Showing 255001 words to 258000 words out of 303099 words

Chapter 86 - Imaan Book 1 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

1615

Hansai ai sai Allah, komai sai yanda nace ayi xa ayi a gidan nan, keee!! wllh ki kara kaifin bakin ki da fitsara..." Inna na nuna mata bakinta tace "Kinga bakin nan nawa, to shi ya kwace ni a kuruciyata, kwata kwata ban daukan nansans" Dariya Imaan ta fara yi, Mama Hadiza dai tayi murmushi tana kallon uwar tata, Inna ta ci gaba da cin abincinta tace "Wacece kuma Safara'u da cikin mintuna kalilan baxa ki kwace Mujaheed a wajenta ba, shi fa Mujaheed wllh tun ba yau ba dama yake son auren ki, irin son da yake maki ba ni har tsoro ya dinga bani lkcn, duk ina lura da shi yyi ta wani takura ki yana sa maki ido d'an banxan, gashi yyi ta latse min ke kuma sbda bashi da tsoron Allah, ashe dai kayansa ce ke, ohh Allah mai girma gashi yanxu har kin tare gidansa kin kwana" Imaan ta rufe fuskarta da kujera tana murmushi, Mama Hadiza ta fara dariya tana kallon Inna, inna ta tabe baki tace "Ni dai ba ruwana, ashe dama Allah ya riga ya kaddara shi din dai ne mijinki, tohh ya muka iya Mujaheed dai jikana ne kuma bbu wanda ya fi ni saninsa gaskiya...." Shigowar Mujaheed ya sa Inna tayi shiru tana ci gaba da cin abincinta, Mama Hadiza dai sai kallonsa take tana murmushi, ya ajiye ledan hannunsa yana kallon Imaan da ta ki dago kanta, Inna ta kallesa ta gefen ido ta tabe baki, xaunawa yyi yana kallon Mama Hadixa yace "Ga abinci na siyo maki Mama" Mama Hadiza tace "Toh nagode" Mikewa inna tayi tana kallon Imaan tace "Mu je in ga dakin ki" Imaan ta mike ta nufi sama Inna na biye da ita Mujaheed ya bi su da kallo, Inna ta dinga bin dakin da kallo bayan sun shiga sannan tace "Kina dai sane har yanxu Mujaheed bai maki lefe ba dai koh? Kuma sadakin ma Ahmadu ne ya bada sbda lalacewa, To ba ruwana kada ki yarda ya kai ki ya baro ki sai ya hada maki lafiyayyen lefe irin na Bulasawa gaskiya, don ba sadaka aka basa ke ba" Imaan tayi dariya bata dai ce komai ba, inna tace "Allah kuwa kar ki yarda ya shigar maki daki bai maki lefe ba ya kai ki ya baro ba ruwana" Imaan sai murmushi take Inna ta xauna gefen gado tace "Ita kuma Safara'u kar ki kuskura ki raga mata, ko mi ta maki ki rama ke dai kar ki yarda ta kai maki hannu, da kinga haka ki ja bakin ki kiyi shiru ki gudu tunda ba karfi ne dake ba, Ni fa nayi dambe yyi sau dari da uwar Bala damben mu na karshe sai da na tsaga mata goshi, da tabon ta mutu, Allah dai ya ji kanta ya gafarta mata, lafiya muka xauna da ita wllh matar kirki..." Shigowar Mujaheed dakin yasa inna ta ja bakinta tayi shiru, sai kuma ta mike tana kallon Imaan tace "Ke mu je" imaan ta mike tana murmushi ta fita dakin Inna na biye da ita suka koma parlor suka xauna. Karfe biyar saura Mama Hadiza tace "Toh inna ya kamata mu kama hanya yanxu...." Inna ta katse ta tace "Haba Hadiza da maraicen nan mutum ya kama hanyar kaduna yanda duniya bbu gaskiya ga yan kinnappin da yan fashi kaca kaca a titi??" Mama Hadiza tace "Shi tafiyar minti araba'in din ne dare yayi Inna??" Inna tace "Ni fa tun ina gidan mijina in dai la'asar ya gota to bana bin babban titi" Imaan dai sai murmushi take, Mama Hadiza tace "Abinda nan da yan kwanaki ma xa su dawo kadunan Inna" a fusace Inna tace "Toh me kike nufi? Nufin ki xama nake son yi masu a gida tsofe tsofe da ni koko? Da ba don maraice yyi ba me xan xauna in yi Hadiza?" Mama Hadiza ta mike ta dau handbag dinta tana kallon Imaan tace "Tafi ki ce ma Mujaheed xan koma" dai dai nan Mujaheed ya sakko parlon, yace "Mama ba dai tafiya ba?" Mama Hadiza tace "Wucewa xan yi, sai ayi ta hakuri kuma" Mujaheed ya saci kallon Inna da ta hade rai tana kallon Tv sai kuma ya kalli Mama Hadiza yace "Is she staying here" Mama Hadiza tace "Don Allah ni dai mu je ku raka ni in wuce" daga haka ta nufi kofa, Mujaheed ya kara satan kallon Inna sannan ya bi bayanta, Imaan na kallon Inna murya can kasa tace "Kar ki tafi Inna kiyi xaman ki a nan kin ji" Inna ta tabe baki tace "Yanxu xuwa xata yi ta 6ata ni gun 'yan uwanta su kullace ni ko don ba ni na haife ku yasa suke min walakancin nan oho, bari dai in tafi kada a sa ni a bakin duniya, amma duk abubuwan da na gaya maki kar ki kuskura ki watsar don xa su maki amfani, in sha Allahu nan da kwana biyu tun da naga gida ko shawara da su Ahmadu baxan yi ba sai dai su ga wayam bbu ni, tashi mu je ki rakani...." Imaan ta mike kamar xata yi kuka ta bi bayanta, fuska daure Inna ta shige bayan mota Mama Hadiza dai bata ce komai ba, Mujaheed ya sauke wani boyayyen ajiyar xuciya, Imaan ta fara hawaye Mama Hadiza tace "Meye haka? Bana son shashanci fa" juyawa tayi ta koma ciki tana share hawayen idonta.



*Imaan isn't for free* it's 300 via


Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788




90.....



Mujaheed na komawa parlor bayan su Mama Hadiza sun wuce ya dau trolley din da suka kawo ma Imaan ya kai mata daki, xaune ya sameta ta jinginar da kanta jikin gado tana hawaye, ya ajiye jakar ya isa kusa da ita ya xauna yana kallonta, Hade kai tayi da gwiwa tana kuka a hankali, ya dagota yace "Ohk I am taking you home next week in sha Allah, yayi hakan?" Tana kallonsa cikin sanyin murya tace "Da gaske?" Yayi murmushi ya ja hancinta yace "Ehh mana, ko Yaya ya ta6a maki karya ne" Ta goge idonta tace "Toh Allah ya kai mu" yace "Baki yi lunch ba har yanxu" tace "Bayan abincin da na ci gidan Aunty Farida, I am not hungry" mikewa yayi yace "Let me get something outside" Bai jira cewarta ba ya isa kofa ya cire makulli ya fita ya kulle dakin ta waje, turo baki tayi ta mike ta kwantar da jakar da ya ajiye mata ta bude zip din, gogaggun kayanta ne kusan kala goma sai Hijabs har kala Biyar a babban jakan da inner wears, sai turarurrukanta da man shafa, rufe jakar tayi a hankali ta ja sa gefe ta ajiye sannan ta koma gefen gado ta xauna. Sai kusan karfe shidda Mujaheed ya bude dakin yana kallonta daga bakin kofa yace "Come downstairs" sai da ya bar bakin kofar sannan ta mike ta fita dakin tana kallon dakin Safeenah ta sauka downstairs, xaune ta samesa parlon da pineapple da aka yi slicing a plate, ta karasa ta xauna tana kallon movie da ake a Tv, yace "Baxa ki sha ba?" Kallon abarban tayi sannan ta dauke kai, ya mike ya dau plate din ya nufeta ya xauna kusa da ita, a hankali ta dau daya ta sa a baki, yyi murmushi yana kallon eye balls dinta ta hade rai tace "Ni dai ka daina kallona" ya jawota jikinsa yace "Ohk na daina" suna nan haka har kusan Magrib suna kallon movie da ake yi a TV, Jin footstep a stairs duk suka juya, Safeenah ce ke sakkowa sama fuska a murtuke, suka hada ido gaba daya da ita, a hankali Imaan ta kwantar da kanta saman shoulder dinsa, Safeenah bata sake yarda ta kallesu ba ta wuce kitchen, Mujaheed dai bai sake kallonta ba Imaan ta bi ta da harara, Mujaheed dake lura da ita yyi murmushi ya daura lips dinsa a cheeks dinta murya can kasa yace "Me ta maki?" Hade rai tayi ta kallesa, ya wara ido ya rungumeta yace "Toh yi hakuri" lamo tayi jikinsa, bayan kusan minti biyar sai ga Safeenah ta fito kitchen din ko ba a fada ba kasan yunwa take ji, suka kara hada ido da Imaan ta dauke kai da sauri ta wuce sama kamar xata tashi sama, shi dai Mujaheed bai ce komai ba, jin ana kiran sllh ya mike yace "Me xa ki ci sai in taho maki da shi when I am coming back from mosque" tace "Ae akwai abincin da muka siyo" yace "Noo ae ya huce" d'an murmushi tayi tace "Almubazzaranci Kuma?" Shiru yyi yana kallonta, tace "Sae ka dawo" daga haka ta mike ta wuce sama, a hankali yace "Imaan" ta juya tana kallonsa yace "Ki sa makulli daki idan kin shiga" Kai kawai ta gyada masa ta wuce sama shi kuma ya fita, imaan ta kusa idar da sllhn Magrib taji ana murda kofar dakin, tana idarwa ta nufi kofar a hankali tace "Waye?" Muryar Safeenah ta ji tace "Idan ba tsoro ba uban me yasa kike sa makulli a kofa, banxa matsoraciya karuwa kawai...." Imaan tayi murmushi tace "Sbda bani da lkcn biye ma jahila in daura ma kai na xunubi shi yasa nake rufe kofata, when ever I have ur time I will leave my door open, wahalalliya kawai" Bubbuga kofar Safeenah ta dinga yi da mugun karfi tana kunduma mata mugayen ashar tana cewa "In kin haifu cikin uwarki ki bude kofar nan yanxu ki ga abinda xai faru, wllh in doke ki in doki banxa in ga uban da xai tsaya maki" Dariya Imaan tayi tace "Allah ya baki lfya, kina ta6a ni xa ki sha mugun mamaki idan kika ga mijin ki ya tsaya min, mate din ki masu ji da karfi boxing suke yi why not ke ma ki fara da ki zo nan kina xubar da mutuncin ki gun 'yar cikin ki" Safeenah tayi wani kara ta kunduma mata wani xagin tace "Ki bude kofar idan ke ba shegiya bace" Imaan tace "Shegun biyu a nan ai, jarababbiya kawai" daga haka Imaan ta koma gefen gado ta xauna tana murmushi, Safeenah sai buga kofar take kamar xata cire, imaan bata sake kulata ba har ta bar kofar tana ci gaba da zage xage, sai kusan bakwai da rabi Mujaheed ya shigo gidan, ya kwankwasa kofar Imaan, mikewa tayi ta isa gun kofar ta tsaya, ganin ba a bude ba Mujaheed yace "Imaan" bude kofar tayi yana kallonta yace "Have u prayed" Bata basa amsa ba ta nufi kan gado ta xauna ta fashe da kuka, da mamaki ya karasa kusa da ita yace "What happened???" Cikin rawar murya tace "Ko ba matarka bace ta xo tana ta xagina tana bubbuga kofa wai xata dokeni, har da ce min karuwa" sae ta kuma fashewa da kuka sosai amma ba hawaye, mikewa yyi ya fice daga dakin, ta bi sa da kallo tana turo baki, Bude kofar dakin Safeenah yyi ya sameta xaune gefen gado waya kare kunnenta tana hawaye, katse wayar tayi lkci daya ganinsa, Yana kallonta da kyau cikin daga murya yace "Let me drop u this warning Safeenah, even by mistake, I mean mistakenly kika sake yi ma Imaan kallon banxa a gidan nan balle ki gaya mata magana mara dadi I will show u the other side of me, I will show you the bad side of me, Billah xa ki iya min komai in shanye in kyale ki amma banda ta6a Imaan, idan kuma kin xata wasa nake try anything silly for the second time wllh i will make you regret it" Wani murmushi tayi tace "Toh mu xuba mu ga" daga haka ta shige bandaki tayi banging kofar ta rufe. Imaan har ranta taji dadin samun Safeenah da Mujaheed yyi kuma duk tana jin abinda yace mata don a bude ya bar kofar, parlor ta sauka don warming din abinci ranta fess. Karfe goma Imaan na xaune gaban mirror tana shafa cream din gashinta a kai aka bude kofar dakin ta juya da sauri, ganin Mujaheed ta ci gaba da shafa man da take, Karasawa yyi kusa da ita ya mika mata wayar hannunsa ta karba tana kallon screen din kafin ta kai kunnenta, ya juya ya fita dakin, tana murmushi tace "Ina yini Aunty?" Daga daya bangaren Aunty tace "Lafiya lau Imaan ya ku ke?" Imaan tace "Alhmdllh, Aunty yaushe su Maimoon xa su xo?" Aunty tace "Idan kun dawo kaduna xa su xo daughter" a hankali Imaan tace "Toh Aunty" Aunty tace "Ki kwantar da hankalinki kinji Imaan, What happened is the best for you in sha Allah, kuma Babu ruwanki da abokiyar xaman ki" imaan bata iya ta ce komai ba, Aunty tace "Toh sai da safe" Murya can kasa tace "Nagode Aunty" daga haka Aunty ta katse wayar Imaan ta ajiye a sanyaye ta ci gaba da abinda take, daga karshe ta mike ta hau saman gado ta kwanta, Mujaheed ya shigo dakin ya dau wayarsa dake gaban mirror ya dawo kusa da ita ya xauna yace "Ain't you taking the fruits again?" Girgixa masa kai tayi, yace "Toh in kira maki Ammi?" Mikewa xaune tayi da sauri tace "Ehh pls" yayi dialing number Ammi ya mika mata sannan ya shiga bathroom, Ammi na dagawa daga daya bangaren Imaan taji dadi har ranta, sallama Ammi tayi, A sanyaye Imaan tace "Ina yini Ammi?" Ammi tace "Lafiya lau Imaan, ya kike?" Imaan tace "Alhmdllh, Ammi Daddy na fa?" Ammi tace "Yana Abuja" Imaan ta yi shiru, Ammi tace "Kiyi hakuri Imaan, Allah plans best, Allah yasa hakan shine ma fi alkhairi gare ki, ki kwantar da hankalin ki" Imaan ta d'an yi murmushi cikin sanyin murya tace "Ae nayi Ammi" Ammi tace "That's good...." Imaan tace "Toh me yasa Ammi ba ku xo da su Mama Hadiza ba?" Ammi tace "In xo in maku me?" Murmushi kawai Imaan tayi a hankali tace "Ina missing din ki ne" Ammi tace "Idan kin xo gida xa ki gan ni ai" Imaan tace "Toh Ammi" Ammi tace "Babu ruwan ki da kula abokiyar xamanki kin dai ji me na ce maki komai ta maki kar ki tanka, ki yi hakuri" Imaan tace "Toh Ammi" Ammi tace "Toh sai da safe" Imaan ta kalli kofar bathroom tace "Baxa ku gaisa da Yaya ba Ammi?" Katse wayar Ammi tayi, Imaan ta dinga kallon screen din sannan ta ajiye wayar ta kwanta ta lumshe ido, tana ji Mujaheed ya fito yayi shirin bacci sannan ya dawo kusa da ita ya dau wayarsa da ta ajiye gefenta yana kallon fuskarta, yace "Tashi ki sha drugs din ki" A hankali ta bude idonta tana kallonsa, ya mike ya dauko mata Magungunan ya ajiye mata sannan ya fita downstairs dauko ruwa, har ta bude Magungunan kafin ya dawo, ya mika mata ruwa a glass cup ta amsa ta sha maganin, ya fita da cup din ta koma ta kwanta haka kawai gabanta ke faduwa, ya shigo ya kashe wutan dakin ya kwanta daya side din yace "Did u perform ablution before going to bed?" Bata amsa masa ba ta juya masa baya, Bayan kusan minti goma ya mirgina a hankali ya dawo kusa da ita, juyowa tayi da sauri tana kallonsa cikin sanyin murya tace "Yaya" Jin yanda xuciyarta ke bugawa murya can kasa yace "Are you okay?" Ta girgixa masa kai lkci daya hawaye ya kawo idonta, kallonta ya dinga yi cikin duhun, a hankali ta rufe ido ta daura kanta jikinsa cikin sanyin murya tace "Bacci nake son in yi" d'an murmushi yyi ya rungumeta, ya kwantar da murya yace "Kiyi baccin ki, don't be afraid" Bata ce komai ba tayi lamo jikinsa har lkcn yana jin yanda xuciyarta ke bugawa, sai da ya ji saukan numfashinta alamar bacci ya fara daukanta bayan wani lkci ya daura lips dinsa forehead dinta ya lumshe ido cikin sanyin murya yace "I... i love you" Bude ido tayi da sauri, ya kankameta yace "Bacci nace kiyi kanwata" Bata san lkcn da tayi murmushi ba ta lumshe ido ta mayar da kanta... Wajajen karfe biyu na dare Imaan ta farka ta gansa tsaye yana sallah, mikewa xaune tayi ta sauka saman gadon ta shiga bathroom ta dauro alwala ita ma ta fito ta bude jaka ta dau daya daga Hijabs dinta. Washegari da karfe goma na safe Mujaheed na tsaye bakin kofar kitchen bayan sun gama breakfast Imaan na wanke plates din da aka yi amfani da, ko na minti daya bai yarda ya bar ta ita kadai ba, ko me xata yi outside her room yana tare da ita, kuma tun da gari ya waye Safeenah bata sakko ba shima bai je dakinta ba, Kamar ance ya juya ya ganta ta sakko stairs yafe da mayafi ta nufi kofar fita, ya bi ta da kallo ganin xata fita, calmly yace "Where are u going to?" Ko kallonsa bata yi ba har ta fice daga gidan, Imaan ta tabe baki tana ci gaba da aikin da take. Sha biyu saura Mujaheed ya fita gidan don siyo ma Imaan dake masa complain din ciwon kafa maganin tube da take shafawa, tun wayewar gari take ce masa kafarta na ciwo, yana fita dama yace ta saka makulli kofarta, Safeenah ce xaune parlor tana ta communicating da 'yan gidansu da suka shigo garin zaria tana masu kwatancen gida, bell taji aka danna daga karshe, ta mike taji sanyi har ranta ta isa kofar ta bude tana cewa "Ashe kun ma kusa...." Umma ce tsaye bakin kofar, Safeenah ta dinga kallonta daga sama har kasa, a takaice tace "Daga Ina kuma wa kike nema??" Umma ta bude baki tana kallonta da mamaki tace "Wa nake nema Safeenah??" Cike da rainin wayo Safeenah tace "Kinga.. tun ina danne xuciyata muna magana a mutunce ki juya asirin ki a rufe ki bar gidan nan Hajiya Rukayya...." Umma ta katse ta tace "Ehh lallai kin cika yar iska mara mutunci Safeenah ni kike gaya ma haka


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login