Showing 150001 words to 153000 words out of 303099 words

Chapter 51 - Imaan Book 1 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

1638

gidanta ne, wllh ba abinda na mata daga sakkowarta ta fara min fada tana min warning" sake baki Inna tayi tana kallon Safeenah tace "Ba lafiya, ta shiga hankalinta kuma? Kinsan wacece ita kuwa yar nan, to bari kiji wllh wannan da kike gani ta fiye ma Mujaheed ke so dubu dari, kaji min mata kamar zabiya dai, ita da gidan yayanta kice ta shiga hankalinta sabida baki da tsoron Allah?? To wllh a kan Imaan sai Mujaheed ya kora ki gidanku yanxun nan, gwara ma ki xageni da ki ta6a min imaan gaskiya, duk da dai kin ma xageni tun daxu kawai dai ni me hakuri ce na ja bakina nayi shiru, kaji min mokadaddiyar mata dai xata sa min jika a baki in shiga uku???" Mikewa Imaan tayi kamar xata yi kuka ta nufi kofa tace "Ni sai kin dawo Inna baxan xauna ba...." Inna ta saki salati tana tafe hannu tace "Na shiga uku ni patuu, Mujaheed ya auri jaraba tunda ta ta6a imaan, ke me ya kai ki kinsan wacece kuwa, ita kenan fa uban ya haifa a duniya, ko kallon banxa ba a mata balle a mata fada... Shi Mujaheed din bai xaunar da ke ya sanar maki bane??" Bin bayan Imaan Mujaheed yyi ganin har ta fice parlon.


*Imaan isn't for free* it's 300 via


Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788


53....


Har Imaan ta sauka Balcony ta nufi gate Mujaheed ya rikota da sauri yace "Kee ina xa ki??" Ta hade rai kamar xata yi kuka tace "Ni dai gida xan wuce bayan ta gama xagina, Ni wucewa xan yi" Kallon Eyeballs dinta kawai yake, xata kwace hannunta ya kalli gate, lkci daya ya jawo ta kusa da shi murya can kasa yace "Toh kiyi hakuri...." ta turo baki ta ki cewa komai, ya dauke kai yayi murmushi yace "Toh baxa ki hakura ba..." Bata fuska tayi tace "Xagina fa tayi..." ya xaro manyan idonsa still smiling ya ja dogon hancinta yace "Ni ban ji inda ta xage ki ba, har da sharri...." Kwace kanta take son yi xata wuce ya ki saketa yace "Ai fa nace kiyi hakuri koh?" Kallonsa tayi fuska daure kamar xata yi kuka tace "Toh baka gaya mata ni wacece bane?" Dariya sosai ta basa, and he couldn't help it don har sai da yyi dariyan ganin maganan sak yanda inna ke yi, ya kamo duk hannunta biyu yace "Haba na gaya mata mana lil sis, amma kiyi hakuri xan sake gaya mata da kyau, yanxu mu koma ciki sai ki hada maku breakfast din mu rabu da ita...." imaan ta turo baki bata dai ce komai ba, yana murmushi yace "Idan mun koma sai kice ma Inna kin hakura don ta daina fada kin ji pls?" A hankali tace "Na ji" Yana kallonta sosai yace "Good girl" daga haka suka koma parlon yana rike da hannunta, Inna kadai ce tsaye parlon tana kallon stairs tana cewa "Ka ji min jarabbiyar mata ta ja Bukar ya kullace ni tunda ni na fito masa da 'ya har xa a sa ta a baki... to wllh hir dinki ni ba ruwana, to Wai ma ke baki da tsoron Allah ne?? duk hakurina yau sai da kika kai ni bango, banda haka kin fito daxu kin gaida ni a tsaye sandandan kamar katon soja, ni dai ban kula ki ba don babba da hakuri da kauda kai aka san sa, sannan na maki magana bamu karya ba kince kwantenar karyar da aka maki na gara bai sauka ba, ko ina aka taba gara a kwantena??? Ni dai duk ban kula ki ba ina ta hakuri shine yanxu xaki ta6a imaan baki san ba a ta6a min ita ba, to haka xa mu yi dake tun ban dawo gidan gaba daya ba?? Yau naga abinda ya isheni... Irin xaman da xa mu yi kenan ni patuuu da wannan figaggiyar yarinyar" Mujaheed ya karasa gun Inna yace "Haba Inna daga xuwa kuma, Imaan din fa ta ma ce ta hakura..." Inna ta kalli Imaan da sauri tace "Wai??" Imaan ta gyada kai a hankali, Inna ta koma ta xauna tana share xufar goshinta tace "Toh Alhmdllh... Sai ta sakko ta hada mana karin kumallo, gaskiya Mujaheed Ina ga baka yi dacen mata ba, tun fa ba aje ko Ina ba ta fara nuna hali, ko da yake ai ni me iya saita mata xama ne, ba haka na saita Rukayya ba ma Allah na tuba" Mujaheed ya kalli Imaan ya mata alamar da ta tafi kitchen din, ta rungume hannunta tace "Toh ni kadai?" Kallonta Inna tayi da sauri tace "Ke kadai me?" Mujaheed ya nufeta yace "Toh mu je" Ba musu ta nufi kitchen din ya bi bayanta, dukawa tayi gun dankalin da Inna ta fara ferewa, ya dau wukar ya mika mata yace "Be careful with the knife...." Bata ce komai ba ta amsa ta fara fere dankalin, ya duka kusa da ita yana kallonta, duk wanda ta gama ferewa sai ta sa a ruwan da ke kusa da shi, shi dai kallonta kawai yake, pieces shidda ta gama ferewa tace "Ai dai wannan ya ishemu ni da Inna..." Ya wara ido yace "Toh ni fa...." Kallonsa tayi da sauri tace "Har da kai?" A hankali ya gyada mata kai, ta tabe baki ta ci gaba da ferewa, wani kara tayi ta jefar da wukar sai ga jini a hannunta, ya daga ta da sauri yace "Subhanallah..." yarfe hannun ta fara yi a rikice tace "Wayyoo Yaya zafi...." Pampo dake kitchen din ya nufa da ita ya kunna yana tsaye bayanta ya shiga wanke mata hannun yana kallon cut din that isn't deep, a hankali yace "Sorry lil sis...." Yana gama wanke mata ya juyo da ita, hawaye ya gani idonta, lkci daya ya rikice yace "Yana maki xafi sosai ne??" ta fashe da kuka a hankali tace "Ba kai bane kace in kara bayan na gama namu da Inna" rungume ta yayi yace "Toh yi hakuri plss, we should have use the potatoe peeler instead" ya daga kanta yana share mata hawayenta da fingers dinsa, turo baki tayi tace "Ni dai sai dai kayi slicing din dankalin baxan yi ba" murmushi yayi yana ci gaba da goge mata idonta a hankali yace "Toh naji, sai ki kunna gas ki debi mangyada a pan" daga haka ya saketa ya koma gun dankalin, fry pan da ta gani ta dauko ta bude jarkan sabon man gyada ta deba a fry pan din sannan ta kunna gas ta daura, ta daura ruwan shayi ta sa lipton, ba dai kayan kamshi tunda bata san inda suke ba, tsaye tayi bayansa tana kallonsa har ya gama slicing dankalin ya mike ya ajiye bowl din a sink, ya juya yana kallonta yace "Toh ya xa ayi?" Yar dariya tayi tace "Baka sani ba Yaya" ya buda hannu alamar bai sani ba din, ta karasa inda yake ta wanke dankalin ta tsane duk yana kallonta, yace "Ke da ba ki girki a gida ma...." Murmushi tayi tace "Ehh amma ai ina ganin Ammi na yi, kuma dai na iya...." Shi dai bai ce mata komai ba, suna tsaye kitchen din har dankalin da ta xuba a mai ya soyu ta kwashe a plate, tana kallonsa tace "Toh ina eggs din?" Ya xaro ido yyi yace "Are you sure, kar kije ki tada min Asthma..." Ta turo baki tace "It's just an ordinary egg, sai in sa onion fa, ba yaji ai" Yana murmushi a hankali yace "Ohk...." Eggs din ya fiddo cikin few minutes ta fara soyawa bayan ta yi chopping onion a board, duk yana lura da ita to make sure she is fine din da gaske, can ya karasa kusa da ita ya tsaya bayanta a hankali yace "You are uncomfortable Imaan" ita dai bata ce komai ba don da gaske tsarkewa numfashinta yake yi ko don bata yi lowering gas din bane amma a gida ai tana soya kwai, ya rage gas din sosai ya juyo da ita tana facing dinsa giving her support with his broad shoulder, a hankali take sauke numfashin hade da shakar kamshin sa mai dadi, ya dinga juya kwan a frying pan har ya ga ya soyu sannan ya kashe gas din, gaba daya ya juye a plate din da ta dauko, ya kashe gas da ta daura ruwan xafi ganin yana tafasa, daga kanta yyi yana kallonta a hankali yace "Are you okay?" Kai ta gyada masa, yace "Ki tafi parlor xan kawo breakfast din yanxu" Bata ce komai ba ta nufi kofa ya bi ta da kallo har ta fita, wani plate din ya dauka ya debar ma Safeenah dankali da kwan ya rufe, sannan ya juye ruwan xafin a flask ya dauka da cups biyu da spoon ya tafi parlon, Inna na xaune sai shar6an bacci take har da minshari, ya d'an yi murmushi yana kallon Imaan dake xaune kasan rug ya ajiye flask din hannunsa yace "Are you sure you are okay?" Ta gyada masa kai, kitchen ya koma ya dauko plate din dankalin ya ajiye masu ya koma kitchen din, Tea mai kauri ya hada a cup sannan ya fita da kayan shayin ya ajiye, plate din dankalin da ya bari a kitchen din da cup din shayi ya tafi ya dauka ya fito, sama ya nufa imaan ta bi sa da kallo, can ta tabe baki ta dauke kai, Safeenah na dakinta tana waya da Mahaifiyarta ta sanar mata duk abinda ake ciki tun shigowar Inna gidan da sassafe, rai bace Hajiyan Marafa tace "Ban da ma kin nace sai shi Allah na tuba me xa ki yi da d'an wajen Rukayya, Ni fa da Rukayya kar ta san kar ne shi sa ban so auren ba, ke kuma kika ce ba ki san xance ba kin samu miji, amma duk wannan mai sauki ne wllh tllh, ni nasan ta yanda xan billo ma lamarin, ki kwantar da hankalin ki sai kace ba ni na haife ki ba dai, ai in sha Allahu yanda nake xaune hankali kwance ba damuwar kowa gidan ubanki haka ke ma xaki xauna gidan Mujaheed Safeenah in sha Allah" Safeenah na goge idonta tace "Toh Mummy..." Hajiyan Marafa tace "Kar ki nuna masu komai, har ita yarinyar me maki rashin kunya kar ki tanka ta, dama tunda Hajiya Rukayya tace min bata san wannan tsohuwar ba a wajen dinner nasan karya kawai take, amma ba damuwa... Ki kwantar da hankalinki dota babu mai sa maki ciwon kai in sha Allah a gidan auren ki, xuwa gidan ki ma sai ya gagare duk danginsa har ita munafukar uwartasa in dai ina numfashi, sannan kin ce har yau bai kwana dakin ki ba ko???" Daga kai Safeenah tayi jin an bude kofa da sauri tace "Mummy xa mu yi waya anjima" Bata jira cewar Mahaifiyar tata ba ta katse wayar, hade rai tayi ta kwanta ta juya baya, Mujaheed ya ajiye abincin hannunsa ya xauna gefen gadon yace "Plss plss kiyi hakuri Safeenah, nasan this is not proper at all cause this is just ur 2nd day a gidana, but plss keep this in mind haka grandma dina take wllh, kowa ya santa kece dai da baki santa ba, har ni ba barina tayi ba sai dai idan ban yi abinda xata yi magana ba, Imaan kuma bata da matsala kawai ba ku fahimci juna bane, she's very nice and sweet to stay with, ko a gida Grandma bata son a ta6a ta be it me or anybody... Ranan xa a ga the other side of her in har aka ta6a imaan kinsan takwararta ce, so plss you need not to worry beside just few hours fa xa su yi su wuce, and I assure you baxan yarda a taka ki ko a raina ki ba coz you are my wife...." Ita dai Safeenah bata juyo ba balle ta tanka sa.... Yace "Ga breakfast din ki" still taki cewa komai, Juyawa yayi ya koma downstairs, kallon Imaan da ta wani hade rai ya dinga yi har ya shigo parlon yace "Baxa ki hada shayin ba...." Kamar jira take tace "Ni ba yunwa nake ji ba dama ai"

*For the sake of My lovely Naomi Baba Abbasss ga nyt update after enough read mores daxu da safe, duk da dai ba wani kirki gareta ba oo* 😍

_You are reading imaan for free and still telling me nonsense and posting in groups ur *Big Wahala*_🤷🏻‍♀️ All I know Is that my book Imaan isn't for free. Gbamm!!

*Imaan isn't for free* it's 300 via


Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788


54....


Shiru Mujaheed yyi yana kallonta, can ya karasa kusa da ita yace "Saboda me baxa ki ci ba?" Kin cewa komai tayi, yyi murmushi ya xauna kusa da ita ya jawo cup da flask ya fara hada shayin, yana gamawa ya ajiye cup din shayin gabanta da plate din dankali, dauke kai tayi xata mike ya rikota, ta shiga kokarin kwace kanta tana cewa "Nace maka ni ba yunwa...." muryar Inna suka ji tace "Lafiya?? meye haka??" Saketa Mujaheed yyi da sauri, Inna na xaro ido tace "Lafiya kake matse yar mutane Mujaheed?" Ta gefen ido ya kalleta bai dai ce komai ba, Inna ta kalli Imaan tace "Me kika masa?" Kamar xata yi kuka tace "Inna nace masa na koshi fa shine wai sai na ci" Inna ta bude ido sosai tace "A'a toh ke kuma baki da tsoron Allah, kika koshi a Ina? Uban me kika ci? Bata fa karya ba Mujaheed... Ni dai ba ruwana, ka rabu da ita ka kada min nawa shayin in sha, ya wuce Allah ya masu hisabi da hanjin cikin nata" Murmushi kawai Mujaheed yake ya gama hada ma Inna shayin ya ajiye gabanta ya debar mata dankalin ta sakko kasa tace "Toh burodi fa?" Yace "Bari in fita in siyo yanxu" Inna tace "Atoh, na taba ganin inda aka sha shayi ba burodi dama" mikewa yayi ya fita parlon Inna ta bi sa da kallo ta rike ha6a tace "Ikon Allah, aure mai saita mutum ya gyara sa, dubi fa wani biyayya na musamman da Mujaheed yake yi yanxu daga ya kwana daki daya da mace, Ikon Allah ya fi gaban haka.... Mujaheed ne xan aika da ya tafi babu musu?? Lallai kamar Rukayya ta tsine masa, ai baxai ma je bane sai ya gama ja min rai ya gama min walakanci, ke ma dai Bulasawa yayi yayi ya yunkuro ayi auren nan ko kya yi hankalin, kinsan fa da ace ke ce kika yi aure da har na gama tarewa can gidan naki, toh wai yaushe ne wannan kaddararren jarabawan sakandarin ne ni patuu, wllh su Ahmadu da Bukar dama can basa tsoron Allah tun tasowarsu kamar dai ba ni na haifesu, Banda haka wani shegen jarabawa ne ya isa ya hana sunnar manzon Allah S.A.W.... Ni dai ba ruwana" Imaan dai bata tanka Inna ba sai fiffita shayin da Mujaheed ya hada mata take ta sha da sauri kafin ya dawo, Inna ta saki baki tana kallonta da sauri tace "Ya haka xa ki handame dankalin gaba daya Imaan, ba namu bane mu biyu" sosai ta ba Imaan da ta cika baki da dankali da kwai dariya, ko sauraranta bata yi ba ta dinga turawa har sai da ta ci kusan rabin plate din da kwai, Inna dai sai kallonta take baki bude, Imaan ta dau wani cup ta dinga fiffita shayin har ya huce ta kwankwade da sauri ta ajiye kusa da Inna tana goge bakinta, Inna ta rufe bakin da ta sake tace "Kunyar Mujaheed din kike yanxu ko me?" Da sauri Imaan tace "Kunya Kuma??? Ni dai kar ma ki ce masa na ci komai a nan, don ba abinda na ci" Bata jira cewar Inna ba ta koma kujera ta xauna tana goge bakinta da kyau, Inna tace "Dama mana, ya xa ayi ki iya cin rabin plate din dankali kamar jaka ai sai dai ni din..." Imaan dai bata kulata ba ta mayar da hankalinta kan Tv, Da sallama Mujaheed ya shigo parlon rike da ledan bread l, ya karaso ciki yana kallon empty cup din shayin da ya hada kafin ya fita, Imaan ta wani daure fuska tana kallon TV, Inna tace "Toh ba kya daure fuska ba dama kin handame komai kamar mayunwaciya, wllh Mujaheed yanda ka san ta shekara bata ci abinci ba, dubi abinda ta bar min fisabilillahi, ko mage aka bar ma wannan xata koshi balle mutum irina, yarinya dai sai ci kamar saniya" Imaan sai kallon Inna take kamar xata yi kuka, Mujaheed dai yayi murmushi ya ajiye bread din hannunsa yace "Toh tunda dai ba da kudin ki aka siyo kayan abincin ba kuma ba Amadun ki ko Bukar suka siyo ba me xai dameki? Gidan yayanta ne fa" Bai jira cewarta ba ya wuce sama, imaan ta dinga kallonta tana murmushi ranta fess, tabe baki Inna tayi ta bude bread din ta yagi kato a ciki a hankali tace "Toh da ban haifesu ba xa su haife ku?? da na sani ma in ki haifan nasu in ga ta tsiya, sai in ga ta yanda xa a same ku gantalallu kawai marasu tarbiya" sakkowa kasa imaan tayi ta dinga 6a66aka dariya, ita dai Inna bata ko kalleta ba ta tsuke fuska tana cin bread. Sai da tayi nakk dama ta mike ta kai plate da cup kitchen duk ta wanke duk abinda aka bata ta kife ruwan ya tsane sannan aka fara goge gogen kitchen din har wall din kitchen dai sai da ta goge sannan ta fito ta share parlorn tasss, sannan aka fara goge goge, tana goge sabbin kujerun da d'an kyallen da take goge goge tace "Babu wanda xai ce datti baxai fito daga parlon nan ba, kaii aji tsoron datti, datti ba kyau...." Ita dai Imaan kallonta kawai take, Inna ta gama goge goge ta wuce


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login