Showing 267001 words to 270000 words out of 303099 words

Chapter 90 - Imaan Book 1 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

1605

kin kwana lafiya to wani ko dare ma baxa ki isa ba kiji in gaya maki, Sai dai in maki fatan Allah ya raba ki da wannan mata lafiya, in dai jikata mutum yace xai cuta ya shiga uku ya lalace a duniya kuma yyi ta ganin ba dai dai ba kenan, kuma kinyi asara duniya da lahira tunda kika rike boka da malamai maimakon Allah da ya halicce ki...." Shigowar Abba yasa inna tayi shiru tana huci, yana kallon Umma ya mika mata takardan hannunsa yace "Bana son ki kara kwana gidan nan yau Rukayya...." Umma ta dinga kallonsa da idanuwanta Kamar xa su fito xuciyarta na bugawa can ta karbi takardan da sauri ta warware tana kallon content dinsa, wani kuka ta saki a parlon tana kallon Daddy hankali tashe ta nufesa tace "Saki na fa yayi baban Imaan.... Wllh saki har biyu yayi min baban Imaan"



*Imaan isn't for free* it's 300 via


Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788




95.....




Shi dai Daddy bai ce komai ba sai kallon Umma yake, Inna tayi mitsi mitsi da ido tana jiran ta ji yyi magana, kawai ya mike ya fita daga parlon, Umma ta fashe da matsanancin kuka ta xauna kasa tace "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un, na shiga uku na lalace" Inna ta wangale kofa da sauri tace "A'a rufa min asiri ba kya shiga uku a parlona dake tare da albarka kaca kaca ba Rukayya, tashi ki tafi kiyi ta kanki, Allah ubangiji yyi mana tsari da irin ku a duniya, Allah ya saka ma d'a na Ahmadu da xuwa gurin boka da malamai da kika dinga yi da dukiyarsa, Allah sarki Mujaheed, a duniya dai kam bai y sa'ar uwa ta gari ba, amma da sauki tunda ga shi da Kaka mai tsoron Allah ba kama hannun yaro, sannan ga Amina matar ubansa ita ma matar kirki, Imaan kuma Allah ya isa tsakaninta dake cutar da ita da kika yi, Allah ya isa mata ya saka mata, in sha Allahu sai Allah ya saka mata" Kuka kawai Umma take tana kallon Inna, Inna ta washe baki tana kallon su Mama Hadiza tace "Yo Mutum ma ya rike Allah hannu bibbiyu ya ya kare da duniyar balle ita da ta rike boka" Ammi ta mike a sanyaye ta fita parlon wiping off her tears, Umma ta hade kanta da kujera tana kuka sosai tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un..." Inna tace "Ni dai ki tashi ki bar min parlona Rukayya kada ki ja min wata fitinar, kada ki ja min fushin ubangiji ki tashi ki tafi" mikewa Umma tayi ta fita parlon tana kuka kamar ranta xai fita, Aunty tayi tagumi duk jikinta yayi sanyi tana kokarin maida hawayen idonta, Mama Hadiza ma dai ta kasa cewa komai don duk da sanin halin Umma da tayi amma gaba daya hakan taji bai mata dadi ba, bata taya xaton hukuncin da yayan nata xai dauka kenan ba, Ina laifin ma saki daya, bbu wanda ta fi tausayi kamar Mujaheed, don ko ba komai mahaifiyarsa ce. Part din Daddy Umma ta shiga da sauri bayan ta bar parlon Inna, Daddy na xaune parlor har lkcn ya kasa gaskata abubuwan da ya ji daga bakin mahaifiyar Sadeeq game da Umma, yasan tabbas Maman Sadeeq baxata tako har gida tayi ma Umma sharri ba gashi tace xata kawo evidence tunda akwai Cctv camera, but he is trying hard not to believe it kada tsanar Umma yyi masa yawa a xuciya, Ammi dai tunda ta shigo bata ce masa komai ba ta shiga daki duk iya daurewan da tayi kada ta xubda hawaye ta kasa ta dinga kuka tana tunanin me tayi ma Umma a rayuwa haka irin wannan kiyayya da take mata da only child dinta, ita dai Allah shaida ba ita tace Abba ya ga Aunty yace yana so ba, tun suna yara suke tare da aunty ba wai rana tsaka kawancensu ya fara ba, dama kuma tun farkon aurenta da Daddy Umma ke mata hassada saboda a wadace take da komai kasancewar bata da kowa gabanta, babu abinda daddy ya raga ta da shi duk da rashin haihuwarta da tsangwamar Inna jefi jefi, ita kuma Umma tana da yara sannan makarantansu masu tsada ne sosai tun a lkcn, sai gashi Abba ya kara auren aminiyarta wanda hakan yasa abu ya kara ca6e masu da Umma, Umma na tunanin hada baki tayi da Amina ta aure mata miji don kusan ko da yaushe Amina na tsohon gidansu ta xo gun Ammi, Ammi ta girgixa kai hawaye na sakko mata tana tantama anya da gaske akwai mutane masu irin halin Umma a duniya kuwa ko ko ita kadai ce dai, don kiyayyar da tsanar yayi yawa, Sai gashi that not been enough tilon 'yar ta an aura ma jinin Umma, tasan dai dai da second daya Mujaheed bai ta6a supporting mahaifiyar sa a kan abubuwan da take ba, but kuma ai dole yyi mata biyayya domin ko uwa ce, gashi yanxu an kara sakinta for the second time ta dalilin Imaan, bayan sakin da aka mata years back ta dalilin ita Ammin, ko saboda haka ai baxata ta6a barin Imaan ta xauna lafiya gidan Mujaheed ba, tunanin hakan yasa Ammi ta kasa daina kukan da take. Tun da Umma ta shigo parlon Daddy yyi mata kallo daya ya dauke kai, durkusawa tayi gefensa hawaye na bin kuncinta cikin rawar murya tace "Don girman Allah ka ceci rayuwata Abban Imaan, ka dubi Allah kayi ma d'an uwanka magana ya janye batun sakin nan, wllh bani da inda xan je in ji dadi da ya wuce gidan nan kayi min rai Abban Imaan kada a raba ni da 'ya yana, duk abubuwan nan da suka faru wllh sharrin shaidan ne da rudin duniya, na kuma yadda nayi laifi, ka yafe min ba don halina ba ka sama min mafita Abban Imaan" daddy dai ya jinginar da kansa da kujera bai ce mata komai ba, kuka take sosai tana kallonsa, Jin yyi shiru ya ki cewa komai cikin rawar murya tace "Domin Allah kada ka biye ta halina Abban Imaan, in ci darajan 'ya yan da na haifa a gidan nan, in ci darajansu don Allah...." Kuka take sosai tana kallonsa, Sai a sannan Daddy ya kalleta amma ya kasa cewa komai, mikewa yayi kawai ya nufi kofa walking slowly ya fita parlon, Umma ta fashe da matsanancin kuka, ta mike ita ma tana kallon kofar dakin Ammi ta nufi dakin ta bude ta shiga, Ammi dake xaune gefen gado ta kasa daina hawaye ta daga kai tana kallonta, Umma ta karasa cikin dakin ta xauna gefen gado tana share hawayen idonta wasu na kuma xubowa, cikin rawar murya tace "Don Allah Hajiya Aisha kiyi ma Abban Imaan magana ya sa Baki a lamarin nan, ya rufa min asiri kada Ahmad ya sake ni, wllh duk sharrin shaidan ne, ko domin albarkacin auren da aka hada na Imaan da Mujaheed kada a bi ta halina" Ammi dai bata iya ta ce mata komai ba tana share hawayen idonta. Daddy na fita daga part dinsa parlon Abba ya wuce, ya buda kofar a hankali ya gan yayan nasa xaune parlon, Mujaheed na duke kasa gefensa ya rike kansa, Abba Kuma ya jingina kansa da kujera yana kallon saman parlon, Xaunawa Daddy yayi yana kallon Abba, bayan few seconds cikin sanyi yace "I am sorry about what happened barrister, amma ba a yanke hukunci cikin fushi, this is very wrong, beside hukuncin is too strict, diyata ta cuta ba wata 6are ba, we have the right to forgive, domin ko wani dan Adam ajizi ne, no one is above mistake, kuskure ta riga tayi sai da Allah ya tsare na gaba ya kuma shiryeta, da sauki tunda a gida ne hakan ya kasance ba a waje ba, we have to solve our problem with outsiders intruding, wannan magana bai kai ka yanke hukuncin da ka yanke ba Barrister, I am really not happy about this, ko ba komai ya kamata Hajiya Rukayya ta ci albarkacin 'ya yanta a gidan nan, don haka na xo neman alfarman ka mayar da ita, duk sharrin shaidan ne ba wani abu ba, Ni na yafe mata, Imaan ma nasan baxata rike ta a xuciya ba tunda uwarta ce, haka ma mahaifiyar Imaan, daga karshe kuma Allah ya shirye mu gaba daya ya raba mu da son xuci'an da xai kai mu ga dana sani mara amfani, Hajiya Rukayya deserve to be pardon albarkacin yaranta...." Abba yayi murmushin karfin hali yace "Babu aure tsakaninmu kuma, babu sauran igiyana a kanta don haka before dusk ta bar gidan nan...." Shiru Daddy yyi yana kallonsa ya kasa cewa komai, Babu wanda yace komai a parlon har bayan kusan minti biyar, Mujaheed ya mike a hankali ya nufi kofa ya fita parlon, Daddy ya girgixa kai very sad yace "Am not happy at this Barrister, a ta dalilin diyata fa ka sake matar ka?? Why? Wannan wani irin xumunci ne namu? Komi Rukayya xata yi gidan nan baxa ta ci albarkacin yaranta ba, don ta cuci Imaan daga karshe ba Mujaheed bane ya auri Imaan din? Plss do something about this Barrister..." Abba ya girgixa kai yace "Ka dai san kwanaki na ta6a mata saki daya, yanxu kuma nayi mata biyu so that's the end tsakanina da ita, taje idan ni na cuceta a iya xaman mu na kusan shekara 35 Allah ya saka mata, idan kuma ita ta cuce ni na yafe mata albarkacin xuri'ar dake tsakanin mu" Daddy ya kasa cewa komai duk jikinsa yyi sanyi. Inna ce ta bude kofar parlon ta shigo tace "Toh Ahmadu ko ni xan fita in samo babban mota a kwashe kayan matar nan a gidan nan ne, kada fa dare yayi a xo ana guje gujen fitar da kaya hakan ba shi da kyau gaskiya" Abba dai kallonta yake bai ce komai ba, Daddy kam ko kallonta bai yi ba, Inna tace "Toh kun yi shiru kuna kallona" Mikewa Daddy yyi ya nufi kofa ya fice daga parlon, inna ta bi sa da wani shegen kallo bayan ya fita tace "Gantalalle kawai, da kyar idan ba hakuri ya xo baka ba da yake ba hankali ya ishesa ba, tunda uwata ta haifeni ban ta6a ganin mutumi irin Bukari ba, Yar taka kwaya daya tak a dinga bin ta da irin wannan cuta haka amma sbda karfin hali ka dinga nuna komai ba komai bane sbda baka tsoron Allah, tun fa yana karami haka yake wllh, duk cutar da xa a masa sai yace ya yafe sbda tsiya, gashi hakan ya bi sa har girmansa, wnn ai bala'i ne da dabiyar tsiya, Ina kuwa xan yafe ma wanda ya cuce ni, ai Allah ma bai ce haka ba, idan ban bi a sannu ba ma ai sai Allah yyi fushi da ni...." Abba dai bai ce komai ba, inna ta ja tsaki tace "Wlh yau da ace ba Imaan matar nan ta cuta ba to ni me iya yafe mata ne, kuma ince Ahmadu ma ya yafe mata, Amma imaan ce fa?? Takwara ta ce fa? Ita daya gare d'a na Bukar fa? Yanxu ko don irin xuciyar Bukar Rukayya ya kamata ta cuci yar sa kwaya daya da Allah ya basa? Me yayi mata da xafi haka, banda ma kyautatawa da tsaya mata da yake yi a lamarinta?? idan ma tana jin haushin Aisha ne Imaan baxata ci albarkacin ubanta Bukar mutumin kirki ba..." Kuka inna ta fashe da har da shessheka tace "Ni Mujaheed ne ma abun tausayi, sam yaron bai yi dacen mahaifiya ba, gashi yaron kirki da yasan ya kamata ga tarbiya kaca kaca, ko ya xai dau wannan xancen oho, Ni dai Allah ya isa tsakanina da Rukayya bakin cikin xuwa makka duk shekara da ta min, shari'a ta da ita sai gaban ubangiji don wllh wllh ban yafe ba, uban wa gareni dama da xai kai ni makkan duk shekara banda Sadeeq din....." Daga haka ta fita parlon tana share idonta. Ammi na xaune dakin Imaan tun bayan fitar Umma, Banda hawaye babu abinda Imaan ke yi har da shessheka, Ammi dai tayi tagumi ta ma rasa abun cewa, cikin rawar murya Imaan tace "Ammi ko don saboda Yaya ai bai kamata Abba yayi haka ba, I don't know how he will take this, why will all this happen because of me?" Ammi dai tayi shiru bata ce komai ba, Imaan na son gaya ma Ammi abinda ya faru ranan Thursday a zaria da ya sa suka dawo gida amma ta kasa gaya mata sbda alkawarin da tayi baxata fada ba a gida, da ta tuna ita ce dalilin mutuwar auren Umma sai ta ji wasu sabbin hawayen sun xubo mata, Ammi ta girgixa kai a hankali tace "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un...." mikewa tayi ta fita dakin a sanyaye, duk da tasan babu sauran aure tsakanin Umma da Abba ta fita xuwa parlon Abba. Karfe biyar saura kamar yanda Abba yace babban motar da xai kwashe kayan Umma tass ya shigo gidan, Umma na can dakinta tare da Rahma da Ummi da Maimoon dake taya ta kuka kamar ransu xai fita, Seeyama ma na xaune dakin ta kasa cewa komai sai hawaye, Aunty dai na tsaye jikin mirror tayi tagumi ba uhm ba uhm uhm.... Har parlor Mujaheed ya samu Abbansa ya duka nan kasa cikin sanyin murya yace "Abba dama nace don Allah a bar kayan yanxu ko daga baya sai ni in kwashe" shiru Abba yyi yana kallonsa, can Abba ya gyada kai a hankali yace "Toh ba damuwa, do you have any idea of where she will be going now?" Mujaheed ya sunkuyar da kansa yace "Xan kai ta Zaria yanxu" Abba yace "Ur home?" Mujaheed ya gyada masa kai, Abba yace "Ina xaka ajiye Imaan?" A hankali Mujaheed yace "Nan kaduna" Bayan few seconds Abba yace "I am sorry Mujaheed, I also Neva saw this coming but I think this is the best, ga can abubuwan da kace min sun faru a gidan ka wanda har ya janyo ka saki matarka bbu sauran aure tsakanin ku, sannan ga wannan, sure i was frustrated, but na shanye abubuwan da mahaifiyar ka take min shekara da shekaru, Ina barin ta tana cin albarkacin ku, but today's own is beyond me, I think this is best, Allah kuma yasa hakan ya fi alkhairi, Ina me baka hakuri coz I know this is sad, sannan abinda yasa nace ta tafi yau saboda wannan mata ta Bulasawa, kaga ko da xata dawo bata ganta ba komai xai xo da sauki, mu kuma sai mu basu hakuri, sai kaga albarkacin mu ta hakura..." Mujaheed bai iya yace komai ba hawaye ya kawo idonsa, Abba ya mike ya shiga daki ya dauko kudi ya mika masa yace "You give her this, sae ta rike a hannu, Allah ya maka albarka" mikewa Mujaheed yyi kansa a kasa yace "Toh ngd Abba" daga haka ya fita parlon.




*Imaan isn't for free* it's 300 via


Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788




96.....




Bayan sati daya da komawar Umma Zaria Abba ya kira Mujaheed parlonsa da yamma, Mujaheed ya xauna kasa yana kallonsa yace "Ga ni Abba" Abba yace "Na ji shiru baka ce xa ku koma gida da matar ka ba, what's happening?" Murmushi Mujaheed yyi yace "Abba Inna ce" Abba yace "Me Innar tayi?" Mujaheed yace "She said I am not leaving with her" Abba yace "Ko saboda me?" Wani murmushin Mujaheed yyi bai dai ce komai ba, Abba ya gyada kai yace "Tashi ka tafi" mikewa yayi ya fita parlon. Inna ce tsaye parlonta inda take shiga ba nan take fita ba tana kallon Imaan, Imaan dai na kwance idonta a kan Tv bata yarda ta kalleta ba, Inna tace "Yau naga abinda ya isheni yarinya mara kirki kawai, to a kan me xaki debar ma mutumi dambuna kuma d'an walakanci ya bar min shi a walakance bai ci ba? waye kuma Mujaheed Allah na tuba mutumin da na yi wahala da shi, meye nasa ne ban sani ba, 'ya yana suna wahala dani ku kuma ku dinga cinye min" ita dai Imaan bata tanka ta ba, Inna tace "Yau naga jarababbiya wai ni xata nuna ma son miji, Yar figigiya dake kin san dadin miji, ba kunya ba tsoron Allah ki satar min nama ki kai masa shi kuma ya ki ci, anya Imaan kina son gamawa da duniya lafiya kuwa?" Shigowar Abba yasa Inna tayi shiru, Imaan ta mike xaune tana masa sannu da xuwa, Abba ya amsa yana kallon Inna ya xauna ya gaisheta, Inna ta shimfida tabarma fuska daure ta xauna tace "Lafiya lau Ahmadu ya aiki" yace "Alhmdllh" Imaan ta gaida Abba sannan ta mike ta wuce daki Inna ta bi ta da harara sannan tayi kwafa, shi dai Abba kallonta yake bai ce komai ba, Inna tace "Daxu ma Bukar ya kirani muka gaisa nace Allah yayi masa albarka, ya rabasa da sharrin mutum da aljan, ya shiga ko ina a sa'a ya fita a sa'a" Abba ya gyada kai yace "Hakan na da kyau ai" mikewa Inna tayi tace "Bari in d'an yi shara in dawo Ahmadu" Abba yace "Magrib ai ya kusa Inna, dama kuma magana na xo xa mu yi" Inna ta koma ta xauna tace "To lafiya dai ko?" Abba yace "A'a lafiya lau, kawai naga ya dace Mujaheed ya dau matarsa su tafi ko, tun da Alhmdllh ynxu bbu wata matsala...." Inna ta katse sa tana mitsi mitsi da ido tana girgixa kai tace "Ae ba Mujaheed ya halitto min ita ba balle in basa ita su tafi, waye kuma Mujaheed?? ku dai wllh ku dinga tsoron Allah komin rintsi, Ahmadu duk matan ka biyu da ka aura ka gaya min warce aka ta6a baka bbu lefe? Shi ma Bukar ya gaya min ko bbu lefe ya auri Aisha, sai Imaan ce xa a kai gidan Mujaheed ba


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login