Showing 219001 words to 222000 words out of 303099 words

Chapter 74 - Imaan Book 1 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

1689

sai dai fa duk an hada groups ana kananun surutai tunda har sannan ba a fito ance ga abinda ke faruwa ba a gidan, sun dai ga families din na ta kai komo bbu annuri, mutane dai dai ne yanxu basu san an fasa auren Imaan da d'an gidan Bulasawa ba, sai dai duk bbu wanda yasan an daura auren da Mujaheed, Safeenah ce tsaye rike da plate din abinci ta cika uban nama tana kallon Mama Hansai dake ma wasu yan uwanta da wasu mutane dake xaune sun hada group bayanin abinda ke faruwa fa a gidan, duk aka saki baki ana kallonta, tana girgixa kai tace "Toh Yaya Ahmadu na ganin haka sai kawai ya daura auren da d'an sa tunda an riga an tara jama'ah kada a ji kunya, shine fa hankalin kowa ke tashe a gidan, kusan dai bbu wanda yyi na'am da auren nan da aka hada...." Hajiya Bari'a kawar Aunty dake wajen ita ma a xaune ta ce "Wani d'an nasa a ciki, shi angon ko kuwa??" Mama Hansai ta tabe baki tace "Kila da da angon ma aka auran da duk matsalolin dake faruwa yanxu bai faru ba, da d'an ita Hajiya Rukayya aka daura auren, wato dai Mujaheed....." Safeenah dake tsaye tana ta saurarenta ta sake plate din hannunta a hankali, lkci daya ta fixgo Mama Hansai tana gwalo kwala kwalan idonta tace "Wani Mujaheed din????" Mama Hansai ta juya da sauri tana kallonta don bata ma san ita ce matar Mujaheed ba, Cikin yanayi na tashin hnkli da rikicewa Safeenah ta dinga jijjigata tana cewa "Wani Mujaheed din kike nufi, ki gaya min wani Mujaheed? mijina aka daura ma aure da Imaan din???" Mama Hansai dai sai xaro ido take ta kasa cewa komai, Safeenah ta saketa a hankali tana tariyo reaction din Umma daxu da irin gigicewan dake tare da ita har da fita waje babu hijab, da kuma Mujaheed da ya fito parlon mahaifinsa hawaye a idonsa, wani karan da ya tsorata mutanen compound din Safeenah ta saki da karfi, dai dai fitowar Ammi da Imaan, Safeenah na hada ido da Imaan dake kuka Ammi na rike da hannunta ta sulale wajen sumammiya, duk aka yo kanta ana salati masu debo ruwa na debowa, masu fiffita nayi, Ammi dai tuni ta ja Imaan suka fice compound din gaba daya.... Gidan Gwaggwo Ammi ta wuce tare da Imaan, parlor suka tadda gwaggwo suna jimami da yan uwanta biyu a parlon, Ammi ta gaisheta da mutanen parlon ta wuce ciki Imaan ta na biye da ita kanta a kasa, Gwaggwo ta bi su da kallo can ta mike ta bi bayansu, gefen gado ta tadda Ammi a xaune tayi tagumi, Imaan kuma ta kwanta kan gadon tana kuka a hankali, Gwaggwo ta xauna kan carpet dake shimfide dakin tace "Toh me kuma ku ka xo yi nan Aisha ko baku yarda da kaddara bane? Komai bawa ya ga a rayuwa fa rubutattce ne daga Allah, dama can Allah ya rubuta Sadeeq ba mijin Fatima bane, abun da ciwo amma hakuri kawai duk xa mu yi, daxun nan Muhsin ya bar gidan nan shi ma duk abun ya damesa gashi ko sanin inda Sadeeq din yake bai yi ba wayoyinsa ma duk a kashe wai, ni ban taba xaton haka daga Sadeeq ba, ko me ya samesa haka Allah ma fi sani, amma gaskiya wannan ba lafiya ba ranan daurin aure ka xo kace ka fasa ba laifin tsaye balle na xaune, ban taba ganin haka a xuri'ar mu ba... Na kuma samu labarin hadin da yayan mijin ki yayi Allah ubangiji ya sa hakan shine mafi alkhairi, ai matar mutum kabarinsa...." Ammi ta katse ta tace "Alkhairi fa kika ce Gwaggwo, wllh auren nan ba alkhairi babu alamarsa, in dai basu sakar min 'ya ta ba barin garin nan xan yi da ita, Allah baxai taba sa 'ya ta ta hada jini da irin Rukayya ba, bana fatan haka kuma in sha Allahu hakan baxai ta6a faruwa ba...." Gwaggwo ta bude baki tana kallon Ammi da mamaki, can tace "To ai baki da iko da 'yar su Aisha, ke har xa ki bude baki kiyi wannan mummunan furucin kin mance halaccin uban yaron nan, gaskiya ban san ki da mance alkhairi da rike sharri ba, Ina ce saboda ke Ahmadu har sakin Rukayya sai da yyi wanda sai da tafi shekara uku bata gidan, ko don ubansa ke kya bude baki kiyi wannan furucin Ammi, meye aibun Mujaheed yaro mai hankali da nutsuwa to wllh ni ko ranan laraba sai da ya shigo gidan nan gaisheni, da kyar ayi wata daya ko sau daya bai shigo min ba, kaji min Aisha dai, 6ata masu xumunci kike son yi ko me? Ke dai ba kawai kiyi ma yar ki addu'a da fatan alkhairi da xaman lafiya gidan mijinta ba tunda ga yanda abubuwa suka kasance, da Rukayya Fatima xata xauna ko Mujaheed? Haba Aisha sai kace ba matsayin uwa kike gare Mujaheed ba, gaskiya banji dadin rashin hankalin nan naki ba, daga ubansa yyi kokarin fidda ke da mijin ki kunya sai ki rufe ido ki nuna masu ke baki da hankali baki da kirki??" Ammi ta girgixa kai tana murmushin takaici tace "Dama ba lallai kowa ya gane abinda nake nufi ba ba kuma lallai kowa ya ga abinda nake hangowa ba, Rukayya ta wuce tunanin ku gwaggwo, wllh Rukayya...." Katse ta gwaggwo tayi ta mike tace "Toh sai ki mayar masu da 'yar su ki dawo mu xauna ba shikenan ba, ai bamu da iko da ita, maida ta ki kwaso kayan ki mu xauna nan tunda ke shashahsa ce..." Daga haka ta fice daga dakin. Duk kiran da Abba ya dinga yi ma Mujaheed layinsa gaba daya a kashe suke, daga karshe gidan nasa kawai Abba ya wuce nan mai gadi ya sanar masa bbu kowa a gidan, yayi reverse kenan xai bar layin kiran Daddy ya shigo wayarsa, da kamar baxai daga ba sai kuma ya daga, Daddy yace "Kana Ina Barrister?" Abba yace "Ina hanya" Daddy ya fada masa eatry da yake son su hadu a lkcn don bbu inda xa su xauna su ke6e su yi magana, Abba yace "Alright" kusan a tare suka isa eatry din, Daddy ya sa waitress ta kawo masu just table water, Abba ya bude ruwan ya sha kusan rabi sannan ya ajiye sauran, Daddy na kallonsa yace "First of all I will like to say I am sorry Barrister, duk da dai you misunderstood me amma ina mai baka hakuri still, ko kadan Barrister Auren Imaan da Mujaheed da ka hada ba wai ban yi farin ciki da hadin naka bane, abun farin ciki ne sosai don ko bbu komai mun kara karfafa xumuncin mu, babban damuwata a auren nan shine mahaifiyar mu... nasan baxata ta6a na'am da hadin ba, Dole xata yi maganganu da bai kamata ba a kan mu, sannan Barrister bamu san ko shi Mujaheed din xai yi na'am da auren ba, we don't know ko yana da ra'ayin mata biyu, infact duka duka yaushe yyi auren ba, beside bai ta6a fitowa ya nuna yana son Imaan ba banda so na 'yan uwantaka unlike Yusuf da ya nuna interest a kanta da farko, Barrister what if mun shiga hakkinsa shi Mujaheed din?? Wani irin xama kake ga xa su yi baya sonta ita ma kuma haka?" Murmushi Abba yyi yace "Ae shi yasa nake ta neman sa ta waya domin ya xo ya datse auren amma ban samesa ba, yanxu haka daga gidansa nake baya nan, but in sha Allahu kar ka damu xa a raba auren" Daddy yace "It's not a matter of a saketa or not barrister, in har shi yayi na'am da auren shikenan, sai kuma mu san yanda xa mu yi da Inna, Imaan kuma I am hoping she learn to live with him as husband in sha Allah, Rukayya da Aisha kuma I don't think xa su iya saka xumuncin mu ya sa mu tangarda, in har Mujaheed yayi na'am da auren kuma Inna ta hakura shkkn Allah ya sa hakan shine mafi alkhairi gare su gaba daya, I think you don't need to add anything to what I just said now barrister mu bar xancen haka...." Daga haka Daddy ya kira waitress don ta kawo masu abinci coz it's almost Asr. Tun da Safeenah ta farfado take bin duk mutanen dake xagaye kanta da kallo kamar me son tuna abinda ya faru, lkci daya ta mike a xubure kamar warce aka tsikara ta fasa wani ihu tace "Shi mijin nawa aka aura ma Imaan, innalillahi wa inna ilaihi raji'un, na shiga uku Hajiya Rukayya ta kai ni ta baro ta cuce ni, ta cuce ni, ta cuce ni, mijina ne ya auri Imaan daga karshe, wayyo na shiga uku...." Da gudu Inna ta karaso wajen ta Rasulu na biye da ita ta dalilin labari da aka je aka basu a bangaren ta wai Safeenah ta suma a tsakar gida, Inna na kallon Safeenah tace "Mu ma duk haka muka ji da aka mana kishiya Safara'u, sai dai duk na ki ya fi ciwo ke da kika tika rawa a bikin kishiya jiya, yau kuma tun safe kike ta yanke yanken kabeji da salak......" Safeenah ta fashe da matsanancin kuka tana jijjiga kanta kmr tababbiya tace "Wllh wllh baxan xauna da kishiya ba kishiyar ma Imaan, don ni kadai aka yi Mujaheed a duniya, don ni kadai aka yi sa, sai na nuna ma Rukayya ba ni ta yaudara ba, baxan fallasa ta ba yanxu sai ta fara sanin su waye family dinmu, sai ta san an aura ma Mujaheed Imaan ne saboda mugun halinta da bakin halinta wllh idan ban nakada ma Rukayya duka ba ban Haifu cikin Mansura ba....." Gate Safeenah ta nufa da gudu kamar mahaukaciya tana rusa kuka tana kiran mummyn ta, Inna ta bi ta da kallo da sauran mutanen wajen da suka bude baki da shock, Inna tayi wani dariya irin ta boss tace "Toh wllh babu tsinannen da ya isa ya raba auren nan da raina, auren nan mutu ka raba takalmin kaza, maxa a tafi a kwaso kayan da aka kai gidan barayi a fito da kayan Safara'u a feshe dakin a xuba na jikata, dama idan ba shi Mujaheed din ba waye ya dace da Imaan banda toshewar basirar mutane? Dama can hange hangen Imaan da kwadayin abun duniya yasa ta hango xuri'ar shegu barayi suka kuma yaudareta suka gudu, ni fa tun ba yau ba nake tunanin hada auren jikokin nan nawa biyu kawai dai Allah bai bani basiran yin magana bane amma yanxu kam faduwa ta xo daidai da xama bbu shegen da ya isa ya raba auren nan, ko shi Mujaheed din yyi yunkurin sakin Imaan ni sai in iya tsine masa ya bi duniya" tana gama fadin haka ta nufi part dinta tana cewa "Ku kira min Ahmadu da Bukar na canxa shawara gaskiya, wnn ai abun arxiki suka hada...." Sai kusan Magrib Umma ta dawo gida duk tayi xuru xuru tun safe banda ruwan shayi babu abinda ta xuba a cikinta, xuwa lkcn duk an watse a gidan sai yan uwa na jiki da suka rage, tana shiga dakinta ta dau wayarta don kiran Mujaheed taga missed calls din Hajiyan Marafa yyi goma sosai gabanta yyi mugun faduwa ta dinga kallon wayar, ta xauna gefen gado, Ummi ta biyota daki tace "Umma Hajiya Baturiya yayar Aunty Safeenah fa ta xo har sau uku daxu..." Umma ta hadiye abu da ya makale makogwaronta da kyar ta hade rai tace "Toh sai aka yi Yaya? Neman me suke min?" Ummi tace "Nima ban sani ba" Umma tace "Toh fita waya xan yi" Ummi na fita dakin Umma tayi dialing number Mujaheed ta ji sa a kashe, mikewa tayi hankali tashe tace "Me Mujaheed ke nufi da kashe wayarsa ne??" Hijab ta kuma sakawa ta fita gidan don xuwa gidan Mujaheed ta iskesa. Tsaye ta ga Inna tsakar gida kusa da apartment din su Ammi inda take shiga ba nan take fita ba, Aunty da Mama Hadiza sai Mama Hansai da few relatives na tsaye dai suna kallonta, rai bace ta ci gaba da cewa "Wllh idan bata yi hankali ba sai ince kar ta sake dawowa gidan nan ta sha xamanta gidansu, kuma a kai ni yanxun nan in dauko jikata ai ba uban wani yyi mata ciki ta haifeta ba, ta dauwama a gidansu kar ta sake dawowa gidan d'a na, mata kawai sai bakar xuciya, Bukar dai ya auri jaraba don Aisha jaraba ce wllh, shi jikan nawa take nuna ma k'i haka ba kunya ba tsoron Allah bata jin kunyata ba balle na ubansa sannan Bukar, shi Mujaheed din ne bata so sbda rashin tsoron Allah kamar wani barawo?? to kuwa har Bukar bata so tunda bata son d'an d'an uwansa, kawai ni dai Allah ya hada 'ya yana da fitinannun mata a duniya... Maxa a kai ni gidansu in dauko jikata yanxun nan" tana fadin haka ta tafi dauko Hijab, Daddy da Abba da shigowarsu gidan kenan su ma suka tsaya from afar suna kallon mahaifiyar tasu.





*Imaan isn't for free* it's 300 via


Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788




79.....



Sai kusan karfe goma da rabi Umma ta dawo gida daga gidan Mujaheed duk tayi wani wujiga wujiga da ita, tun magarib da ta fita ta je gidan nasa take ta xaune cikin compound wai ko xai dawo amma shiru har karfe goma da wani abu bbu shi bbu alamarsa hakan yasa ta baro gidan hankali tashe tana hawaye ga Hajiyan Marafa sai kiranta take a waya ba kakkautawa, daga karshe ma kashe wayar tayi gaba daya, direct part din Inna ta nufa tana share xufar fuskarta, kowa ya ganta yasan tana cikin tashin hankali ne ba na wasa ba, xaune ta samesu da Mama Hadiza, Mama Hansai da Ta Rasulu, sai Aunty, Umma ta rakube jikin kujera tana kokarin boye hawayen idonta kar su gani, ta gaishe su gaba daya, duk suka amsa banda Inna dake cin abinci, Umma tayi kasa da murya kamar ta kirki tace "Inna daga gidan Mujaheed nake yanxu, tun magariba nake gidan amma shiru shiru bai dawo ba ban san dalili ba, tsorona kada wannan hadin ya ja mana matsala mai karfi a xumuncin mu tunda Aisha kirikiri ta fito ta nuna bata so, ita ma Imaan din da kanta ba so take ba, shi kansa Mujaheed nasan tashin hankali ne yasa ya shiga duniya, kuma daxu naji ke da kanki kince sai an raba auren, to Mujaheed fa har ynxu bbu labarinsa wllh yanxu haka ma daga gidansa nake Inna...." cikin rawar murya ta kare maganar tana kallon Inna, Inna ta tura abincin gabanta ta kalli Ta Rasulu tace "Kin ji bala'i koh? Rukayya ni xa ki ma sharri kice nace a raba aure da raina a duniya ba wai na mutu ba, ni dai nasan daxu a parlon Ahmadu nace ba ayi shawara da ni ba na kuma nuna bacin rai na sosai, amma bayan wannan ban san komai ba, ban kuma ce komai ba, yo dama ai Mujaheed shine dai dai Imaan ganewa ne ba ayi ba da wuri, shi fa Sadeeq din nan dama ubansa ne mai kudin ba shi ba, kuma da kyar ma idan Mujaheed bai fi sa kudi ba, kudin uban yaron ke rarumowa ya xo nan yana mana burga yana yaudaran jikata wllh, lkci daya kuma Allah ya toni asirinsa, ai wannan auren da kike gani Rukayya mai raba sa kilan mutuwa kawai xai yi a banxa a hofi, kawai ni dai abinda na sani shine dolen Mujaheed ya hada akwatuna irin wanda su Bulasawa suka kawo mana da gwalagwalai idan ko ba haka ba wllh sai in ce a raba auren baki na a leko don jikata ba gantalalliya bace, sannan da kyar idan baxae karo Sadaki ba, ke dai da Aysha da wuya ku ga annabi wllh, ban ta6a ganin mutane irin ku ba a duniya, ita ta tashi ta gudu da yarinya kamar mahaukaciya ba don su Ahmadu da suka dakatar da ni ba wllh da naje da dauko jikata da daddaren nan" Umma da hankalinta ya kai kololuwa gun tashi ganin Inna ta juya xance gaba daya on like da safe da ta dage sai anyi saki ko tayi ma su Abba Allah ya isa, tasan kuma ai shkkn aikin gama ya gama tunda Inna ta canxa labari don dama wajenta kadai take da hope, ynxu kuma bbu hope din, mikewa tayi ta fice daga parlon da sauri, bata yi nisa tana tafiya ba ta xauna nan kasa kan hanya ta rushe da kuka sosai tace "Na shiga uku na lalace na cuci kai na, yanxu d'a na aka makala ma sauran ciwo ina ji ina gani?? Wllh sai na raba auren nan ko ta halin yaya, Mujaheed baxai taba hada jini da xuri'ar Aisha ba, da auren nan ya rayu gwara in mutu kawai, in sha Allahu sai ya saketa sai dai idan ba ni na haife sa ba, wato yana ma son auren kenan tunda har ya gudu ba labarinsa....." ta kuma fashewa da matsanancin kuka xuciyarta na mata xafi, ko mutuwar ubanta bata ji ciwonsa irin yanda take jin ciwon wannan auren ba, ji tayi dama ayi backward din komai ta bar Sadeeq ya auri Imaan, ko bakomai xata yi mingling da manyan mutane da dangin Bulasawa ayi hotuna su kai Imaan kantamemen gidanta, yanxu Imaan ta auri Sadeeq ba ma lallai taga irin rayuwar da suke da Sadeeq din ba balle ta ji haushi ko ya dameta, ita da ganin Imaan sai in ta xo gida, amma wnn wai yaron cikinta ne xai yi rayuwa da Imaan din tana ji tana ganin komai da idanuwanta, tashi tayi tana kuka sosai ta wuce apartment dinsu tana cewa "In sha Allahu sai ya saketa, sai in bani nayi nakudar sa ba, in sha Allahu bbu aure tsakaninsu,


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login