tayi murmushi ta rufe kafan tace "Kagani ai" fuska a tamke yace "When xa ku fara exams na first term?" Ta buda manyan idonta tace "Saura kusan four weeks ai Yaya" yace "Good ana gama saukan ku dama idan Inna xata taho gidana ku taho tare" ta xaro ido tace "Saboda me Yaya?" A tsawace yace "I am giving you instruction, don't question me" daga haka ya mike ya juya ya nufi kofa rai bace, ta bi sa da wani kallo bayan ya fita, murya can kasa tace "Tabb, waye xai je gidan ka, ni dai baxan je ba" Xaune ya tadda Inna kan tabarma ta daura kafa daya kan daya tana ba Safeenah labarin irin wahalan da tayi da Mujaheed tun daga ranan da aka haifo sa duniya.... Inna na kallon Safeenah da kyau tace "Ko ke baki ga bakin d'an tsut ba??" Duk da irin yanda Safeenah ta dinga dakewa coz at first she wasn't interested with the story gaba daya hankalinta na daki ganin Mujaheed bai fito ba har sannan, amma bata san lkcn da ta fashe da dariya ba har da sakkowa kasa tana kallon Inna, Inna ta hade rai tace "Ke Safara'u ba batun dariya ba wllh, ya tsotsi uwar ne ba kadan ba sai dai Allah ya bata lada, sai kin gansa wani narkeke da shi malam, don dama nonon Rukayya ba dai kyau ba gaskiya" Dariya kawai Safeenah take har da kyakyatawa, Inna ta tabe baki tace "Uhn ni dai ba ruwana" Mujaheed dai yayi still bakin kofar daki ya kasa karasowa cikin parlon, Inna tace "Toh wllh da ya dawo wajena yana da shekara uku sai...." Katse ta Mujaheed yyi fuska daure ta hanyar ce ma Safeenah "Tashi mu tafi" ita dai sai dariya take, Inna tace "Ya haka ina bata tarihi Mujaheed" Mujaheed yace "Toh sai ki jira idan an baki mai gadin gidan tarihi...." Inna tace "Meye laifina Mujaheed, matar ka ce fa kuma sai mu xauna tana kallona Ina kallonta kamar kishiyoyi" Mikewa Safeenah tayi tana dariya tace "Toh Inna mu xa mu koma xan xo ni kadai in sha Allah sai ki bani karshen labarin" Inna na washe baki tace "Toh Safara'u shiga ku yi sallama da Imaan din kiyi mata Allah ya sauwake" D'an dariyar dake fuskar Safeenah ya dauke bata dai ce komai ba ta shiga dakin, tsayawa tayi bakin kofa tana kallon Imaan dake xaune saman gado from head to toes, imaan ta wani daure fuska, Safeenah ta ja tsaki tana yatsine fuska ta fice daga dakin. Dai dai nan aka yi sallama bakin kofa, Inna ta mike da sauri tana amsawa tace "Bisimillah Bukar, Mujaheed ne kadai da amaryarsa, shigo" Sadeeq ya shigo parlon yana murmushi, hannu ya mika ma Mujaheed dake tsaye bakin kofa yana kallonsa, Mujaheed ya amsa still looking at him suka gaisa, Inna na washe baki tace "Toh xauna Bukar" Xaunawa Sadeeq yyi kan lallausan rug dake parlon, Inna na kallon Safeenah tace "Saurayin imaan kenan Safara'u, tana gama sakandari nan da wata daya xuwa biyu dama xa a fara maganar auren su, baki ga ba yaro mai kirki da sanin ya kamata wllh" Safeenah tana kallonsa tace "Sannu da xuwa" Sadeeq ya mata godiya yana murmushi, Safeenah ta nufi kofa tana kallon Mujaheed sannan ta kalli Inna tace "Toh Inna bari mu je sai na sake dawowa" Mujaheed yayi ma Inna sallama ya fita Safeenah na biye da shi, sai da suka d'an yi nisa ya tsaya yace "Ki tafi bangaren mu ki jira ni, I forgot i need to discuss something with grandma" da mamaki ta dinga kallonsa, can tace "Toh sai mu koma tare ai" ya wani hade rai yace "Wannan sirrinmu ne, do as I say plss" Bai jira cewarta ba ya juya ya koma parlon Inna, ta bi sa da kallo da mugun mamaki, Inna ta xubo ma Sadeeq abinci ta cika masa nama tam ta ajiye gabansa xata dauko ruwa kenan Mujaheed ya shiga, cike da damuwa tace "Naga abinda ya isheni.... mai ya dawo da ku kuma Mujaheed ba kun tafi ba, wllh shi kadai na ma girkin ban da ku...." Sadeeq bai san lkcn da ya fara dariya ba, Mujaheed ya wani hade rai yana kallonta, tace "Ni dai ba ruwana, mutane dai ba gaskiya meye kuma na dawowa bayan mun yi sallama kun tafi" Mujaheed bai fasa karasawa cikin parlon ba ya xauna, Inna ta ajiye ma Sadeeq ruwa da malt biyu tace "Toh ni ban san yanda xan yi da kai ba gaskiya Mujaheed, ko in jiko maka garin kwaki ina ma da gyada wllh" Sadeeq ya hadiye dariyarsa yace "Wllh Kaka ya min yawa xa mu ci wannan tare" Inna ta tsuke fuska tana kallon Mujaheed tace "Katon ba sai ya cinye gaba daya ba kana xaune Bukar...." Sadeeq na murmushi yana kallon Mujaheed da ya hade rai yace "Bismillah Dr" Mujaheed yace "Alhmdllh, I am okay" Inna tace "To maa sha Allah, maxa maida hankali ka cinye kayan ka Bukar, Ni dai nasan sai ka fita xai tsigaleni tass.... Toh wannan duk bai dameni ba tunda Allah ya ga xuciyata kai na ma girki, ban san da xuwansu ba" Sadeeq couldn't stop smiling ya dau spoon ya debi abincin ya kai baki bayan yayi Bismillah, Inna ta xauna tace "Ita ma imaan d'an kadan na debar mata gashi can rufe a kitchen, toh ni basu sanar min xa su xo ba da nayi girkin da su, meye a ciki don dai ka ba mutum abinci, kawai fa ganin mutumi nayi gantsantsan a kaina mata na tsaye bayansa, na ja bakina nayi shiru na basu hanya, shi sa na tafi kitchen na adana maka abincin ka kada su gani su tafi da ni a baki suce na masu rowa, kasan mutumin yau" Mujaheed dai bai tanka ta ba, ta gaji da xubanta tayi shiru, yana ta xaune har Sadeeq ya gama cin abinda xai ci, bayan Inna ta tabbata da gaske ya koshi ta kalli Mujaheed tace "Toh don Allah kayi hakuri ka ci sauran, kaga dai a nutse ya ci abincin irin na yan gayu" Sadeeq ya fara dariya ya kasa kallon Mujaheed dake kallon Inna ba yabo ba fallasa, Inna ta tabe baki ganin Mujaheed bai ce komai ba ta dauke abincinta ta wuce kitchen ta rufe, dawowa tayi tana kallon kofar daki tace "Toh imaan dakin xai bi ki fisabilillahi, ki fito mana" sai da Inna ta kara magana imaan ta fito da hijab, Sadeeq ya dinga kallonta, rakubewa tayi jikin kujera tana kallonsa a hankali tace "Ina yini" yayi murmushi yace "Lafiya lau, how are you feeling now" tace "Na ji sauki" yace "Maa sha Allah, hope you've eaten?" Ta gyada masa kai, Inna dai sai kallonsu take tana murmushi, imaan ta saci kallon Mujaheed dake kallonta fuska daure, Dauke kai tayi da sauri, Sadeeq yace "Toh shkkn kaka na cika alkawari tunda na dawo na ci abinci, ni xan koma" inna tace "Wllh na ji dadi Bukar Allah maka albarka, tashi ki raka sa ke" Kudi ya fiddo aljihunsa dubu ashirin ya ajiye kasa kan carpet da ya tashi yace "Kaka tukuicin girkin, naji dadi kuma nagode" Inna tayi tagumi a hankali tace "Naga abinda ya isheni... Bukar dai baya gajiya, abincin ma sai an bada tukuici?? Toh Allah maka albarka, ni dai na gode baxan tsaya ina jayayya da kai ba kamar karamar yarinya, nagode" Yana murmushi ya nufi kofa, Inna na kallon Imaan ta hade rai tace "Ke dai sususu ce wllh, baxa ki tashi ki rakasa ba toh" imaan ta turo baki ta mike ta bi bayansa, Inna na kallon Mujaheed tace "Toh kullum aikin kenan fa wllh, sai ya ajiye min damin kudi haka kafin ya fita har na rasa yanda xan yi da kudi a dakin nan, ni fa ya fi min mutane da dama a duniyar nan don yasan abinda ya kamata, ku ma dai ku ji tsoron Allah ku dinga koyi da shi..." Mikewa Mujaheed yyi ya fice daga parlon. Tsaye Mujaheed ya tadda su kusa da flower sai wani sunkuyar da kai imaan take shi ko sai kallonta yake kamar lkcn ya fara ganinta, kamar mai counting steps dinsa ya dinga tafiyar don basu lura da shi ba, murya can kasa Sadeeq yace "Plss ki kalleni dear let me feel relieved, I've missed you alot, but staying far away from you and just listening to ur voice is d best to me" Ita dai ta kasa dago kanta, a hankali ya kamo hannunta ta dago manyan idanuwanta tana kallonsa, yyi murmushin sa mai tsuma xuciyar wanda ya gani cikin cool voice dinsa yace "I love you Imaan, I am always dreaming to be with you by my side as my wife.... I wish xa ki ga yanda na kagu ki xama matata.... I just can't..." Sai kuma yyi shiru ya lumshe ido, Imaan tayi still ganin Mujaheed da ya tsaya yana kallonsu, da sauri ta xame hannunta daga na Sadeeq, Mujaheed ya dauke kai ya ci gaba da tafiya gently, Ko Sadeeq bai juya ba yasan shi ne, kuma ya ki kallonsa, har sae da Mujaheed yyi nisa sannan Sadeeq ya bi sa da wani kallo, can ya gyada kai smiling, Imaan tace "Xan je in kwanta na gaji" yace "Sure dear, hope cramps din yyi sauki?" Xaro ido tayi sai kuma ta rufe fuska da sauri, ya dinga kallonta yana murmushi, ya kai bakinsa kusa da kunnenta a hankali yace "A day will come da xaki san kunya baxae amfane ki ba" turo baki tayi har sannan ta ki kallonsa, murya can kasa yace "I want just a favor from you... And don't deny me plss" tana kallonsa tace "Na me?" Yana murmushi yace "I will text it to you idan na shiga mota ynxu coz I am not ready to dig u out from underground now" xaro ido tayi tana kallonsa, ya hade rai yace "And if you deny me, I won't be happy imaan" Bai jira cewarta ba ya fara tafiya yace "Expect the text now, gobe I might come in the evening in sha Allah" ta bi sa da kallo har yyi nisa sannan ta juya a sanyaye ta koma part din Inna. Bayan magrib imaan na xaune dakin Inna bayan ta gama shirin bacci xata kwanta ta tuna wayarta da text din da Sadeeq yace xai turo mata tun da rana, mikewa tayi da sauri ta dau Hijab ta saka ta fito parlor tasan ma kila yana ta kiranta, Inna dake xaune parlon tana cin abinci ganin ta nufi kofa ta tabe baki tace "In ji baki mance komai naki a dakina ba Imaan" imaan tace "Xan dawo fa, wayata xan je in dauko a gida" cike da damuwa Inna tace "Me kuma xa ki dawo ki min?? Tun safe fa kike nan" Imaan bata saurareta ba ta fita parlon, daga nisa ta hango mutum na tahowa kamar Yusuf kamar kuma Mujaheed, duk da Yusuf ta san ya daina xuwa part din Inna sai tare da Abba, Tsayawa tayi har sai da ya iso kusa da haske taga Mujaheed ne, turo baki tayi ta juya da sauri ta koma part din Inna, Inna da ta bar abincin da take ci ta tafi tana share dakinta ta daga kai tana kallonta tace "Naga jaraba... Har kin dawo??" Imaan ta bi ta gefenta ta shige dakin tana cewa "Ko ba Yaya bane" Inna ta ci gaba da sharanta tace "Toh dama ki kakkabe min xanin gadona ki gyara gadon fess ni ba gantalalliya bace, ba haka nake barin dakina ba in kwana tare da wari" Inna ta mike ganin Mujaheed tace "Wannan shine anyi ba ayi ba, yanxu kayi auren ma baxa mu sarara ba Mujaheed kullum kai ta mana sintiri a gida, ba daxu da rana ka xo ba to me kuma ya dawo da kai, ko akwai ajiyar ka a parlon nan ne baka dauke ba har yanxu" Bai tanka ta ba ya nufi kofar dakin ya bude ta bi sa da kallo baki bude, imaan ta koma can karshen gado kamar xata yi kuka tana kallonsa, Ya wani mugun daure fuska yace "You had better keep on running away from me coz wllh wlh am promising you this... if I should get hold of you I won't take it likely with you.... I will seriously deal with you" a fusace Inna tace "Naga abinda ya isheni, don Allah Mujaheed ka rufa mana asiri, me ta maka kake kunduma mata xagi haka, yarinyar da kamar baxata yi ba daxu Allah ya rufa mana asiri Bulasawa ya rufa mana ya mata allura ya bata magani taji sauki shine yanxu xaka xo kana xaginta kana nuna ta da yatsa kana gaya mata maganganu marasu dadin ji, to ni dai ba ruwana ka tafi ka ba mu waje, ni na ta6a jin inda aka aurar da mutum kuma yyi ta sintirin dawowa gida kamar dai da ajiyarsa da ya mance bai dauka ba, ni dai gaskiya na gaji da kai kar ka sake xuwa min, tunda kayi auren ka kayi xamanka a gidanka ka bar min jikata ta sarara...." Kawai Inna gani tayi ya shige dakin ta fasa ihu tana kwala ma Ahmadu kira iya karfinta, ba kuma wanda xai ce ba wani mugun abun ta gani ba, Imaan ma duk ta rude xata gudu bandaki ya fixgota kawai sai ji tayi xabga mata mari mai lafiya, ta rike fuskarta a gigice, inna na ganin haka ta fice da gudu xuwa waje tana kiran Abba, Mujaheed na kallonta da idonsa da suka kada cikin harshen turanci yace "Muharramin ki ne mutumin nan da kika mika masa hannun ki ya kama, dama iskancin da ku ke yi da shi kenan, yana tsaye kusa da ke kamar xai shige jikin ki kina jin dadi koh? To wllh yanxun nan xan je in sami daddynki in sanar masa komai" a rikice imaan ta rikosa ta dinga basa hakuri tana cewa "Yaya ni bani nace ya rike ni ba, don Allah kayi hakuri baxan kara ba wllh, don Allah kayi hakuri" sosai xuciyarsa ke tafarfasa yana kallonta, ta hade hannayenta hawaye na sakko mata tace "Don Allah kayi hakuri baxan kara ba da gaske Yaya" tana fadin haka ta boye fuskarta a jikinsa tana kuka, har ransa yake jin kukan nata, Bai san lkcn da ya jawota jikinsa ba cikin sanyin murya yace "That's very wrong imaan, I've told you times without numbers... that guy is just here to ruin ur life, to cause you heartbreaks, he is after ur body... He is..." Kasa ci gaba yyi don sosai ransa ke tafarfasa, imaan dai sai sauke ajiyar xuciya take tana kuka a hankali bata ce komai ba, nan ko ko kiris bata yrda da abinda Yayan nata ke fada ba don ita tasan Sadeeq na sonta kamar yanda ita ma take sonsa fiye da xaton mai karatu, dago kanta yayi yana kallon kwayar idonta da ya rine murya can kasa yace "For my sake xa ki rabu da shi plss Imaan?" Ta fashe da kuka cikin rawar murya tace "Ni dai ina son sa Yaya, kuma ai aurena xai yi..." Kallonta Mujaheed yake ko kiftawa babu xuciyarsa na bugawa, da kyar tace "Kayi hakuri plss Yaya, da gaske Ina son sa, but in sha Allah baxan bari ya sake rike hannuna ba"


🌟⭐⭐⭐🌟assslamun alykum ina bawa masoya littafina imaaan hkrn xasujini shru xan dau hutune xuwa bayan.sallah in allah ya kaemu tnx u fans imaaan inbaki biyaba karki karanta🌟⭐🌟

_Maa Sha Allah, koma wacece ko wanene yayi wannan Broadcast din na sama👆🏻 ya sani.... Da *NI* da *shi/Ita* xa mu hadu gaban Ubangiji, ba fa a kan komai ba sai kan gantalallen Hausa Novel wanda baxai kare mu da komai ba, baxai amfane mu da komai ba ranan gobe kiyama, wanda muke fatan ma ba xunubi muke kwasan ma kanmu ba muke kuma rokan Allah ya yafe mana, wato irin xagi da cin mutunci da mai Broadcast din ya ja min jiya wllh tllh xa ayi mana hisabi da koma wanene, don ni dai na yafe duk xagi da na sha amma mai post din ya sani xa mu hadu gaban ubangijin da ya halicce mu in sha Allah, and that's if he or she believes there is God_
Ni ba fitinanniya ba ni ba mafadaciya ba, ni ba mai sa ido ba, ni ba mai takura ba, amma duk da haka ban tsira ba a media sai an cakale ni na mayar da martanin da bana so dai, duk da babba da hakuri aka san sa amma a dai dinga jin tsoron Allah, mutane dai ba gaskiya basa tsoron Allah, a dai dinga jin tsoron Ubangiji ni ba ruwana.🤦🏻‍♀️

Least I forget akwai wani hoton dake circulating na wata mai pink kaya wai Khaleesat Haiydar, to gaskiya ban san yarinyar ba ayi hakuri a daina turo min ana tambaya ko ni ce don ba ni bace, plsss ba ni bace oo... this is not 2012 I am begging you pple ba ni bace...😟 Ranan da na gama Imaan xanyi attaching pic dina a karshen page din sai ku gani😁

One love fans😍


Imaan isn't for free* it's 300 via


Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788


56....


Saketa Mujaheed yayi har sannan bai daina kallonta ba sai


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login