Showing 126001 words to 129000 words out of 303099 words

Chapter 43 - Imaan Book 1 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

1627

Kallonta yayi yace "Me xaki ce mata.." ta kashe masa ido tace "That's our secret big Bro" Xaunawa yyi saman kujera yana kallon Inna, Inna tace "Yanxu wannan yaron dake neman Imaan ya fita, baka ga yanda ya dinga fada imaan bata gaya masa bikin ka ranan Juma'ah bane, gaba daya bai ji dadi ba, Allah kadai yasan me Bulasawan da kansa xai baka, mutum miloniya meye kuma baxai bada ba" a fusace Mujaheed yace "Sai dai ya baki ke da kike bukata, amma ni bana bukata, kuma don Allah kiyi hakuri ki daina maganata a gaban mutane bana so, ni abinda nake da shi ya isheni xaman duniya ba sai na hangi na wani ba" Yana fadin haka ya fice daga parlon, Inna ta tabe baki tace "Uwarka Rukayya ka gaggatsa ma magana ka fita ba ni ba wllh, ba abinda ya hada ni da kai dama, kawai Ahmadu ne ya haifeka ni kuma na haifesa, Ni ban yi mamaki ba tunda goyon Rukayya ce kai din ai, xaka yi fiye da haka" Maryam na dariya ta mike ta fita a parlon ita ma, da daddare Imaan na fitowa daga wanka daure da towel tace "Wai ina kuka je daxu da yaya tun safe" Maryam dake operating laptop tace "Wato kina wanka hankalin ki na wajen ki fito kiyi tambaya" Dariya Imaan tayi tace "Eh mana" Maryam ta ajiye laptop din a gefe tace "Ae babu inda ba mu je ba..." Imaan tace "Kamar Ina da Ina?" Maryam tace "Ya fa ce kada in gaya ma kowa har ke" Imaan ta xauna kusa da ita tace "Don Allah ki gaya min, ai ba gaya masa xan yi ba" Maryam tayi dariya tace "Anya xan iya gaya maki kuwa, ce min fa yayi amana, kuma sbda ke muka je wajen...." Imaan kamar xata yi kuka tace "Don Allah ki gaya min, wllh baxai sani ba, abinda ma ba shiri muke da shi ba yanxu"


*Imaan isn't for free* it's 300 via


Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788


44....



Maryam tayi dariya tace "Kai Imaan haka kike da son jin abinda bai shafe ki ba?" Imaan ta marairaice mata tace "Ni dai ki gaya min" Maryam na murmushi tace "Ke ba ko ina mu ka je ba, kawai dai ya kai amaryar tasa plazan da xa ayi mata dinkunan bikin ne ya bada kudi, sai kuma gold na rings guda uku da ya siya mata for the wedding, sannan muka koma gida muka ajiye ta, after that muka je kasuwa siyo drinks da Ummansa tace ya siyo, sai flasks da bedsheets da xata yi souvenir ma kawayenta....." Imaan ta ja tsaki tace "Toh meye na cewa kar ki gaya min, ko ni ina ruwana?" Maryam tace "Ke wasa nake kawai Inna yace kar in gaya ma amma ba ke ba" Imaan ta mike tana goge jikinta tace "Toh shine xa ki ce saboda ni ku ka je inda ku ka je?" Maryam tace "I am just pulling ur legs, kin taba ganin amaryar tasa kuwa?" Imaan tace "Ehh na taba ganinta a gidansu" Maryam tace "She is beautiful but her fairness isn't natural" Imaan tayi dariya tace "Artificial ne kenan" Maryam tace "Probably... And she isn't friendly, she didn't even acknowledge my present sosai, kamar bata son mutane, sai kin ga ma yanda ta amsa min gaisuwan da na mata, she just shunned me..." Imaan tace "Tohh ba sai ki fasa bin su ki dawo gida ba, Toh me yayan yace?" Maryam tace "He couldn't say anything to her, amma shi ma naga bai ji dadi ba, coz he even introduced me to her again, amma ta ki cewa komai" Rai bace imaan tace "Toh wai me yasa baki dawo gida ba??" Maryam tace "Ae ban san hanya ba, beside I am not with money, ga shi in gaya maki sai wani shagwaba take masa a mota, shi ko a cikin magana goma bai fi ya amsa mata uku ba" Imaan tayi dariya tace "That's their problem" Maryam tace "Yea least I forget, na yi maki deciding abinda xa ki siya ma Bf din ki for his birthday" Imaan na shafa lotion dinta tana kallonta ta madubi tace "And what's that?" Maryam tayi murmushi tace "But wait... did he invite u for the birthday party?" Imaan ta gyada mata kai, Maryam tace "Kuma xa ki je?" Langwabar da kai Imaan tayi a hankali tace "Toh I haven't decided yet, ban sani ba tukun" Maryam tace "Toh after ur decision xa a bar ki kije a gida kuwa?" Imaan ta xaro ido tace "Dama wa xan gaya ma?? Tab... Am telling nobody" Da sauri ta dawo kusa da Maryam ta xauna tace "Plss Maryam wannan ya xama sirri tsakanina da ke, Kinga even Maimoon da ta ke kawata ma ban gaya ma ba, don Allah kar by mistake ki ce ma Ya Mujaheed anything about the birthday" Shiru Maryam tayi tana kallonta, hankali tashe Imaan tace "Ko dai har kin gaya masa?" Maryam tayi yake tace "Haba dai why will I, of course ban gaya masa komai ba" Imaan ta sauke wani ajiyar xuciya tace "Better" Maryam tace "May be... A day to the birthday sai mu fita babban shopping mall in nuna maka abinda ya kamata ki siya masa" Imaan tayi shiru tana tunani, can tace "Toh Allah ya kai mu" kayan baccinta ta saka ta hau saman gadon ta dawo kusa da Maryam tana kallon abinda take yi a laptop dinta.
Slowly ranakun suka dinga tafiya har ya rage saura kwana biyu bikin Mujaheed da Safeenah, gida ya cika da Yan uwa da abokan arxiki, matan kawu Bala, Hansai da yaranta kai duk yan uwa dai an cika gidan barin part din su Umma, duk inda kaga Imaan toh xaka ga Maryam a gidan kamar da can sun saba da juna sosai, seriously Mujaheed ya sa ma Imaan ido a gidan, ita kuwa ko sanin yana yi bata yi ba. Da yamma Imaan na parlon Inna tare da Maryam sun kawo mata abinci, sai bin Inna dake ta neman makullin bandakinta suke da kallo, duk ta hada xufa ta wani tsuke fuska, komai sai da ta daga a parlon amma babu makulli babu labarin sa, Mama Hadiza ta fito daga daki da alamar ita ma neman makullin take tace "Toh wai ina kika ajiye makullin Inna?" Inna tace "Ke ki rabu da ni don Allah, nasan inda na ajiye xan ta neme neme, da ba don rubabbun dake shigo min nan ba har xan wani kulle bandaki kamar warce ta ajiye gwalagwalai a ciki har shegen makullin ya bata?? Ni dai ba ruwana a ma daina xuwa min nan gaba daya, tunda ba ni ke aurar da mutumi ba" Dariya Maryam ta dinga yi Inna ta daga kai daga duken da take tana kallonta, Sallama aka yi bakin kofa Inna ta mike tsaye ta amsa sallaman, Ta rasulu ta shigo tana kyabe fuska, Rahma ta ajiye mata karamin jakarta ta juya ta fita, Inna na washe baki tace "Sannu da xuwa Ta Rasulu kinga na rasa inda na jefa makullin bandaki, gudun kar a shigar min bandaki na kulle na saka makullin a bakin zani to yanxu gashi ko sama ko kasa" Ta rasulu tace "Toh ai gwara da aka nema aka rasa gaba daya, kinga bayan bikin sai a balle kofar kawai, don wani na iya xuwa ya maki dadin baki ki kunce makullin ki basa, mutane dai basu gaji mutunci ba, kinga yanda aka 6ata tsakar gidan da shinkafa ga yara jage jage kamar daga kauye, ni dai ba kowa ma ya kamata a dinga bari yana shigowa ba ma wllh, sai kace ba bikin yan gayu ba" Inna tayi tagumi tace "Naga abinda ya isheni, kin ji wata fitina koh, Kai mutane dai jarababbu ne, kice tsakar gida na nan duk wari?" Ta rasulu ta tabe baki ta wuce cikin dakin tace "Ae kuma sai ki yi, abinda tsoron Allah yayi karanci a xukatan mutane yanxu" Inna tace "Toh ni kuwa xan je in basu hakuri su rufa mana asiri kada gidan 'ya yana ya lalace mu shiga uku, sannan biki dai ba ace a xo da yara ba" Mama Hadiza ta leka dakin ta gaida ta rasulu sama sama ta fita parlon gaba daya, Imaan ta tabe baki xata tashi Inna tace "Toh ke kin gaida ta rasulun ma kuwa" daga cikin daki ta rasulu tace "Ina fa ta gaida ni tana kallona ina kallonta, yaran yanxu kam sai ka kyalesu, mu dai muna masu fatan alkhairi Allah kuma ya basu miji na gari, har wannan figaggiyar ta kusa da ita ma ni bata gaisheni ba ai" Imaan ta gaida ta daga inda take tana turo baki ta mike ta fice a parlon, Maryam ta mike ita ma ta gaidata ta fice Inna na cewa "Iyayenku ku ka ma haka ba mu ba wllh" Daren ranan Daddy ya iso daga Abuja, bayan ya huta suka d'an taba hira da Mama Hadiza da yake a part din ta sauka, sannan ya fita don xuwa ya gaida Inna, Imaan ta bi bayansa da sauri, bayan sun sauka balcony yana kallonta yyi murmushi saboda yasan akwai abinda take son gaya masa kenan tunda ta biyosa, yace "Do you need anything Imaan..." A hankali tace "Daddy kaga mutane sun yi yawa a gidan nan plss ni dai ina son xuwa gidan gwaggwo in xauna har a gama biki in dawo Saturday" Da mamaki yace "Bikin yayan naki kuma Imaan?" Tace "Daddy I will be very uncomfortable, ai da rana xan wuce gidan gwaggwo din ba da safe ba" Yace "Toh ita kuma Maryam fa, won't she be lonely" Imaan tayi dariya tace "Ae tare xa mu je daddy, ita ma tace min she's already uncomfortable tun daga jiya da mutane ke ta xuwa" Murmushi Daddy yyi yace "Ohk then sai ki gaya ma Ammin ki" Imaan ta wara ido cike da jin dadi tace "Toh Daddy nagode sosai, ai dama Ammi...." Shiru tayi hango Mujaheed da ta yi yana tahowa daga part dinsu, Daddy ya kalli inda take kallo, ganinsa ya tsaya har ya iso inda suke, da ladabi Mujaheed ya gaida Daddy, daddy ya amsa yace "Ya shirye shirye M.A" Murmushi kawai Mujaheed yayi, Imaan tayi wucewarta gaba ta bar su tana cinno baki, da sallama ta shiga parlon inna, Ta Rasulu na xaune kan darduma ta daura kafa daya kan daya ta rungume hannu tana sakace hakori, Inna kuma na xaune kan tabarma ita ma ta daura kafa daya kan daya, Umma na parlon xaune ga bucket cike da cin cin da alkaki da ta shigo da sai kallon ta Rasulu take kasa kasa, Ta Rasulu ta kyabe baki tace "Yo ai duk matsiyata ne Asabe, ni shi sa ba ruwana da kowa wllh, ba ruwana" Inna tace "A'a dama fa nasan a wajensu tsiya ya kare, ni ina ruwana da su Ina ta kai na, oh oh wlh" Ta Rasulu ta kalli Imaan sannan ta kalli Inna tace "Matar nan na amfani da iccen da kika bata kuwa?" Inna xata yi magana Daddy ya shigo da sallama Mujaheed na biye da shi a baya, Inna tace "Allah dai ya baku lada wannan hidima da kuke ta yi da Mujaheed, ko kudin jirgin da ka kashe yau ma ai xaune yake da kansa, Allah dai yasa ya ji k'an ku nan gaba, yayi ma imaan abun kirki ranan bikinta" Daddy ya xauna yana murmushi ya gaisheta sannan ya gaida Ta Rasulu, Umma ta gaishe sa sama sama, ya amsa yana tambayarta taro, ta Rasulu ta rike ha6a tana kallon Daddy tace "Ohh Bukari kana nan dama, rabona da kai fa tun da ka xo daurin auren ishaq" Daddy yace "Ina nan Baaba, sai dai yanxu a Abuja nake" Ta Rasulu tace "Toh Allah yayi maku albarka, ya kare ku sharrin masu sharri, ya sa ku gama lafiya da mu, ya ba matanku ikon yi mana biyayya yanda ya kamata" Yana murmushi yace "Ameen Baaba" Mujaheed ya gaida ta Rasulu, ta Rasulu tace "Sannu ango, amma kuma duk naga ka rame baka cin abinci ne?" Inna tace "Ke ma dai da wata magana ta Rasulu, ina xai ci abinci yana tunanina, kin xata rabuwa da ni abu ne mai sauki?" Dariya Daddy yayi yana kallon Mujaheed, Mujaheed ya kalli Inna ta gefen ido bai dai ce komai ba, Umma ta wani daure fuska tana hararan Inna ta gefen ido, Ta Rasulu tace "Toh kayi hakuri Mujaheed, abinda bayan bikin da sati daya kawai sai ka xo ka dauketa ka mayar da ita gidan naka gaba daya, ohh sa6o turken Wawa" Inna tace "Ae shine na ga, nayi kokarin fahimtar da shi hakan amma ya kasa kwantar da hankalinsa, sai in koma can gaba daya Imaan kuma ta dinga xuwa duk Juma'ah ta koma lahadi" Daddy dai sai murmushi yake, Imaan ta saci kallon Mujaheed taga kallonta yake, dauke kai tayi da sauri, Inna tace "Toh ni dai ta Rasulu ga ki ga Bukar yau, sai ki masa bayanin mutumin nan na bayan tsauni a tsanake, tunda ni na kasa fahimtar da shi da Ahmadu suna ganin kamar ko boka ne, Ni ko me xai kai mu gun boka mu masu tsoron Allah" ta Rasulu tace "Wllh Bukar ku maida hankalin ku don sai anyi da gaske da 'yar nan taka Imaan, tana da makiya ne ba na wasa ba, sannan wannan ciwace ciwacen nata ma ance ba banxa ba da sa hannu, sai an tashi tsaye kyam kada a kai mu a baro, bangaren aure kuma ance xata auri wanda ke bala'in sonta, wasu xa su yi murna da auren wasu kuma bakin ciki da hassada baxai bari su yi ba, wasu kuma takaici baxai yarda su yi murna ba, sannan da matsalaloli iri iri a xaman auren, matsaloli masu girma ba dadin ji kuwa, ni dai ba fata nake ba amma gaskiya abun ba dadin ji, kuma ance sai ta cika maka parlor da jikoki, toh ni abinda ban gane a nan ba shine... Kyashin fidda kudi kake a nema ma tillon yar ka lafiya ko kuwa kudin ne baka da shi Bukar?" inna tace "A'a sai dai kyashi, amma yana da shi wllh, Toh wllh sai ma kin tafi bayan biki xa su xo su sameni shi da d'an uwan suce in rabu da ke ba hanyar kirki kike nuna min ba, Toh wai dama Allah ba yace mu tashi ya taimake mu ba??" Daddy ya kasa daga kai, ta rasulu
ta saki salati tana tafe hannu tace "Sai su ce ki rabu da ni kuma?" Inna tace "Wllh kuwa tatas xa su min suce in raba kaina da ke, ai ga shi nan xaune da ransa ba sharri na masa ba kullum na kawo masu xancen sai su gwaleni suce karya ce inyi ta kaina, to ni ya xan yi da su??" Mujaheed ya sunkuyar da kai sai murmushi yake, imaan ta boye fuska bayan kujera tana dariya kasa kasa, Daddy dai ya kasa dago kai, Ta rasulu tace "Dago kanka ka kalle ni Bukar, wllh wannan 'yar taka idan ba a tashi tsaye kanta ba duk sai mun shiga uku a duniyan nan, idan ma xaka fiddo kudi ka fiddo kudi a nema mata magani ta xama mutum, tunda har kuka iya karyata ni kai da Ahmadu to xa ku iya karyata Asabe ma" Inna tace "Yo na nawa kuma? Ai sun ma karya ta ni, sai dai Allah ya shirye su, ni dai na yafe masu" Daddy dai kansa na kasa, Ta Rasulu tace "Yanxu bayan biki sai ka ba Asabe dubu dari, idan ma ya kama muje tare da ita da Imaan din ne sai duk mu tafi...." Inna tace "Haba sai kace xa ki cuce ni, ai kawai ki je ke daya ba komai wllh" Daddy yace "Toh Allah ya kai mu xa a bada" Mikewa yayi yace "Na gaisheku xan je in huta" a tare suka hada baki wajen cewa "Toh Allah maka albarka" yace "Ameen" sannan ya fita parlon yana girgixa kansa. Umma da duk ta hada xufa gaba daya jikinta tana murmushin karfin hali tace "Toh Inna ayi hakuri da wannan din don Allah, ni xan koma in ji da baki" Inna tace "Toh ai ya fi babu, Allah dai yayi albarka" tana murmushi tace "Ameen" ta fice parlon da sauri tana share xufar goshinta a ranta kuwa hamdala take da Allah ya bayyana mata Ta Rasulu.
Washegari Thursday duk yan matan gidan na ta shirye shiryen fita saloon da yin lalle, ita dai Imaan sai kumbure kumbure take...


*Imaan isn't for free* it's 300 via


Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788



45.....


Mujaheed na dinning a xaune Maryam ta sakko downstairs tare da Maimoon, yana kallonta yace "Maryam" ta kalli direction din sannan ta tafi tace "Sai yanxu kake breakfast?" Yace "Ehh... xauna" ba musu ta ja kujera ta xauna, ya ajiye cup din coffee dake hannunsa yace "When did she tell you is the birthday?" Maryam ta langwabar da kai tace "She told me nothing about it again, tun ranan bata gaya min komai ba" Yana kallonta da kyau yace "Karya kike Maryam" ta xaro ido tace "Karya kuma ya M.A, bana ma tunanin Birthday din na nan don bata ce min komai ba, kuma kaga gashi ana ta hidiman biki, kila ma ta manta idan ma Birthday din na nan" yace "Make me a promise Maryam" tace "What promise" yace "You will watch her movement keenly" dariya tayi tace "Ohk then, amma kuma abun mamaki ina ma xata je ana biki" Yace "Just do what I say" tace "Toh na ji" yace "Good tashi ki tafi" Mikewa tayi ta bar dinning din, ya dau coffee dinsa ya ci gaba da sha a hankali. A bedroom Maryam ta tadda Imaan dake ta shiryawa slowly wai don a tafi a mance da ita, Maryam tace "Naga alamar baki son xuwa saloon din nan imaan" kamar xata


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login