Showing 66001 words to 69000 words out of 303099 words
taking in" kin tsayawa tayi tana kirkiran murmushi ta wuce sa da sauri, tsoronta daya kar ta gamu da Mujaheed, har dai ta isa parlon inna, Inna dake tsaye bakin kofa har lkcn ta sake baki tana kallon uban ledojin ta bi ta da kallo har ta ajiye na hannunta, Inna tayi kasa da murya tace "Imaan ina kika samo wannan kuma?" Imaan ta kwashesu gaba daya ta kai dakinta da sauri duk ta ajiyesu sanin Yusuf xai iya biyota, Tana fitowa dakin tace "Ni dai kawai kiyi shiru inna kar ya Mujaheed ya sani wllh duka xai min" Inna ta hade rai tace "Duka?? da kuwa ya dokar ma kansa fitina da bala'i, kuma da karshen xamansa ya kama a gidan nan" Imaan ta xauna saman kujera har sannan gabanta bai daina faduwa ba, Yusuf ne ya shigo parlon, inna ta wani tsuke fuska, yana kallon Imaan yace "Daga inna kike Imaan?" Inna tace "Yau naga jaraba, to ina ruwanka isuhu ko ka aiketa ne? Ku dai 'ya yan Ahmadu ku daina sa ido wllh, meye kuma wani daga ina take kamar xamanka take a gidan, ni dai ba ruwana, ku dinga tsoron Allah kuyi mai fishshe ku a gidan nan" juyawa Yusuf yyi ya fita parlon, inna ta kulle kofarta ta sa makulli, ta kalli imaan tana murmushi tace "Kar dai sabon saurayin ne yyi maki uban siyayyar nan takwara" Imaan tace "Wllh kar ki gaya ma kowa idan ba haka ba kazar ma baxan tsam maki ba" Inna tace "Ke ma dai da wata magana wllh, sai kace wata yarinya?? Wa xan gaya ma ni patuu, wannan ai sirri ne tsakaninmu" Imaan ta shiga ta fiddo ledan kajin guda biyu tace "Toh idan yaya ya shigo fa?" Inna tace "Oh oh Allah, waye kuma wani yaya, ina ruwana da shi, ko me xai xo ya min? Ko ya xo ma ni baxan bude kofata ba bbu ruwana, idan ma ya xo damuna yake ba abinda yake tsinana min"
*The book Imaan is not free, you read for free ur cup of coffee*🤷🏻♀️
It's 300 via Fcmb 3276052019
Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp digit 07087865788 to be included in the payment group.
21.....
Ammi ta bi Imaan da kallo ganin xata shiga daki tace "Kee" juyowa tayi tana kallon uwarta ta, Ammi tace "Ajiye min plate din kika yi kika fito?" Imaan tace "Ammi na wanke wllh" Ammi tace "Toh ki tafi ki sha maganinki ki daina min wannan yatsine yatsinen da kike yi" a hankali tace "Na sha Ammi, kai na ke min ciwo da bayana" Ammi tace "Allah ya sauwake" Har Imaan zata shiga daki sai kuma ta fasa ta dawo ta xauna kusa da Ammi murya can kasa tace "Ammi don Allah idan na gaya maki abu baxa ki min fada ba?" Ammi na kallonta tace "Idan ya kama in maki fada ae dole in maki" Shiru tayi tana kallon Ammi, Ammi tace "Ina jin ki" Sauke idonta kasa ta yi tace "Dama..." Sai kuma tayi shiru, Ammi tace "Dama me?" Murya can kasa tace "Wannan mutumin da kika ji ina waya da shi da daddare shine da naje shopping mall daxu muka hadu" Marairaicewa tayi tace "Ammi wllh ban san ma ni ya siya ma ba" Ammi tace "Me ya siya maki?" Ta ja baya kadan tace "Chocolates, da abubuwan ci...." Ammi ta dinga kallonta, kafin tace "Ina suke?" Imaan na kara matsawa daga kusa da ita tace "Na kai part din inna, ina tsoron kar ki min fada" Ammi tace "Ni xa ki ma karya baki san xai siya maki ba koh??" Kamar xata yi kuka tace "Wllh Ammi ban sani ba, we just met at the supermarket" Ammi tace "Toh shi yaron a ina kika san sa?" Tace "Ai na ce maki abokin ya Muhsin ne kuma Yayan Classmate dita Mariya ce, a gidan gwaggwo muka hadu" Ammi tace "Toh yyi kyau, you had better be careful Imaan, kin san Abbanki won't take it likely with you if he should find out, ni dai kar ki ja min matsala bbu ruwana, banda shashanci ya maki yawa you ought to have known ur left from right now" shiru Imaan tayi bata ce komai ba, can ta mike a hankali ta wuce dakinta. Mujaheed na zaune parlon inna bayan ya dawo aiki ran Tuesday ita ko tana can tana shara, Imaan na kwance tana bacci kan 3 seater, tun da ya kalleta sau daya bai sake kallonta ba, bayan wani lkci inna ta shigo parlon, kakkabe kujeru ta dinga yi tana cewa "Ni dai gaskiya wannan yarinya ta Bukar tana takurani duk ta kare min kujerun sun lotse, sai dai naji kunya idan nayi manyan baki, yarinya dai kamar kyanwa kwanciya baya karewa, gashi yau laluran ciwon kafar ya tashi bata je islamiyyan ba ma, Allah ka dubi jikata ka yaye mata wannan bala'in da ba a san kansa ba, ni bari ma kwanan nan xan shirya inje in samu ta Rasulu in ji yanda xa ayi, sai dai duk abinda Ahmadu da Bukar xa su ce su ce, ai dai ba gun boka xa mu je ba" ganin ruwan kumfa inna ke kokarin kadawa Mujaheed yace "Ni dai magana na xo mu yi, ki bar wannan aikin naki da baya karewa ki saurareni" ta kallesa ce "Toh idan aiki ya kare ae kazanta ta tabbata kenan, ni ko ina xan yarda in daina aiki in mutu cikin dauda, ko kai baka ji dadi da kamshi da ka shigo parlon ba" yace "Abba nake son ki yi ma magana inna, wllh bana son tafiyar nan, ruwan garin ma ba iya sha nake ba balle abinci, kwanaki da muka je da ku har muka dawo ni ban ci abun kirki ba fa" Inna ta saki baki tana kallonsa, can tace "Toh yanxu ya kake son ayi?" Tace "Kawai ce ma Abba za ki yi xa ki aikeni kano in kai maki wani sako sai Yusuf ya kai su gaskiya" inna tace "Tohhh, yanxu kiransa xan yi kenan?" Yace "Ehh ki kirasa, sae kice masa ya min magana don kinsan in kece kika min ba xuwa maki aiken xan yi ba" Inna ta mike ta dauko wayarta tace "Toh kirasa" Dialing number Abba yyi ya sa a speak on ya mika mata, imaan sai tsaki take tana turo baki ita a dole an hanata bacci, sai dai ba wanda ya tanka ta, Abba na d'aga kiran inna tace "Yaro??" Abba yace "Ina yini" Tace "Toh lafiya lau, sae dai wuni nayi ina aiki wllh har bayan window na duk na share, na goge gilashin windon" Yace "Alhmdllh, fatan dai lafiya?" Ta gyara xama tace "Ina fa lafiya, wato kai dai ka haifa ma kanka fitina da abinda ya fi karfin ka ne baka sani ba har yanxu Ahmadu, wai dama don Allah ina ne asalin ko wani mutum dai bahaushe?" Abba yace "Ban gane ba inna" a d'an fusace tace "oh oh Allah, Asalin kowa nake tambayarka, ina ne asalina da na Ubanka?" yace "Asalin kowa kauye inna" Inna tace "Toh Alhmdllh, yanxu wannan mutumi Mujaheed ya xo ya sameni, ko gaisuwar kirki ba mu yi ba, ya fara bani sako in baka, wato cewa yyi ince maka shi baxai je kauye ba gaskiya, don kwanaki ma da mu ka je a gantale ya dawo ba abinci, har yana koya min karyar da xan maka na cewa xan aikesa kano ko uban wa gareni kano oho, wai sai Yusuf ya kai su kauyen, bai san ni yar gaskiya bace, ba a cin amana da ni, yanxu fisabillahi Ahmadu in ji kaga abinda yasa tun suna yara nake cewa ka dinga kai su can koh?" Mikewa Mujahedin da ya bude baki yyi yana kallonta, imaan ta sauko kasa ta dinga 6a66aka dariya, Abba yace "Toh yayi kyau ki kyalesa kawai, sae su tafi da Yusuf din" inna tace "Atoh, ni dai ba ruwana, ka tashi tsaye da rokan Allah kan Mujaheed" daga haka ta katse wayar ta tayi kasa da murya tana kallon Mujaheed tace "In dai ranka bai kwanta xuwa kauyen ba kada kaje gaskiya, duk bambamin da Ahmadu xai yi xuba masa na mujiya, haka kawai kaje ka cutu, don gaskiya ko ni bana cin abincin gidan hansai, to idan na ci na tsuge da xawo ya za ayi da ni???" Mujaheed ya juya a mugun fusace xai fita jin dariyar da Imaan take ya juyo ya haureta da karfi ya fice, wani ihu ta fasa ta rike kafar, inna ta mike da sauri tace "Fita ki bisa ni ba ruwana kada a dameni ya xa mu dinga magana ki mayar da mu mahaukata kina dariya" Imaan ta mike tana kuka sosai ta fita parlon tana dingishi ta wuce part din su, Ammi ta fito kitchen da sauri, Tace "Lafiya, me ya faru?" Cikin kuka tace "Yaya ne ya haure min kafar dake min ciwo da karfi gashi yanxu ya rike Ammi, Wllh ban masa komai ba" tana fadin haka ta xube kan kujera tana kuka sosai, Ammi ta karaso tana kallon kafar, har gun ya tashi yyi ja, Hijab dinta ta dauka ta sa ta fita parlon bata xame ko ina ba sai bangarensu, Yana xaune dinning takaici ya ishesa Anty kuma na kitchen da su Maimoon. Nan parlon Ammi ta tsaya tace "Mujaheed me Imaan tayi maka ka haureta a kafa?" Kallonta yyi ya dauke kai bai ce komai ba, ta karasa dinning din fuska daure tace "Tambayar ka nake malam, ka fara hauka ne xaka haureta a kafa, to Wllh even by mistake kada ka sake don zan dau mummunan mataki a kanka" Anty ta fito kitchen da sauri tace "Lafiya Hajiya Aisha?" A fusace Ammi tace "Wllh ku ja masa kunne ya fita harkar Imaan a gidan nan, duk ranan da ya sake gangancin ta6a lafiyarta xa ayi tashin hankali a gidan nan, haka kwanaki ya mareta na kai xuciya nesa ban ce komai ba, to this shud be the last, kada ya sake idan ba haka ba wllh sai na rama mata" Hakuri Anty ta dinga bata, Mujaheed ya mike ya wuce sama ba tare da ya sake kallonta ba, Ammi ta nufi kofa xata fita suka kusa cin karo da Umma xata shigo sun dawo anguwa da Rahma, ko kallonsu bata yi ba ta fice, tana komawa dama daki ta shiga ta dauko man xafi ta fito ta shiga shafa mata a gun, Imaan ta dinga yarfe hannu tana kiran daddy, bayan Ammi ta daina shafa wa a hankali tace "Ammi xuwa kika yi gun yaya?" Ammi tace "Baxan je ba ko shi ya haifa min ke?" Imaan na kallonta tace "Fada kika masa" Ammi tace "Abinda ya fi fada ma" imaan ta zaro ido tana kallonta, can tace "Ni da baki je ba Ammi ni ne fa nake ta masa dariya...." Da gudu ta mike bayan ta kauce marin da Ammi tayi niyyar sauke mata, ta wuce daki tana turo baki ta kulle kofar ta sa key, tana jin Ammi na cewa "Xaki fada min ko kanin ubanki ne yayan, daga yau ma kika sake xaunawa inda yake wllh sai na kakkarya ki a gidan nan" Inna ta saki baki tana kallon Mujaheed har ya gama, tura tuwon gabanta tayi tace "Ba lafiya, ita Aishar? To yaushe ta xama haka, atoh gaskiya imaan dai ta zama yar jaraba tunda akan ta uwarta taje tana maka bala'i, wato Allah kadai yasan abinda yarinyar ta tsara ma uwar, saboda irin wannan halayyar tata yasa aka rasa gane kan ciwonta fa har yau, to meye kuma yarinya karama da hada gurmi a gida, ae da sai kace ma Aishar A'a ni ba ruwana baxan yi fada da ke ba don kin haifeni, ai ke kusan sa'ar uwata ce, to kawai kuma sai ka tsaya kallonta kayi shiru" Mujaheed yace "Ni baxan ce mata komai ba ko sbda daddy, amma ta sake min haka a gidan nan gaskiya sae dai duk abinda xae faru ya faru" Inna tace "Ni ko sai naje na sameta wllh" da sauri Mujaheed yace "A'a kar ki ce mata komai" Inna ta ja tsaki tace "Ba dole in sameta ba xata sa ka gaba tana jaraba a kan figaggiyar yarinya mai hada gurmi" tana fadin haka ta fice parlon, Ammi na shafa ma Imaan man xafinta a kafa Inna ta shigo ba ko sallama, Ammi ta mike tace "Sannu da xuwa inna" inna tace "Aa ba wani sannu da xuwa, yanxu Aisha a kan yar ki xa ki sa Mujaheed gaba kina masifa inda kike shiga ba nan kike fita ba kamar xa ki make sa, to ma ina ruwanki kina 6are xa ki shiga harkan 'yan uwa, ubansa fa wan ubanta ne uwa daya uba daya, to ke kuma a wa Allah na tuba, Ba kunya ba tsoron Allah xaki shiga fadan 'yan uwa, abinda ma ina xaune parlon d'an shafa kafar nata yyi ya fita shine munafukar nan ta dinga ihu tana min birgima ni kuma na koreta, ni dai ba ruwana kar ki lalata mana xumunci gaskiya, ko xane Imaan Mujaheed yyi yau kanwarsa ce kuma yana da ikon yin haka, to banda shi da ya tsaya mata kan lalurorinta shekarun baya da ba sai dai ta mutu ba, ni dai a dinga jin tsoron Allah, gashi nan dai albarkacin Bukar bai kula ki ba, toh ni dai kada a sake sa min jika a baki ba ruwana, banda ma bifillatani agwai da wauta ina shi ina shiga sha'anin family" tana kai wa nan ta fice a parlon, Ammi ta rufe man hannunta tana kallon Imaan tace "Wllh na sake ganin ki xaune inda Mujaheed yake a gidan nan sai na kusa sumar da ke" Imaan dai ba ta ce komai ba. Misalin sha daya Imaan ta mike daga kwancen da take da kyar xata shiga daki ta kwanta, duk jikinta ciwo yake mata ga wani xafi da jikin yayi, Ammi dake xaune parlon tace "Kina ji na" imaan ta juyo tana kallonta, Ammi tace "Dama gobe kice masu baki jin dadi baxa ki iya tafiyar ba, don babu inda xa a dake, ina xaman xamana a kwaso min wahala a bar ni da jiyya" Imaan tayi shiru tana kallonta, can tace "Toh" daga haka ta wuce cikin daki ta kwanta. Washegari karfe tara su Maimoon, Ummi da Rahma suka gama shirin su na tafiya, kaya kala biyu ko wannensu ya dauka Abba duk ya basu kudin kashewa, Yana kallon Ummi yace "Tafi ki duba ko mamana ta gama shirya wa" Ummi ta fita parlon xuwa part din su Imaan, Ammi ta fito daga bedroom din Imaan kenan rike da cup din shayi don da mugun xaxxabi ta tashi safiyar ranan, Ummi ta shigo parlon da sallama, gaisheta tayi tace "Abba yace Imaan ta fito" Ammi tace "Ae kam yau ta tashi babu lafiya" Ummi na komawa ta fada ma Abba haka, Abba yace "Subhanallah ba lafiya kuma" mikewa yayi ya fita, a dai dai part din su Imaan ya hadu da Mujaheed ya dawo daga bangaren inna, Abba yace "Imaan wai bata da lafiya yau" Mujaheed yace "Subhanallah" Abba yace "Let me check on her" Mujaheed bai ce komai ba kamar ya juya yayi tafiyarsa sai kuma dai ya bi bayan Abba, Ammi suka gaisa da Abba, Mujaheed yayi kasa da kai ya gaisheta, Ita ma ba tare da ta kallesa ba ta amsa bbu yabo bbu fallasa, Abba yace "Toh ya jikin nata?" Ammi tace "Toh da sauki, tun jiya dama bata jin dadi" Abba yace "Ikon Allah" Ammi tace "Tana ciki" Abba ya nufi dakin nata, Mujaheed ya bi bayansa kansa a kasa, kwance suka sameta cikin duvet amma still sai shivering take, Abba ya cire duvet din yace "Sannu mamana" Bude idanuwanta da suka rina tayi a hankali, Abba yace "Ina ke maki ciwo" girgixa masa kai kawai tayi, Mujaheed ya duka kusa da ita a hankali ya kai hannunsa jikinta, Abba na kallonsa yace "Ko dai a tafi asibiti" Mujaheed xai yi magana aka bude kofar dakin inna ta shigo a rikice tace "Ahaf, ni dama nasan xa a rina, ba ayi hauri ba ma ya aka kare balle anyi, wllh Ahmadu da ya tattakure ya tattakure kawai sai gani nayi ya haureta"
*The book Imaan is not free, you read for free ur cup of coffee*🤷🏻♀️
It's 300 via Fcmb 3276052019
Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp digit 07087865788 to be included in the payment group.
22. Imaan
Abba ya juya ya kalli Mujaheed jin abinda inna tace, Imaan ta mike xaune da kyar tace "Ba fa kafana ke ciwo ba" Inna tace "Toh ina ke maki ciwo" Komawa tayi ta kwanta bata tanka ta ba, Ammi dake tsaye bakin kofar dakin sai kallonta take, Abba na kallon Mujaheed da ya kasa cewa komai yace "Amma me yasa xaka haureta jiya?" Ya sunkuyar da kai yace "It wasn't intentional" Abba ya gyada kai yace "It wasn't intentional, OK that's good kayi kokari" Daga haka ya juya ya kalli Ammi yace "Ta shirya ta fito mu je asibiti" daga haka ya fita dakin, Mujaheed ya harari Inna fuska daure xai fita tace "Oho dai ta rufa ma ka asiri amma ko tantama babu haurin da ka mata ne ya ja mata wannan ciwo" Ammi ta basa hanya fuska daure, kansa a kasa ya fita dakin, Inna tace "Kyansa duk inda imaan xata ga Mujaheed daga yanxu ta gudu tayi ta kanta, ni dama tun da naga yanda yake laftar 'ya yan jama'ah a anguwa yana d'an yaye bai fi shekara 3 ba nasan akwai bala'i a gaba wllh, duk ya bi ya addabi 'ya yan mutane da cizo da yakushi a anguwa, kowa ya gansa sai ya adana d'an sa, lkcn d'an Hansai Garba na kamarsa kullum sai ya ciji garba yakushesa, Hansai tayi ta jin haushi don ta xo jegon Huraira a gida, in takaice maki kafin Hansai ta bar gidan idan aka bude jikin garba duk ta6on cixon Mujaheed ne,