Showing 270001 words to 273000 words out of 303099 words
lefe sbda ance maku gantalalla ce? Mutane dai bbu tsoron Allah ko digo a xuciyarsu, tirr wlh" Murmushi Abba yyi yace "Inna ai ba yace baxai yi bane, xai mata in sha Allah, wannan ai dole ne" inna tace "Toh yayi mu gani tukun, gwalagwalai hudu na kirga a lefen da Bulasawa yyi mata wllh tllh, duk atamfofin kuma babu na kasa da dubu hamsin, ga leshi duk 'yan dubu dari dari, to me yafi haka ma'ana?? kaiiii Ahmadu ku ji tsoron Allah, wllh Imaan ba banxa take ba, a kan lefen nan ma ni sai in soke auren nan gaba daya in ga ta tsiya don uwa ta bata ce min je ki kya gani ba, haka kawai ya cutar min jika ya kai ta ya barota bbu kayan aure jikata ta walakanta, to Allah ya tsine ma wanda yace auren xumunci ne ko ba ayi lefe ba bbu komai, don da alama an rada maku hakan ne shi yasa ku ke shashantarwa, to wllh bari ku ji, sai na ga akwati guda dai dai har sha biyu sannan Imaan xata bar gidan nan, idan ba haka ba gwara inyi ta kallon abata, ba ruwana ni yar gaskiya ce..." daga haka ta mike ta fita daga parlon tana cewa "A dai dinga tsoron Allah komin rintsi, ance maka don kai ka haifi Mujaheed sai in ki gaya maka gaskiya, haka kawai mutumi ka lallabo ka xo min nan don ka min dadin baki a cuci Jikata, Albarka uwata ta dinga sa min kafin ta rasu wllh..." Murmushi kawai Abba yake, can ya mike yana girgixa kai ya fita parlon. Karfe tara na dare Mujaheed ya shigo parlon Inna da sallama ya ganta xaune saman darduma tana xuba gyangyadi ga carbi a hannunta, tsayawa yyi yana kallonta, can yyi murmushi ya nufi kofar dakin walking without making any sound, yana bude kofar dakin Inna ta bude ido daya a hankali tana kallonsa har ya shiga dakin, yana shiga Imaan na fitowa daga bathroom daure da towel, xaro ido tayi ganinsa, lkci daya ta nufi gefen gado da sauri ta xauna tana kallonsa kamar xata yi kuka tace "Yaya shine xaka shigo bbu sallama, gashi ban sa kaya ba, kuma idan inna ta gan ka fa? Don Allah ka fita plsss" Juyawa yayi xai rufe kofar dakin ya ga Inna tsaye kyam bakin kofar tana kallonsa, duk da yanda ya so dakewa kada yyi dariya sai da yayi dariyan yana sunkuyar da kai, ta cakumosa fuska a murtuke tace "Dakina yyi maka kama da otal Mujaheed? Yaushe ka lalace haka bani da labari, bbu kunya balle tsoron Allah ka afka ma yar yarinya daki daga ita sai tawul ta fito wanka? Me hakan ke nufi fisabilillahi? Meye manufar shigo mata tana tsirara?" Ya wara ido yace "Toh xa ki hanani shigowa gun matata ne Inna?" Inna tace "Toh wllh ka gaggauta neman tubar ubangiji, ta ina ta xama matar ka baka fita hakkinta na aure ba Mujaheed? ga sadakin ka can a cikin dirowa sai in dauko maka in baka tsiyar ka yanxun nan kar ka kawo min nansans, Ina ce da shi kake takama?" Ya shafa kansa yana murmushi yace "Toh ai Aunty ta fara hada mata lefen sai ki bani matata mu tafi koh?" Inna tace "Wacece kuma Aunty? To wllh ka rufa ma kanka asiri ka amso kudadden ka ka samu yar gayu ka bata ta hada ma jikata lefe, kwata kwata ban yarda da siyayyan Aisha da Amina ba, duk yaushe suka waye? sai kaga kayan da suka hada ma Yusuf duk rubabbu ba kyau, Kamar daga kauye" dariya kawai Mujaheed ke yi yana kallonta tace "Atoh ni ba ruwana" tana rike da shi ta juya xata fita dakin yace "Toh sakeni mana Inna" Bata sauraresa ba har suka fita dakin ya juya yana kallon Imaan da tayi masa gwalo, wani murmushi yyi yana gyada kai Inna ta kulle kofarta sannan ta sakesa, ta xauna tace "Kudin akwatuna nawa ka bata?" Yace "Idan ta gama hadawa xa ki gani ai" tace "Ni da xa a ji ta nawa ma a siya mata sakk irin na Bulasawa har kayan ciki" Mujaheed bai tanka ta ba, bayan kusan minti goma Imaan ta fito sanye da hijab har kasa sai xuba kamshi take, kallonta kawai Mujaheed yake har ta xauna, Inna tace "In xuba maki abincin ne ko ko?" Gyada mata kai Imaan tayi, Inna ta mike tace "Ina xan bari ki lalace a shiyana Bukar yyi tunanin bana baki abinci ne ya kullace ni" daga haka ta shiga kitchen, Mujaheed ya bi ta da ido sannan ya mike, imaan na ganin haka xata tashi yyi saurin rikota, kamar xata yi kuka murya can kasa tace "Yaya ka bari kaga Inna xata fito ynxu fa.. " xaunar da ita yyi kusa da shi ya jawota jikinsa ya daura forehead dinsa kan nata yana kallon lips dinta murya can kasa yace "Ke kika ce mata sai na maki lefe koh??" Xaro ido tayi tana son komawa baya yaki saketa, rufe fuskarta tayi jikinsa hankali tace "A'a wllh, ita ce dai ta fadi haka...." Rungumeta Mujaheed yyi yana son dago kanta taki yarda, Inna na fitowa kitchen rike da plate din abinci tayi kasake baki bude tana kallonsu, sai kuma ta saki salati, da sauri Imaan ta fara turasa tanq xaro ido amma ya ki saketa, Inna ta ajiye abincin hannunta a kasa tace "Mujaheed iskancin naka a parlor na xae kare yau kuma? Haka kawai mutumi ka shiga ka matse min yarinya ba tsoron Allah??" Bata jira cewarsa ba ta tafi da sauri ta bude kofar parlon tace "Taho ka fita kada Ahmadu ya fitar min da kai yanxun nan, wannan wani irin iskanci ne da lalata, mutumi ka shigo xaka lalata yar mutane a parlona, meye ma'anar hakan ma dai tukun?" Imaan dai tuni ta janye daga jikinsa kamar xata yi kuka, a fusace inna tace "Ke kuma jarababbiyar yarinya kin wani sakar masa jiki kin makalkalesa shashasha kawai jarababbiya, to wllh kai ki xai yi ya baro ki don ma kiji in gaya maki, waye kuma bai san iskancin namiji, ohhh ni patuu yau naga iskanci gun yara, a parlon nawa kuma babu tsoron Allah xaka makalkaleta Mujaheed, Toh wllh bari Ahmadu ya shigo ba dani xa ayi wnn iskancin ba dama kada Mujaheed ya sake xuwa min nan wllh ni ba gantalalliya bace kuma ni ba yar iska bace" Imaan ta mike tana turo baki ta wuce daki, Inna na kallon mujaheed a fusace tace "Baxa ka xo ka fita ba ko sai na tafi na kira ubanka, banda baka da tsoron Allah imaan din ma nawa take gaba daya fisabilillahi da xaka matse ta haka kan kujera Mujaheed? Ni wllh ban taba ganin haka ba tunda uwata ta haifeni, to me xaka mata?" Mujaheed ya mike yace "Da kin yi ki shiru kiga abinda xan mata ai" daga haka ya bi ta gefenta xai fita dakin ta kai masa dundu a baya tace "Toh Allah ya isa wllh, ka je kai da Allah, wanda bai yi iskanci ba ma a rayuwar ya ya kare balle yyi iskanci" murmushi yyi bai kuma tsayawa sauraranta ba yyi wucewarsa. Washegari da safe Imaan ta tafi gaida Amminta daga part din Inna bayan inna ta jaddada mata ko minti biyar kada tayi a can don ita tsoron kowa take a gidan bata yadda da kowa ba, A bedroom Imaan ta samu Ammi xaune, ta duka kasa jikin gado tana kallonta a hankali tace "Ammi Ina kwana" Ammi tace "Lafiya lau, kin tashi lafiya?" Imaan tace "Alhmdllh, daxu da kika xo ina wanka" Ammi tace "Ohk, kinyi breakfast?" Kai Imaan ta gyada mata, Ammi ta yi shiru sannan tace "Me Mujaheed din yace maki kan komawar ku?" Imaan ta sunkuyar da kanta tace "Inna ce tace A'a" Ammi tace "Ba Aunty ta fara hada maku kayan ba" Imaan dai bata ce komai ba, Ammi tace "Idan ma xa ki daina biye ma Inna ke daina biye mata ki bi mijinki ku tafi, Daddy ma yayi magana jiya" Kai kawai Imaan ta gyada mata, Ammi tace "Ki tafi kitchen ki debi abinci, idan kuma shayi xa ki hada sai ki hada, ko in soya maki kwai?" Imaan tace "Ammi nayi breakfast fa" Ammi tace "Toh shikenan" Shiru ne ya biyo baya, Ammi tace "Kina ji na?" Daga kai Imaan tayi ta kalleta tace "Ina ji Ammi" Ammi tace "Bana son ki saka duk abubuwan da suka faru a ranki, no matter what you've got to respect ur mother in law, in ma tana son ki in ma bata son ki, duk wani abu na kyautata da kika san ya kamata ki dinga mata albarkacin d'an ta da kike aure yanxu, kaninnsa ma gaba daya ko suna sonki, ko basa son ki kiyi masu abinda ya kamata, babu ruwan ki da abinda suka maki a baya duk wannan ya wuce, kuma nasan baki riko, lkci lkci sai ki ce ma Mujaheed din ya kai ki ki gaisheta a can Zaria, just that you have to be very prayerful, never get tired of praying domin addu'a shine makamin mumini, mijin ki kuma kiyi masa biyayya yanda ya kamata, nasan ba sai na tsaya maki wani bayani a kan aure ba you are educated Imaan, kin san komai, sai dai kawai kamar yanda kike yi a nan gida haka nake son ki ci gaba da kasancewa cikin kamshi da tsafta, sannan ki dinga kama jiki don wani lkcn na sanki da shegen son jiki, ko yaya ne ki dinga aikin da baxai takura ki ba, kin dai ga yanda nake barin gida na a ko da yaushe very neat, try to keep ur home clean kuma ya kasance cikin kamshi ko da yaushe, duk da nasan ki da kokarin gyaran daki da wankin bandaki, but put in more effort daughter, Allah ubangiji ya albarkaci auren ki, ya baku xaman lafiya me dorewa, da hakurin xama da juna.... Kasa cewa komai Imaan tayi kanta a kasa hawaye na sauka idonta, Bude kofar dakin aka yi Ammi ta kalli direction din ta ga Inna tsaye bakin kofar, Ammi ta sauka saman gadon tace "Sannu Inna" Inna tace "Sannu, me kike kitsa mata tun daxu bata dawo ba Aisha??" Murmushi Ammi tayi tace "Kawai nasiha nake mata Inna" inna tace "Ai kullum cikin yi mata nake" tana fadin haka ta kalli Imaan tace "Tashi mu tafi, nasiha kuma wanne ne ban maki ba tun da kika dawo wajena idan ba gulmar uwarki bane ya tashi" Imaan ta kalli Ammi a sanyaye, da fillanci Ammi tace mata ta tashi ta tafi, inna ta saki baki tana kallonta, mikewa Imaan tayi ta nufi kofa, Inna tace "Ba ruwana da munafurci wllh" daga haka ta bi bayan Imaan suka fita, bayan sun fita apartment din Inna na kallon Imaan tace "Me ta ce maki wai?" Imaan ta turo baki tace "Toh Ina ruwanki?" Da yamma Inna ta dinga bin Imaan da kallo ganin yanda ta shirya cikin riga da skirt har da shafa powder, Jin shiru bata fito ba bayan ta shiga daki Inna ta mike ta bi bayanta a hankali ta leka cikin dakin, a duke ta sameta jikin gado waya kare kunnenta, Inna ta buda baki a sanyaye tana kallonta, Da sauri Imaan ta katse wayar hannunta ta ajiye tace "Daddy ne fa nake kira" Inna ta karasa ta dau wayarta tana kallo kamar xata yi kuka tace "In dai Mujaheed kika kira da wayata ke da Allah, ba ruwana" Imaan ta mike ta fice daga dakin tace "Ai dai ba ke kika saka katin ba Daddy ne ya saka maki naga" Maimoon ce ta shigo parlon tana kallon Imaan tace "Abba na kiran ki Imaan" Inna tace "Ya dawo ne?" Maimoon tace "Ehh ya dawo yanxu" Inna tace "Toh su kuma gantalallun nan da suka tafi raka katuwa Rukayya basu dawo bane?" Maimoon tace "Ehh kila xa su yi sati daya a can" Inna na tafe hannu tace "Toh maza maza su dawo don rukayya Bata da tarbiyar da xata yi ma yaran nan kada ta kai min jikoki ta barosu in shiga uku...." Imaan ta dau Hijab dinta ta saka ta bi bayan Maimoon suka fita parlon, Abba na xaune parlor hannunsa rike da remote Imaan ta shiga parlon ta xauna kasa ta sunkuyar da kanta tace "Ina yini Abba?" Abba yace "Lafiya lau Mamana" Imaan tace "Ya aiki?" Yace "Alhmdllh" Bude kofar aka yi Mujaheed ya shigo da sallama, suna hada ido Imaan ta sunkuyar da kanta tana wasa da fingers dinta, Mujaheed ya xauna kasa a hankali yace "Barka da dawowa Abba" Abba yace "Yauwa, ya aiki?" Yace "Alhmdllh" Abba yace "Maa sha Allah, kana ji na Muhd?" Mujaheed ya kallesa yace "Ina ji Abba" Abba yace "Ka dau matar ka ku wuce gida yanxu, Allah ya ba ku xaman lafiya... na yarda xaka rike Imaan yanda ya kamata don nasan tarbiyar da nayi maka, so I need not to say much, Kai dai kayi kokari ka rike min ita da amana, sai kuma ayi ta hakuri, daga nan yanxu ku tafi ku yi ma Hajiya Aisha sallama da Amina sai ku wuce ba sai kun je gun inna ba" Mujaheed ya kalli Imaan da ta rufe fuskarta ta fara hawaye, ya d'an yi murmushi cikin sanyin murya yace "Toh nagode Abba, Allah ya kara girma" Abba yace "Ameen, Allah maku albarka, ya baku xaman lafiya" Mujaheed ya amsa da Ameen ya mike a sanyaye yana kallon Imaan da ta ki motsi, Murmushi Abba yyi yace "To tashi ku je Mamana" imaan ta mike da kyar tana share hawayen dake sakko mata da hijab ta bi bayan Mujaheed da ya nufi kofa suka fita parlon.
*Imaan isn't for free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
97.....
Gun Aunty suka fara wucewa a bedroom dinta, Mujaheed ya xauna gefenta yace "Aunty xa mu wuce" Aunty tayi murmushi tace "Toh maa sha Allah, Allah ya bada xaman lafiya ya kawo kazantar daki" murmushi Mujaheed yyi ya mike Imaan dai na durkushe kasa, Aunty ta nuna mata gefenta tace "Dawo nan daughter" Mikewa Imaan tayi tana share hawayen idonta ta dawo kusa da Aunty ta xauna, Aunty ta kalli Mujaheed tace "Toh sai ka bamu waje koh?" Juyawa yayi ya fita dakin yana murmushi. Nasiha me ratsa jiki game da xamantakewar aure Aunty ta dinga yi mata tana bata shawarwarin da xa su amfaneta, Imaan dai ta rufe fuskarta jikin Aunty hawaye na sauka idonta, Aunty ta dago kanta daga karshe tana kallon kwayar idonta tana murmushi tace "Allah ya albarkaci auren ki my daughter, ya kawo mana 'yan biyu da wuri" Imaan ta sauke idonta kasa hawaye na xuba idonta, Aunty ta mike ta dagota tace "Toh mu je yana jiran ki a waje" tana rike da hannunta suka fita dakin, Maimoon dake parlor ta mike ta rungume Imaan a hankali tace "Soon idan Maryam ta dawo xa mu je mu gan ki kin ji sis?" Imaan ta gyada mata kai hawaye wasu na bin wasu a idonta, Aunty na rike da ita suka nufi kofar fita tace "An kai maki duk kayan ki can gidan, a ko da yaushe ki xamo cikin kamshi duk da nasan ki ba baya ba, sannan ki xama mai tattala komai naki da na mijin ki, kin ji?" Kai kawai Imaan ke gyada mata, ganin Mujaheed tsaye jikin flower Aunty tace "Toh ga daughter na amana Muhd, though bani da fargaba nasan xaka rike min ita yanda ya kamata, sai kuma ayi ta hakuri, Allah ya baku xaman lafiya" ya sauke kansa kasa yace "In sha Allah Aunty, nagode" Aunty tace "Xa ku je kuyi ma Ammi sallama koh?" Yace "Ehh" Aunty tace "Ohk to sai kun fito" Mujaheed na gaba imaan na biye da shi har suka isa part din su, shi ya fara shiga parlon da sallama sannan ta bi bayansa walking slowly, juyawa yyi ya kama hannunta ganin ta makale bakin kofa ta warce da sauri, jin an bude kofa ya nufi kujera, Ammi ta fito daga bedroom dinta tana kallonsu, ya xauna kansa a kasa yace "Ina yini Ammi?" Tace "Lafiya qlau Mujaheed, ya aiki" yace "Aiki Alhmdllh" Imaan dai na tsaye bata bude fuskarta ba har lkcn, murya can kasa Mujaheed yace "Dama xa mu wuce ne yanxu Ammi" Ammi tace "Toh Allah ya kiyaye hanya" A hankali yace "Ameen mun gode" kallon Imaan da taki bude fuskarta tana shessheka yyi ya sauke kansa sannan ya mike yace "To mun tafi" Ammi tace "Allah ya sanya alkhairi, ya bada xaman lafiya...." Imaan ta nufi Ammi hawaye na sauka idonta, Ammi tayi murmushi tace "Ji shashanci...." Rungumeta Imaan tayi ta fashe da kuka, Ammi bata iya ta ce komai ba, Mujaheed ya juya a hankali ya fita daga parlon, Ammi ta dago kanta tana kallonta, lkci daya jikinta yyi sanyi tace "Ki xama me biyayya ga mijinki kinji Imaan, Allah ya albarkaci auren ku, ya baku xuri'a dayyaba, nasan baxa ki bani kunya ba" Kuka kawai Imaan take bata iya ta amsa mata ba, Ammi tayi karfin halin kin barin tayi hawayen ita ma ta kama hannun Imaan har bakin kofa tace "Allah ya tsare" daga haka ta sake ta Imaan ta fita daga parlon still crying, Parking space ta tadda Mujaheed tsaye ya rungume hannayensa ya kafeta da ido, kin karasawa gun sa tayi ta tsaya, ya bude mota sannan ya nufeta ya kamo hannunta ya bude front seat ta shiga ya rufe motar, ya xaga ya shiga maxaunin driver yyi horn mai gadi ya bude masa gate ya fita gidan da motar, yana hawa saman titi ya kamo hannunta a hankali cikin sanyin murya yace "Ki daina kukan nan haka plss, tare da yayan ki fa kike" Kamar ya kara tunxurata yin kukan hakan yasa yayi shiru, har ya tsaya gun masu siyar da fruits ya siya ya dawo motar Imaan bata bude fuskarta ba,