Showing 258001 words to 261000 words out of 303099 words

Chapter 87 - Imaan Book 1 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

1677

a gidan d'a na? Ni????" Safeenah tayi wani dariyar rainin wayo tace "D'an ki? D'an ki fa kika ce? To wllh you are mistaken, kuma xaki san a da Mujaheed yake d'an ki, a da kike da iko da shi ba yanxu ba, bari ki ji abinda baki sani ba... Ke da Mujaheed sai dai hange daga nisa, sai kin san mu gidan mu ba bokaye muke bi ba matsafa masu shan jinin mutane muke bi, kuma tun muna magana ta fatar baki cikin mutunci ki juya ki ja tsummar kazamar rayuwarki ki bar gidana, shaidaniya annami...." Wani wawan mari Umma ta sauke mata tana huci, ta kuma sauke mata wani, Safeenah ta dafe kuncinta ta yo waje da ido da karfi tace "Ni kika mara Hajiya Rukayya?? Ni kika mara?" Umma na nuna ta cikin bacin rai tace "Na mare don uwarki, sakayyar da xa ki...." Umma bata rufe baki ba Safeenah ta sauke mata nata tagwayen marin masu lafiya, Umma ta gigice ta dafe kuncinta cikin shock tace "Ni kika mara Safeenah?" Cikin tsawa Safeenah tace "An mare ki Rukayya kiyi abinda xa ki yi, nace na mare ki, uban waye ke da baxan mare ki ba, meye a ciki don na mari shugabar bokaye da malaman garin kaduna?" Duk wannan abun Imaan na tsaye stairs tana kallonsu don da karfi Safeenah ke magana, lkci daya Umma ta shako Safeenah da karfi tana huci tace "Yau sai dai wata ba ke ba don ubanki, yau sai dai Mansura ta haifi wata" Safeenah ta cakumota ita ma, nan suka fara dambacewa bakin kofar suna ba juna kashi ba kakkautawa, Safeenah ta samu nasaran hayewa kan Umma ta dinga dukanta iya karfinta tana huci tana cewa "Sai na illata ki yau yanda baxa a gane ki ba idan kika bar gidan nan, ta dalilin hassadan ki da bakin ciki da mugun hali aka min kishiya kika dinga ja na gidajen bokaye da malamai don a lalata auren yarinya da saurayinta har aka fasa auren aka makala ma mijina, kin cuce ni, kin cuce ni, kin yaudare ni, Allah ya isa tsakanina da ke, axxaluma, wllh sai na illata ki yau duk abinda xai faru sai dai ya faru...." Kasa motsi Imaan tayi da farko ta makale jikin stairs tana kallonsu, ganin duka ba na wasa take ma Umma ba ta sakko da sauri tayi kan Safeenah, Safeenah na ganin haka ta raba hankalinta biyu wanda hakan ne ya ba Umma da jini ke fita bakinta da hanci damar hankadeta da karfi daga kanta ta shako wuyarta, Mari me lafiya Imaan ta wanka ma Safeenah ta fixgo gashinta da karfi tace "Yau na tabbata ke jaka ce, jahila kuma mahaukaciya.... " Safeenah tayi wani kara xata fixgo Imaan Umma ta danneta kasa, nan suka hade da Imaan suka dinga jibgarta tana ihu, Imaan bata ta6a sanin tana da karfi haka ba, don dukan Safeenah take kamar an aikota, hakan yyi dai dai da shigowar Hajiya Baturiya da Hajiyan Marafa da wata kawarta, a rikice Hajiyan Marafa ta dinga salati tana komawa baya, Imaan na ganin haka ta daga Safeenah da sauri, tana jan Umma da ta mike ita ma su bar wajen, Hajiyan Marafa ta durkusa gaban Safeenah da jini ke xuba bakinta tana salati da karfi tana cewa me xan gani haka, Hajiya Baturiya tayi wani kukan kura kamar mahaukaciya tayi kan Umma da ta nufi stairs da gudu tare da Imaan.



*Imaan isn't for free* it's 300 via


Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788




91.....




Imaan da har wani rawa jikinta yake ta bude kofar dakinta bayan sun haura sama kamar kiftawar ido ta shige, kiris ya rage Hajiya Baturiya ta cafke Umma, Umma ta shige dakin da mugun sauri ta tura kofar da karfi Imaan na taya ta suka sa makulli, wani mahaukacin bubbuga kofar Baturiya ke yi tana kunduma ma umma munanan ashar tana cewa sai ta illata ta yau, Imaan dai na tsaye tana kallon kofar gabanta na faduwa sosai ta dinga sauke numfashi, bayan kusan minti biyar ta juya a hankali ta ga Umma xaune bakin gado ta rike kai sai sauke numfashi take ita ma, dauke kai Imaan tayi ta tafi gun window ta tsaya, har lkcn Baturiya da Hajiyar Marafa basu fasa bubbuga kofar kamar xa su balla ba suna tsine ma Umma suna cewa idan ta isa ta fito, Imaan dai sai kallon kofar take tana tsoron kada ya balle su shiga uku, don ba bugun wasa suke ma kofar ba, jin budewar gate ta juya da sauri tana kallon compound ta window, Mujaheed ne yayi parking ya fito daga motar hannunsa rike da leda, wani ajiyar xuciya Imaan ta sauke, lkci daya ta ji hankalinta ya kwanta, jin su Baturiya basu hakura da buga kofa ba suna tsine tsine ta nufi kofar tace "Lallai da gaske kun cika dangin mahaukata gantalallu, mu kuma ba mahaukata bane shi sa baxa mu kula ku ba, kuma aniyar ku ta bi ku" Muryar Safeenah taji da karfi tana cewa "Wllh wllh sai dai matsiyaciyar uwar ki ta haifi wata yau, sai kin san kin ta6a ni yau, sai nayi rugu rugu dake na illata ki, na lalata maki kamanni na maki wannan alkawarin" Imaan tayi wani dariya har da tafe hannu tace "Nasan darajan iyaye ni baxan xage iyayen ki ba, duk da sun gama xagin kansu tass a idona, don tunda nake ban ta6a ganin gantalallu marasa aikin yi irin family din ki ba, kuma a kanku tsiya ya kare, ga alama na gani" Imaan na fadin haka ta juya tana murguda baki ta koma gun window, xage xage suka dinga yi in Unison kamar barbarians ko wacce na fadin abinda xata ma Imaan, Umma dai har lkcn tana xaune ta rike kai, Muryar Mujaheed Imaan taji da mamaki yana cewa "What's happening here?" Babu warce ta tankasa cikinsu, sai dai duk sunyi tsit sai kas kas din chewing gums, Hajiyan Marafa da kawarta da Baturiya suka ja gefe suka tsaya ko wannensu na huci, Mujaheed ya daure fuska sosai yana kallon Safeenah cikin daga murya yace "I am asking you Safeenah me ke faruwa a nan?" Safeenah dake tsaye da kumburarren baki tana masa wani shegen kallo cikin tsawa tace "Ban sani ba Mujaheed" Kofar dakin Imaan ya nufa da sauri yana bubbugawa yace "imaan? Imaan?" Fashewa Imaan tayi da kuka sosai ta iso kusa da kofar cikin rawar murya tace "Yaya cewa fa suka yi xa su kasheni" Mujaheed ya kalli Safeenah da sauri yace "What?? Hauka kika fara yi Safeenah?" Hajiyan Marafa tace "Uwarka Rukayya ce mahaukaciya ba 'ya ta ba Mujaheed, nace uwarka ce mahaukaciya.." kallonta kawai Mujaheed ke yi ko kiftawa bbu, lkci daya idanuwansa suka sauya kala, ya dauke kai cikin daga murya yace "Open the door Imaan" a hankali Imaan ta murda makullin kofar ta bude kadan ba duka ba, Safeenah na ganin haka tayi kanta da gudu xata fincikota tana huci, cikin zafin nama Mujaheed ya hankadeta a tsawace yace "What are you trying to do??" Shiga dakin yyi ba tare da ya shirya yin hakan ba ganin Hajiyan Marafa da Baturiya sun tunkaro kofar da sauri, ya rufe kofar ya sa makulli, Imaan ta makale bayan kofar xuciyarta na bugawa, still Mujaheed yyi ganin Umma dake xaune rike da kai gefen gado, da mamaki yace "Umma...." Sai a lkcn Umma ta dago kai tana kallonsa tace "Mujaheed kada auren Safeenah ya kara minti biyu a kan ka, ka sallameta yanxun nan" tana magana hawaye ya fara sauka idonta kamar an bude famfo, sai kawai ta rushe da kuka, Mujaheed ya nufeta with shock ya duka gabanta yace "Me ke faruwa Umma? Me Safeenahr ta maki??" kuka kawai Umma ke yi tana girgixa kai, irin kukan takaicin nan, Mujaheed da ya rude gaba daya ya mike da sauri yana kallon Imaan dake makale jikin bango har sannan yace "Tell me what happened Imaan, me ke faruwa??" Imaan ta sauke idonta kasa, kamar baxa ta ce komai ba sai kuma tace "Dambe tayi da Umma..." Da karfi yace "What?? Safeenar tayi dambe da Umma?" umma na kuka tace "Kwarai kuwa Mujaheed, Safeenah ta xageni ta daga hannu ta mareni sannan ta hau ni da kokuwa" kuka ne ya ci karfinta, ta rike kai tana rusa kuka sosai, lkci daya idanuwan Mujaheed suka kada sosai, ya juya ya nufi kofar ya bude ya fita, bai gansu corridor din rooms din ba ya sauka downstairs da sauri, Ganin yanda Umma ke kuka Imaan ta nufeta a hankali tace "Kiyi hakuri Umma" Umma bata kalleta ba kuma bata daina kukan da take yi ba tana girgixa kai, Imaan ta sauke kanta kasa ta nufi kofa walking slowly, dai dai staircase din karshe ta tsaya tana leko parlon kamar munafuka, Hajiya Baturiya na xaune tare da Hajiyan Marafa da kawarta sai Safeenah banda kundume kundume babu abinda suke suna kara fadin abinda xa su yi ma Umma yau, Safeenah na ganin Imaan ta mike kamar mahaukaciya ta nufeta dw gudu, Imaan na ganin haka ta juya da sauri xata gudu ta koma sama ta ci karo da Mujaheed dake sakkowa a bayanta, shigewa jikinsa tayi jikinta na rawa, ya shiga sakkowa stairs din a hankali yana rike da Imaan, Safeenah dai na tsaye tana huci tana kallonsa don tunda take bata ta6a ganin irin expression din fuskarsa ba tare da shi, can ta sauke idonta kan takardar hannunsa har ya iso gabanta ya mika mata takardan looking straight into her eyes da idanuwansa da suka dawo kamar garwashi, kin amsawa tayi tana kallonsa da idanuwanta da ta gwalo xuciyarta na bugawa, ganin bata amsa ba ya isa kan kujera ya ajiye yana mata wani kallon da ya firgitata cikin muryar da bata ta6a saninsa da shi ba yace "I don't want to see you in my house in the next 30 mins Safeenah...." Ba ita ba har Imaan sai da ta d'an yi shock jin furucin sa, Hajiya Marafa ta mike da sauri ta isa gun takardar ta dauka ta warware, Ita dai Safeenah na tsaye ta kasa ko da motsi tana kallon Mujaheed, lkci daya Hajiyan Marafa ta ajiye takardan bayan ta gama karantawa ta nufesa da mugun sauri tana kallonsa cikin daga murya tace "Mujaheed ita 'yar tawa xaka ma sakin walakanci?? Ita Safeenahr ka saka" Bata jira amsar sa ba ta sauke masa wani lafiyayyen mari, Mujaheed ya dinga kallonta ko kiftawa bbu, wani marin ta kuma sauke masa ta cakumosa tana kunduma masa xagi tana huci tace "To wllh karya kake, nace karya kake, baka isa bane, bbu saki a auren mu...." don kanta ta sakesa bayan ta gama jijjigasa, ya sauke idonsa sannan ya nufi inda ta jerar da takardan ya dauka da pen din ya fara wani rubutun a kai, cikin few seconds ya nufi Safeenah dake tsaye kamar Status tana bin sa da kallo ya kamo hannunta ya sa mata takardan cikin cool voice dinsa yace "Na sake ki saki daya, saki biyu, saki uku, within the next 30 min ki tattara duk wani abu naki ki bar min gida na, xa mu hadu a court da ku for insulting my own mother" Imaan ta dinga kallon Mujaheed ko kiftawa bbu very shock as well, Muryar Umma suka ji a stairs, a hankali tace "Allah ya maka albarka" Wani kara Safeenah tayi cikin gigicewa ta nufesa tana cewa "Wllh ina sonka Mujaheed, ka saurareni ka ji abinda yasa na aikata abinda na aikata, wllh mahaifiyar ka ce ta ja min komai, ni ban san boka ko malam ba, wllh ita ta cuceni ta kai ni don mu raba auren Imaan da Bulasawa, sai ga shi Allah ya nuna mana ishara an aura maka Imaan din, she is the cause of everything happening here, don Allah ka saurareni Mujaheed wllh baxan iya rabuwa da kai ba xan iya rasa raina, Ina sonka Mujaheed...." Calmly Mujaheed yace "Ko da gun masu tsafi ta kai ki I can't change her from who she is, she still remains my mother..." Duk da wajen Umma Hajiyan Marafa ta yi niyyar nufa kamar wata xararriya amma ganin Safeenah ta sulale kasa yasa ta tsaya gun 'yar tata ta durkushe kusa da ita ta dagota ta fasa wani ihu, Hajiya Baturiya da kawar Hajiyan Marafa duk suka taho gun cikin rikicewa, Mujaheed da idanuwansa suka koma kamar garwashin wuta ya kama hannun Imaan da ta kasa motsi suka bar wajen, tuni Umma ta koma sama tana goge hawayen dake sakko mata ba kakkautawa, xaune suka tadda Umma gefen gado ta rike kai, Mujaheed ya isa kusa da ita ya durkusa cikin sanyin murya yace "Kiyi hakuri Umma, I am sorry all this happened, don Allah Umma kiyi hakuri..." kuka ta fara yi sosai ta kasa ce masa komai, Imaan dake tsaye kusa da mirror ta sunkuyar da kanta ita ma hawaye ya cika idonta, Mikewa yyi yana kallon Imaan yace "Get set we are leaving now" Yana fadin haka ya fita dakin, Imaan ta nufi Umma dake kuka har lkcn ta durkusa a hankali tace "Umma kiyi hakuri" Umma dai bata ce mata komai ba.... Su Hajiyan Marafa sun kwasa gaba daya sun je kai Safeenah da ta ki farfadowa duk ruwan da suka dinga xuba mata hospital, Bayan Umma ta fita dakin ta koma parlor ta xauna Mujaheed ya shigo yana kallon Imaan dake rufe jakarta bayan ta dau Hijab, xaunawa yyi gefen gado, ganin mood dinsa ta nufesa ta xauna kusa da shi a hankali kafin tace komai ya kamo hannunta yace "Pls Imaan let this be a secret between us, kar ki ce ma kowa komai a gida plss" ganin yanda idanuwansa suka rine ta rungume sa a hankali tace "In sha Allah Yaya, sorry about all what happened" sun fi minti biyu a haka sannan ta xame jikinta tana kallonsa, mikewa yyi cikin sanyi yace "Am waiting for you outside" daga haka ya nufi kofa ta bi sa da kallo cike da tausayin sa har ya fita, tasan shi daya yasan abinda yake ji ynxu, ace mahaifiyar ka ga abinda take yi kuma tasan bbu karya a xancen Safeenah, shi ma kuma yasan haka, but dole uwa uwa ce. Bayan few minutes Mujaheed ya bar gidan tare da Imaan da Umma after making sure bai bar komai nata a cikin gidan ba, duk a compound ya bar mata su kuma ya kulle gate dinsa ta waje, Imaan na xaune gaban mota abubuwan da suka faru na sake dawo mata fresh, Umma dai tayi jigum bayan mota, Mujaheed kuma ya maida hankalinsa gaba daya kan driving din da yake sai dai kana ganinsa kasan yana tare da damuwa sosai, a haka suka shigo garin kaduna wajajen la'asar.... Imaan bata san lkcn da tayi wani murmushi ba lkci daya farin ciki ya baibayeta ganinsu a layinsu, Mujaheed na isa gate yyi horn Mai gadi ya bude masa gate yana daga masa hannu, bai iya ya tanka sa ba har ya shiga compound din yyi parking, Imaan ta bude motar a hankali ta sauka, bayan ya sauka, Umma ma ta sauka motar kanta a kasa, Imaan sai kallon apartment dinsu take tana jin kamar ta tafi da gudu, bbu wanda take son gani lkcn sai Amminta, maimakon mai gadi ya rufe gate sai ganin motoci har uku suka yi sun shigo compound din, Mujaheed ya dinga kallon motocin haka ma Umma da ta daga kai tana kallo, Bude first car din aka yi mahaifiyar Sadeeq ta fito motar cikin shiga ta alfarma sae ga wasu wa enda da alamar kawayenta ne su ma sun fito, Umma ta dinga kallonta ko kiftawa babu, lkci daya cikinta ya hautsine, tun da Imaan ta gansu jikinta yyi mugun sanyi, Umma na hade hanya ta nufi entrance din parlor da sauri....




*Imaan isn't for free* it's 300 via


Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788





92.....




Mama Hadiza xata fito parlor suka kusa cin karo da Umma bakin kofa, Bin ta da kallo Mama Hadiza tayi ganin saurin da take yi kanta a kasa har ta shige parlor, Mama Hadiza ta tabe baki ta fito compound din, imaan dai ta kasa kallon direction dinsu kamar mara laka ta nufi apartment din su xuciyarta na bugawa, Mujaheed ya gaishe su, Hajiya Khadijah ta amsa a takaice, bai kara kallonsu ba ya wuce ciki walking slowly, Mama Hadiza na kallonsa ta amsa gaisuwar da yake mata, bai tsaya ba ya shiga parlor ya rufe kofar, Mama Hadiza ta nufi su Hajiya Khadijah tana masu sannu da xuwa duk da bata san su ba tace "Toh ku shiga ciki mana" Hajiya Khadijah tace "Mai gidan mu ke nema, Allah ya sa dai yana nan" Mama Hadiza tace "In ji dai lafiya Hajiya?" Hajiya Khadijah tace "Lafiyar kenan dai, wajen sa muka xo" Mama Hadiza tace "Ai kam bai nan...." Hajiya Khadijah ta d'an yi shiru sannan tace "Kaninsa fa?" Mama Hadiza tace "Wai lafiya Hajiya? I am their sister" Hajiya Khadijah tace "Sorry I didn't introduce my self, ni mahaifiyar Sadeeq ce, kin gane yanxu kuwa?" Mama Hadiza ta bude ido tace "Ohh Allah sarki sannu da xuwa Hajiya, to mu shiga daga ciki mana, sannun ku da xuwa" Hajiya Khadijah tace "Yauwa mun gode, amma tunda basa nan da mun tafi gun kakar Imaan din koh?" Mama Hadiza tace "Ehh toh mu je can din, ai tana nan" Hajiya Khadijah tace "Toh nagode" a tare suka tafi part din Inna da frnds dinta da Mama Hadixa dake gaba suna biye da ita, Mama Hadiza ce ta fara shiga parlon Inna da sallama, sannan su ma suka shiga, Inna ta fito daki rike da tsintsiya ta dinga bin su da kallo, sannu suka shiga yi mata gaba daya, bata tanka su ba ta nufi bakin kofa bayan sun shigo ta duka ta dau doormat tana kakkabewa a waje tace "Sannu kuma sai kace me ciwo ni patuu" Mama Hadiza tace "Inna mahaifiyar


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login