Showing 225001 words to 228000 words out of 303099 words

Chapter 76 - Imaan Book 1 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

1622

ni tun ba yau ba nasan Rukayya na xuwa gun boka da malamai, amma wllh tllh in har da sa hannunta a rugujewar auren jikata ita ma nata auren na lilo tangal tangal yanxu...." Sai kuma Inna ta fashe da kuka sosai tace "Allah dai ya hada Ahmadu da jaraban duniya, Rukayya jaraban duniya ce, wato hade kai tayi da surka suna xuwa gun boka bbu kunya ba tsoron Allah, Ni dai wlh in har aka binciko min aka gano cewar ita ta wargaza auren Imaan akwai tashin hankali a gidan nan gaskiya, don da kai na xan yi fatali da kayanta waje, dama darajan Mujaheed kawai take ci a wajena" Mama Hadiza ta sauke ajiyar xuciya tace "Ni na ma rasa abun cewa wllh..." Inna tace "Yo ba dole ba, kuma fa tana ciki tana jin su, wa ya sani ma ko xawo ta dinga saki a dakin, ni dama ciki suka shiga suka kamata su lakada mata duka da cacan bakin da suka dinga yi tsakar gida" Mama Hadiza tace "Toh Inna kin san halinta kuma me yasa xaki kare ta a wajensu?" Inna tace "Ka ji ki ke kuma, ke baki ga yanda jikinsu yyi sanyi ba, ai ynxu mance batun kishiyar da aka ma Safara'u xa su yi su fuskanci Rukayya su yi fata fata da rayuwarta, ai bamm na hada mata...." Dariya sosai Aunty tayi tana kallon Inna, Inna tace "Lallai ba ku san ni ba kenan har yanxu, Ahmadu da Bukar kawai nake jira su dawo daga gidansu bafillatanar can da ta gudu min da jika su ji wnn abun al-ajabin, dama Ta Rasulu sai da tace min bata yadda da fasa auren nan da Bulasawa yyi ba, shi sa ma yau da sassafe ta tafi don xuwa binciko mana m ke faruwa, na rantse da Allah in har da sa hannun Rukayya a fasa auren nan sai nayi sanadin karshen xamanta a gidan nan..." Tana fadin haka ta tashi ta wuce daki, Mama Hadiza ta girgixa kai tace "Rukayya tayi asara duniya da lahira, yanxu meye amfanin surkai su xo tsakar gida suna maki cin mutunci haka, ni wllh Mujaheed nake tausayi bai yi sa'ar uwa ba kwata kwata, tun fa ba yau ba ake abu daya da matar nan ta ki sa Allah a ranta, anya Rukayya xata gama da duniya lafiya kuwa??" Aunty dai bata ce komai ba amma ita ma mamakin maganganun Hajiyan Marafa da tawagarta kawai take... Karfe sha biyu saura Gwaggwo ta shiga parlon Inna da sallama, Imaan dake sanye da Hijab har kasa da Nikab na biye da ita a baya, Inna dake xaune parlon tare da Mama Hansai ta amsa sallaman, Imaan ta wuce daki walking slowly, Inna tayi ma Gwaggwo kallo daya tana sakace hakori ta dauke kai, Mama Hansai ta shimfida mata darduma tana mata sannu da xuwa, Gwaggwo ta xauna bayan sun gaisa da Hansai tace "Sannu Hajiya Asabe" Inna ta kalleta tace "Yauwa sannu Hajiya Biba, amma a gaskiya ki dinga sa 'yar ki a hanya, kwata kwata Aisha bata ji bata maida ni bakin komai ba, ya xata maida kanta mahaukaciya daga anyi abu don fitar da mu kunya gaba daya, kema kuma baki son gaskiya don da kina son gaskiya tun jiya ya kamata ki tiso keyarta ki koro su, nan nan nace mata kada ta je ko ina amma yarinyar nan ta ki saurarata, gaskiya raina ya baci matuka don tun tsakar daren jiya nayi niyar tahowa gidan in sameta su Ahmadu suka hanani" Gwaggwo dake ta saurarenta tace "Allah ya kyauta, a dai ta hakuri..." Inna tace "Atoh, tamkar yar ciki na na dauketa amma dubi iya shegen da ta min, kowa a gidan na ya girgixa da auren nan, to amma abinda hakuri bai yi ba rashinsa xai yi? ni fa har cewa nayi sai Mujaheed ya rubuta takarda amma d'an banxan ya gudu da dukkan alama yana so, to yana so mana tunda tun jiya bbu shi bbu alamarsa ya shiga duniya" Gwaggwo tace "Toh Allah dai yasa hakan ne mafi alkhairi, ga ta nan dai na kawota, ba ma ta jin dadi amma tunda nayi ma iyayenta alkawarin dawo da ita shi sa na maido ta yanxu" Inna ta yo waje da ido tace "Kuma bata da lafiya sai ayo min nan da ita, ta fito ta koma barin su ai Hadiza na can" Gwaggwo ta mike tace "Ni dai xan koma Hajiya Asabe Allah ya sanya albarka" Daga haka ta nufi kofa, Inna tace "Toh ko ruwa baxa ki sha ba" Gwaggwo tace "A'a nagode, sai anjima" daga haka ta fita parlon, Inna ta tabe baki tace "Aisha dai ta lalace wllh" tana fadin haka ta tashi ta tafi daki gun imaan, kwance ta sameta ko nikab din fuskarta bata cire ba, Inna ta tuge nikab din ganin yanda idonta yyi jajir ga jikinta yyi xafi ba kadan ba tace "Ae ni na shiga uku, fasa auren da Bulasawa yyi yasa kika rame haka kika sa ma kanki ciwo Imaan?" Imaan ta mike xaune da kyar hawaye na saukowa idonta ta kamo hannun Inna cikin rawar murya tace "Don Allah Inna ki taimakeni, wllh shi fa Yayana ne taya xa ace ya aureni???" Inna ta marairaice tace "Nima dai shi na gani, wnn uban sa6o har ina ni patuu, sai kuma ace kinyi ciki kin haifa masa 'ya ya ko? To ta ina xa fara wannan ta6aran ni Asabe??" Imaan ta fashe da kuka sosai ta rufe kanta da pillow tana shessheka, Inna ta xauna gefen gado tayi tagumi tace "Anya su Ahmadu da Bukar suna da hankali kuwa ni Patuu? A ina suka ta6a ganin anyi haka tukun??" Imaan dai kuka kawai take kamar ranta xai fita, Inna tace "Naga abinda ya isheni...." Mama Hadiza ce ta shigo dakin bayan sun hadu da gwaggwo a compound sun gaisa ta sanar mata ta dawo da Imaan, Inna na ganinta ta mike tace "Hadiza anya su Ahmadu na da saiti kuwa, ta ina Imaan da Mujaheed xa su yi aure ne wai ban gane ba, yayanta ne fa Hadiza?" Mama Hadiza tace "Kamar ya Inna?" Inna tace "Toh abinda tace min kenan wai yayanta ne kuma haka ne wllh yayanta ne" Mama Hadiza na kallon imaan tace "Halan baki je islamiyya bane Imaan???" Inna ta daure fuska tace "Kaji wata magana, yarinyar da ta haddace kur'ani har sauka tayi aka bata kyaututtuka kice bata je islamiyya ba Hadiza??" Mama Hadiza na kallon Imaan fuska daure tace "Ta ina Mujaheed ya xama Muharramin ki? Ko kin fara hauka ne? Idan an kai ki gidan sai ku ci gaba da xaman yaya da kanwa a can, amma na sake jin kince yayanki ne sai na bata maki rai wllh, shashasha kawai...." Murya can kasa Inna tace "Atoh dai, nima ban san ta ina ya xama yayanta ba, ubanta Bukar ubansa Ahmadu, uwarta Aisha uwarsa Rukayya" ko kallon Inna Mama Hadiza bata yi ba ta juya ta fice daga dakin, Inna ta xauna gefen gado tayi tagumi tace "Gashi har yanxu shiru bbu Mujaheed din babu labarinsa, ko shima yana can yana ta damuwar an hada sa da kanwarsa ne" ita dai Imaan bata ko kalleta ba sai kuka take a hankali. Har Inna ta gama tsarinta kallonta kawai Abba da Daddy suke yi, Inna tace "Wllh kuwa Ahmadu, motocin da suka shigo sun yi biyar ga dai Hadiza shaida, to shine nace gaskiya idan maganganun iyayen Safara'u ya tabbata kashin Rukayya ya bushe a gidan nan kuma xamanta ya xo karshe, ynxu dai muna bin komai a hnkli ne don ba mu gama tabbatarwa ba tukun, duk da dai gaskiya tun ba yau ba nasan Rukayya na shige shige" Abba dai kansa na kasa, Daddy kuwa har xuciyarsa bai yrda da xancen Inna ko na second daya ba, can ya mike yace "Inna lkcn Asr yyi xan tafi masallaci ynxu" Daga haka ya nufi kofa Inna ta bi sa da kallo sannan ta kalli Mama Hadiza tace "Irin na xauna ina shirga masu karya din nan, to in sha Allahu a gabansa asirin Rukayya xai tonu dumu dumu..." Abba ya kalleta yace "Allah ya kyauta, xa mu xuba ido mu ga inda matsalar yake kafin a dau mataki" Inna tace "Atoh dai nima haka nace a hankali xa mu bi komai har mu gano gaskiya, ba wani gaggawa" shi dai bai ce mata komai ba, tace "Toh wai ni jama'ah ina xancen jikana ne, tun jiya fa har yau shiru, ko gidansa xan dau mayafi in tafi?" Abba yace "Daxu mun biya gidan baya nan" salati Inna ta saki tana kallonsa tace "Toh me ya samesa?" Mama Hadiza tace "Gun aikinsa fa?" Abba yace "Sadeeq ya je baya nan" cike da damuwa Inna tace "Toh anya lafiya kuwa??" Mikewa Abba yyi shi ma dai duk abun ya damesa sosai, yace "Bari in tafi masallaci Inna" daga haka ya fita parlon yana tunanin to Ina Mujaheed xae tafi tun jiya. Daren ranan Inna ta fito tsakar gida tana salati tana kiran Abba da karfi, Daddy ne ya fito part dinsa ya sakko yana tambayar me ya faru, Ko saurarensa bata yi ba balle ta kallesa ta karasa part din Abba tana kwalo masa kira, Yusuf ne ya fito parlon Aunty na biye da shi, yace "Lafiya Inna? Me ya faru" Daga sama har kasa ta kallesa tace "Kai rabu da ni, kai ne Ahmadu, ni ba duk xatona kana gun amaryarka ba ashe kana gidan nan har yanxu baka shigo ka min jajen abinda ke faruwa ba...." Ganin Abba tace "Wllh Ahmadu na kasa gane kan Imaan, abinci fa na tilasta ta ci sai gashi ta dinga amai kamar xata mutu ga jikinta duk xafi kamar garwashi, ka ga dai yanda nake tsaye kyam to bata iya tsayawa haka, kada wani cuta ya kamata fa in shiga uku ka taho mu je ka kaita asibiti, a gaskiya bata da lafiya sosai wllh" shi dai Daddy na tsaye bayanta yana kallonta, Abba yace "mu je to" daga haka ya fara tafiya Inna ta bi bayansa Aunty da yusuf na biye da su, kafin su je har Mama Hansai ta kintsa Imaan da duk ta wani langwabe, Abba yasa ta sa hijab suka wuce asibiti.... Daren ranan asibiti Imaan ta kwana tare da Aunty sbda karin ruwan da ake mata, tausayinta sosai Aunty take ji don abun ya hade mata biyu ne, ga heartbreak ga kuma unexpected marriage, ga shi duk ta wani rame, wajen karfe daya Imaan ta farka daga baccin da take, Aunty dake xaune kan farin kujera ta jinginar da kanta da gadon ta dago jin motsin ta, mikewa tayi tace "Sannu Daughter, ya jikin?" Imaan ta kamo hannunta lkci daya hawaye ya kawo idonta cikin sanyin murya tace "Aunty don Allah baxa ki taimakeni kiyi ma su Abba magana su yi hakuri kada su ce ya Mujaheed ya aureni ba??" Aunty na kallonta da tausayi tace "You need much rest imaan ki kwanta ki yi bacci ko na hada maki shayi?" Imaan ta girgixa kai hawaye na sakko mata tace "Aunty kice wani abu plss" Aunty tace "Imaan meye da Mujaheed din da baki son auren sa?" Imaan ta xaro ido tace "Aunty yayana ne fa" murmushi Aunty tayi tace "Eh yayan naki, ae da aure tsakanin ku ko, Mujaheed is good ba shi da wani flaws da xai sa ki daga hankalin ki, ke da ma kika fi kowa sanin sa, kinsan halinsa ya san naki so what more, in just few days time da xa ku yi tare am telling you sai kun gode ma iyayen ku da suka hada ku aure, but wait ynxu ki gaya min me yasa baki son auren, amma kada ki ce min yayan ki ne, don ke kika laka6a masa wannan matsayin, tell me yana da wani abu ne da ba ki so" ta fashe da matsanancin kuka tace "Wllh Kunyan sa xan dinga ji Aunty, ni kunya nake ji...." Sosai ta ba Aunty dariya, Aunty ta rungumeta tana murmushi bata dai ce komai ba, cikin rawar murya Imaan tace "Allah kunya xan ji Aunty" Aunty tace "Toh ki kwanta yanxu ki huta sosai, gobe sai mu yi magana" da haka ta lallaba ta ta kwanta, amma imaan bata yi bacci ba daren ranan, da ta tuna wai ynxu Mujaheed fa mijinta ne sai taji kamar ta bace duniyar gaba daya da wannan abun kunyan kawai, washegari sai da rana aka sallamosu suka dawo gida. Sadeeq ne durkushe gaban Mum dinsa dake xaune tana kallonsa da mamaki, ya hade kansa da kneels dinsa hawaye na sakko masa yace "Mummy I don't know what just came over me, don Allah ki tausaya min ki ba Abbana hakuri ya sami iyayen Imaan ya basu hakuri I cant imagine loosing her, don Allah ki taimakeni ki masa magana ya same su sai a daura mana auren" Mummy tace "Anya kana da hankali kuwa Sadeeq??" Ya dago kansa yana kallonta hawaye na sakko masa yace "Sure mum, ni ban san me yasa nayi abinda nayi ba, help me speak to dad plss" mummy tace "Kaje ka samesa da kanka Sadeeq I won't invole my self coz har ynxu ur Dad is angry with me bcos of what u did" tashi yyi ya nufi kofa ta bi sa da kallon mamaki don tun shekaranjiya sai yau ya shigo gida kamar an jefo sa, mikewa tayi duk jikinta yyi sanyi sosai tana tunanin to me ya sami son dinta, ita tun farko tasan ba yin kansa bane fasa auren nan da yyi, then who is after her son? Waye yyi masa haka? Girgixa kai tayi tace "I will surely find out...." Tana fadin haka ta fita dakin. Inna na xaune parlonta ta sa Mama Hadiza gaba bayan Magrib wai sai ta samo mata layin Mujaheed kawai ita dai, Mama Hadiza ta kira for the third time da damuwa tace "A kashe fa wayar yake Inna ba a kunna ba har ynxu, gashi kina jin ance switched off" Inna ta xaro ido kamar xata rusa kuka tace "Anya Hadiza Mujaheed ba kashe kansa yaje yayi ba kuwa??" Sai kuma ta fashe da kuka tana kallon Mama Hadiza tace "Da mun shiga uku mun lalace" Mama Hadiza ta hade rai tace "Haba Inna ya kashe kansa a kan me kuma?" Sallaman da suka ji bakin kofa yasa duk suka yi shiru, Imaan dake kwance daki duk tana jin su ta mike xaune da sauri xuciyarta na bugawa jin muryar wanda yyi sallaman, Inna ta kalli Mama Hadiza tace "Waye kuma wannan yake min sallama?" Mama Hadiza ta amsa sallaman tana kallon bakin kofa, Sadeeq ne ya shigo parlon kansa a kasa, Mama Hadiza ta dinga kallonsa da mamaki, Inna ta mike da sauri tace "Naga abinda ya isheni, waye kuma wannan Hadiza?? Wa yake nema a parlon nan" A hankali ya durkusa gabanta cikin raunin murya yace "Don Allah ku yi min rai kaka kar ku raba ni da Imaan, ban san me ya sameni nayi abinda nayi ba, don girman Allah ku yafe min kaka, wllh Ina son Imaan baxan iya rayuwa ba ita ba don Allah kaka ki taimakeni kada su Abba su ce baxa su bani ita ba..." Hawaye sosai yake yana kallonta hankali tashe, Mama Hadiza ta bude baki tana kallonsa, lkci daya taji tausayinsa sosai ba kadan ba don gaba daya a hargitse yake ga wani rama da yyi ba na wasa ba, Inna ta xauna ta rushe da kuka tayi mitsi mitsi da ido tana kallonsa cike da masifa tace "Amma dai kai gantalalle ne wawa, da can uban me ya hau kanka ka yaudari jikata ka sa mata cuta ka gudu?? kunyata mu fa kayi a idon duniya makiyan mu na ta mana dariya ta ko wani lungu da sako, uwar me xa mu maka ka xo mana nan d'an nan, wllh maxa ka fita kada Bukar ya gan ka don ba ruwana, gwara ma Ahmadu...." A rikice ya kamo hannunta yace "Wllh kaka ban san me ya sameni nayi haka ba, don girman Allah kar a raba ni da Imaan xan iya rasa rai na" Imaan ta mike ta shige bathroom ta dinga kuka kamar ranta xai fita, Inna ta gwalo ido tana kallonsa tace "Baka san abinda ya same ka kayi haka ba kuma?" Kuka sosai yake mata yace "Wllh ban sani ba Kaka, ban san me ya faru ba, ban san me yasa nayi haka ba, Kar ku hana ni Imaan don Allah, nasan ke kadai xa ki saurareni kaka" Inna ta fashe da kuka tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Lalacewa ta sameka baka rike Allah da karfi ba Bukar, ni dama nasan da akwai abu a kasa don wannan ba halinka bane, yanxu ni ya xanyi da kai an riga an daura ma mutumi auren yarinya??" Dago kai yyi da sauri yyi still yana kallonta ko kiftawa babu, Mama Hadiza ta sauke wani boyayyen ajiyar xuciya tace "Ka bari iyayenta su dawo xa a san abinda xa ayi Sadeeq...." Sadeeq ya kalleta yace "Don Allah ki sa baki Mama I can't imagine me loosing her, u just can't imagine it" Mama Hadiza tace "You don't worry ka tafi gida, in sha Allah xa a san abun yi" Inna na matsar kwalla tace "Ehh ka tafi xa a san abun yi, ae kai din mutumin kirki ne" xuciyarsa na bugawa yace "Toh anjima xan iya dawowa Kaka?" Mama Hadiza tace "A'a ka bari dai gobe dare yyi yanxu, I will talk to my brothers..." mikewa yyi ya isa gabanta ya durkusa hawaye na sakkowa idonsa a hankali yace "Nagode sosai Mama, Allah ya kara girma" Mama Hadiza ta kasa cewa komai wani tausayinsa ta dinga ji har ranta, cikin sanyin murya tace "Don't worry ka tashi ka tafi Sadeeq" mikewa yyi a sanyaye ya nufi kofa wiping off his tears ya fita parlon, Inna ta kalli Mama Hadiza ta fashe da kukan takaici tace "Kinga maganan iyayen Safara'u a fili ko Hadiza? Kinga


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login