Showing 45001 words to 48000 words out of 303099 words
Umma da ranta idan yayi dubu a lkcn ya baci, Anty tace "A'a jira, yi min transfer din kudin Imaan din yanxu tukun, sauran ko daga baya ne sai ka yi" Mujaheed ya kasa cewa komai, Anty tace "Malam ka min shiru ina maka magana m" ya dau wayarsa gabansa na faduwa sai dai bai yadda ya kalli Umma da ko ba a fada masa ba yasan kallonsa take, ya gama danne dannensa yace "Anty ina jin ba network...." Ta mike ta isa kusa da shi ta amshi wayar tace "Baxa ka raina min hankali ba" sanin Gtb yake amfani da lkci daya ta danna transfer code dinsu tayi komai ta sa har account number dinta bayan ta sa amount sannan ta mika masa tace "Sa min pin" Karba yyi ya sa pin din ta amshe wayar, duk ya kasa kallon Umma, sai da Anty ta ga transfer din yayi sannan ta basa wayarsa ta koma ta xauna, lkci daya aka turo masa debit ya bude ya ga 30k ta yi transfer, Abba yace "Toh ka dau kayan ka kai mata sai kace mata kai ka siya mata" Kasa tashi yayi, Abba ya hade rai yace "Are you stupid ina maka magana kana xaune, wato abinda kake nufi shine baka jin maganar kowa gidan nan sai na uwar ka koh, ina fa lura da kai kuma nake sharewa" Tashi Mujaheed yayi ya dau ledan kayan ya nufi kofa, Umma ta mike fuu ta wuce sama, Anty tayi wani murmushi a ranta tace "da sauki ai tunda ba bin sa xa ki yi ba" A hankali Mujaheed ya murda kofar apartment dinsu Imaan ya shiga da sallama murya can kasa, Imaan ce durkushe parlon da yar ves sai skirt iya cinya, nose mask na hancinta tana goge gogen kayan da ke daukan k'ura a parlon, ta mike ta cire abun bakinta tana kallonsa, Ammi ta fito parlor jin an shigo, yyi kasa da kai ya ajiye ledan hannunsa kan kujera yace "Abba yace a kawo mata" daga haka ya juya ya fita ya kulle kofar, Imaan xata bude ledan Ammi ta mata tsawa, dakatawa tayi da sauri, fuska daure Ammi tace "Kina ganin ya shigo amma kika ki wucewa daki da wannan shegun kayan jikin ki koh, tun daxu nake maki magana ki nemi kayan arxiki ki sa ko don saboda ciwon ki sannan kada wani ya fado amma kin maida ni mahaukaciya, ke kam wace irin yarinya ce Allah ya bani, in ji hankalin ki ya kwanta da ya shigo ya ganki a haka?" Imaan sai kallonta take da mamaki tace "Ammi yaya ne fa" Bude baki Ammi tayi tana kallonta, can tace "Sai aka yi ya don shi ne?" Tace "Toh Ammi shi ne fa ba wani ba ya shigo, dama dai ya Yusuf ne kin san baxan tsaya haka ba" Ammi ta kasa daina mata kallon mamaki tace "Shi yayan muharramin ki ne Imaan?" Imaan ta xaro ido tace "Ammi yaya fa har wanka ya taba min ina karama, kuma da ba shi ke sa min kaya ba ma idan ban sa ba, ni dai bana jin kunyarsa wllh, dama dai yaya Yusuf ne shi ko dankwali bana tsaya kusa da shi ban sa ba, shi kuma yaya ni xan ma iya cire kaya a gabansa, toh har yau ba yana shafa min magani a kafana da bayana ba, ko wajen inna idan yana nan ina....." Ammi taga bude baki fa ba nata bane ta dau daya daga pillows na kujera ta jefa mata a mugun fusace tace "Ban taba sanin ke shahararriyar mahaukaciya bace sai yau, wato iskanci yasa kike cewa ya shafa maki maganin xafi koh, to in sake gani sai na ci uban ku ke da shi, kuma kar ki fasa cire kaya gabansa tunda ke shashasha ce, sai kace warce bata taba shiga ajin islamiyya ba wai kina cire kaya gaban namiji da ba muharramin ki ba" Imaan ta nufi daki kamar xata yi kuka tace "Ni fa ba yanxu nake cewa ba Ammi, da da nake nufi, kuma naga ai yayana ne shi tunda ba ni da wani yayan" ganin Ammi ta yo kanta ta shige dakinta da gudu ta sa makulli tana turo baki kamar xata fashe da kuka.
15..
*Imaan* is not free subscribe and read hankali kwance🤷🏻♀️It's 300 via Fcmb 3276052019
Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp digit 07087865788 to be included in the payment group
Ammi ce xaune parlon inna ta sanadin aikawa da innar tayi a kirata, ta fi minti sha biyar parlon amma inna bata ce da ita komai ba sai goge gogen kayan kallonta take, Ammi ta bukaci ta yi mata goge gogen inna tace ta bar shi, bayan wani minti biyar din Ammi tace "Inna na daura girki ne wllh...." Inna tace "Kin daura girki? Tabdi... Toh ita warcan 'yar da kika bari meye amfaninta da baxata dinga duba maki girkin ba, ina ce yau alhamis babu islamiyya" Ammi tace "Barci na baro ta tana yi" Inna ta tabe baki tace "A haka dai kullum, Allah dai ya mana tsari ya fidda d'a na kunya, amma gaskiya ni tunda nake tafasasshen ruwan Imaan bai taba shiga baki na ba, toh uwar me xata je ta dafa ma mijin ma idan tayi aure, kullum ayi ta laka ma yarinya ciwo ana daure mata kugu wai bata da lafiya, to ni dai ba ruwana ba wanda xai xagi d'a na, idan ma an samu to Allah ya isa" Ammi dai bata ce mata komai ba, Inna ta xauna tace "Tana yar yarinya da ita tayi ta langwabewa, tana abu salalo salalo, ana ma ciwo sharri to ni dai ba ruwana, dama magana nake son yi mama ke da Amina, to Aminar bata ga damar xuwa ba har yanxu, tana can sai ta mula ta mulmule sai kace xata ma Maryam haka....." Inna bata rufe baki ba Anty ta shigo da sallama, Tace "Sannu inna..." Inna ta tsuke fuska tace "Yauwa" Anty ta xauna tana kallon Ammi tace "Uwar Imaan kwana biyu" Ammi tayi murmushi tace "Ae kam duk mun buya" Mikewa inna tayi ta ci gaba da goge gogenta, Anty tace "Goge goge kike Inna" a fusace Inna tace "Toh baxan yi goge goge ba in mutu cikin wari yar nan, ko ke baki ga ko ina tsaf ba, ko hancin ki bai ji kamshin dake tashi parlon ba, wllh tun safe ban xauna ba ina ta aiki baki ji bayana ba kamar ya balle in huta, ke hatta simintin da kika tako kika shigo nan sai da na goge sa fess yau, ai kazanta bata da kyau, ni dai in sha Allahu cikin kamshi xan mutu ba ruwana, kuma tirr da kazami, ai ina lura duk cikin jikokina babu wanda ya dauko tsafta ta sai Mujaheed" Anty da Ammi dai sai kallonta suke, ta xauna tace "Yo Mujaheed mana, shi kadai ne Allah ya ceta ta wannan fannin, duk inda kazanta take ma shi bai xuwa, kullum tsaf xaka gansa abunsa, baxa ku yarda da xance na ba sai kun shiga dakinsa, ko don raino na ne shi din oho, ga shegen kyankyamin tsiya.... shi kuma wannan katon Isuhu ba shi da aiki sai saka gogaggun kaya da fesa turare amma duk kika basa abinci to wllh a nan xai bar maki kwanon ya tsallake ya wuce, to ina tsafta a nan, ai ta nan ake gane kazami, dakinsa kuwa karkari ya kakka6e gadon ya kara gaba, ita ko wannan mai laluran Imaan ga dai gashi har gashi amma ba gyara malam, kullum gashin nan a kume xa ki gansa sai ta fi sati da sattuka bata sharce ba, to ina tsafta a nan, da an mata magana sai tace xafi yake mata, ai duk mace ta gashi ake gane kazantar ta ni kwarkwata ma nake guje mata wllh, sannan babu tattali kullum sai ta bar min adikonta a nan idan ta xo, ga su can na tara yafi kala dari yanxu, Ko uwarta xan ci da su oho, ni ce ma Bukar xan yi ma ya daina siya mata turmin atamfa gwara a siya falle a mata riga da sket banda dankwali, Atoh shi kenan yayi ta asaran dukiya atamfa dai masu tsada amma tayi ta walakanta adiko, Maimoon kuwa dama kayan datti sai ta tara ta tara taga babu sarki sai Allah, babu wanda xata saka sannan xata kwashesu ta hau wanki duk su cika gida, to ina mace a nan, babu kazantar da ya fi wannan wllh, sauran yan matan kuwa ni wani lkcn ma sai in ji kamar wari suke wllh...." Murmushi Anty tayi, Inna tace "Wallahi ba batun dariya ba, to dai kowa tasa ta fishshesa a gidan nan ba ruwana da kowa ta kaina nake, yanxu dai abinda yasa na kira ku ba wani abu bane...." sai kuma ta yi shiru, su dai kallonta kawai suke, tayi kasa da murya tace "Ku lissafa min daga ranan asabar xuwa yau kwana nawa kenan" Ammi tace kwana shidda" Inna tace "Toh yau kwana shidda rabon Mujaheed da Imaan su xo min nan su gaisheni, yanxu fisabillahi daga sun min ba dai dai ba na nuna bacin raina sai su kullace ni, meye laifina don nace ban yarda shanye min fura da suka yi ba" Anty ta bude baki tace "Gaskiya basu kyauta ba har kwana shidda" Inna ta fara matsar kwalla tace "Ni fitinata har ya kai Mujaheed ya ki takowa nan yau har kwana shidda, daga gyara kayanka sai ya xamo sauke mu raba? Ke Amina na kira ki ne a matsayin uwarsa don ba ruwana da wancan katuwar da ta haifesa, ke kuma Aisha saboda Imaan yar ki ce" Anty tace "Amma Inna ca nake kince kada su sake xuwa maki idan ba haka ba xaki bar gidan" Inna xaro ido tace "Oh oh Allah kaji wata magana don Allah, to Amina idan na bar gidan nan ina da gidan uban da xanje in tsugunna, duk ba xance bane dai da tsorata mutane, bacin rai ai babu abinda bai sawa, don nace kada su sake xuwa kowa yasan fada kawai nayi, me suka min da xan hanasu xuwa nan?? Allah ya tsine ma fura da nonon in dai saboda shi xan kori jikokina, meye kuma wani fura da nono kamar mayyar bafillatana" Anty na danne dariyar ta tace "Ahh to gaskiya basu kyauta ba" Inna ta kalli Ammi tace "Ke kuma Aisha kinyi shiru kina kallona ko baki da abun cewa ne?" Ammi tace "Kiyi hakuri Inna, ina komawa xan sameta" Anty tace "Nima Mujaheed na dawowa aiki xan samesa In sha Allah" Inna ta gyara xama tace "Toh, sai ku ji dalilin da yasa xa su min haka su kaurace min, yanxu duk saukin kai na su basa gani, ni ba mafadaciya ba, ni ba fitinanna ba, ni ba mai sa ido ba, ni ba mai kwadayi ba, ni ba mai mita ba, toh meye xasu wani dauke kafa daga magana dai ta fahimta, to sai dai idan Ahmadu ne ya hure masu kunne ya masu hudubar tsiya, banda haka su har wani wayo garesu da xasu dauke kafa daga xuwa inda nake" Anty ta fara dariya, Ammi kam murmushi kawai tayi, Inna tace "Aa don Allah ku duba xancen da kyau, wllh xuge su aka yi, kuma ba kowa xai yi hakan ba sai mutumin nan Ahmadu don Bukar baya haka shi, ni gaskiya na ma daina sa Ahmadu a lamarina daga yanxu tunda tsanata yake cusa ma yaran a rai, anjima kuma xan sa kira min Bukar yaji abinda ake ciki, kwana daidai har shidda fa" Ammi ta mike tace "Ki yi hakuri Inna ina komawa xan mata magana bari in je in duba girki na" Inna tace "ke ta girki ma kike ga maganar al'ajabi ana yi a nan Ahmadu ya xuge yara, haba don Allah abinci dai abinci dai kamar ana yunwa Amina" Ammi ta nufi kofa tace "Toh sai dai anjima inna" Inna tace "Toh Allah bamu alkhairi, ki dai tsitsiyeta kiji dalili" fita Ammi tayi parlon bayan ta ma Anty sallama. Inna ta tabe baki tace "Kinga bafillatanin mutum, kinga agwai?? Wllh ki ji tsoronsa, barin idan kika ga ya fiye shiru shiru banda haka ki ga fa babu abun kirki da tace har ta bar parlon nan, Bukar dai na ganin boni, mata kamar kurma, ni kwanciyar hankali na ma Imaan bata dauko halinta ba, Imaan xata iya kwatar kanta a ko ina da bakinta, tun daga ranan da na karanta mata ta daina gaida Uwar Mujaheed gashi har yau bata gaisheta, gashi har Ahmadu da Bukar sun gaji sun kyaleta, kusan ma Imaan ce kadai ta dau halina a gidan nan wlh, banda haka ya xata dinga gaida katuwar mata bata amsa mata, da ta fi ta iskanci kuwa kinga ta daina gaishetan gaba daya" Anty dai dariya kawai take, Inna tace "Toh ni dai ki taimake ni Amina ki rufa min asiri, Mujaheed na dawowa ki titsiyesa a daki kiji me na masa da ya dauke kafa a nan" Anty tace "In sha Allah Inna, bari in je nasan ma ya dawo yanxu tunda biyar har ta yi" Inna tace "To yi maxa" tashi Anty tayi ta mata sallama ta fita inna ta mike ta ci gaba da goge gogenta tana cewa "Ahmadu dai ya lalace, da dai ba haka yake ba"
Dariya sosai Imaan ta dinga yi bayan Ammi ta bata sakon inna, tayi mai isarta ta mike daga kwancen da take tace "Ba Inda
xanje Ammi, tun Sunday kinji ta kai karana gun Abba, to haka ya fi, ita da bakinta tace wannan time din ba wasa take ba Abba ya ja mana kunne sosai don muna xuwa part dinta xata tsallake ta gudu ta bar gidan" Ammi tace "Toh nace bayan magrib kije ki gaisheta, kina gaidata ki juyo" Imaan ta fashe da kuka ba hawaye tace "Ammi don Allah ni baxan je ba, ina xuwa xata ce na mata wani abu" Ammi ta mike tace "Toh idan na baki abincin ki kai mata kar ki kai" daga haka Ammi ta bar parlon, Imaan ta fara kukan gaske, har ranta bata son xuwa gun inna. Anty na gama girkin dinner dab da magrib ta fito kitchen, ganin Mujaheed xai fita masallaci tace "Dr idan ka dawo mosque ka sameni bedroom" Yace "Toh" daga haka ya fita parlon, tare suka dawo masallacin da Yusuf, bayan sun haura sama Mujaheed ya shiga dakin Anty, Yusuf ya shiga dakinsa, Anty na xaune kan darduma ta shafe addu'o'in da take ta mike ta dauke pray mat din ta linke tana kallonsa tace "Toh ka tsaya min kamar soja a kai ka xauna" murmushi yayi yana shafa kansa ya xauna gefen gadon, tace "Yanxu M.A idan kowa ya guji inna kai ma sai ka gujeta" ya d'an buda ido yace "Inna kuma?" Tace "Eh mana" yace "Ban gane ba Anty" tace "Kirana tayi daxu wai kwana shidda rabon da kaje bangarenta kai da Imaan" Mujaheed yyi murmushi bai ce komai ba, Anty tace "Toh ka gama murmushin ka tashi ka ta fi ka gaisheta" mikewa yayi yace "Wa?? Ai har abada ni da xuwa apartment dinta, beside irin warning da Abba ya min ma is not funny don haka..." Anty ta karasa masa tace "Baxa kaje ba koh?" Yace "Allah Anty kinga kwana biyu shiru bata ce an mata komai ba hakan bai fi ba?" Anty tace "Toh ni dai nace ka tashi ka je" ya mike xaune yace "Anty ki bari kawai ba inda xanje" Anty tace "Wato ban isa da kai ba kenan, idan Hajiya ce tace kaje xaka ce mata ba xa ka ba?" Yayi murmushi yace "Anty Hajiyan ma hanani xuwa bangaren tayi gaba daya" Anty tace "Toh tashi ka fita ka ban waje" ya marairaice mata yace "Wllh Anty ina iya xuwa yanxu tace nayi mata wani abun" Anty ta hade rai tace "Cewa nayi ka gaisheta kawai ka juyo" Ya lumshe ido ya bude yace "Wllh da ba don ke bace ni ba inda xanje Anty" Anty tace "Naji din tashi ka fita, idan ka dawo kuma ka xo ka gaya min, gobe da safe kuma xan je in ji ko ka je" Murmushi yyi ya mike ya fita dakin. Tun da Imaan ta fito parlonsu rike da warmer din abinci take tsaye jikin wani flower taki tafiya, kiris ya rage ta fashe Inda take tsaye, daga nisa ta hango Mujaheed yana tahowa waya kare kunnensa, labewa tayi ta koma bayan flower din ta tsaya da sauri, sai da ya d'an wuce inda take ta fito tayi wani kara a bayansa, still yyi na few seconds, ta fashe da dariya ya juya yana kallonta, ya wani hade rai yace "Kee" Ta wara manyan idonta tace "Toh ai baka ji tsoron ba ma" Wani kallo ya dinga mata, ta turo baki ta wuce sa, sai da ya ga tayi nisa sannan ya bi bayan ta, tsaye ya ganta tana lekan parlon inna don kofar ba duka aka rufe ba, ya cire takalmansa outside the balcony yayi tiptoeing har bayan ta, fingers dinsa ya kai gefen cikinta yayi tingling dinta, ihu ta fasa ta sake abincin hannunta, tuni ya janyeta wajen don gaba daya tuwo da miyar dake warmer din ya tarwatse a kasa, ta xaro ido a rikice tace "Innalillahi yaya ka xubar" daga cikin parlor inna ta dinga cewa "Me aka 6arar??" Ummi ta bude kofar, Imaan dai sai kallon abincin take kamar xata yi kuka, Inna ta mike ta taho wajen tace "Meye hakan?" Kamar xata yi kuka tace "Yaya ne ya xubar da abincin da na kawo maki" Inna tace "Toh sai ki kwashe ki mayar mata ta canxa min wani ba ruwana" Imaan ta shige parlon ta xauna ta rungume hannu tace "Salon Ammi ta doke ni ba ga abinci nan Ummi ta kawo maki ba" Inna tace "Aa wllh kinga ina cin wani abu banda tuwo, Ummi maxa kwashe ki kai ma Aisha kice yar ta ta xubar ta