Showing 210001 words to 213000 words out of 303099 words

Chapter 71 - Imaan Book 1 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

1599

ba ta sha shayin da ta hado mata sannan mai make up tayi mata make up kamar jira, yau ma dai wani ubansun lace din ta saka da ya fi na jiya, Maryam kam cewa tayi kanta na ciwo don ma kada a tilasta ta saka kaya, da ta tuna yanda suka yi da Sadeeq jiya sai ranta yyi mugun baci, in kuma ta tuna abinda Imaan ta gaya mata wai ba ruwanta sai tayi wani murmushi tana tausayin Yar uwar tata, Maimoon da Mariya suka cakare cikin ankonsu na ranan aka dinga hotuna. Karfe sha daya Yusuf ya fito dakinsa xuwa parlon Abba ta dalilin kiransa da yyi a waya, gaisawa yyi da mutanen dake parlon nasu don tun safe yake daki da few frnds dinsa, da sallama ya shiga parlon Abbansa yana kallonsa ya xauna yace "Gani Abba...." Abba xai yi magana Daddy ya shigo parlon da sallama, Yusuf ya gaishesa, Daddy ya amsa gaisuwarsa sannan ya xauna yana kallon Abba yace "Ina hanya ka kirani Barrister..." Abba ya kalli Yusuf yace "Kaje waje ku shigo tare da Sadeeq, ya kira yana waje...." Yusuf yace "Sadeeq Bulasawa?" Abba yace "Ehh" mikewa Yusuf yyi ya fita, Daddy ya kalli agogo sannan ya kalli Abba yace "Why is he here?"



*Imaan isn't for free* it's 300 via


Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788



75.....



Tare Yusuf suka shigo parlon Abba da Sadeeq, Sadeeq yyi kasa da kai ya cire glasses din idonsa ya xauna saman rug ya gaishesu cikin sanyin murya, amsawa suka yi a tare suna kallonsa, Yusuf ya xauna shi ma yana duban Sadeeq da ya ki dago kai, calmly Abba yace "Hope all is well Abubakar?" Sadeeq bai ce komai ba kuma bai dago kansa ba, daga daddy har Abba kallonsa kawai suke, Yusuf ma haka, Can Sadeeq ya dago kansa ba tare da ya yarda sun hada ido da ko daya daga cikinsu ba a hankali yace "I am sorry I am saying this late, ina son don Allah ku min alfarma ayi hakuri da daurin auren nan yau saboda wasu dalilai...." Kallon mamaki Abba da Daddy suka shiga yi masa, Yusuf da ya xaro ido shi ma ya dinga kallonsa, Sadeeq ya shafa kansa murya can kasa yace "I think I am not ready for marriage now, I am sorry I am saying this at the die minute, but this is just d fact, ku yi hakuri...." Yusuf na masa wani kallo ya mike a mugun fusace yace "How dare you say such at this time, who do you think you can take for granted here...." Abba da gaba daya Sadeeq ya gama kulle masa kai cikin cool voice yace "What exactly are you trying to tell us here now Sadeeq.... What do you mean?" shiru Sadeeq yyi bai ce komai ba, can ya kallesu yace "I think it's good a fasa auren nan sai wani lkcn, ku min afuwa...." mikewa Daddy yyi cikin tsawa yace "You are very stupid...." Abba ya mike da sauri ya nufi d'an uwan nasa sanin xuciyarsa yana kallonsa a nutse yace "keep calm Abubakar, keep calm..." Mikewa Sadeeq yyi kansa a kasa yace "I am sorry..." Daga haka ya nufi kofa ya fita daga parlon, Yusuf ya bi sa da kallo da mugun mamaki, "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" shi ne kalmar da Abba ya dinga furtawa ya kasa tsaye waje daya, daddy ya koma ya xauna a hankali trying his best to be calm, Abba ma ya koma ya xauna har lkcn yana nanata Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, silent din kusan minti biyar ne ya biyo baya a parlon, kowa da tunanin da yake a ransa, can Abba ya daga kai ya kalli daddy, lkci daya wani tausayin d'an uwan nasa ya rufe sa, how will such thing happen to his only child, cikin sanyi Abba yace "Look Abubakar you need not to worry, haka Allah ya tsara kuma Alhmdllh, I am sending them their pride price immediately, sannan plss do not say anything to anybody about this yet...." Daddy dai bai ce komai ba ya jinginar da kansa da kujera ya lumshe idonsa, Yusuf duk jikinsa yyi sanyi ya ma kasa kallon iyayen nasa ya rike kansa kawai, Abba ya mike walking round as if looking for a solution, sosai xaka ga damuwar dake tattare a fuskarsa, Daddy ya mike daga karshe calmly yace "Bani sadakinsu in mayar masu yanxu Barrister" sanin halin daddy yasa Abba yace "Xan maida da kaina Abubakar, ba sai ka je ba" duk ynda daddy yyi Abba ya basa sadakin kin basa yyi hakan yasa ya koma ya xauna xuciyarsa na tafarfasa, he just can't believe this is happening to his daughter, can Abba xauna ya dau wayarsa ya shiga kiran layin Alhaji Ahmad Bulasawa, sai da ya kusa katsewa ya daga, bayan sun gaisa Abba ya d'an yi shiru sai kuma a nutse ya shiga tambayar Bulasawa dalilin da yasa xa su yi masu abinda suka yi, Alhaji Ahmad Bulasawa dake sauraronsa keenly yace "I really don't get you Alhaji, me ke faruwa, anyi wani abu ne??" Mamaki ne ya cika Abba jin abinda Bulasawa ke cewa, bbu bata lkci ya shiga yi masa bayanin ynda suka yi da Sadeeq yanxun nan, cikin daga murya Bulasawa yace "He is seriously stupid, wato abinda ya xo yace maku kenan, to wllh ko ya ki ko ya so aure ba fashi, my reputation is above everything, ana saukowa masallaci dama daurin aure na nan bbu fashi in sha Allah, till we meet there...." Bai jira cewar Abba ba ya katse wayar, Abba ya kalli Daddy don wayar a hands free ya sa, Daddy ya girgixa kai yana murmushin karfin hali yace "I will never give out my daughters hand in marriage to that son of him, tunda har da kansa ya nuna baya auren that's the end, ba neman kai nake da Imaan ba, don't forget she is all I have got, da a cutar min ita gwara an cuceni ko wani irin cuta ne kuwa, we are returning their pride price and everything immediately, Allah ya hada kowa da rabonsa na alkhairi, Allah yayi mata xabi na gari, bak'i da suka xo from far don taya ni farin ciki xan sallamesu ana saukowa masallaci in sanar masu bbu auren kuma, and I will forever be grateful coz they are all here bcos of my only child, in sha Allah xa mu je a daura auren Yusuf nata kuma Allah ya musanya mata da mafi alkhairi" daga haka daddy ya mike ya nufi kofa, Abba da duk jikinsa yyi sanyi sosai yace "Sadeeq" tsayawa daddy yyi amma bai juyo ba, Abba yace "Don't say anything about this to anybody, not even ur frnds, ka ji abinda nace" Daddy dai bai ce komai ba ya fita parlon kawai, Abba ya jinginar da kai so sad, Yusuf dai ya rasa abun cewa gaba daya he is just shocked, can Abba ya kallesa yace "Go nd get set Yusuf, it's almost time, and don't say anything to anybody yet" mikewa Yusuf yyi jiki ba kwari ya fita parlon Abba ya bi sa da kallo. Gida ana ta shagalullukan biki bbu abinda yasan me ke faruwa, Imaan dai tana bedroom dinta baccin da bata yi jiya ba duk ya dameta, daga karshe ta kwanta ta dinga bacci, bbu wanda ya tasheta cikin mutanen dake dakin don da ganin yanda take baccin ma kasan gaba daya she is restless sai juye juye take. Abba ya dau sadakin da su Bulasawa suka kawo ya tafi gidan da kansa don mayar masu don sosai ya gamsu da abinda d'an uwansa yace na cewar bbu xancen aure kuma tunda Sadeeq din ya fito da kansa ya nuna ya hakura to gwara kowa ma ya hakura ko don gudun kada ya jefa Imaan cikin wani hali, kuma hakan shine abu na karshe da xai so ma only child din d'an uwansa, ko kadan Bulasawa bai ji dadin kudin da Abba ya maido ba don kin karba yyi, Abba yayi masa bayani a nutse yanda xai fahimce me yasa suka yi haka ya kuma nuna masa dole su yi hakan don ceto imaan, ba irin kiran da Bulasawa bai ma Sadeeq a waya ba amma ya ki dagawa, Abba na murmushi yace "Toh kaga Alhaji, kawai Allah yyi masu xabi na gari, tunda kaga haka auren ba alkhairi bane garesu" Bulasawa dai ya kasa cewa komai amma gaba daya shi ma ransa ya sosu, Abba yyi masa sallama daga karshe ya bar parlon nasa bayan ya sanar masa xuwa gobe ko jibi xa a maido masu lefe, shi dai Bulasawa har Abba ya fita bai iya yace komai ba, can ya dau wayarsa ya shiga Kiran mahaifiyar Sadeeq, tana dagawa strictly yace "ki sameni parlona ynxu, kuma duk inda Abba yake I want him immediately, in sha Allahu kuma baxai kwanan min a gida ba yau, and he is returning all my asset that is with him today, I have nothing to do with him any longer" Bai jira cewarta ba ya katse wayarsa. Karfe daya saura Abba suka wuce masallaci tare da frnds dinsa da kawu Bala, sae kawu Audu, bayan ya samu waje yyi parking ya kira Daddy don ya ji yana iya, daddy ya sanar masa yana hanyar xuwa mosque..... Ana sakkowa masallaci aka daura auren Yusuf da Hafsat a kan sadaki dubu dari biyu, auren da jama'ah da dama suka shaida, sae kuma daurin aure na biyu da ake jiran waliyyan ango amma shiruu, wanda hakan yasa aka fara dago kila babu auren ne tun kafin su Abba su sanar da hakan, Abba na kallon daddy dake kusa da shi murya can kasa yace "Abubakar xan daura ma 'ya ta aure yanxu, auren da ina da tabbacin kowa xai yi alfahari da shi in sha Allah, ko ba ynxu ba kuwa, da raina baxan ta6a yarda ka ji kunya a idon duniya ba, kuma ikon da nake da shi a kan Imaan yasa xan daura mata auren huce takaici duk da banda ni da kai da Yusuf sai Bala bbu wanda yasan abinda ake ciki" Daddy dai sai kallonsa yake don tun idar da sllh ya ki cewa komai, Abba yace "Ka je a kai ne waliyyin ango, Bala kuma dama shine waliyyin amarya..." Yana fadin haka ya fiddo kudi a aljihunsa ya mika ma Daddy yace "This is 200k, sadakin da xaka bada...." Abba na fadin haka ya koma gun su kawu Bala da abokansa, ko kadan daddy bai yi welcoming idea din Abba ba, kwata kwata bai son ma imaan dole, bai son tashin hankalinta ya xama biyu, na rashin masoyi ga kuma aure without her consent, gashi bai san da wa Abba xai hadata ba idan kuma yace xai yi magana Abba sai yaga kamar ya nuna masa bashi da iko da imaan, gaba daya he was just confuse haka ya tafi dai don yin ynda Abba yace, Daddy bai taba xaton sunan da yaji an kira na angon ana daura auren, haka ya dinga kallon Abba ko kiftawa bbu, Yusuf kansa was more than shock ya kasa daina kallon iyayen nasa, can ya lumshe ido ya bude xuciyarsa na bugawa.... Abba ya sakar ma Daddy cool smile ganin kallon da yake masa, maimakon Daddy ya mayar masa sai ya dauke kai kawai. daga karshe dai Yusuf fita yyi to avoid gaisawa da frnds don gaba daya shock ya xame masa biyu..... Tun bayan call da Mariya tayi answering a dakin Imaan yanayinta ya sauya gaba daya, tafi minti biyu tsaye har sannan wayar na hannunta, Maimoon dake diban ma Imaan dake xaune saman darduma ta idar da sllh abinci a plate ta kalleta ganin ko motsin kirki bata yi tace "Lafiya Mariya" Mariya bata yarda ta kalli Maimoon ba sbda hawayen da ya kawo idonta, Maryam ta ajiye dankunnen da take kokarin sakawa ita ma tana kallon Mariya tace "Hope all is well dear?" Fita Mariya tayi daga dakin da sauri sai a sannan ta fashe da wani kuka, gaba daya suka bi ta da kallon mamaki, Imaan ta ji gabanta yyi mugun faduwa ta mike daga saman darduman, Maimoon ta mike ta bi bayan Mariya hankali tashe, Maryam ma ta bi bayansu, Imaan ta kalli agogo dake nuna biyu da 'yan mintuna sannan ta sauke idonta a hankali tana karanto addu'a a ranta ko xata samu natsuwa daga bugawan da xuciyarta ke yi, wayarta ta dauko tana dubawa ko xata ga even if it's text from Sadeeq na sanar mata cewar an daura masu aure amma bata go komai ba, ta xauna gefen gado tana goge hawayen dake xubo mata. A hanya Daddy na kallon Abba dake driving xa su koma gida yace "Barrister I don't think what u did was a way a out, ya kake son yyi da mata biyu? A lkci daya kawai" Abba dai bai ce komai ba sai driving yake a nutse, kawu Bala dake cikin motar yace "Gaskiya ne, kada a 6ata daya goma bata gyaru ba, sannan kai baka yi shawara da kowa ba Ahmad" Abba yace "I did what I think is best brothers, da d'an uwana ya ji kunya gwara nayi koma mene, we will sort everything out right daga baya in sha Allah," A haka har suka iso gida babu wanda ya sake cewa komai. Rabon abinci Umma suke yi amma gaba daya ta kasa kunnuwa ta xuba idanu tana jiran dawowarsu Abba da xancen bbu daurin auren Imaan, Safeenah dake hada uban salad sai taunar cingam take ita ma dai tana jiran news, irin cakarewar da tayi kai kace ita ce amaryar, tun sassafe dama ta iso gidan ana ta aiki da ita duk da ta bar Mujaheed yana headache tun cikin dare bata ma san ko xai je daurin auren ba, Umma na ganin shigowarsu Abba duk da ba ita ce mai girki ranan ba haka ta bi bayansa tana masa sannu da xuwa da fara'a tana cewa Allah yasa an daura a sa'a Allah kuma ya bada xaman lafiya, a takaice ya amsa da Ameen, tace "bari in kai maku abinci parlor" ganin mood dinsu gaba daya daga shi har Daddy har ma da kawu Bala taji kamar tayi tsalle don murna, da dukkan alamu dae tayi nasara, Abba na kallon Daddy da ya nufi part dinsa walking like the gentleman he is yace "Sadeeq" juyowa Daddy yyi, Abba yace "Mu tafi can parlona for lunch..." Daddy bai masa musu ba ya dawo suka wuce parlon Abba, Ammi na compound ita ma amma tun shigowarsu ta sha jinin jikinta ganin yanayin Abban Imaan da kawu Bala kai kana ganinsu kasan da matsala don haka bai boyu a fuskarsu ba, Abba ma ne kadai ke d'an yake, abinci iri iri da aka yi Umma ta dinga dire masu a parlor tana cewa "Allah ubangiji ya nuna mana na yan baya, Allah ya basu xaman lafiya gaba daya yasa anyi a sa'a" Babu wanda ya tanka ta a parlon har ta fita tana murmushi sai dai bata ji dadin kin cewa komai da suka yi ba, gashi gaba daya ta hana yan uwanta maxa xuwa daurin aure balle ta kirasu taji yanda aka yi gun daurin auren, fitowa tsakar gida tayi tana hangen inda xata ga Yusuf ko xata d'an samu labari ganin frnds dinsa na ta shigowa compound din... Abba yayi breaking din silence din parlonsa yana kallon daddy da ya jinginar da kansa da kujera yyi nisa tunanin da yake, yace "Naga kamar hankalin ka bai kwanta gaba daya da auren nan da aka daura ba ko Sadeeq?" Kallonsa daddy yyi yace "Not at all, ina dai mamakin al'amarin ne, sannan am hoping this shouldn't be a big blow to my daughter, you know her condition.... Bana son wani abu ya sameta coz baxan iya dauka ba" Abba ya dafe kansa shi ma yana tunanin ta inda xa su fara fasa news din nan wa mutanen gida.... Mama Hadiza ce xaune parlon Abba tare da yayyinta bayan kiran da kawu Bala yyi mata a waya, kai kana ganinta xaka hango tashin hankalin da ke fuskarta karara, lkci daya ta shiga furta Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Daddy dai kansa na jingine da kujera, Abba ya girgixa kai yace "Abinda ya faru kenan Hadiza, mu ma haka lamarin ya xo mana" Hawaye ya kawo idon Mama Hadiza tausayin Daddy ya cikata, hakan bai kamaci only child dinsa ba, to ko ya ita kuma Ammi xata dau xancen balle ita Imaan din gaba daya, Hawaye ta dinga yi sosai tace "Allah ya isa tsakaninmu da shi, ya cuce kansa ba mu, Allah ya saka ma Imaan..." Abba ya d'an yi murmushi ya ciro wayarsa a aljihu yyi dialing number Mujaheed don sure bai gansa gun daurin aure ba, sai da ya kirasa sau biyu sannan ya daga, Abba ya amsa sallaman da yyi yace "Ban gan ka gun daurin aure ba why?" Mujaheed dake kwance ya mike xaune da sauri yana kallon agogo ganin time cikin sanyin murya yace "I slept off Abba, kiranka ne ya tashe ni ban san lkci ya wuce haka ba, har an daura kenan?" A takaice Abba yace "A'a ana jiran ka, I want to see you home now my frnd..." Mujaheed ya gyada masa kai ya kasa cewa komai har Abba ya katse wayar, hade kai yyi da gado trying hard to control himself... Aunty ce ta fara shigowa parlon Abba sannan Ammi ta dalilin kiran da Abba yyi mata ta wayarta wai su taho tare da Ammi, Kallonsu ta dinga yi bayan ta shigo parlon, Mama Hadiza dai kanta na kasa ta ci kuka har ta gode Allah, Ammi ma ta dinga kallonsu lkci daya taji gabanta ya fadi ta xauna kasa a hankali jin kafafuwanta sun kasa daukarta, Aunty ta xauna ita ma cike da karfin hali tace "In ji dai lafiya Abba?" A takaice Abba yace "Lafiya lau" Kawu Bala yace "Lafiyar kenan Amina..."


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login