Showing 42001 words to 45000 words out of 303099 words
haka, a gida ne kawai" yace "Toh su waye?" Tace "Cousins dina" yace "Really?" Ta gyada masa kai, yace "Can I know them" murmushi tayi tace "Ya Yusuf ne sai yaya.. Ohh yaya yusuf ne ma kadai, mun daina shiri da yaya yanxu" yace "Can I know the Yusuf?" Tace "Yea he is my cousin, an engineer yana aiki a nan yana yi a Kano yana yi a zaria" yana parking kofar gidan su yace "Shi dayan fa?" Tace "Yaya?" Ya gyada mata kai tace "Shi wani lkcn yana Abuja wani lkcn yana nan, yanxu yana nan" Sadeeq yace "Maa sha Allah, to me yasa bakwa shiri?" Tace "Yanxu ya fiye mugunta baya kuma kulani kamar da" tana magana ta bude kofar motar tace "Nagode" ba karamin daure ransa yyi ba yace "Wait ara min fone naki pls, I want to confirm ko Muhsin ya tafi da nawa cos I can't find it here" komawa tayi ta xauna ta basa wayarta ya amsa ya gama danne dannensa sai ga ring din wayarsa, ya mayar mata yace "ohhh thanks yana nan ashe" ta fita motar tace "Thanks" yayi murmushin da ya bayana dimples dinsa yace "You are welcm" Xaune ta ga Mujaheed gun mai kiosk a kofar gidan yana kallonta, duk da yanda gabanta ya fadi ta dauke kai da sauri ta wuce cikin gida ta rufe gate.
*I want to use this medium to bring this to the notice of my Fans, akwai wani namiji mai amfani da information dina gaba daya both Facebook and WhatsApp, a lot suna chatting da shi a tunaninsu ni ce, to bani bace ba wllh, masu nemana Facebook idan sun yi searching xa su ga account biyu iri daya, to ni nawa account din daga followers kadai ma mutum xai gane it's real me bcos the followers are much, idan mutum ya duba post na timeline dina ma xai gane account dina ne, duk da ko wani update nayi shi ma sai ya sata yayi, ga lambarsa kamar haka masu chatting da shi ta WhatsApp 09031263639.... Billah namiji ne kuyi ta kanku, har card wasu na tura masa da sunan xa su siya littafin Imaan to bani bace, da yawa na cewa sun biya Noor Hayat ban sa su group ba ban basu littafi ba to shi suka ba kudinsu ba ni ba. Beware fans katon namiji ne yake claiming khaleesat Haiydar kuma ni na bar sa da fitowar rana da faduwarsa, duk da ban ma yarda shi din Muslmi bane, Allah ya Isar min, a yanda ya fara a gantale haka xai kare a gantale*
Littafin Imaan is 300 via... Fcmb 3276052019
Hauwa Bello Jiddah
Show ur evidence of payment through my WhatsApp digit... 07087865788, subscribe and read happily without feeling any guilt.
_Su ma masu editing min novel su sa abinda ban yi niyyar sawa ba, bayan fitar da shi da suke ban yi complain ba... we shall meet in the hereafter in sha Allah_ 😇
14. Imaan
Mikewa Mujaheed yyi ya bi bayanta, tunda Imaan ta shiga gidan daman take waigen kar ya biyo ta, ido hudu suka yi da Umma da ta fito tare da wata bakuwa, ta dauke kai ta ci gaba da tafiyarta da sauri, Mujaheed na ganin Umma dama ya canxa direction dinsa, Umma na kallon sa tace "Daga ina kake?" Yace "Ina xaune a waje, xan wuce wajen aiki ne yanxu" Umma ta bi Imaan da kallo sannan ta kara kallon sa, ya d'an buda ido yace "Umma ni ban gane kallon nan ba, ki tambayi mai kiosk din can tun daxu nake wajen a xaune wllh" Kawar Umma tace "Yi wucewan ka kaji Muhammad" Murmushi Mujaheed yyi ya wuce ciki, tafiya suka ci gaba da yi Umma tace "Gani nayi kamar tare suke da warcan mai laluran da ta wuce yanxu" Hajiya Saude tace "A'a da xan shigo daxu fa na gansa xaune inda yace maki, to minti na nawa a ciki ko minti sha biyar fa ban yi ba" Umma ta sauke wani ajiyar xuciya tace "Da kin san irin k'i da tsanar da nake ma uwar yarinyar nan har cikin raina ko Hajiya Balaraba, wllh abun ba kyau, xan iya komai a duniya don ganin na walakantata, yanda nake jin tsanarta a rai ko kishiyata Amina ban jin ta haka, sai in ki cutar Amina amma ita xan iya cutar ta, sai ga tsanar har ya shafi wannan figaggiya irin ciwon da ta haifo duniya, duk na tsane su kamar yanda na tsani mutuwata, bayan na dawo gidan nan da kyar fa na raba Mujaheed da yarinyar, sai da na tashi tsaye kyamm" Hajiya Balaraba tace "Ikon Allah to sonta yake shi din?" Umma tace "Auzubillahi kaji wata magana wai so, ni na haifi Mujaheed na san halinsa, wllh ba so bane kawai shakuwa ce tsantsa da shisshige masu da yake, sannan yarinyar ta yi mugun sabo da shi, kuma a da kafin in dawo shi ke tsaye kan bata magunguna da dai abubuwa da ya shafi lalurorinta, kin san sickler ce sosai...." Hajiya Balaraba tayi dariya tace "Ba fa a shaidar d'an yau Hajiya, ke kin shiga xuciyarsa ne kika ga ba sonta yake ba?" Umma tayi wani murmushi tace "Kin san akwai wani abokinsa Ibrahim iyayensa hamshakan masu kudi ne, shi ma yaron ya jike jagab da naira, da ban yi da gaske ba wllh ita Imaan din ya so hadawa da yaron wai ya nemeta, ga yaron mai hankali da nutsuwa, wllh sai da na masa jan ido sosai, don in dai ina raye abun arxiki baxai taba xuwa inda Aisha da 'yar ta suke ba, baxan bari ba in sha Allah ina nan ina sa ido in ga wanda xai jajibe yarinyar da gwara babu da ita, kullum fa ana hanyar asibiti kamar 'yar da aka sama ta mugun hanya, to fa da nayi da gaske da Mujaheed shine ya hada yaron da kanwarsa Ummi, yanxu ana gama bikin Seeyama xa a fara xancen na Ummin, Uban yaron fa abokin gwamnan garin nan ne na kut da kut" Hajiya Balaraba tace "Toh Allah dai ya kyauta" Umma tace "Sannan shi Mujaheed din akwai wata yar talakawa da yake mutuwar so wai farida, ni a bincike na ma cewa aka yi idan ban tashi tsaye ba wllh sai ya aureta don yayi mugun kwallafa rai a kanta, baki ga hidimar da yake mata da iyayenta ba, duk ya talike a kansu har haya na samu labarin yana biya masu don nasa mutane su sa masa ido a anguwar, in sha Allah na kusa cire masa yarinyar a ransa gaba daya sai dai idan ba ni ce na haifesa ba, sa'anninsa na neman 'ya yan masu kudi shi ya buge da neman talauci salon su mallake min shi su tsiyace shi, iyayen fa matsiyata ne na gaske wllh" Hajiya Balaraba tace "Toh shi ina ya samota?" Umma tace "Wllh wai ya dawo daga Abuja ranan, kin san wani lkcn jirgin kasa yake biyowa ta a nan anguwar ya ganta dai dai layinsu wai xata Unguwar sanusi, shine fa ya rage mata hanya daga nan kuma ta makale masa ina jin, ni dai ina nan ina kokarin cireta a ransa gaba daya" Hajiya Balaraba tace "Gaskiya kam, Allah dai ya mana tsari" Umma tace "Ameen" sallama suka yi Umma ta koma ciki. Bude kofa Imaan tayi ta fito misalin karfe tara na dare don kwashe socks da kananun kayan da Ammi ta wanke mata a cloth line, da kyar take tafiya don ji take kamar xaxxabi xai rufeta ga ciwon kai, tun bayan Isha Mujaheed ke xaune kan farin kujera ta wajen parking space dinsu, yana jin fitowarta kuwa ya mike ya tsaya kusa da wani flower dake opposite cloth line din, bbu wuta gaba daya a wajen hakan ya ba Imaan mamaki sai tayi tunanin mutuwa bulb din yayi, nan ko shi ya cire bayan ya dawo masallaci, sai da ya jira ta fara kwashe kayan nata sannan ya cafkota ta baya, yasan next action dinta hakan yasa ya rufe bakinta da sauri, tayi mugun tsorata wanda hakan yasa ta fara numfashi da sauri, yayi freeing bakinta yana kallonta don gaba daya ya ma mance da laluran nata, ya dukar da ita da sauri yace "Ke relax now, nine fa, stay still and relax" kasa yin hakan tayi babu bata lkci kuma Asthma dinta ya tashi a wajen, daga ta yayi ya shiga apartment dinsu da ita, Ammi ta mike tana kallonsu, ya xaunar da ita kasa, Ammi ta wuce dakinta ta dauko inhaler dinta ta mika masa ya amsa ya bude cap din ya kai mata baki, sai da Ammi ta ga numfashinta ya fara dawowa steady sannan ta juya ta wuce bedroom dinta. Kwanciya Imaan ke son yi ya dagota yana kallonta yace "Ina ke maki ciwo" Hawaye cike idonta ta nuna masa kafarta, yace "Kin sha magani?" Ta girgixa masa kai, yace "Ina magungunan?" Ta nuna masa bedroom dinta, dagata yayi suka wuce dakin nata, ya dau magungunan ya bude su sannan ya fita xuwa kitchen ya dauko ruwan gora da glass cup ya koma dakin, bata maganin yayi ta karba ta sha, ya mike ya dauko na tube da take shafawa a kafanta da bayanta, dawowa yayi kan gadon ya durkusa kusa da ita ya daga rigar baccin jikinta xuwa thigh dinta, ta bude ido tana kallonsa, duk ta wani langwabe tana sauke numfashi a hankali, shafa mata man xafin ya shiga yi, kamar xata yi kuka murya can kasa tace "Wayyo Yaya yana min ciwo" hararanta yyi bai dai ce komai ba, ta runtse ido ta kama hannunsa tace "Ni wllh ciwo yake min ka min a hankali" Buge mata hannun yyi ta janye da sauri, haka ta dinga yarfe hannu har ya shafe mata maganin daga thigh har fararen toes dinta, gaba daya jikinta ya dau xafi wanda at anytime xaxxabi zae iya rufeta, a hankali tace "Yaya saura bayan" yana kulle tube din yace "Baxan yi ba" da kyar ta mike xaune ta sauke rigan jikinta xuwa waist dinta ta koma tayi rub da ciki, yace "Ki shafa da kanki baxan shafa ba" a hankali tace "Baxan iya ba ae, don Allah ka shafa min" da kamar baxai shafa ba sai kuma ya bude tube din ya matso methylated cream din ya fara shafa mata a bayan a hankali, lumshe ido tayi cikin sanyin murya tace "Yaya kai na ciwo yake min sosai, kamar xaxxabi xan yi" ya hade rai yace "Ina kika tafi daxu?" Ta bude ido da sauri tace "Gidan Gwaggwo naje" yace "Waye ya ajiye ki a mota?" Ta xaro ido sai kuma ta turo baki bata san duk yana kallonta ba, yace "Ba tambayar ki nake ba" kamar xata yi kuka murya can ciki tace "Ya Muhsin ne fa" mintsilinta yyi a bayanta yace "Ni xa ki ma karya?" Ta yi wani kara ta mike xaune da sauri tana shafa wajen, ganin kallon da yake mata ta xaro ido tayi wani karan ta koma tayi rub da ciki tace "Wayyo bana so yaya" yace "Nace wa ya ajiye ki daxu?" Ta rufe idonta tace "Ya Muhsin" yace "You are still lying koh? Wannan yayi kama da motar Muhsin?" Ta turo baki tace "Ya canxa mota" yace "Ohk, idan kika bari na fita dakin nan baki gaya min ko waye ba, this case will pend har ki gama langwabe langwaben ki kuma I promise i will deal with you" kamar xata yi kuka tace "Yaya abokin ya Muhsin ne fa, tare muke da shi sai ya sauka a wani anguwa xai yi wani abu shine abokin ya ajiye ni shi, ka kira ya Muhsin din ma ka tambayesa wllh" yana gyada kai yace "ke yanxu kin girma baki da aiki sai shiga motar karti suna ajiye ki kofar gida koh?" kallonsa take kamar xata fashe da kuka ya mike ya ajiye tube din xai fita, a hankali tace "Yaya baka gama shafawa ba" wani shegen kallo ya mata ya fice dakin. A stairs ya hadu da Umma xata sauko parlor, ya jira ta wuce tana kallonsa tace "Mura kake nake jin kamshin aboniki?" Ya wara ido yace "Oh, eh daxu naji kamar xan yi muran shine fa na shafa a kirji" Umma tace "Toh Allah ya sauwake" daga haka ta wuce shi ma ya wuce sama ya shiga dakinsa, gun injections dinsa ya nufa ya dau pcm da syringe yasa a aljihunsa sannan ya sakko parlor, Umma tace "Ga fa abincin ka can ka bari yana galallawa a dinning" Mujaheed yace "Ohk xan ci Umma" tace "Yanxu ina xa ka?" Yace "Card xan amso waje" daga haka ya fita, sanin halin Ummar tasa, hakan yasa ya fita gidan gaba daya, bayan kusan minti bakwai ya dawo ciki ya nufi part din su Imaan, Ammi na kitchen tana wanke wanke jin an bude kofar parlor ta leko suna hada ido yace "Allura na dauka na pcm naga tana xaxxabi" yana magana yana ciro alluran a aljihu Ammi bata tanka sa ba ta koma kitchen Bedroom dinta ya bude ya shiga ya sameta yanda ya bar ta har ta fara bacci, ya isa kusa da ita ya xauna bakin gadon ya fara hada alluran yana gamawa ya juya yana kallonta yace "Kee" tayi nisa baccin dama gata mai nauyin bacci, sanin haka ya ja hancinta yace "Imaan" bude ido tayi da kyar xata kara rufe idon yace "Baxa ki tashi ba?" A hankali tace "Yaya me xan yi kuma" Ta bude ido sosai ganin abinda ke hannunsa ta mike xaune da sauri tana jan rigar ta xuwa chest dinta tace "Yaya wa xaka ma alluran?" Yace "Gado" kamar xata yi kuka tace "Ka mance na sha magani ne" yace "Kar ki bata min lkci my frnd" ta fashe da kuka tace "Na shiga uku Ammi ni ban ce a min allura ba" Tana fadin haka xata mike ya fixgota ya kwantar da ita ya daga rigar jikinta ya mata alluran ya mike ya fice daga dakin, sai da Ammi ta shigo dakin tana mata mugun kallo sannan ta hakura da kukan ta koma ta kwanta nan da nan kuma bacci ya dauketa. Imaan na dawowa schl ranan litinin taga calls har biyu da ta yi missing, bayan ta idar da sllh tana xaune kan darduman ta dau wayar tayi dialing number din, har ya katse ba a dauka ba, few seconds later sai ga call din ya shigo wayarta, dagawa tayi ta kai kunne, sallama aka yi daga daya bangaren cikin cool voice, tayi shiru da farko, can kuma tace "Waye ne?" Yace "Baki amsa sallama ne?" Tace "Not a must in amsa a fili, who are you" yayi murmushi yace "Ohk then, how are you?" Tace "I asked who are you first?" Yace "Tsoro kike ji?" Tace "Sorry i think it's a wrong call" yace "Why do you say so?" Tace "Because without any doubt I know it's only my dad, mum.... and very few dat have my contact" yace "Ohk... Muhsin ya sa in kira in ji ko kin shiga gida lafiya" ta d'an bude ido da mamaki amma ta kasa cewa komai, yyi murmushi a hankali yace "How are you Imaan?" Murya can kasa tace "Alhmdllh" yace "I guess yanxu kika dawo schl?" Tace "Sure" yace "Alryt, sai islamiyya ko?" Tace "Eh" yace "Ohk then Allah ya kiyaye hanya, amma tare xa ku yi sauka da su Mariya?" Tace "In sha Allah" yace "Saura wata nawa?" Tace "Two months" yace "Maa sha Allah, we will talk later kar kiyi latti" tace "Sai anjima" daga haka ta katse wayar ta mike ta fara shirin Islamiyya. Bayan Magrib Mujaheed na xaune parlon Abbansa da duk yan gidan, Yusuf ma dake xaune wayarsa kawai yake ta dannawa a parlon, Anty duk ta fiddo ankon bikin Seeyama suna nuna ma Abba, Umma dai na xaune ta hade rai don gani take kamar Anty shishshigi kawai take mata, Anty tace "Toh Abba ga kaya nan, gaba daya kala uku ne" Mujaheed yace "Toh duka kala ukun xa su yi?" Anty tace "Ehh ko kana da damuwa da hakan??" murmushi yyi bai ce komai ba, Yusuf ya daga kai yace "Amma fa Anty yayi yawa sai kace su ne..." Mugun kallon da mahaifiyar tasa tayi masa yasa yyi shiru ya ci gaba da danna wayarsa, Abba yace "Kice expenses ne ba na wasa ba, to da wanne ku ke son mutum ya ji, ina laifin ma kala biyu?" Umma tace "Haba Alhaji, abu dai na rana daya lkci daya, ni fa da cewa ma nayi kala hudu hudu Amina tace a bar shi a kala uku kawai" Abba ya gyada kai bai dai ce komai ba, Anty tace "Idan ma baxa ka siya masu ba ga yayyinsu sai su masu" Umma tace "Atoh dai" Yusuf yace "Mu dai sai dai muyi masu kala bibbiyu" Anty tace "Toh ka rike kudin ka" Dariya yayi yace "Shikenan ni sai in ma Rahma da Ummi M.A yayi maku sannan yayi ma Maimoon" Umma tace "Sai kayi ma Kakarku ko kala biyu ne ita ma, shikenan it's settled" Yusuf ya dinga kallon Umma bai ce komai ba, Abba yace "Toh mamana fa?" Anty ta buda ido tace "Ai kuwa Imaan... kaga na ma mance wllh, shikenan sai Mujaheed yayi mata kaga hakan ma is settled" Abba yace "Ehh sai Mujaheed yayi mata" Umma ta yi ma Anty wani kallo tace "Wani Mujaheed din, shi Yusuf me ya hanasa yi mata?" Anty tace "Saboda kince yayi ma Kakarsu, kinga Mujaheed sai yayi ma Imaan" A fusace Umma tace "Toh an ruguje wannan tsarin kowa tayi ma 'yar ta, Inna kuma Alhaji ko baban ita Imaan din su yi mata" Abba yace "Ba tsarin da ya ruguje Hajiya, Mujaheed yayi ma ke, Amina... da maimoon sai Imaan, Yusuf kuma yayi ma Ummi, Rahma da Inna, kuma a cire ma imaan nata a kai mata yanxun nan" Anty ta cire ma Imaan kala uku, Abba ya kalli Mujaheed yace "Dauka ka kai mata" Mujaheed ya kalli